Novel Document

Yaro Ma Namiji Ne Complete Novel Document

Description/Story:

Yaro Ma Namiji Ne Complete Hausa Novel Document Written By Mai Dambu

 

Description

Ranta a jagule yake tun jiya da Umma ta fad’a mata Abul khairi yana tasowa daga kasar ghana zaizo hutun karshin shekara wani bakin cikine ya rufeta domin tana cikin zaman lafiya yana dawowa tashiga damuwa kenan domin duk Samarikanta duk ya koresu wanca hutun da yazo batasan me yake nufi da ita tarasa me ta tsare masa haka Yaro karami yasata a gaba gawani iskanci da yatsira shine yanda yake wasu abubuwa a gabanta kaman wanda yake gaban budurwansa ,duk wannan tunani tayi shine lokaci da suka iso unguwarsu domin tana cikin Keke napene don ta dawo daga aikine.

Suna isowa kofar gidansu ta hango shi yana zaune akan motar abokinsa wanda suke rashin kunyarsu tare.

Dakatar da me napen tayi yana isawa tafito tabashi kud’insa rashin canjane ya basu matsala.

Daga can Abokinsa yata6a shi ” kai Abul khairi ga sugar Mommynka ta dawo fa…”
“Ameer dagaske ina take..”

“Ke kauce gata a kofar gidansu suna neman chanji..”
Sauka yayi a motar tana tafiya kana ganinsa kasan yakai cikaken namiji Yaro me kimanin shekara ashirin da hud’u d’an gatan Yaron da iyayensa suke alfahari ga ilimin addini gana boko.

Cikin takun kasaita ya isa wajensu “Assalamun alaikum..”

Me nape ne ya amsa masa da ” wa’alaikum salam..”

“Malam je ka da kud’i zan biyata ”

Cike da mamaki me nape ya kalleta ” hajiya kina jin Yayanki yace natafi da kud’inki”

Raita a 6aci ta kalle me nape ” ay bashi ya baka ba don haka kabani canjina ”

Wani murmushi Abul khairi yayi domin ya fad’i haka ne don ya zolayeta kuma yayi nasaran haka dubu d’aya ya zaro ” malam bata nata gashi Allah ya bada sa’a”

Bakin ciki ya hanata ma karben kud’inta shine ya karbe me nape ya tafi abinsa cikin zauren na biyu ya same ta yasha gabanta.

“Wai menayi ne haka dakika tsane ni haka y’au fa na dawo kamata yayi ki manta da kome tunda yawuce abinda ya faru tun baya kike ajiyewa a ranki ba kyau yana sa mutum tsofa..”

Wani kallon banza tayi masa a madadin yaji haushi sai ya wani lumshe idanunsa masu d’ankaren kyau ga girma wani iska yaja a bakinsa kafin ya fara tsotsan bakinsa.

Tana ganin haka ta girgiza kai “Bani hanya na wuce ko na mare ka..” matsawa yayi yana kallonta daga sama har kasa, himmar din da tasa irin me kama jikine gashi duk yabi jikinta ya kama wannan Coca cola shif dinta yafita rass dasu albarkattun kirjinta sunan yanda suke wani murmushi yayi sanna yafara magana da haka.

“Didi Rukaiyya na zata zanzo na samu wani ya d’auke minke amma ba damuwa wqnnan karo da karfina nazo…”
Ya fadin haka ya bata hanya ta wuce bin bayan yayi da kallo yanda take tafiya sai da tsigar jikinsa ya tashi harta gashin jikinsa sai da suka mike tsaye “Didina kenan kina wuta ina binki da soyayya”

Yana fita yasame Ameer yana jiransa “Kaga ni kwanciya zai shiga nayi sai anjima kenan”

“Ba damuwa ango tsohuwa” da haka kowa ya kama gaban.

Rukaiyya tana tashiga matan tasamu gidan da suke tsakar gida suka hawu jefa mata habaici Inna kulu ce fara sauran suka amsa mata yaransu suka saka dariya bata ko d’ago ta kallo su ba tashiga kofarsu tasamu Innata tana soya masar shinkafa “Sannu Inna ya aiki”

murmushi Inna tayi “Uwat ay ke yakamata na tambaya ya aiki”

dariya tayi domin kullum haka sukeyi ita da Innarsu “Aiki sai godiyar Allah kome yana kyau”

“Aha masha Allah jeki huta nasa kind’ebu rana sai kace ba damina ba ” inji Inna.

“Yawwa Inna wanka ma zaiyi yanzu”

Daga waje Inna Kulu fara magana ” ay dole Yarinya tarik’a tana neman abokin hutu babu dole akare da bin abonkan aikin ana gurjan sauran abinda suka rage ko ba haka”
“Haka ne Inna Kulu…”

 

 

Read / Download Yaro Ma Namiji Ne

 READ THE NOVEL
DOWNLOAD COMPLETE DOC.

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

 


 

Back to top button