Uncategorized

Macijine Shi Page 37-38 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 37/38

________________cike da zallar madarar mamaki budurwar nan ke kallon fattu,tunda take arayuwarta ba wani mahaluƙin daya taɓa daga hannu  da sunann ya faɗa mata koda baƙar magana ne, amma wai yau itace tsaye gaban wata kucakar yarinya,sannan agaban bayinta ,dafe da kunci,wai da sunan an sharara mata maruka har biyu?

Lallai wannan yau ko ƴar gidan uban waye saita gane kurenta, zata san cewa ni Zulaihat nafi ƙarfin awulaƙantani ,kuma azauna lafiya.

Gaba ɗaya barorin gimbiya Zulaihat atsorace suke ,kuma kawunansu sunkuye a ƙasa, yayin da zuciyoyinsu ke bugawa cikin tsoro da fargabar abinda zai biyo baya.

Fattu kuwa tana tsaye riƙe da ƙugu,ta ƙurawa gimbiya Zulaihat idanu,kamar yadda itama ke kallon fattun,lokaci ɗaya fattu taji mugun tsabar Zulaihat cikin zuciyarta,haka kawai zata wani daga hannu ta dallamin uban mari?ai wllh saidai acinyeni agidan nan,amma idan wannan banzar tayi min abu saina rama dan ba tsoronta nakeji ba ehe.fattu ke wannan zancen ,cikin zuciyarta tare da murguda baki bayan ta kammala zancen zucinta.

H

Ahargitse gimbiya Zulaihat ta fara juye-juye ,can ta hango wani ƙarin flower vase na tangaran,da hanzari tayi gurin da tare da rarumoshi tayi kan fattu tana huci.

Tsorone ya gama kama fattu,yanzu idan ta jibga mata wannan ƙaton abun akai ,ai wllh sai kanta yayi raga-raga,tab yaseen bazata tsaya ba.baya fattu ta farayi cikin tsoro tana mai kallon gimbiya Zulaihat,

Ita kuwa gimbiya zulaihat ganin fattu na ƙoƙarin gudawa yasa ta dakawa hadimanta tsawa akan su riƙe mata fattu,wani irin zafi takeji cikin zuciyarta,wllh zata iya kashe fattu yadda takejin tsanar fattun cikin ranta,dan haka tayi rantsuwa yau saita illata fattu,ta yadda  ko hannunta bazai ƙara moruwa ba,bare ta sake gigin marin wani.

Cikin azama kuwa suka tsakumi fattu suka riƙe ta,ihu fattu ta fara cike da tsoron abinda matar nan zata mata,” wayyo Allah na Hamma kazo, zasu cinyeni danya da raina ,wayyo hammana!wayyo Hamma kana ina!! Fattu ta faɗa cikin ihu,lokacin da tajita ahannun waɗannan manyan yan matan masu shegen ƙarfi.

Zulaihat kuwa cikin rashin imani da tsana take faɗin,”wllh yau saikin komi wacece ,kin siya babban kuskuren taɓa Zulaihat,kuma yau zaki girbi abinda kika shuka” Zulaihat ta faɗa cikin fushi tana daga wannan flower vase ɗin da iya ƙarfi ta  zata sakarwa fattu.

“Zulaihaaaatttttt!!!!” Aka kwalla kiran sunan gimbiya Zulaihat din ,cikin wani irin sauti mai ƙarfin gaske ,wanda saida dukansu suka tsorata .

Afirgice Zulaihat ta saki flower vase ɗin nan daga hannunta ya fadi ƙasa. 

Ba kowa bane yayi mata wannan bahagon kiran face Adeeb ,wanda ya fito ne dan shigowa da fattu gurin mai martaba,lokacin ya gama basu labarin irin taimakon da fattu da baffanta sukayi masa ,da kuma dalilin tahowa da ita nan ɗin .shine mai martaba yace ya shigo da ita ciki.

Dama kuma yana zaune ne ,amma zuciyarsa tana can gurin fattu,dan yasan ta da shegen tsoro,abu kaɗan ne zai firgitata.

Dan haka cikin sauri yake tafi lokacin daya fito daga part ɗin sarki,

Yana doso babban farko kuwa ya fara jin ihuj fattu tana kiran sunansa.dan haka da gudunsa ya ƙaraso cikin falon,yana zuwa idanunsa sukayi masa mummunan gani,Zulaihat na ƙoƙarin illata masa Hulwa.

Cike da tsoro bayin nan suka saki fattu tare da zubewa kasa suna gaida Adeeb.

Wani shegen kallo da Adeeb ya watsa musune yasasu ficewa daga falon da gudu cike da tsantsar tsoro .

Fattu kuwa da gudu ta nufi Adeeb tana kuka,cikin sauri shima yake saukowa daga matakalar benen, uku -uku,hurhuɗu yake tsallake step din, atsakiya falon suka hade da fattu,tana zuwa ta faɗa ƙirjinsa tare da ƙanƙame shi tana kuka.”Hamma mutafi daga gidan nan,tsoro nakeji,wannan matar muguwace daga zuwa ta ta mareni har sau biyu,kuma tasa wadancan doyoyin suka rikeni wai zata baremin kai” fattu ke faɗin haka cikin kuka tana kwance akan ƙirjin Adeeb.

Wani irin tausayin fattu ne yake mamaye ilahirin jikin Adeeb,tare da tsantsar jin haushin Zulaihat cikin ransa.

Ahankali yake shafa bayan fattu yana shiiiiiiiii da bakinsa alamun rarrashi.

Karanta Littafin>>> Macizai Ne Page 1-10 Hausa Novel

Idanunsa sun kada sunyi mugun jaaaa ya kafesu akan fuskar Zulaihat,wacce tayi mutuwar tsaye tana kallon wannan yarinyar kwance akan ƙirjin Adeeb,wanda ita bata taɓa samun wannan damar ba.banda bugawa ba abinda zuciyarta keyi,lallai akwai gagarumar matsala,wacece wannan yarinyar?meye alaƙarta da Adeeb? 

Cikin daukewar tunani da tsananin kishi daya rufewazulaihat idanu,kunsan matan larabawa da bakin kishi,Zulaihat ta nufi kansu Adeeb gadan -gadan.tana zuwa ta sanya hannu tare da ƙoƙarin fizge fattu daga jikin Adeeb.

Wasu zafafan marukane guda biyu suka sami gurbin zama akan fuskar Zulaihat ɗin,wanda sun fitowa daga hannun Adeeb.

Kusan minti biyu Zulaihat ta dauka kafin ji da ganinta sudawo daidai.

Ihu ta kurma cikin azaba tana mai dafe kumatunta” habeebee nika mara?akan wannan jakar?wacece ita?meye alaƙarka da ita ?  Da har zata kwanta akan ƙirjinsa,kaikuwa kana rarrashinta?Zulaihat ta faɗa cikin kuka da rikicewa.

Wani matsiyacin kallo Adeeb yayi mata, yana mai gyarawa fattu kwanciyarta akan ƙirjinsa kafin yace ” ita ɗin mutumce mai matukar muhimmanci arayuwata,mafi kusanci da zuciyata wacce zan iya aikata komai akanta,ki kiyaye nan gaba,hukuncin da zan miki bazaiyiwa kowa daɗi ba ” Adeeb ya faɗa cikin wata iriyar murya mai kama da ta basasa,yana mai nuna Zulaihat da hannunsa.

Cikin karawa kukanta ƙarfi Zulaihat tace” kana nufin harni,tafini muhimmanci agareka?” Ta faɗa cikin ruɗu.

Wani banzan kallo Adeeb ya wurgawa Zulaihat kafin yace ” ke wacece?wane matsayi kike dashi agareni,karki ƙara haɗa kanki da  Hulwa banza shashasha marar zuciya da kamun kai ” Adeeb ya fada yana mai juyawa da fattu suka fara tafiya zuwa sama.

Cikin kuka kamar zata shiɗe Zulaihat tace ” wacece ita”

Saida sukayi taku kusan uku ,kafin Adeeb ya juyo cikin murtukakkiyar fuskarsa yace ” MATA TACE ita” ya faɗa yana mai tsare Zulaihat da idanu.

Wani wasan ihu Zulaihat ta kwalla tare da ficewa da gudu ta nufi waje.

Harara Adeeb ya bita dashi kafin ya juya suka ci gaba da tafiya ,duk abinda suka faɗa fattu batasani ba, dan da Yaren larabci sukayi maganarsu.

Saida sukaje bakin ƙofar part ɗin sarki sannan Adeeb ya tsaya tare da gogewa fattu hawayenta.yace “kinga duk kin bata kwalliyarki da hawaye, kiyi shiru zamuje gurin abie ne yanzu kinji?karki damu bazata ƙara yi miki komai ba”ya faɗa yana mai riƙe kumatunta.

Kallonsa fattu keyi tare da shagwabe fuska tace ” Hamma Ni tsoro nakeji” 

“Ba abinda zai sameki ,bagani ba?” Ya faɗa yana kama hannunta suka shiga dakin abie.

Zulaihat kuwa tana ficewa daga falon,kai tsaye mota taje ta shiga tana kuka kamar ranta zai fice,da mugun gudu take tafiya hatta bar cikin masarautar ,kai tsaye wani hotel ta nufa tana zuwa dama akwai dakin dake amazaunin nata cikin hotel ɗin.

Karanta Littafin>>> Yar Harka Page 1-10 Hot Romantic Novel

Fridge ta buɗe tare da ɗauko wata kwalba ta buɗe cikin sauri tare da kafa kai ,saida ta shanye abinda ke ciki tass kafin ta jefar da kwalbar. Waya ta dauka tare da kiran wata number tace tana jira.

Ko minti biyar ba’ayin saiga wani saurayi kyakyakywa ya shigo ɗakin ,yana zuwa lokacin harta fara fita daga hayyacinta ,tana surutai,” saina kasheta ,saina ranta da yarimana ,nawa ne Ni kadai.

Rungume saurayin tayi suka fara aikata alfasharsu,subhanallah,Zulaihat Allah ya shirya.

Adeeb kuwa suna shiga dakin abie ,fattu ta kama gefen rigarsa ta rike gan! Cikin hannunta .ammi ce ta ƙaraso tare da kamo hannun fattu tana murmushi tace “ƴata yar albarka sannu kinji” ammi ta faɗa tana mai rungume fattu.

Abie ma murmushi taye yana mai kallon fattu ,lokaci ɗaya yaji yarinyar ta kwanta masa arai tana da hankali da nutsuwa.

Nan ammi tace agurinta fattu zata zauna ,ita zata kula da ita ,sannan zata taya Adeeb cigiyar mahaifan fattun.

Bayan sati guda Sarki ya hada wani gagarumin taro na farin cikin dawowar babban dansa magajin faɗa,wanda aka gayyato sarakuna daga kasashe daban -daban.

Kuma nan da kwana biyu taron zai gudana,dan haka gyara ake yiwa masarautar sosai.ko ina ka kalla an gyara shi yayi mugun kyau,

Adeeb kuwa shima yanzu ya shiga busy,yana ɗan bin kamfanoninsa na kasashe daban -daban yana duba yadda harkokin ke tafiya,dan haka yau kwana hudu baya gida .kuma basu hadu da  fattu ba .

Gaba ɗaya fattu ta shiga damuwa,kullum tana cikin dakinta da aka bata mai shehun kyau,saidai akawo mata abinci taci ,tayi wanka ta kwanta.

Ko falo baya fita.itama ammi gaba ɗaya bata zama tana ta uzuri.

Gashi bata ita tare su ba,Gara ammi wataran  takan dan yi mata Hausa kadan kadan.

Yau dai fattu tana zaune shiru ,tace bari ta fito falo dan yasan huta kuma ta duba Hammana.

Tana sanye da doguwar riga milk mai fadi kanta yanke da mayafin rigar,ba kwalliya akan fuskarta amma tayi kyau sosai.

Download>>> Dr. Bobby Complete Novel Document

Falon ta fito tana binsa da kallo,ya hadu iyakar hafuwa, sai ƙamshi ke tashi ta ko ina.

Tana ɗan zagayenta afalon ,taji anbude kofa.

Juyawa tayi ɗan ganin waye ya shigo,

Rashad ne ya shigo ɗakin shida zulaihat.suna tafe suna dan magana ,da alama kuma rarraba jin Zulaihat ɗin yake.

Turus suka tsaya suna kallon -kallo atsakaninsu su ukun.

Ita dai fattu kallonsu take tana tunanin,dama wannan matar agidan nan take ?tun ranar bata sake ganinta ba,sannan 

Kuma ta gane wannan. Saurayin,shine wanda ya taba mata kumatu awancan ɗakin,dan haka da sauri fattu ta kawar da kanta gefe tare da hade fuska, nemar guri tayi ta zauna akan lumtsuma luntsuman kujerun da suka yiwa falon ƙawanya.

“Kai !!Rashad me wannan fitsararriyar keyi anan?aikuwa wllh saina koya mata hankali”Zulaihat ta faɗa tana ƙoƙarin ƙarasawa kusa da fattu.

Da sauri Rashad ya riko hannunta yana mai faɗin “haba -haba ke matsala ta dake gaggawa ,ba yanzu muka gama magana dake ba,zaki taimakeni,nima zan taimakeki, cikin sauƙin kowa ya sami abinda yake so.

Idan kika yi wani abu yanzu ,to shirin mu ga zai wargaje,kuma kinsan wancan horon bashi da sauƙi ko kaɗan.ba dai jini ne za’ayi taron nan ba? Rashad ya faɗa yana mai sakin wani shegen murmushi.

Jinjina kai Zulaihat tayi tana mai hararar fattu.

Cigaba Rashad yayi da maganarsa”to ki kwantar da hankalinki, ranar zamu aiwatar da ƙudirinmu akanta ,zamu tarwatsa koma menene ke tsakaninsu,Ni sam na kasa gane inda ammi ta dosa ,bata bamu goyon baya kamar yadda ya kamata,amma zamuiyi komai da kanmu.

Kedai kawai ki danne zuciyarki akan komai har zuwa jibin” 

Rashad ya faɗa cike da ƙarfafawa Zulaihat gwuiwa.

Jinjina kai tayi cikin murmushi tace ” nasanka nasan halinka,kuma zaka iya Allah ya nuna mana lokaci, amma wllh na tsani yarinyar nan sosai acikin raina” Zulaihat ta faɗa tana hararar fattu.

Fattu kuwa murguda mata baki tayi itama tana mai cewa cikin ranta” oho dai saidai kiyi ta hararata amma wllh baki isa ki doke  in gyaleki ba ,ba ruwana da wani kin girmeni ehe” fattu ta faɗa tana mai dan dukan cinyarta har saida ƙaran ya fito sukaji.

Kallonta sukayi gaba dayansu ,Zulaihat tace ka “gani ko dukda batasan me muke cewa ba,amma kalli abinda take ?wllh daka barni na tattara yarinyar nan,ai Prince baya gida bare yace wani abu”Zulaihat ta faɗa cikin muryar bacin rai.

“No karki fara,ko baya gida yanzu ai kinsan zai dawo ko?kuma ma gaskiya bazan bari ki taba min kayana ba,dan gaskiya ina hango hutu agurin man sosai ” Rashad ya faɗa yana wani kashe ido tare da kallon fattu.

” Wllh Ni haushi ma kake bani ,akan wannan kucakar zaka wani tsaya bata lokacinka,me zaka samu jikin wannan banzar?”cewar Zulaihat cikin haushi.

” Ke wllh ƙarya kike kinsan wannan yarinyar tafiki komai na mata ,kalleta mana da kyau ki gani ,aikinsa  ba karya ,malam komai yaji yadda ake bukata” cewar Rashad cikin wani irin shegen voice .

Tsabar haushi daya kama Zulaihat tashi tayi afusace ta bar falon tana ƙunƙuni.

Karanta Littafin>>> Abban Sojoji Page 1-10 Hausa Novel

Adeeb yana can ƙasar farin yana gudanar da binciken kasuwanci sa ,gefe guda kuma ya dage sosai wajen neman iyayen fattu,yasa hoton sarkar nan Tata da rigarta tare da nuna yana neman wanda yasan waɗan nan kayan,saidai bai yarda ya nuna wata alama da zata nuna shike neman wanda yasan wani abu game da  kayan  ba,dan nunawa yayi shidin talaka ne sosai .

Kullum suna waya da ammi yana tambayarta fattu ,sannan yace ta rinƙa koya mata Yaren larabci ,kuma ammi tana kokarin koyawa fattun ,dan yau take son kawo tsohuwa salima ,ta zauna tare da Fattun dan ta koya mata Yaren sosai,tunda ita ta iya hausa sosai.kuma kusan ahannunta Adeeb ya girma ,ita tayi renonshi.

Wai ina batun baffa ne?

Allah Sarki baffa lokacin da aka kaishi dakin hukunci ,saida yayi kwana biyu basu wai-waiceshiba,yana can yana fama da zazzabi sakamakon dukan da sukayi masa.sau daya ake kawo masa abinci.

Ranar kwana na biyun ne da yamma aka fito dashi dan zartar da hukunci,lokacin mai gari ya danji dama -dama an gyara masa karayar daya samu har uku .jauro kuma yana nan cikin halin bakin ciki,dan kuwa jauronsa ta lalace ,bazata ƙara amfanuwa ba,ta motse ta zama ƴar ririya kamar sillen kara.

Shiruwa abokin ta’asar tashi,yanan ido daya ya tsiyaye ,rabin fuska ya zagwanye ,ya zama kamar horo,arɗo ma hannu ya shanye ya zama kamar lauje.

Cikin fushi da bacin rai tare da bakin ciki mai gari yace , sakamakon ta’adda cin da baffa da yar shegen daya kawo musu cikin gari sukayi,an karbe duk wasu shanayensa da tumakai harda gidansa ,matsayin diyyar abinda mayyar daya kawo gidansa tayi,sannan ankoreshi daga garin ,saboda ƙarya da cin amanar yan garin da yayi ,na cewa fattu yarsace.

Baffa yayi kuka sosai,akan wannan rashin adalcin da akayi masa.amma haka ya haƙura ya miƙawa Allah lamarinsa.

Koda ya dawo gida tuni labari ya isa kunne gwogwgo hansai,dan haka yana shigo taci kwalarsa tace ya bata takardar ta bazata iya zama da faƙiri ba.

Nan take kuwa baffa yayi mata saki daya .kuma sam ta hana ƴaƴan ta subi baffa. Shi kadai ya bar garin cikin mawuyacin hali.

Allah Sarki baffa ,Allah ya saka maka wannan zalumcin da akayi maka.

Acan misra kuwa ,amma na hango zaune akan wata ƙayatacciyar kujera , da waya ahanunta ,magana take cike da nuna yanayi na jimami, masu mata hidima na can gefenta azaune.

” Zanyi duk iya ƙoƙarin na,ɗan ganin naja yarinyar ajikina, in Sha Allah muke da nasara” amma ta faɗa tana mai ajiye wayar.

Murmushi tayi kafin tace” Maryam zaki san koni wacece ,zanyi abinda saiya girgizaki,saina rabaki da dan da kike takama dashi” amma ta faɗa tana mai gutsirar apple.

Amma dai itace kishiyar mahaifiyar Adeeb,wacce lokacin da Adeeb yazo ta bar ɗakin mahaifin Adeeb cikin ruɗani.

Washe gari da safe fattu ta tashi da wani irin matsanancin ciwon mara,sai kuka take tana riƙe da cikinta.

Tsohuwa salima nata rarrashinta tare da bata haƙuri,dan tana tunanin period me zai yiwa fattun.

Sosai fattu ke jin mugun ciwon mara,sai murƙususu take cike da azaba tana kiran ” Wayyo Hammana zan mutu “

Wani irin amai ne ya yunkuro mata,da gudu ta mike ,da nufin zuwa toilet ,saidai taku daya biyu, jiri  ya kwasheta ta tafi luuuuuuuu tayi kasa…..

Karanta Littafin>>> Matar Hariji Page 21-30 Hot Romantic Novel 

Masu karatu  masoya,ina godiya da addu’ar ku gareni ,kuma jiki alhamdulillah naji sauƙin sosai ,

Na gode sosai da kulawa,

Much luv sosai da sosai.

Mrs babi ce 💘💘💘

Share and comments 

Fisabilillah.

More comments 

More typing.

Back to top button