Sarkakiya Complete Novel Document
Sarkakiya Complete Novel Document By Mommyn Fareesa
Description/Story:
Sarkakiya Complete Novel Document
Written By Mommyn Fareesa
Description
Kano state
misalin k’arfe 4:48 na yammacin yau Alhamis”babban masallacin juma’a dake Anguwar hotoro cike yake mak’il da jama’a sbd wa’azin da wani babban limamin masallacin ke gabatarwa. duk mazan dake ciki kusan ko wane hankalinsa na’a kan malamin illah dai tsirakun wasu daga cikin mazan dake wajen hankalinsu ke baya A kansa…..Adaidai lokacin kuma wani yalwatacen sanyayyan k’amshi me tarin yawa ya fara kaiwa wad’anda ke zaune daga bakin k’ofar shigowa cikin masallacin ziyara”hakan yasa duk mutane suka maida hankalinsu Akan k’ofar suka zuba ido sbd son ganin waye keda wannan k’amshi?…..wasu maza ne biyu ke daga gaba kafin uban gidan nasu dake A tsakkiya yafara sako kansa cikin masallacin”sai wasu maza guda ukku dake take masa baya”sanye yake da fara k’ar d’in shadda giznah y’ar ciki da malun malun”wacce ta jik’u da zazzafan Aikin hannu, na golden d’in zare daya k’awatata matuk’a,”wacce maik’on shaddar kawai ya Isa me kallo hasashen kud’inta”ga hulla k’ube daya Aza saman lallausan gashin kansa bak’i me sulb’i da taushi irin na buzaye”hakan ya bama yalwatacciyar fuskarsa me cike da Kamala da kwarjini had’e da dattako fitowa”saidai dayake ba gwanin fara’a bane sai fuskar tasa ta kasance Ad’aure”dukda wajen tarin mazaje ne babu mata Amma hakan be hana mazan gurin binsa da kallo tamkar TV ba”wasu najin tsananin farin cikin ganinsa ya ziyarci wajen wa’azin badan komai ba sai dan sbd idan zai fita su biyosa su nemi taimako!tunda sunsan shid’in me bayarwa ne dan ALLAH…..*Mahmood ji k’amshi* kenan! matashin saurayi da Ake damawa dashi ta fannoni da dama Acikin garuruwan dake Nigeria musammun ma Acikin birnin Kano, kasancewar shid’in young bolonia ne!….. kyakykyawan mutum fari dogo me jini Ajika ,jinin buzaye da kuma rumawa”shekarunsa na haihuwa 35yrs ne kacal”saidai yanada Abubuwan ban mamakin da suka wuce shekarunsa “cikakken sunansa shine *Mahmood Bashir Idris ji k’amshi !* Idan Ana lissafin masu dukiyar dake zaune Acikin birnin kano tofa dole Asako family d’in Mahmood ji k’amshi”idan basuzo sahu na biyu ba Tofa dole zasuzo sahu na ukku! Mahmood kyakykyawa ne Ajin farko”irinsu Ake kira one in million”farar fatar jikinsa data jik’u da hutu dajin dad’in rayuwa,idan harshe zai canza kai tsaye zakace shid’in ba d’an Nigeria bane” yanada murd’ad’dan jiki daya horu da exercise”yayinda doguwar fuskarsa ke d’auke da zaga yayyen saje bak’i daya had’u da gashin baki ya k’ara k’awata kyawun fuskar tasa matuk’a”lips nasa pink ne masu shek’i,basuda girma sosai sai fad’i”duk idan yatsuke su to Akwai muguntar dayake shirin yi…..kallo d’aya zaka masa ka fahimci besan hayaniya ,sannan be d’aukar wargi”da yawa Acikin magauta na masa kallon d’an bariki sbd beyi Aure ba har iya yanzun”bayan yanada tarin dukiya ,nassaba,iko da kuma power Amma be tab’a Aure ba”hakan yasa wasu ke masa sharrin yana neman mata”sarai duk Abinda mutane ke fad’a Akansa yana dawo masa Akunne”sau tari ma wasu kanyi zancen ta inda basu zaton zai gane”saidai baya nuna ya gane d’in “sbd shi mutum ne me tsananin iya taku”dukda yana me dukiya mahaifinsa ma me dukiya Amma bayada tsarin yawo da body guard nasa”Aganinsa yawo dasu kamar yana jin tsoron wani Abokin halittane, ko kuma bazai iya kare kan saba kenan?”duk idan ya tashi fita shi kad’ansa da driver yake fitarsa”idan kuma yaso masu rakkiya yaransa biyu *muftahu da lawan* yakan fita dasu”sai kuma Abokansa guda ukku”*Dr Amoh ,Kamal Abbah, sai kuma SP Abdul*! ko Ayanzun ma tare dasu ya shigo Acikin masallacin! Mahmood be cika son surutu ba Ammah yana firansa da wanda yaso yakuma gadama”ga wanda beson yayi mgn dashi tofa zaya iyasa masa kallon mutum me wuyar sha’ani kuma miskili”saidai yafi miskili ban haushi”baya disgi ko yarfi babu wani dalili”hasalima disginsa Akan mata yake”idan yana gaban mata ko Agidan sune bayada walwala…..tun kafin su zauna wasu daga cikin mutane ke matsawa Ana basu waje”Dr Amoh nata wani ciccin magani da hura hanci shiga Aminin young bolonia!……yakai d’an uwa me Albarka yi k’ok’arin nemawa kanka *mace ta gari* da kuma *Aboki na gari* ! sai daga k’arshe kuma *y’an uwa na gari*! Acikin wannan duniyar wa’annan Abubuwan ukku nada matuk’ar wahalar samu “idan mutum be dace dasu ba tofa gaskiya ya shiga cikin *SARK’AKK’IYAR* rayuwa! saidai fa mafi wahalar samu Aciki mace ta gari”Ammah kar muyi kwance mu bamu zama na gari ba muce mace ta gari mukeso”idan kadace da macen k’warai in sha Allah zaka gane waye Aboki na gari da kuma y’an uwa na gari Agareka……iya nan Mahmood ya saurara zuciyarsa na Lulawa dashi wani dogon tunani me nisan zango”be gama dawowa nutsuwarsa ba saida yaji mlm liman na Addu’a Alamar ya gama wa’azin za’a yi zikiri kafin gabatowar sallar magrib “Ana shafa Addu’ar Mahmood ya mik’e tsaye yanufi k’ofa cike da shan k’amshi sbd ya tsani Atasashi gaba Ayita kallo”Atake y’an tauwagar daya shigo dasu su biyar suka rufa masa baya da wasu daga cikin mutanan dake son ya taimaka musu….
Kaiiiii!! dallah ku gafara bazai kula kowaba “ku dena maula ku tashi ku nemi na kanku mana ! Dr Amoh ya dakatar da mutanan cikin dasun kai 15 da suka biyosu inda sukayi parking jibga jibgan motocin *Mahmood ji k’amshi* ! Haba Amoh “dan Allah ka barsu da kansa yayi musu mgn Aganina hakan ba huruminka bane”cewar Kamal fuskarsa cike da nuna rashin jin dad’in Abinda Dr Amoh d’in yayi”yayinda uban gayyar kuwa tamkar babu shi Awajen be tanka musu ba”cike da nutsuwa yake takawa har yanufi wajen motar da driver ya bud’e masa da nufin ya shiga ciki “yayinda shidai SP Abdul bece komai ba sai ido kawai daya zuba musu yana kallo”mutane kuma basu fasa bin Mahmood ba,wasu na kawo gaisuwa ,wasu na masa kirari,wasu kuma na fad’in ya taimaka musu”shidai be kula kowaba ya shiga motar ya rufe,befi mintina 3 da shigaba driver ya fito ya nufi wajen mutanan ya fara raba musu kud’ad’en da both d’in yabada Abasu….Dr Amoh tamkar zuciyarsa tayi bindiga daya lura kud’in da Ake rabawa”musammun daya tuna d’azun fa ya nemi tallafin million 5 Awajen Mahmood ,sbd ya taimaka ma wasu mutane dake cikin Asibintinsa gajiyayyu sai yak’i tankashi Amma gashi yanzun ya bada kyautar manyan kud’ad’e gabansa Araba…..sunyi jiran kusan mintina 30 kafin gaba d’aga suka shige cikin motocin da suka zo dasu…..kai tsaye Anguwar *kabuga!* Aka wuce da both”SP Abdul kuma police station ya wuce bakin Aikinsa “yayinda Kamal da Dr Amoh kowa yayi inda zashi……babban gida ne na gani na fad’a! wanda kaf Acikin Anguwar babu gida me girma da kyau da tsari kamar gidan *Alh Bashir Idris ji k’amshi* duk iya bin diddik’in mutum be Isa ya iya gane tsayi ko fad’i ko Adadin girman gidan ba”duk bayan shekara 2 sai Anyiwa gidan gyara”Akwai sassa da yawa Aciki tun daga kan na masu gidan,masu Aiki,yaran gidan ,da kuma sashen bak’i dana kuma danginsa idan sunzo daga ji k’amshi “gida ne Anguwa guda ya k’awatu da dogon gini na Alfarma da manyan bushiyoyi”tun daga wajen get zuwa cikin gidan securities ne burjit”Akwai lambu ,da kuma swimming pool daga can bayan gida”Akwai kuma wajen hutawa daban daban “tun daga k’asa har zuwa saman bene”kusan tsarin gidan irin gidajen dake waje ne”idan ka shiga babban parlourn gidan Akwai kofofi sunfi 10 ko wace idan ka bita Akwai inda zata kaika”saidai up stairs da downstairs duka Mahmood nada bangare ,hakama Abbah….. kasancewar idan yamma tayi sosai Alh Bashir kan zauna Amain parlour yana lazimin marece yana kuma kallon TV”hakan yasa duk marece matansa biyu ke zama Anan suma”wani lokacin harma da yaransa mata duk suna zama “kasancewar yaransa mata 9 d’aya ta rasu”Mahmood ne kawai namiji Acikinsu”kowa kuma yasan ya fifita soyayyar Mahmood Akan ta kowane d’a Agidan…. kyakykyawan dattijon na zaune saman kujerah 3 seeter “ya saka medical glass fari saman fuskarsa “yana sanye da jallabiya milk kansa babu hula “hannunsa guda rik’e da tasbaha yana lazimi”Ayanayin shekaru bazai wuce 65yrs ba”saidai dayake hutu dajin dad’in rayuwa dake yawo Ajikinsa ya b’oye Ainahin shekarun nasa”kai tsaye me kiyasi zai iya kiransa d’an kimanin 58 to 60 yrs”kallo d’aya zaka masa ka fahimci lokacin k’uruciya Ansha k’walisa”gashi kuma tsohon d’an boko da suka san darajar biro da dakarda….lolx….matansa guda biyu na zaune gefensa sun sakasa A tsakkiya”Autar gidan me suna batulah na zaune k’asa gefen k’afafuwansa tanata shagwab’a “yana jinta yayi dai shiru”gaba d’aya hankalinsa na wajen Mahmood “sbd yasan da yamma yake dawowa gida yabaro office ,saisu fita masjeed tare sai bayan sallar isha’i su dawo gida”Hjy karimah(ummah) ta dubi Abbah fuska babu walwala tace”haba Alh! yaka mata kayima yarinyar nan Abinda takeso mana”karka manta Auta ce fa”yarinyar da duka shekarunta sha biyu Ai bata wuce riritawa Awajen kaba ko?Hjy balaraba(mamah) ta karb’e zancen da cewa” Nima dai Abinda na gani kenan”gaba d’aya tun daga kan su jidda har zuwa kan batulah baka damu da lamarin suba”jiyafa bahijjah tazo nan Akan kabata jari,nera million d’aya kabata”Amma idan na waje ne zaka basu fin haka Alh “dan Allah idan yaranka basu huta suka fantama da dukiyarka ba saiwa kakeso ya huta da ita??…..shiru tayi sbd kansa daya d’ago yana binsu da kallo one by one , fuskarsa babu walwala”tambayar kansa yakeyi wai meyasa balaraba da karimah basa kishin junansu ne da mata ke nunawa ??”shidai iya saninsa tsawon shekara 30 kenan yake tare dasu, tun k’uruciyarsu har girma yafara kamasu sbd kowaccensu zata haura 45yrs Amma bega Alamar suna kishi da juna ba”be iya furta musu komai ba sbd sautin dakakkiyar muryan sanyin idaniyarsa da yaji ta daki dodon kunnansa”ya d’ago kansa ya zubama Mahmood Ido murmushi na bayyanah kansa saman kyakykyawar fuskarsa inda Mahmood yayi gadon Asalin kyau”Atake yaji duk wata damuwa dake zuciyarsa game da matan nasa ta gushe”Abbah sannu da gida! ya fad’a Anutse, sanyayyan murmushi na bayyanah saman fuskarsa ya nufi inda uban yake zaune ba tare daya damu da matan mahaifin nasa daketa kallon saba”Afuska kamar suna sonshi”Azuciya kamar su dab’a masa wuk’a!….tun kafin ya iso Hjy karimah tayi Azamar tashi ta canza waje tana murmushin yak’e “batulah kuwa tashi tayi tabar wajen sbd tasan halin yayan nasu bah kyau Idan ka shiga hannunsa “musammun ita data lura yafi kowa tsana Acikin gidan….my friend idonka kenan?”cewar Abban yana kallon sa”sai bayan ya zauna ya masa sannu da gida,ya kuma gaida ummah da mamah kafin ya sunkuyar dakai k’asa cikin cool voice d’insa dake furgita matan zamani yace” mun d’an fita dasu Amoh da Kamal ne Abbah “kafin ya bashi Amsa su mama sun mik’e tsaye da nufin subar musu wajen”Abbah ya dakatar dasu da cewa” inaso ku sanarwa shamsiyya ,jidda, bahijjah da hajarah gobe Akwai family meeting da k’arfe 10 na safe in sha Allah”inaso kowa ya hallarah dasu da sauran yaran”da mamaki kowace ta kalli y’ar uwarta suna juya Ido”sai kuma Atare suka Amsa masa dato suna barin wajen”my friend! Abban ya kira sunansa yana maida kallonsa garesa”beyi mgn ba sai kansa daya d’ago ya zuba masa manyan fararen idanunsa dayake yawan lumshe su”idan kuwa ya tsare mutum dasu dole ya rud’e ya susuce shiyasa wasu da yawa basu iya jure kallon cikin idon Mahmood….inaso ne na sanar musu da zancen da mukayi dakai Ajiya”cike da ladabi ya gyad’a masa kansa tare da cewa “zanje ciki kafin time d’in sallar ya Ida Abbah “All right”irin wannan kyau dakayi my friend kodai sarakuwa na samu ne?? b’ata fuska yayi tamkar wani yaro haka yatura baki gaba yak’i yin mgn ya mik’e tsaye kamar zai tashi sama yabar masa dadd’an k’amshin turarensa “Abbah na murmushi irin nasu na manya Ahankali yace”inaji Ajikina ka kusan mallakar matar Aure Mahmood……
*Gombe state*
munibah! munibah!! munibah!!! wai kina gidan ubanwa ne inata kira kin mun banza ?? dattijuwar kyakykyawar macen data shigo cikin madaidai cin tsakar gidan ke fad’i cikin masifa da d’aga murya”saidai jin shiru ya sakata jan tsaki ta zauna saman wasu kujeru dake Ajiye cikin barandar dake tsakar gidan tana cire mayafin dake jikinta….. Adaidai lokacin kuma wata had’ad’d’iyar zukek’iyar budurwa chacoolate colour”wacce shekarunta bazasu wuce 24 yrs ba ta fito daga cikin parlourn sanye da doguwar hijab tana fad’in lafiya dai *dada*?! kin kirani Ina sallah ne”Masha Allah ! yarinyar Akwai baiwar murya bayan ta kyau….dallah rufe min baki wacce tafi kowa tsoron Allah”to bari kiji! iskancin da kikeyi Acikin gidan nan yazo k’arshe ,kuma Anzo mak’ura “zab’i biyu zan baki”wanda kikeso Aciki shi zaki d’auka kibi”Amma wlh na gaji da ciyar dake da shayar dake bana Anfanuwa dake daga kawai na haifi uwarki”ni wlh *Maryam* ta cuceni data mutu ta barmin ke bata barmin wata tsiyaba”shima shegen uban naki d…..dan Allah dada ya Isa haka !”meyasa wai duk idan kin tashi cin mutuncinki sai kin saka iyayena Aciki?”musammun ummata dake kwance a kabari?dada taja tsaki tare da fad’i zoki zauna muyi mgn “nidai dan Allah dada ki saka Aka mun Abinci”rabona da Abinci tun safe gashi har la’asar ta wuce “ta fad’a kamar zatayi kuka tana zama kan kujerar dake fuskantar dadan….idan kinso Abinci sai me rai da lafiya kalar wanda kikeso zakici”Abinda nakeso dake”Alh bukar zaizo gobe da sanyin safiya zai tafi Abujah”kuma dake yakeso ya tafi ,zaiyi kusan wata guda Acan”kinga ya bani dubu d’ari biyu yanzun A shago”ki dena wulak’anta mutumin nan *munibah* sbd yana sonki”yanzun haka Million d’aya zai bani idan kin Amince kin bishi”sannan bayan tafiyarku ya dinga turo mun kud’i “kuma kema yace zai baki kud’i yasiya miki komai kikeso”idan kuwa kika bujurema umarnina kamar yadda kika sabayo Abaya to wlh korararki zanyi daga gidan nan “sbd bakida wani Amfani gare ni”*ishaq* da kika kwallafa Aranki bema k’asar yana Sudan”kuma ke d’in ba’saar Aurensa bace kinfi k’arfin sa”idan zaki nemi kud’i da kyawunki da k’uruciyarki ki nema idan k’in k’iya ke kika sani”saidai wlh wlh!! Ina kan bakata “bayan nida bilkisu k’anwar mahaifiyar ki bakida kowa Aduniya”ubanki tun kina Aciki yaso Asalwantar dake kafiyar Maryam ta hana faruwan Hakan da rabon zuwanki duniya”be sanki ba, besan wace k’asa kikeba ,shin An haifeki ko kuwa Maryam ta zubar da cikinki?? duk be sani ba”sbd haka gara kibi umarni na ko kuwa na koreki…… munibah ta d’ago kanta tana watsama kakarta lulu eyes nata dake d’igar hawaye murya na rawa tace”na Amince ki koreni kamar yadda kikace dadai nabi umarninki ta hanyar sab’awa Allah “inaso ki sani dada *babu bi ga Abokin halittah wajen sab’awa mahalicci*! bazan tab’a bari ki wulak’anta mun rayuwa ba kamar yadda kika wulak’anta rayuwar Anty bilkisu “mahaifiyata ma ta bujure miki ne sbd ba hanyar Allah kike biba”da Ace Abbu na Raye da bazaki samu damar yiman haka ba…..lafiyayyen marin da dada ta d’auketa dashi yasaka tayi shiru batace komai ba ta tashi da gudu ta fita daga cikin gidan”dada taja tsaki tare da fad’in na rasa wace irin y’ar iskar yarinya ce me k’amshin tsiya Allah ya had’ani da ita haka?”Arzik’i na kiranmu shegiyar tana k’in zuwa”itafa taurin kanta har yafi na uwarta Maryam “har Asiri nayiwa y’ar banzar yarinyar nan sbd ta sakko tabi Abinda nakeso Amma tak’i “tafiso muyita zama Ina Abincin siyarwa bayan gata da kyau bazamu mora ba”to wlh dani take mgn idan yazo zance yaje da ita ta k’arfin tsiya naidai yabani kud’i nah kawai”ta fad’a tana tashi ta wuce d’aki ranta na bata *munibah* gidan su madinah k’awarta zata tafi…..
Halan kuwa hasashen dada gaskiya ne”Afarfajiyar gidan su ta sami madinah zaune tana waya da saurayinta Bilal”saidai tana ganin yanayin da Aminiyar tata ta shigo dashi ya sakata saurin yanke wayar ba shiri “*munibah* ta iso gefenta ta zauna ta saki kuka me cin rai”innalillahi wa inna ilaihir raju’un “Allah dai yasa ba dada bace tayi miki wani Abun??”dan Allah ki cigaba da hak’uri Allah na tare da masu hak’uri “in sha Allah jarabawarki takusan zuwa k’arshe……kullum haka kike cewa madinah! Amma Abubuwa sai k’ara rikicemun sukeyi,na k’arbi jarabawar rashin iyaye da bana dasu da Adalin kaka ( Abbu)”yanzun ga jarabawar b’atan wayata wanda sanadin hakan na shiga garari na rasa yaya ishaq”ga kuma son lalata rayuwata da mahaifiyar mahaifiyata ke k’ok’arin yi”yanzun kuma ta kawo wani zance “sai tayi shiru ta saka kuka me k’arfi “madinah ta rungumeta tana cigaba da bata baki”saida zuciyarta tayi sanyi sannan ta shiga sanar mata nufin dada Akanta…..innalilhi wa inna ilaihir raju’un!wlh bama saita koreni ba guduwa kawai zanyi madinah”haba beauty idan kin gudu Ina zakije,kinsan hannun wa zaki fad’a?? Balle mace kamarki me kamala bako wane namiji zai d’auke Ido Akanki ba”na riga na gama mgn madinah Allah na tare dani”da Ace yaya ishaq na nan babu inda zan tafi”koda nan gidan na dawo dada bazata bari ba”karki manta kwanaki haka tazo tayi muku rashin mutunci Akan ku fita harkata keda mamy”hakan yasa bakoda yaushe nake zuwa gidankuba sbd gargad’in mahaifinki Akaina”gashi tun bayan kwana 3 naketa gwada kiran yaya ishaq Awayarki data zuwairah me Aikin dada Amma bana samunsa ya zanyi da rainah?? Beauty idan kin gudu kije Ina?”kuma wane garin zakije,kinama da kud’in mota,idan kinje wajen wa zakije?? Kaduna ko katsina ko Kano zanje na kama hayar d’aki na nemi sana’a na dingayi muna kuma waya dake duk halin danake ciki Ina sanar miki”gaskiya hankalina be kwan taba da wannan shawarah taki me zai hana muje wajen y’an hisbah na rakaki ki sanar musu halin da kike ciki ?? Amma babu fa’ida Akan guduwarki munibah…….✍️
Turk’ashi🤭😳 shin me zai faru munibah zatayi nassarar guduwa??
Wannan shi Ake kira da wasa farin girki book ne dayazo da zafi da kuma sabon salo karku manta da sunan littafin sannu Sarkakiya Complete Novel Document A hankali komai zai warwara
File Name | Sarkakiya… Complete Novel Document |
Title | Sarkakiya Complete Novel Document |
Author | Mommyn Fareesa |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 17/11/2024 |
File Size | 100KB |
Format Size | TXT |
Book Price | ₦500 |
Phone No | 08100084251 |
Download Sarkakiya Complete Novel Document By Mommyn Fareesa
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.