Hausa novels

Ruwan Zuma Page 23 Hausa Novel

(23) Ko da Haydar ya shigo ya samu Laila tana hawaye tsayawa yayi daga bakin k’ofa yana kallonta domin bai san dalilin kukanta ba. Zuciyarsa ce ta karaya na wannan hali da suka tsinci kansu a ciki. Laila ta d’ago ta dubeshi tana share hawayen fuskarta tace, “Dama tun farko burinka kenan ka auri babbar mace?�? “Ban gane ba.�? Ya iso cikin falon ya zauna a gefenta cikin d’aurewar kai. “Duba nan.�? Ta mik’a mishi wayarta ya kar6a ya fara karantawa. A shekarar daya gabata ne wato 2019 a shafin Twitter wata babbar mata ta auri saurayi k’asa da shekarunta mutane suke ta kushewa, wasu sun maida hakan abun dariya wasu kuma suna ganin hakan bai dace ba, a cewarsu yafi kamata mace ta auri namijin daya fita a shekaru saboda wasu dalilansu. A cikin wannan muhawaran ne Haydar shima ya tsoma baki yake cewa, ‘Ni banga abun kushewa a nan ba, shi yaga mata yace yana so kuma ya aureta. Kowanne mutum da ra’ayinsa, bro Allah ya baku zaman lafiya.�? A k’asa abokinsa Nasir ke cewa, ‘Kai kam dama tun farko kafi son matan da suka girmeka. Ko In tayaka neman sugar mummy ne ta riritaka Alhaji?�? Haydar yace, ‘I hope to find one.. bana son yara ne kawai, I dislike their inexperience and lack of understanding of life. Sai ya zama kamar kana raising yaro ne ana ta maka shirme a gida.�? A nan hirar ya k’are ya ajiye mata wayan a gefenta. “Yes burina kenan saboda bana son yarinta ko kad’an. �? Ya bata amsa yana kallon cikin idanunta domin ta yarda dashi. “Kenan tun farkon had’uwarmu k’udurinka kenan?�? Girgiza kai yayi yace, “Ganinki na farko da nayi nasan kin fi k’arfina kuma ban kawo hakan a raina ba ko kad’an. A zaman da muka yi tare ne na fad’a sonki ba tare da nayi shawara da zuciyata ba.�? Shiru suka yi na wasu sakanni sannan tace, “Ka duba sauran links d’in da aka turo mini ka shiga kaga abunda aka fad’a a kanmu.�? Haydar ya d’auki wayar ya duba yaga har yayi locking kansa, “Me password d’in?�? Ya tambayeta. Daburcewa tayi na ‘yan sakanni kamar mara gaskiya tace, “Aliyu. Wani Aliyu? Shine bai sani ba kuma bashi da niyyar tambayanta domin bashi bane a gabansu ba. Yana bud’e wayar ya shiga text messages d’inta ya duba links d’in da aka turo yabi d’aya bayan d’aya yana karanta mummunan sharrin da aka musu, ana had’awa tare da hotunansu da aka d’auka a kwanakin baya wanda take bashi labari. Yana karantawa ransa na 6aci zuciyarsa na k’una tamkar zata fashe saboda k’azafin zina da aka musu tare da sharri kala-kala. ‘Gulma da d’umi-d’uminta. Wannan shine Aliyu Haydar matashi d’an shekara ashirin da biyar da aka kamashi turmi da ta6arya tare da Hajiya Laila mai shekara arba’in kuma mai zaman kanta. Sakamakon kamasu da aka yi ne Alhaji Abdul CEO Lu’a Ventures ya fasa aurenta bayan ya samu labarin cewa tana can tare da Haydar a wani Hotel da sunan sun je yiwa juna bankwana, kenan ba yau suka fara aikata alfasha ba. Saboda gudun tonon asiri yasa kaninta da yayanta suka d’aura mata aure da yaron ba tare da saninta ba. “Waya juya zancen nan haka Haydar? Wa yake son 6ata mini suna ne? Me na yiwa mutane?�? Tayi tambayar idanunta na tara wasu hawayen tana jin bak’in ciki mara misaltuwa. “Yanzu kowa yaga wannan abun, abokan kasuwancina, ‘yan uwana har da surkina da yake ganin girmana yanzu shima zai fara wasiwasi a kaina. Wallahi ban ta6a zina ba, ban ta6a yinta ba Haydar.�? Haydar kwantar da kanshi yayi saman kujera ya runtse idanunshi yana maimaita sharrin da aka musu tare da maganganun mutane, wanda wasu sun yarda da hakan har suna tsine musu wasu kuma fatan shiriya kawai suka musu. Ya za’ayi ya goge wannan abun daya faru ya zama tamkar ba’a ta6a yi ba? Yasan za’a soki aurensu tunda yana ganin irin hakan a social media sau da yawa, amma bai ta6a kawowa a ransa za’a jefesu da k’azafin zina ba. D’ago da kanshi yayi yaga ta d’auki wayar tana cigaba da karanta sak’onnin mutanen yayi saurin kar6ar wayar ya ajiyeta a gefe. Hakan da yayi yasa hankalinta ya dawo kanshi tana kallonshi cikin mamaki. Gyara zamanshi yayi ya dubeta cikin nitsuwa yace, “Laila.�? Kamar baza ta amsa ba amma ganin yanda ya nitsu sai taga ya mata kwarjini ainun tamkar ba Haydar d’in da take yiwa kallon yaro ba. “Na’am.�? Ta amsa tana kawar da idanunta gefe. “Tambayarki zanyi ina son ki bani amsoshinsu. Kin ji?�? Gyad’a mishi kai tayi yace, “Good. Shin a cikin duniyan nan akwai wanda ba’a ta6a zaginshi ba?�? “Babu.�? “Shin a cikin mutanen da kika sani kike tare dasu kuke harkokin yau da kullum zaki iya bugan k’irji kice dukkansu sonki suke yi na gaskiya?�? “A’a.�? Ta fad’i hakan a sanyaye tana jiran taji ina maganarshi ta dosa. “Shin d’an Adam yana iya kaucewa k’addararshi ko kuma ya rayu ba tare da Allah ya jarabceshi ba?�? Wanna karon girgiza kai tayi tana jin wani nauyi da yake kanta na raguwa, domin ita take yiwa mutane tuni da hakan amma yau gashi ita ake yiwa tuni. “Shin kin ta6a aikata abunda ake zarginki a kai?�? “Ban ta6a ba.�? “Kenan bai kamata ki damu har kiyi kuka da idanunki don wani bawa yaga daman miki sharri ba. Kowanne mutum da kika gani a duniya yana tafiya ne da tashi jarabawar, sannan komin mulkin mutum, iliminsa, kyawunsa, arzikinsa ko sa6aninsu ba zai ta6a kaucewa maganan mutane ba sai an samu wanda zasu zageshi, koda kuwa tunda yazo duniya bai ta6a aikata laifi ba. Kiyi duba ga Annabi Muhammad SAW masoyin Allah, wanda aka yi duniya dominsa amma a hakan wasu suna zaginsa suna binshi da sharri, har aka samu masu iya jifanshi da duwatsu. Ki fad’a mini idan har shi aka iya mishi haka mu kuma su waye da zamu kaucewa hakan? A tunaninki Allah ba zai kwato mana hakkinmu bane a kan sharrin da aka mana? Ko kuma gaskiya ba zata fito ba duk daren dad’ewa?�? Ya kamo hannunta wanda yau ne karon farko da ya fara yin hakan a rayuwarsa. Wannan lokacin kallonshi take yi cikin yadda da maganganunsa ba tare da ta mance ko kalma d’aya ba. “A hakan Laila ba’a rasa wanda suka k’aryata sharrin da aka mana ba suka fad’i gaskiya ba, kamar yanda na wancan mutanen ya wuce har aka daina maganarsu muma watarana haka za’a daina yayin maganarmu kuma zai zama tamkar ba’a yi ba. Mutanen social media haka suka zama, kowa ya 6uya a bayan keyboard ne yana fad’in k’arya da gaskiya don kawai ya jawo hankalin mutane kanshi, ko kuma don wata manufa tashi ta daban. Abunda zakiyi ki karya guiwar masu yin hakan shine ki nuna hakan bai dameki ba, ki nuna musu kin fi k’arfin su fad’i k’arya a kanki har yayi affecting rayuwarki. Ke ba yarinya bace Laila, kina da experience na rayuwa sosai, kiyi amfani da hakan sannan ki barwa Allah komai, shi zai tona asirin duk mai yin hakan. Kina jina?�? Gyad’a mishi kai tayi tana zare hannunta daga nashi kana ta share sauran hawayen dake fuskarta tana jin k’arfi a jikinta da kuma cikin zuciyarta gabad’aya. “Nagode.�? Kawai ta iya furtawa tana matsawa kad’an daga gurinshi. Hakan da tayi bai mishi dad’i ba domin ya lura kamar bata son ya ta6ata ne. Ko dai ta manta shi mijinta ne a yanzu? “Waya turo miki links d’in?�? Ya tambayeta yana maida kanshi jikin kujeran domin yaji alamar maganin da yasha ya fara aiki. “Ban san waye bane kuma bani da numbern. Ina gwada kiran layin Abul naga an turo mini message d’in, ni bana ma Twitter amma nabi ta link d’in nayi downloading.�? Haydar gyara zamanshi yayi ya k’ara d’aukan wayar ya shiga True caller ya duba sunan mai numbern yaga suna ne wanda bai gane ba, koda ya nuna mata itama cewa tayi bata san me sunan ba. “Ki basu kwana biyu zasu yi su gaji su daina. Zan bincika duk wanda yayi hakan domin d’aukan pictures d’inmu da ake yi har ana editing bai mini ba.�? “Ka bari kawai ba sai ka bincika ba, koma waye ne ya yiwa kanshi.�? Tayi saurin katseshi domin bata son yaje ya bincika ya gane Abul ne yake mata haka ko kuma Madu. Ina zata kai wannan kayan kunyan ace duk wannan bak’in cikin na jikinta ne ya aikata musu haka? Haydar da baya ganewa jikinsa ya tashi tsaye yana bata baya yace, “Ina band’aki? Zan yi wanka.�? Laila ta mik’e tsaye tana cewa, “Sorry, muje.�? Tayi hanyar side d’in Mas’ud amma tana k’ok’arin bud’ewa taji k’ofar a gark’ame. Ta k’ara jijjiga k’ofar ta gane key aka saka aka kulle. To waye ya kulle? Shi kuma Haydar bai zauna ba illa ma kawar da kanshi da yayi ga barin kallonta, saboda kallonta kad’ai na k’ara jawo masa matsala. D’akin Abul da Sabrin duk ta gwada bud’ewa amma a rufe, a nan ta tabbatar wannan aikin Mas’ud ne. Me yake nufi da hakan? Shin bai san halin da suke ciki bane da zai yi tunanin had’asu a d’aki d’aya? Wayarta ta d’auko tayi dialing numbernshi amma a kashe. Extra keys d’in d’akunansu kaf a side d’in Mas’ud d’in ake ajiyewa incase wani ya jefar da nashi. Ya zata yi? Haydar ta har lokacin yana tsaye ya kasa gaba ko baya yace, “Lafiya?�? “Muje d’akina, sauran d’akunan a kulle suke.�? Da haka tayi gaba yabi bayanta da kallo yana jin tamkar ya fasa ihu. Mas’ud da Hamidu kuma tun d’azu yake tunanin me zai musu ya rama abunda suka mishi idan sun had’u gaba saboda sun cuceshi. Sai da ya tabbatar ta shiga d’akin sannan ya bi bayanta yana doro tamkar mai ciwon baya. Yana shiga ya samu ta kwaso wasu kayanta a cikin band’akin ta jefasu a ciki wardrobe d’inta da sauri. Halin da yake ciki yasa bai ma lura da yanayin d’akin nata ba ya tasamma cikin band’akin ba tare da ya bari ta kalleshi da kyau ba. Yana shiga ya fara kwa6e kayan jikinshi kana ya sakarwa kanshi ruwan sanyi na minti biyu kafin nan yayi wanka. Ya jima tsaye ruwa na dukanshi sannan ya kashe shower ya nemi towel ya d’aura a k’ugunshi kana ya fito. A cikin d’akin ya samu Laila ta kawo mishi jakarshi har ta shimfid’a k’aton bargo a k’asa ta ajiye pillow a kai. Tashin da zata yi ta hangoshi a bakin band’aki ya hard’e hannayensa a saman k’irjinsa yana mata kallon ‘me kike nufi�?? Zuciyarta ce ta buga da k’arfi ta nemi nitsuwarta ta rasa domin ba k’aramin kyau da kwarjini ya mata. Da sauri ta fita falo ta bashi guri domin ya kimtsa, a can falon kuma wayarta ta d’auka ta gwada kiran Abul amma bai shiga ba wanda dama hakan ta san zai faru. Sai da ta tabbatar Haydar ya gama abunda zai yi sannan ta shiga d’akin da sallamarta ya amsa, zaune yake a kan kujeran dressing mirror yana sanye da jallabiya fara sol wacce tayi masa kyau ba kad’an ba a idanunta. Wai me yake damunta ne? Ta yiwa kanta tambayar tana kawar da kanta gefe ta bud’e wardrobe tana d’auko kayan baccin da zata saka. “Kinyi regretting aurena?�? A bazata ta jiyo tambayar wanda yasa tayi saurin juyowa tana kallonshi a razane. Tashi yayi ya tako har gurinta kana ya tsaya a gabanta ya k’ara cewa, “Kinyi regretting aurena? Zaki iya za6ana a karo na biyu a rayuwarki?�? “Haydar…�? Zata fara magana ya katseta. “Just answer me. Ina son sanin matsayina ne a gurinki domin na lura tamkar ba aure kika d’auki aurenmu ba. Kamar an miki dole ne alhali ke da kanki kika yi choosing d’ina.�? “Bana dana sanin saninka ko aurenka Haydar, but halin da nake ciki a yanzu ina buk’atar space domin abubuwan da suka faru a yau sun yi mini nauyi a zuciyata. Ka daina tunanin hakan a zuciyarka.�? Ta k’arishe maganan tana ra6ewa ta gefenshi zata wuce ya kamo hannunta. “Kenan kina sona?�? Yayi mata tambayar yana kallon kwayar idanunta. “Daa bana sonka da bazan amince in aureka ba.�? “Then say it.�? Ya k’ara k’arfin rik’on daya mata. Laila tabi hannunsu da kallo yanayinta na canjawa, damuwarta na barin zuciyarta ta d’ago ido tace, “Yes, I’m in love with you. Shikenan?�? Haydar dawo da ita yayi gabansa murmushi na su6ucewa a bakinsa a karon farko tun da ya shigo gidan amaryar tasa. “I’m in love with you too.�? Ya fad’i hakan yana had’e goshinsu guri guda yana lumshe idanunsa tamkar mai jin baccin. “Haydar.�? Ta kira sunanshi cikin kwa6a amma a hankali jin ya sumbaci kunnenta tare da wuyanta. “Shshh.�? Yayi shushing d’inta yana jawota jikinshi yayi hugging d’inta tsamm tamkar za’a kwace mishi ita. Laila bata kwace jikinta ba domin tasan yana buk’atar ko sau d’aya ne ya gane cewa da gaske ya aureta ba mafarki yake yi ba. Ganin labarin na neman canja salo yasa tayi saurin barin jikinshi ta shige band’aki jikinta na rawa, duk inda ya kai hannunsa a jikinta sai da tabi ta ta6a tana jin zuciyarta na tsananta bugawa, wai yau ita ce d’aki d’aya da Haydar a matsayin mijinta? Kenan mafarkan da tayi kwanaki zasu iya zama gaskiya? Ta jima a cikin band’akin sannan tayi wanka ta saka silk nighty d’inta ta fito. Turaren humra da bata rabo da sawa ta shafawa jikinta sannan ta fita falo zuwa gurin Haydar jin yayi kiranta. Wai da gaske ta zama matar Haydar? A kan sallaya ta sameshi kamar wanda ya idar da sallah yace, “Kiyi alwala muyi sallah.�? D’an k’aramin murmushi tayi tana mamakin k’arfin halinshi, haka ta koma d’aki ta d’auko hijabinta tare da sallaya suka yi sallah, a ranta kuma so take ta bashi wannan daman da zai ji ‘eh shima Ango ne ko da kuwa wani abun ba zai shiga tsakaninsu ba. Bayan sun idar ya juyo ya mata addu’o’i ida dai kanta a k’asa, tama rasa me take feeling a lokacin a cikin kunya ko jindad’in auren wanda take so a karo na biyu. Bayan ya gama addu’o’in ya jawo ledar daya shigo da ita ya bud’e musu yana cewa, “Naji ance yau wuni kika yi baki ci abinci ba.�? “Bana jin cin komai ne.�? Ta bashi amsa tana yamutsa fuska. Hakan da tayi kuwa kyau ta masa ba kad’an ba, murmushi yayi mai k’ayatarwa yace, “So cute.�? Dariya sosai Laila tayi shi kuma ya tallafe ha6arshi yana kallonta tamkar ta zama tv yana jin dad’i a ransa daya iya kore mata damuwarta har gashi tana dariya. Ganin ya k’ura mata ido ne yasa Laila ta tsagaita dariyar tace, “Kana da abun dariya.�? “Don nace kinyi kyau?�? “Haydar.�? Ta kwa6eshi a karo na ba adadi. “Naga alama sunan yana miki dad’i.�? Ya fad’i hakan cikin zolaya. Murmushi tayi tana tuno maganganun Ummii wanda su suke k’ara nitsar da ita akan aurenta da Haydar Idan ta tuna. Minti kad’an da haka suka rufe kazar Laila ta d’auka tayi kitchen da ita shima Haydar yabi bayanta. A can ya wanke bakinsa tace, “A nan kayi alwala ko?�? “Yes. Na lek’a d’akin na samu kina ta shafe-shafe sai na fito.�? Ya bata amsa yana kashe wutan kitchen d’in suka fito. Juyowa Laila tayi tana zaro idanunta, shi kuma gaba yayi ya barta a gurin yana murmushin mugunta. “Kace mini wasa kake yi.�? “Ni da matata. Menene a ciki?�? Ya shige d’aki ya barta a gurin baki a bud’e. Sai data kashe wutan falon sannan ta shiga d’akin ta sameshi a kan shinfid’arsa yana danna wayarsa yana murmushi. Wani irin kishi ne ya tsaya mata a makwogoro da tayi tunanin ko da wata mace yake chatting. Rai a 6ace tazo ta wuceshi ta hau kan gadonta tare da kashe wutan d’akin gaba d’aya tana jin d’aci a harshenta. “Laila.�? Ya kira sunanta cikin duhu. “Na’am.�? “Nifa ban saba kwana a k’asa ba.�? Ya fad’i hakan yana tashi tsaye ya hau kan gadon tare da jawota jikinshi. A tare suka yi ajiyar zuciya kana ta fara k’ok’arin barin jikinshi ya tsayar da ita yace, “Just in jiki a jikina nake so and nothing more.

Mum Fateey 👌

Back to top button