Description/Story:
Hajar Hausa Novel Document
Written By Nafeesa Yusuf Nagoda
Description Of Hajar Hausa Novel Document
Wane mahalukin ne da yake lungun ƙunshi a unguwar Dala bai san gidan gini ba, aiko unguwar ka shigo sai ka san gidan gini ballanta ƴan unguwa, gida ne wanda yayi fice yayi shura a fannin hargitsi da rashin zaman lafiya, hakan ya samo asaline daga iyalan gidan da suka kasance ƴan bala’i da jaraba, Magidancin gidan da ya kasance wani soloɓiyo matansa biyu suke juyasa tamkar waina a tanda yadda sukaga dama, Allah ya azurtasa da ƴaƴa mata har guda biyar da maza uku, matarsa ta farko ƴaƴanta biyar ta biyun kuma guda uku, kullum a gidan gini sai anyi hatsaniya tsakanin matan gidan domin tamkar suna ganin hajin junansu, kwata-kwata basa jituwa kullum cikin tashin hankali suke, ƴaƴansu mata ko wacce ta shigewa uwarta, wataran idan faɗa ya kacame har saita kai ga maƙota suna shigowa rabasu saboda wataran har dambe suke idan cacar baki tayi zafii, tin maƙota na shigowa rabasu har ta kai ga an watsar dasu ana barinsu suyi faɗansu iya iyawarsu su rabu dan kansu, kai wataran idan abu yayi tsamari har sai an raunata wasu, idan akai wannan gagarumin dambe haka gidan yake yin kaca kaca, filin tsakar gidan da ko daɓe babu sai burjin ƙasa ya koma tamkar gidan mahaukata da shirgin da akai jefe-jefe da doke-doke wajen dambe, haka Magidancin nan zai shiga tsakaninsu yana ƙoƙarin rabasu amma faɗa yaƙi ƙarewa daga matan har ƴaƴan nasa basa saduda sai ya yanke jiki ya faɗi wanda a sanadin haka ya haɗu da hawan jini, Malam Adamu mai gini shine magidancin wannan ɗan bala’in gida. da matansa biyu ta farko Rabi’atu wacca ake kira Maama saita biyu Fatima wacca ake kira Umma.
★Wani irin gyatsine take tana hura ɗan siririn hancinta ta fito tsakar gidan da yake duk cakwalkwali saboda ruwan da aka sheƙa daren jiya, hannuta riƙe da brush dinta da ta matso tooth paste akai, can wajen da suke tara ruwa cikin manyan tukanen ƙarfe irin wanda ake abincin gidan biki ta dosa, ta ajiye brush din hannunta akan wata murguɗaɗɗiyar kujera, ta ɗauki buta ta buɗe tukunya ɗaya ta kantami ruwa ta wuce hanyar banɗaki dake cikin wani lungu da wata siririyar kwata wacca ta ɓulla har cikin banɗakin tayi waje, ƙofar banɗakin ta langa-langa ta bubbuga, daga banɗakin aka yi mata gyaran murya, a hasale tace “koma waye aciki yayi sauri ya fito a matse nake!!!”, wajen minti biyar tana jira amma ba a buɗe ƙofar banɗakin ba, ta sake bugawa da ƙarfi tace “wai wace shegiyar ce aciki ne??, dalla malama ki fito”, daga cikin banɗakin aka ja wani dogon tsaki, a hasale ta banka ƙofar daman bata da sakata bare mukulli, turo ƙofar kawai ake sai a tokareta da wani mulmulen dutse da yake cikin banɗakin, Maimuna da take cikin banɗakin riƙe da buta a hannu ta kalli Hajar sama da ƙasa ta daka tsaki ta fito daga ciki, daman ta gama amfani da bayin amma da ta ji Hajar tana jiranta shine taƙi fitowa.
Hajar ta karkaɗa kai ta dubeta tace “zaki sani ne??” ta shiga bayin tayi uzirinta ta fito, ta tsugunna gaban rariya tayi brush ta wanke fuskarta, ta miƙe ta shiga ɗakin umma wacca itace mahaifiyarta, umma da take zaune kan darduna tana irga cinikin kulelen da tayi jiya da yamma tace “makaranta zaki tafi Hajara?, toh wane zai auno min wake ya siyo min manja?”
Hajar ta buɗe wardrobe ɗin da ta gama fatattakewa gata wata old modern gaba ɗaya ƙofofinta sun cire saidai a jingine su, ta zaro ironed uniform ɗinta tace “toh bari na shirya saina je na auno miki waken”, umma tace “dama haƙura kikai da zuwa makarantar nan gashi kin makara kuma anyi ruwan sama nasan ajinku ma ya cika da ruwa”, Hajar tace “A’a nidaii umma zani kinsan shirye-shiryen jarabawa muke, yau za ai mana thumb print wanda za muyi amfani dashi wajen rubuta NECO”, Umma ta lalo kuɗi ta miƙa mata tace “wake kwano ɗaya sai manja rabin kwalba”,
Hajar ta karɓi kuɗin ta ajiye kan shirgin ƙullin kaya tace “ita Sabra ba zata makarantar ba??”, Umma tace “Eh babu inda zata gaskiya, makarantarsu tafi taku lalacewa ko taje ma nasan dawowa zatai aii duk ranar da akai ruwa ba ayi”, Hajar tace “tom”, umma ta ƙulle ragowar kuɗinta a haɓar zani ta fita, Hajar ta janyo uniform ɗinta ta saka wanda sukay mata kyau duk da cewa ba wasu kayan ado bane, ta ɗauki kuɗin ta ɗakko slipers dinta a bayan ƙofa ta saka ta fita tsakar gida, umma ta gani tana wanke gwangwanayen kulele can bakin rariya, suka haɗa ido da Maimuna da take faman haska madubi a fuskarta tana mulka wani sabulu, Hajar tace “Banza mai bleeching”, umma ta juya ta daka mata harara ta nuna mata ƙofa tace “akul zoki fita aiken da nayi miki”, Maimuna ta ɗaga murya tace “uwar kice mai bleeching shiyasa ta haifeki fara”,
Maimuna ta cigaba da shafe fuskarta da take tamkar ta larabawa amma ƙafar nan da hannu baƙi ƙirin sai kace tayi dilke da gawayi, Sa’adatu ce ta fito daga ɗakin Maama itama dai fuskar nan taci bleeching daidai gwargwado tace “wai me naji mara kunyar yarinyar nan take faɗa miki ne??”, Maimuna tace “aina gwaɓa mata maganar da ta dace da ita shegiya nunar rana”, Nabila ma ta fito daga ɗaki tace “aii ni haushi kike bani Maimuna, ki zauna kina takun saƙa da waccan ƴar tatsitsiyar yarinyar har tana gwaɓa miki magana”,
Sa’adatu ta dungurewa Maimuna kai tace “shashasha kawai” ta koma ɗaki, umma duk tana jinsu bata ce musu komai ba kawai wankin gwangwanayenta take, Nabila ta ɗauki buta ta shiga bayi, Maimuna ta cigaba da ɗashe fuska da sabulu. Hajar tana fita daga gida ta kama hanyar shagon iliya mai awo, duk arean shine mai awon da yake fitowa da wuri, wani ɗan madaidaicin shago ne da ake siyar da kayan awo na masarufi da dai sauran ƴan tarkace, wasu maza ne a bakin shagon ɗaya yana kan benci ya kara rediyo a kunnensa ɗayan kuma yana ɗura manja a kwalba a kan wani tebur da yayi daƙal-ɗaƙal da mai da ƙura, Hajar ta tsaya a bakin shagon tace “salamu alaikum”, mai ɗura manjan wanda shine mai shagon wato iliya yace “wa’alaikumus salam”,
Hajar tace “mal iliya a bani wake kwano ɗaya manja rabin kwalba”, iliya ya shiga shago ya auno wake ya fito waje ya zuba manja a farar leda ya haɗesu a babbar leɗa ya miƙa mata, ta ciro kuɗinsa ta basa tace “Allah yasa dai manjan mai kyaune, ba irin na jiya mai warin mushe ba”, iliya yace “idan an samu wata matsalar a dawomin da kayana saina baku kuɗinku”, ƙasa ƙasa Hajar tace “uhmm sai kace gaske..” ta kama hanya zata bar bakin shagon mutumin da yake kan benci ya cire rediyon kunnensa yace “ke hajara akwai kulele??”, ta juya tace “ka cire ke ɗin mana ka bar hajara, babu kulele sai anjima”, ya kaɗa kai irin ai halinki ne yace “toh idan an gama ki kawomin ta ɗari biyu nan sai na baki kuɗin”, ta yamutsa fuska tace “saidai ka tura yaro ya siyo maka” tayi gaba abunta, iliya ya koma kan benci ya zauna yace “ita da sauƙi fa”, munkaila yace “inafa sauƙi, kasan maƙotanmu ne mun haɗa katanga dasu ta fuskar baya, wallahi shekaran jiya suna hatsaniyar nan tasu da suka saba iyalina ta shiga yi musu sulhu, wannan ja’irar yarinyar ce ta kwaɗa mata bokitin ƙarfe a hannu tazo kwaɗawa ƴar uwarta. harfa saida ta fitar mata da jini”, iliya yace “aii mal Adamu bashi da iko da gidansa ace bazaka iya tsawatarwa matanka ba, abinda sukaga dama za suyi, ni ban taɓa ganin lusarin namiji kamarsa ba, sai kace wanda suka shanyesa”, munkaila yace “ai a shanye yake, kai kana ganin wannan mutumin kasan shanyayye ne ainun, yanzu fa ƴaƴan nan nasa shafe-shafen nan na zamani suke, ni jiya da naga wata ma acikinsu ban ganeta ba saida naga tukubar hancin”
iliya ya kyalkyale da dariya yace “ai jiya wata tazo nan siyan shinkafa wallahi data miƙomin kuɗi na ɗauka wani ne ya zuro hannu ta bayanta ya miƙomin kudin ba ita ba”, munkaila yace “Allah dai ya kyauta ya shirya mana zuri’a”. iliya ya tashi zai bawa wani yaro da yazo aunar masara, munkaila ya kara rediyonsa a kunne ya lumshe ido yana karkaɗa kai. Hajar na komawa gida ta tarar da umma tana tashin wuta a kurfotu, ta wuce ɗaki ta ajiye aiken ta fito ta kalli umma tace “ni zan tafi bazan daɗe ba inayin thumb print zan dawo”, umma tace “bazaki jira na dama kunu ba??, haka zaki tafi makarantar ciki kwalam”, Hajar ta kalli gawayin da umma take ƙoƙarin cinna masa wuta taga akwai lema ajikinsa tace “idan na dawo nasha, bari na gaida Baba”. ta shiga ɗakin Baba da ƴar sallama, yana zaune gefen katifa yana jan wata doguwar cazbaha, ta tsugunna tace “barka da safiya Baba, an tashi lafiya??”
Baba ya dubeta da wani irin yanayi, duk cikin ƴaƴansa mata yafi jinta a zuciyarsa, yace “lafiya lau Hajara, makaranta za a tafi?”, tace “eh Baba, zanje ayi mana thumb print na jarabawar NECO da zamu zana”, yace “Toh Allah ya bada sa’a” ya ciro ɗari biyu a aljihun wandonsa ya miƙa mata, ta sa hannu biyu ta ƙarba tace “nagode Allah ya saka da alkhairy”. ta miƙe ta fita, a bakin ƙofa suka kusan yin karo da Mu’azzam wanda shine babban yayanta da suka haɗa uwa da uba ɗaya, Mu’azzam ya ɓalla mata harara ya haɗe rai yace “bani hanya..”, da sauri ta matsa masa hanya ya shiga ita kuma ta kama hanyar soro.
★A hankali yake murza steering ɗin ɗumemiyar motar da yake driving, wayarsa da take gefensa ta hau tsuwwa, looking at the road ya kai hannu yayi picking ya kara a kunne yace “Salam Mami, har yanzu dai ban gane street ɗin ba, i thought Dala kika ce koh??”
Ya ɗanyi shiru sai kuma yace “ohk nagane, inajin nabi wrong way ne”, wayar ya katse ya fara juya motar a ɗan tsukun layin da kwaltarsa ta gama ragargajewa, da yake expert ne wajen lailaya mota ya juyata cikin sauƙi ya koma ɗayan side ɗin kwarɓaɓɓen titin, yana fara tafiya wani mai mashin ya yanko gabansa tamkar an wurgosa, da sauri ya ɗauke kan motar yayi gefe da ita, motar ta faɗa cikin wani ruwan kwatami na ruwan sama da kwatocin gidajen mutane da suka ɓulla cikinsa, ruwan kwatar da jar ƙasa ya feshe Hajar da take tsaye a bakin wajen tana jiran napep, gaba ɗaya uniform ɗinta suka ɓaci da jar ƙasa, ga wani wari da ruwan yake na kwata, Hajar tabi jikinta da kallo ta hangame baki, a matuƙar zafafe ta dubi motar da tayi mata wannan aika aikar lokacin da mutumin ciki ya buɗe ƙofar driver……✍️
File Name | Hajar… Hausa Novel Doc. |
Title | Hajar Complete Novel Document |
Author | Nafeesa Yusuf Nagoda |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Fiction Story |
Published Date | 27/10/2024 |
File Size | 600KB |
Format Size | TXT |
Book Price | 500 |
Phone No | 08141826023 |
Download Hajar Hausa Novel Document By Nafeesa Yusuf Nagoda
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.