Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 121 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

 

Story And written By

*Hafsat Bature*

 

Not edited

 

Ammi ta jima zaune a wurinta,kafin daga bisani tayi mata sallama ta fita,A hankali ta gyara kwanciyarta samam gadon,lumshe idanuwanta tayi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata abunda ya faru lokacin Da Sgr Ya farmaketa,wani irin Æ™ululun baÆ™in ciki ne ya tokare mata maÆ™oshinta,a irin kallon da take yi mashi yanzu Mara tausayi mara Imani,sanna kuma ba sonta yake yi ba, Jikinta yake so,shiyasa yake yi mata komai da mugunta don yaga yaÆ™arar da ita,kafin Ya koma U.s,tunda yasan rabasu Za’ayi,

Yinin ranar tana kwance samn gadon,Anan Abba ya same ta,Yayi mata ya jiki,da kuma ban haÆ™urin abunda Sgr yayi mata,taji daÉ—in yadda Abba Ya nuna 6acin ranshi,kuma yace duk abunda takeso Yanzu shi za’ayi,bayan fitar Abba,Su jahad da Amrish suka dawo cikin É—akin,Yanzu kowa Ya Zuba Ido Yana jira dawowar SGR,

Wuraren Ƙarfe shida na mare ce,Omar Ya fito daga cikin toilet,Jikin shi sanye da Jallabiya,Yana Æ™oÆ™arin Zama gefen Gadon,Wayar shi dake ajiye gaban mirror ta soma ringing,miÆ™ewa Yayi izuwa gaban madubin ya tsaya,Hannu yasa ya É—auki wayar,Ya duba me kiran nash,A hankali Ya furta Sunanshi”Rafayet,”kafin ya É—aga kiran tare da manna wayar a kunnashi,
Tunkafin yayi magana,Sgr ya ambaci sunanshi”Omar,”cikin sanyin murya,tamkar bata shi ba,
Ajiyar zuciya Omar ya sauke”Rafayet,Meyasa ka tafi ka barni?Nasan ban kyauta maka ba,dana barka a wannan yanayin,Amma banji daÉ—in tafiyar da kayi ba,”
“Bani da za6ine Omar,bansan ya zanyi ba,banyi tunanin zaka É—aga kira na ba,Saboda kowa fushi yake yi dani,”
“Dole suyi fushi dakai,abunda kayi sam bai dace ba rafayet,duk in na tuna cewa É—an uwanane ya aikata hakan sai inji É—aci araina,why Rafayet?
“Omar,I ave regretted,i hate my self,ban kyautawa kowa ba,Zan ba kowa hakuri,In yi nesa da kowa,”
Waɗannan kalaman na Sgr ba ƙaramin ta6a mashi zuciya su kayi ba,tuni Ya karaya,
“Am Sorry Nayi maka laifi na É—auko Sehrish batare da saninka ba,”
“Don’t worry about that,Nima nayi niyar na dawo da ita gida,just ina fargabar abunda zai biyo bayane,”
“Rafayet,ka dawo gida kawai,Ka nemi afwar Abba da uncle,nasan zasu sauko ne,”.  .
“Its Okey,Zan dawo,amma sai zuwa sha biyu na dare”.  .
“Shikenan,i will be waiting for u,Ko bacci bazan bari ya É—aukeni ba,har sai naga É—an uwana,Nayi hugging É—insa ajikina,”
Sun jima suna waya da juna,Kafin daga bisani su kayi sallama,yana ajiye wayar gaban mirror,Hosana ta bango ƙopar ɗakin nashi,cak ya tsaya yana kallonta ta cikin madubi,doguwar rigace ajikinta mai baza daga ƙasa,babu mayafi akanta,da alama gayu akayi mashi,ta sauko da Curly hair ɗinta,An shafa jan baki ja,

A tsiyace ta toge tare da ruÆ™e qugunta”Ya Omar,”
A sukwane Ya juyo yana kallonta,from head to toe,Ba Æ™aramin kyau tayi mashi ba,cikin sanyin Murya ya ambaci sunanta”Hosana,”
MurguÉ—a mashi baki tayi,Yace”To fa!Halan wani laifin nayi,”
ÆŠaga mashi kai tayi alamar eh,
Ashagwa6e tace”Ya Omar wai dagaske idan aka É—aura mana aure bada ni zaka tafi U.s ba,Wai a gida zaka barni,”?
“Wurin wa kika ji hakan”?
Bubbuga Æ™afarta tayi”Nidai ka amsa mun tambayata,”
Jinjina kanshi yayi tare dacewa”Eh,Anan zan barki,amma zan dinga zuwa duk Æ™arshen…..  ..’
Bai ƙarasa maganar ba saboda wani kallo da yaga tana jifarshi dashi,kallon baka isa ba,
“Ya omar ae wlh baka isa ba,Ko kana so ko ba kaso,Dole ne duk in da zaka tafi mu tafi tare,Ƙafata Æ™afarka,Nida kai mutu karaba takalmin kaza,”ta Æ™arasa maganar tana jefarshi da harara,
“Oh,a haka zan tafi dake can?Kina murguÉ—a mun baki,Sai kace wani tsaranki,Nifa in kika takuramin Allah,Zan fasa auren ne,”
Turo baki tayi”Yo he me?Ka fasa,Kai kasani wlh ya omar,Maza rubibina suke yi saboda kyau na,Don ma dai kawai ina sonka yasa nake kulaka,”
Ƙumshe dariya yayi acikin bakinsa,don baisan tayi tunanin ko wasa yake yi mata,juya mata baya yayi batare daya ƙara tanka mata ba,

Yayi tunanin zata fita daga É—akinne Amma sai yaga ta tattare bazar rigarta,ta haye saman gadonshi can tsakiyarshi ta baje tana kallon ceilling,
Girgiza kai yayi”Oh ni Omar na É—ebo ruwan dafa kaina,”Yayi maganar acikin zuciyarshi,

“Ya Omar”ta ambaci sunanshi yayin da idanuwanta ke kallon ceilling kamar me nazarin wani abu,
“Na’am,”ya amsa mata,

“Ya Omar,idan aka É—aura auren kai kana America,Ni ina a nigeria,To wai taya za’ae in samu Ciki,”
Rass Yaji gabanshi Ya faÉ—i,A firgice ya juyo yana kallonta,Hankalinta kwance tayi mashi tambayar,Abun ya É—aure mashi kai,mamaki ne ya kamashi,
“Ke!Waya faÉ—a maki cewa dole sai muna atare zaki samu ciki,”?
“Yo oho,Nidai nasani ae,Ko kaza sai da zakara take samun cici,Kaga kenan,Nima sai kana tare dani zan…..”bata Æ™arasa maganar ba,da gudun gaske ta turo daga saman gadon ta nufi hanyar fita,A hanzarce ya damÆ™o hannunta,Ya juyo da ita,a jikin bangon yayi mata rumfa,sai faman zazzare mashi manyan idanuwanta takeyi,
“Saboda rashin gaskiya,daga ganin na nufoki,kika watsa da gudu ko”?
Runtse idanuwanta tayi”Ya omar,wai menene haka,kalli yadda ka takure,”
“So nake ki faÉ—amun,Wayake koya maki waÉ—annan maganganun da kike gaya min,ko kunyata bakya ji”
Turo baki tayi”Babu kowa,”
Sam bai yarda da ita ba,A matsayinta name ta6in hankali baya tunanin zata Iya sanin wannan,Sai dai ko gaya mata akeyi ko kuma tana kallon a wayarta,
“Kiji tsoron Allah,ki faÉ—amun gaskiya,taya akai kikasan cewa dole sai muna atare da juna zaki samu ciki”
A Æ™ule tace”Nifa babu kowa,”
Jinjina kanshi yayi”where’s ur phone”?
“Tana a É—akinmu,”
“Ok,je ki É—aukomin ita”

“Toh,”ta amsa mashi tare da juyawa da gudu taje É—akinsu ta dauko wayar ta dawo bedroom É—inshi Ta miÆ™a mashi”Gata,”
“Cire pass word din”
Ashagwa6e tace”Sunanka ne,”
Ta6e baki ya ɗanyi,Acikin Zuciyarshi kuwa ba ƙaramin daɗi yaji ba,
Yana rubuta sunanshi Omar,Nan take pass word É—in Ya cire,
Bincike yashiga yi mata acikin wayar,Gallery ya fara shiga kaf ya duba videos É—in dake a wurin,baiga abunda yake zargi ba,ita kuwa sai faman sakin murmushi takeyi,
É—agowa yayi suka haÉ—a ido da ita”Kin gogesu ko”?
“`Wai me kake magana akai Ya omar,”
Moving yayi kusa da ita,lalla6ata ya shiga yi”Pls My hosana,Ki fadamun gaskiya,Bazan maki komai ba,A ina kike sanin abubuwan da kike faÉ—amun,”?
Kafin ta bashi amsa,aka kwankwaso ƙopar ɗakin,
“Omar,zoka buÉ—e mun Æ™opa,”muryar abbansu ce,da sauri ya saki hosana,ya Æ™arasa bakin Æ™opar ya bude mashi,
“Abba,”omar ya kira sunanshi,
“Kunyi waya da rafayet”?fuskarshi da alamun damuwa yayi maganar,
Omar yace”eh,munyi magana dashi,”
“Dan Allah omar,kasan yadda za’ae ya dawo gida,”
Murmushi Omar ya É—an saki kafin yace”Abba,kana missing dinshi ne ko,”
“Omar bazaka gane ba,inaso ya dawo ne,”tun da ya shigo bai lura da hosana ba,don tuni ta la6e bayan labule,kamar wata mara gaskiya,
“In sha Allah zai dawo abba,Yace mun around 12 na dare zai shigo gidan,”
Ajiyar zuciya abba ya sauke tare da cewa”Allah ya kawoshi lafiya,Naga an fara kiran Magrib,Ka hanzarta shiryawa mu tafi masallaci,”
Amsa mashi yayi da toh,Bayan fitar abba,Shaf shaf Ya shiga toilet Ya ɗauro alwala,Kafin Ya fito tuni hosana ta bar ɗakin,Dama haushinshi take ji ya tsareta da tambayoyi kamar wata ƙaramar yarinya,acewarta

Wuraren Æ™arfe 10 na dare,Wayar jahad ta soma ringing,a lokacin har Bacci Ya fara É—aukarta,Tana kwance gefen Sehrish,Hosana dake bayanta tuni bacci yayi awon gaba da ita,Oummansu kuwa na zaune saman darduma tana karatun qur’ani,

A saman mattress ɗin ta ajiye wayar,Bayan ta ɗauketa ta duba mai kiranta Sunan Fawan ne ya bayyana akan screen ɗin wayar tayi matuƙar yin mamakin ganin kiranshi,

Picking call É—in tayi tare da kara wayar a kunnanta,
“Assalamu Alaikum”
On the other hand,Fawan ya amsa mata”Wa’alaikum Salam,Ya kike”?
“Lafiyalou,”
“Sorry fa,bansani ba ko na tashe ki daga bacci,naji muryarki kamar kin fara ko”?
Murmushi ta É—anyi kamar tana agabanshi”Hakane na fara amma banyi nisa ba,”
“Dama junaid ne,ke son magana dake,ya bi ya ishe ni ya hanani sakat,Kinsan yanzu babu waya a hannunshi,Ina fa bacci sai gashi har bedroom É—ina,wai in kira mashi juliet dinshi,Sai kace baisan hanyar zuciya É—akinku ba”
Wani irin farin ciki ne Ya lullu6e Jahad,a hanzarce ta miƙe daga zaune,
“Gashi ku gaisa”jim kaÉ—an taji muryar junaid,
“My juliet,”batasan lokacin da ta saki murmushi ba,
“Na’am My romeo,Dama kana tunawa dani,”?
“Yeah,ae bakison zuwa duba jikina,shiyasa nake fushi dake,”
“Kaine ka juyamun baya,tun rana ta farko da nazo wurinka,Ka nuna tamkar baka sanni ba,abun ya tsayamun araina,rana ta biyu dana zo,kaÆ™i kallona,rana ta uku dana zo,Kana yin tozali ka rufe idanuwanka,kamar kaga wani mugun abu,”
Sai da takai Æ™arshen maganarta,Sannan yace”Am sorry,just forget about it,I really missed u,In ba damuwa inason ganinki yanzu,”
Da sauri ta kalli agogon bangon dakin
“Ƙarfe goma fa?Kuma oumma na kallona bansan ko zata barni in fito ba,”
“Idan ta tambayeki,Ki sanar da ita cewa,Mijinki ne ke kira,Ae an biya sadaki,”
Jin wannan maganar yasa jahad ta fashe da dariya,Har oummansu dake karatun qur’ani saman darduma sai da ta É—ago ta kalleta,
“still baka canza ba,kana nan a romeo É—in dana sanka,”
“Of course,I will be waiting for u pls,”yana kai Æ™arshen maganarshi yayi rejecting É—in kiran,
Ajiye wayar tayi,A hankali ta sauko da ƙafafunta ƙasa,Jikinta na sanye cikin night gown pink colour,ta ɗaure gashin kanta da ribbom,
Sai da ta miƙe tsaye sannan ta soma tunanin abunda zata ce ma Oumma,
Gaban wadrobe taje ta bude ta lalubo hijab Ash colour ta zura ajikinta,saɗaf saɗaf Ta nufi hanyar fita,jin Oummansu Ta janyo doguwar aya,tasan bazata katse taba,balle tayi mata magana,da sauri ta buɗe ƙopar ɗakin ta fuce, babban falon ta nufa tana ta ƴan waige waige,duk ta ƙosa tayi tozali dashi,

A hankali Yake saukowa downstairs,Jikinshi na sanye cikin sleeping dress dinshi,riga da wando,Yayi haske sosai,Ga wani irin kyau daya ƙara,kwantacciyar sumar kanshi tayi tsayi sosai,Saboda bata samu aski ba,Gashin ya fara taruwa,

Hannayenshi duka biyun na acikin trouser pocket dinsa,A hankali ya Æ™arasa saukowa cikin palourn,Kaitsaye ya nufe ba,kasa janye idanuwanta tayi daga kallonshi,Sai da ya Æ™araso kusa da ita,Suna fuskantar Juna,tun daga Æ™asa har sama yake kallonta,lokaci guda suka sakarwa juna Æ™ayataccen murmushi,dimples din kowannansu Ya lotsa,zunzurutun kyau abun ba’a magana,
Miƙa mata hannunshi yayi,ta zura nata asaman nashi,Ya ruƙe hannun sosai acikin nashi,wani irin daddaɗan ƙamshi ke fita daga jikinshi,
“Mommy tace mun zaka zo wurina muyi shawara ko”?
“Eh hakane,tace daga yanzu in zanyi shawara dake yakamata nayi,”
Ba ƙaramin daɗin maganar nan taji ba,
“Tunani me kyau,Banaso wani ya ganmu anan,Kunya nake ji,”
“Zan jiraki a bakin swimming pool,Ki kawo mana Coffee,Yadda zamu ji daÉ—in tattaunawa,”
Zaro ido ta É—anyi”Dare fa yayi har 10,ko baka duba agogo bane,”
“I know,ae ba jimawa zamuyi ba,Just 30 mins,”
“Shikenan yanzu xan zo,”takai Æ™arashen maganar tare da juyawa da sauri ta nufi kitchen,
Fitowa daga falon yayi kaitsaye Ya wuce bakin pool din,A ɗaya daga cikin ƙayatatun kujerun dake a wurin Ya xauma yana jiran zuwanta,wata irin iske ce mai daɗin gaske take kaɗawa a wurin,

Badajimawa ba,Jahad ta dawo hannunta É—auke da Cup guda biyu ta ajiyesu saman table din gabanshi,Kafin ta zauna itama,sunji daÉ—in yanayin sosai suna shan Coffee dinsu suna fira,Tsawon 30 minutse kafin Suka bar wurin Kowa ya koma É—akinshi,

Wuraren ƙarfe Goma Sha biyu na dare,Motar Sgr ta shararo da gudun gaske izuwa cikin gidan,Bayan Amstrong yayi parking ɗinta Ya fito tare da zagayawa Ya buɗe mashi mota,A hankali Ya zuro ƙafarshi ɗaya kafin Ya ƙarasa fitowa waje,

Jikinshi na sanye da jallabiyar nan daya fita da ita a lokacin da ya É—auki Sehrish,hannunshi na ruÆ™e da leda fara mai É—auke da sunan asibitin Dr harriet,Sallama yayi ma Amstrong kafin Ya nufi cikin gidan,Baisamu kowa a palourn ba,kaitsaye ya nufi upstairs,A hanzarce Ya fada part É—inshi,A rufe ya samu Æ™opar palourn,Hannu yasa ya turata,Sannan ya shiga daga ciki,ko’ina fess an gyara mashi,Sa6anin yadda ya tafi tabarshi,Bedroom É—inshi ya shiga nan ma ya tarass An gyarashi,yayi mamaki sosai,bai ta6a tunanin za’a samu wanda zai kawar da Æ™azantar da ya bari saman gadon ba,Ajiyar zuciya ya sauke,Kafin ya Æ™arasa ciki,toilet Ya shiga,After Some minutes Ya fito daga wanka,Jikinshi sanye cikin bathrobe,A gaban mirror ya tsaya yana kallon fuskarshi,Bakomai yake fargababa,face haÉ—uwarshi da Abbansu,Da kuma Uncle abusufyan,yayi danasani sosai,Baisan da wani ido zasu kalleshi ba,zama yayi saman front chair din madubin,Ya zabga tagumi da hannu É—aya,ya damu sosai akan son sanin wani hali Sehrish take ciki,taci abinci ko bata ci ba,ga allurorinta da bai kammala yi mata ba,hada medicine dinta,Duk yau batasha ba,

Yana cikin wannan zancen zucin,Omar ya faɗo ɗakin nashi,ta cikin mirror ya hangoshi,farin cikine Ya lullu6eshi,Da sauri ya miƙe tare da juyawa ya nufeshi,Hankalin Omar ya ɗan tashi ganin yadda Sgr ya canza,Yayi rama,ya kuma yi haske sosai,kamar ka ta6a jini ya fito,yana ƙarasowa suka rungume juna sosai,kamar zasu haɗiye kawunansu,
“Nayi missing dinka sosai,É—an uwana nakaina,”Omar ne yayi maganar,Yayin da hannunshi ke abayan rafayet yana dan bubbugashi,
Tun da ya kwantar da kanshi a kafadar Omar,Jikinshi yayi sanyi sosai,Hawaye suka cicciko tab a idanuwanshi,sam ya kasa buÉ—e baki yayi magana,Shi kaÉ—ai yasan halin da yake ciki,
ÆŠago dashi Omar yayi”Rafayet”ya ambaci sunanshi tare da kai hannunshi saman fuskarshi,
“Ka rame sosai,Duk ka canza,Kodai atare kukayi jinyar,”?
“I don’t ave peace of mind,ina cikin matsanancin tashin hankali Omar,na damu sosai,bansan ya zanyi ba,”
Lallashinshi Omar yayi tare da janyo shi suka zauna gefen gadonshi,Sosai ya shiga yi mashi nasiha akan abunda ya aikata,a Æ™arshe yace”Tun wuri Rafayet,Kaje ka samu abba da uncle abusufyan,ka nemi yafiyarsu,Sannan ka sanar dasu cewa Kana son matarka,Kuma zaka tafi da ita u.s ba amatsayin mai aiki ba,idan har kayi wannan shikenan zaka zauna Lafiya,Nima kuma zan samu kwanciyar hankali,”
Muryarshi asanyaye yace”Shikenan,zanyi hakan amma nasan zaiyi wuya uncle ya yafe mun,”
“Zai yafe maka,ka jaraba yin hakan,Yanzu ka tashi ka shirya ka fara zuwa wurin Abba,Nasan baiyi bacci ba,”
Amsa mashi yayi da toh,duk tausayinshi ya kama Omar,MiÆ™ewa Omar yayi tare da kallonshi”Ka kulamun da kanka,Duk yarda ku kayi dasu saika sanarmun ”
Har yakai bakin Æ™opar Sgr ya dakatar dashi”Na manta,Akwai injection din Sehrish tare da medicine É—inta,Dana zo dasu,”

“Tana kwance a É—akin oummansu,”ya Æ™arasa maganar tare da fucewa daga É—akin,

Shaf shaf Ya kammala shiryawa cikin Sleeping dress dinshi,White colour masu ɗigon baƙi,Bayan ya feshe jikinshi da turare Ya sauko down stairs,Direct Ya nufi ɗakin abbansu,A ƙopar ɗakin ya tsaya cike da zullumi,almost 5 mins yana a tsaye bai motsa ba,Ya kasa sanya hannunshi balle ya kwankwasa ƙopar,

Ji yayi bazai iya haɗa ido da abbansu ba,jiki asanyaye ya juya zai bar ƙopar ɗakin,Ba zato ba tsammi sai ga abbansu,A tsaye Ashe Yaji ma a bayanshi yana kallonshi,bai jima da shigowa ciki ba,gabanshi ne Ya faɗi rass,Da sauri ya duƙar da kanshi kasa,duk yabi ya dabarbarce,
“Ka dawo kenan”?daÆ™yar ya iya buÉ—e baki yace”Eh,”
“Banyi tunanin zaka ji kunyar haÉ—a ido dani ba,”yayi maganar yana kallon fuskarshi,shiru Sgr baice komai ba
“Munga takardar saki mun gode,”yana kai Æ™arshen maganar,Ya soma Æ™oÆ™arin bi ta gefen Shi zai wuce ya shiga ciki,Da sauri Sgr ya ruÆ™o hannunshi,Rai a6ace abba yace”Ka sakarmun hannuna tunkafin ranka ya 6aci,Mara mutunci kawai,wlh rafayet ka bani kunya,ban ta6a tunanin zaka yi mun haka na,Kana É—aya daga cikin Æ´a’Æ´ana waÉ—anda nake alfahari dasu,Amma sai gashi Ka watsa mun Æ™asa a ido,”tuni hawaye sun wanke mashi fuskarshi,hankalin Sgr ba Æ™aramin tashi yayi ba,
Muryashi na kerma Ya ambaci sunanshi’Abba,”
“Ni ba abbanka bane,ban haifi É—a irinka ba,Tunda ban isa na sanyaka abu kayi mun ba,”jin wannan maganar yasa hawayen dake kwance cikin idanuwanshi suka soma gangarowa saman fuskarshi,Gaba É—aya Ya tafi Zai zube saman guiwowinshi,da sauri Abba ya ruÆ™oshi”kada ka kuskura ka zukunnamun,Saboda bakayi a lokacin daya dace ba,”
“Am sorry abba,Nasan nayi kuskure,kuma nayi danasani,pls abba,kada kayi fushi dani,”

Zuciyar abba ta karaya sosai,daurewa kawai yake yi,ba don son ranshi yake furta mashi kalaman bakinshi ba,
“Idan har kanaso,In shirya dakai,Kaje ka fara neman Yafiyar abusufyan,Sannan ka dawo wurina,”Yana kai Æ™arshen maganar,Ya buÉ—e É—akin Ya shige,

Ya jima a tsaye batare da ya motsa ba,DaÆ™yar ya iya jan Æ™afarshi Ya doshi É—akin abusufyan,A Æ™opar É—akin ya tsaya cike da zullumi,yafi jin shakkar tunkararshi akan kowa,hannu yasa yayi knocking É—in Æ™opar,Kusan sau uku yana kwankwasawa amma ba’a buÉ—e mashi ba,tunanin tura Æ™opar yayi sai gashi ta buÉ—e,Da sallama abakinshi ya shiga É—akin,Hasken bedside lamp ne ya haskaka mashi gadon abusufyan,Yana akwance yayi nisa acikin baccinshi,Was wasi ya tsaya yi acikin zuciyarshi Ya tafi koya tsaya,in har abusufyan bai yafe mashi ba,Abba ma bazai yafe mashi ba,Taya zai samu kwanciyar hankali?mahaifinshi na fushi dashi,

Kasa tafiya yayi,wuri ya samu gefen gadon uncle ya zauna,batare daya tayar dashi ba,Don yaci alwashin bazai ta6a tafiya ba,koda kuwa zai kwana a dakinne har sai Uncle ya yafe mashi,har wuraren ƙarfe 1:30 na dare yana zaune babu alamun bacci atattare dashi,Yayin da abusufyan keta sharar baccinshi,

Daya gaji da zamanne ya kwantar da kanshi gefen saman gadon,har bacci yayi awon gaba dashi,Lokacin da aka fara kiraye kirayen sallar asuba,Wayar abusufyan dake ajiye saman side drawer ta soma ringing,da ƙarfi kiran ya shigo,har cikin kunnanshi yajiyo sautin,A hankali ya ɗan buɗe idanuwanshi masu ɗauke da bacci don bai ishe shi ba,daga kwancen da yake ya wurga idanuwanshi kan Agogon bangon ɗakin,Lokacin sallar asuba yayi,dama sai da ya kawo hakan aranshi,don kuwa bamai kiranshi a wannan lokacin in ba abba ba,domin ya tashe shi sallar asuba,sam bai lura da mutun a gefenshi ba,daƙyar ya samu ya miƙe yana yin hamma,tare da yin miƙa,kafin ya sauke hannunshi ne karaf idanuwanshi suka sauka akan Sgr dake kwance yana ta sharar bacci,Gabanshi ba ƙaramin faɗuwa yayi ba,don baiyi tsammanin ganin mutun adakinsa ba,kuma farat ɗaya bai waye shi ba,don har sai daya ɗan raza,Cike da mamaki yake binshi da kallo,Abun yayi mugu mugun ɗaure mashi kai.
“Rafayet”!ya ambaci sunanshi da Æ™arfi,hannu yasa ya É—an bubbugi kafadarshi,nan fa ya fara sambatu yana faÉ—in”Am sorry uncle,ka yafe mun,bazan Æ™ara ba,Nasan nayi kuskure amma ba’a son raina ba uncle i ave realized my mistake,a shirye nake dana kar6i koma wani irin hukuncine daga gare ka……..”duk cikin bacci Sgr yake wannan sambatun batare daya sani ba,hada hawaye akan fuskarshi,tsananin tausayinshi ne ya kama abusufyan,ya lura da irin ramar da yayi,sam babu natsuwa atattare dashi,dama sai da ammi ta sanar dasu cewa duk irin raÉ—aÉ—in da zasuji na abunda ya aikata,Basu kaishi ba,don saiya fi su jin jiki,tuni idanuwan abusufyan sun cicciko tab da kwalla,

Slowly yakai hannunshi saman sumar kanshi,bai ta6a tunanin Sgr zai iya sauke girman kanshi ba,Yazo neman yafiya a wurinshi,sai gashi da kanshi ya bashi mamaki,Allah kadai yasan tun lokacin dayazo É—akin yana jiranshi ya farka,

Bubbuga kafaÉ—arshi yayi tare da ambaton sunanshi”Rafayet!Rafayet”!a firgice Sgr ya farka,yana faman zare blue eyes É—inshi,Koda su kayi ido biyu da Uncle abusufyan da sauri ya sunnar da kanshi Æ™ansa,cike da jin kunyarshi,
“Tun yaushe kazo ne”?
Cikin sanyin murya yace”Tun wuraren Æ™arfe sha biyu da rabi,nazo na same ka kana bacci,”.
“Meyasa baka tashe ni ba”?
“Saboda Banaso na takura maka ne,”daÆ™yar yake magana,saboda nauyinshi da yake ji,
YaÆ™i yarda su hada ido,Baisan yaushe Sgr ya fara jin kunya ba,Tabbas Ya fara ganin Canji atare dashi,’
“Kanason magana dani ne”?yayi tambayar yana kallon fuskarshi,.
É—aga mashi kai yayi alamar eh
“Okey,Ina sauraronka,”yayi maganar tare da matsowa Ya sauko da Æ™afafunshi kasa,Kafin Ya mayar da hankalinshi kan Sgr,
“Uncle,”ya ambaci sunanshi,tare da saukowa daga saman gadon,Ya tsugunna agabanshi,abun mamaki abun al’ajabi,Kamar a mafarki haka abusufyan ke kallon lamarin,Yau Sgr ya sauke girman kan nan nashi,Ya zuÆ™unna agabanshi,Lallai yau babba rana ce agareshi,

RuÆ™o hannunshi yayi acikin nashi,Calmly Ya soma magana”Pls uncle,Kaina bisa wuya na,ka yafe mun,Nasan nayi hurting dinka sosai,wlh na gane kuskurena………’tun da ya fara magana,bai bari sun haÉ—a ido da abusufyan ba,shi kuwa ya kafe shi da ido yana kallonshi,
“Ka yanke mun duk wani hukunci daya dace dani wlh i will accept it,amma dan Allah uncle,kada ku rabani da ita,bazan iya jure rashinta ba,atare dani,na saba da ita sosai……’tunkan yakai karshen maganar,Abusufyan ya katse mashi hanzarinshi dacewa”Zaka tafi da ita a matsayin mai aiki ko kuwa”?
Da sauri yace”A’a,Zan tafi da ita,A matsayin matata,in har kun amince mun,”

Murmushin gefen fuska abusufyan ya É—an saki,batare daya bari Sgr ya gani ba,ci gaba da magana abusufyan yayi”Naji daÉ—i daka gane kuskurenka,Dama ni can ban ruÆ™e ka araina ba kawai banji daÉ—in abunda ka aikata mata ba,Amma bbu komai,komai ya wuce Allah ma muna yi mashi laifi ya yafe mana balle mu Æ´an adam,Don haka na yafe maka rafayet,Allah ya yafe mana gaba É—aya,Sannan bazan Æ™ara shiga tsakaninka da matarka ba,Yanzu ya rage tsakaninku da Ammi ne,tace zata yi adalci atsakaninku idan har ku duka kun amince da junanku toh,idan kuma har É—aya daga cikinku ya musa,to zata raba aurenku ne,”
Cikin sanyin murya yace”bansan da wasu kalmomin zanyi amfani wurin gode maka ba uncle……”
“Kada ka samu damuwa,komai ya wuce,Allah ya baku zaman lafiya kaida matarka…….”daga haka Abusufyan ya zarce dayi mashi nasiha,duk ya kashe mashi jikinshi,fuskarshi É—auke da murmushin nasara ya futo daga É—akin Abusufyan ya nufi bedroom É—in abbansu,knocking É—in Æ™opar yayi,
“Wanene”?Muryar abbansu ce,
“Ni ne abba,”
BuÉ—e kopar abba yayi jikinshi sanye da jallabiya da alama shirin zuwa masallaci yayi,
Tunkafin yayi magana abba ya ruga shi cewa”kaje wurin abusufyan É—in”?
“Eh,daga can nake,”nan ya kwashe duk abunda suka tattauna a tsakaninsu ya sanar dashi,farin ciki ne ya lullu6e abba,har baisa lokacin daya rungumo Sgr ajikinshi ba,
“Allah yayi maka albarka My son,”
“Ameen abbana,”
“Nima na yafe maka,”
Har cikin ranshi ba ƙaramin sanyi yaji ba,
Bayan ya raba jikinshi daga nashi,Ya ruÆ™o hannunshi zuwa cikin É—akin”mu shiga daga ciki,in bakayi alwala ba,kayi sai mu tafi masallaci,’
Ba ƙaramin daɗi sgr yaji ba,Mommynsu na kwance tana bacci lullu6e da bargo,toilet ɗin ɗakin ya shiga,Abba ya tsaya a tsaye yana jiran fitowarshi,After some minutes Ya fito,
Suna hada ido da babansu Ya sakar mashi murmushi,mayar mashi da martanin murmushi yayi tare da cewa”inaso zan canza kayan jikina”
Shikenan,Zan jiraka a palour,Daga nan ka tashi su Omar,su fito mu tafi masallaci,”
Amsa mashi yayi da toh,kafin ya futo daga dakin,Jiki na rawa ya haura upstairs bai nufi ko’ina ba sai bedroom É—in Omar,tunkafin ya shiga ya soma kwala mashi kira,
“Omar,Omar,”a firgice Omar ya farka,tare da miÆ™ewa zaune yana tambayarshi lafiya,fadawa saman gadon Sgr yayi tare da rungumeshi ajikinshi,Yana dariya,
Tun da yaga haka,Ya gane cewa Sun yafe mashi
“Omar ka tayani murna,Uncle da abba sun yafe mun,kuma yace bazai Æ™ara shiga tsakanina da reesh ba,Ya amince na tafi da ita,”
Omar yayi farin ciki sosai,Amma kuma akwai sauran rina akaba,idan su sun amince mashi,Itafa Yarinyar!!!

Shafa bayanshi Omar yayi”Am so happy rafayet,ashe da rabon asha shagalin bikina tare dana ka,Kafin mu wuce U.s,tare da matayenmu,Alhamdulillah My dream will come true,

Zuciyar kowannansu a wanke take da tsantsar farin ciki mara misaltuwa,
“Amma wani hanzari ba gudu ba,jiya kaje wurin Sehrish kuwa?naji kayi magana akan maganinta”?
“Bansamu naje ba,amma idan muka dawo daga masallaci,Zan je na duba Lafiyarta,”
“Hakan ma yayi,bari na je nayi alwala sai mu wuce masallaci”acewar Omar,yakai Æ™arshen maganar tare da saukowa daga saman gadon,Toilet ya shiga Sgr kuma Ya wuce part É—insa,don ya canza Kayan jikinshi,

Batare da 6ata lokaci ba suka hallara gaba dayansu matasan gidan a babban falon gida,atare suka wuce masallaci,

*Boss Bature*

Wuraren ƙarfe 8 na safe a lokacin Su oumma sun hallara a kitchen suna shirya breakfast ɗin gidan tare dasu Mommy,da hajiya azeema,

A wannan lokacin ne Sgr ya shirya tsaf cikin fararen suit,wankan ya hau dashi sosai,fitowa yayi daga part dinsa Ya nufi corridor din dakinsu Sehrish,a baƙin ƙopar ɗakin ya tsaya,tare da sanya hannunshi yayi knocking din ƙopar ɗakin,
Daga ciki yaji ance”Wai wanene”shiru bai tanka ba,Ya sake kwankwasa kopar,Da Æ™arfi yaji a bude Æ™opar,a ruÉ—e ta sanya hannu abakinta,ido ya raina fata,sam batayi tsamanin Baban yayansu bane,
“Yaya rafayet,ashe kaine,wlh nayi tunanin wanine daban”abun ma dariya yaso ya bashi,
“Rishi kake nema”?tunkafin ya bata amsa taci gaba da cewa”In ma oumma kake nema,tana a kitchen,Jahad kuma ta tafi wurin aunty hafsaf,Ni kaÉ—aice nake jinyar sehrish,baiwar Allah wlh saita baka tausayi,duk ta rame,duk taji ciwo abakinta,abinci ma daÆ™yar take iya ci ……’
Surutunne ya ishe shi”its Okey,Zan wuce,”matsa mashi hanya tayi ya nufi cikin É—akin,
“Tayi breakfast”?yayi tambayar yayin da idanuwanshi ke akan sehrish dake kwance magashiyyan tana bacci,
“Inafa,bataci komai ba tun jiya da daddy yabata farfesu tasha,tare da É—an tea bata Æ™ara cin komai ba,koda daddare sai da oumma ta bata abinci ta amayar dashi duka……’
Surutun Hosana ba ƙaramin mamaki yake bashi ba,Amsa kaɗan yake buƙata amma sai zuba takeyi mashi kamar radiyon da bata da saiti ,lallai Omar zaiyi fama,
“Its okey,Kije ki amso mata breakfast É—inta yanzu ina jiranki ”
“Toh,”ta amsa tare da fucewa daga cikin dakin

Xama yayi daga gefen gadon ,ya zuba mata waɗannan sexy eyes ɗin nashi yana kallonta,tsananin tausayinta ne ya kamashi, hannu yasa ya zame bargon data lullu6e half body dinta dashi,Still blue gown ɗin nan ce ajikinta,bata canza kayan jikinta ba,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,har baiso ya ƙyafta idanuwanshi daga kan fuskarta, hannu yakai saman side drawer inda ya ajiye ledar allurorin nata tare da magungunanta,shaf shaf Ya ɗura ruwan allurar acikin syringe,so yake ya tayar da ita daga baccin amma ya kasa,Saboda baison Ya katse mata shi,don ya lura da yadda take yinshi cikin kwanciyar hankali,

Ajiye injection ɗin yayi sama drawer din,slowly yakai hannu yana ƙoƙarin shafa wuyanta,Hosana ta banko ƙopar ɗakin hannunta ɗauke da tray,A firgice Sehrish ta farka,Tana kokarin mikewa zaune,duk ta rikice,har yanzu bata daina jin fargababa,
“Reesh are u okey,”?jin muryarshi yasa ta mayar da eye balls É—inta akanshi,koda suka haÉ—a ido lokaci guda Ta É—aure fuskarta tamau babu annuri ko misÆ™ala zarratin,janye idanuwanta tayi daga kan fuskarshi,hankalinshi ya É—an tashi da ganin irin kallon da tayi mashi mai cike da tsantsar tsana,kuma wani abu daya É—aure mashi kai lokacin da suka haÉ—a ido,Sai yaga tana gyara wuyan rigarta,saboda Æ™irjinta daya fito sosai,kamar taga wani wanda ba muharraminta ba,Tashin sense,

MiÆ™a mashi tray É—in hosana tayi”Gashi Ya rafayet,Mommy ce ta haÉ—a mata breakfast É—in ,”
“Okey,”ya ambaci hakan tare da sanya hannu ya kar6i tray din,É—an madaidaici,ya daurashi akan lap É—inshi daya haura saman gadon,
Juyawa hosana tayi da gudu tabar dakin saboda taje taci abincinta,
“How was your body?hosana ta sanar dani cewa jiya baki ci isasshen abinci ba,haka ne”?
Rai a6ace tace”eh,saboda bana jin yunwa,”
Ajiyar zuciya ya É—an sauke kafin yace”okey,Yanzu ya kamata kici,ko don saboda maganinki da zaki sha,”
Bata tanka mashi ba,ta sauko daga saman gadon dakyar take iya taka ƙafarta,toilet ta shige,yana jiyo nishinta daga inda yake zaune,wahala take sha ba ƙadan ba,idan zatayi fitsari,sai data wanke fuskarta ta kuskure bakinta,Tukunna tafito daga toilet ɗin,ta koma saman gadon ta zauna,batare data kalleshi ba,
cup É—in dake É—auke da Tea ya soma kokarin kwafa mata a bakinta da nufin ya bata da kanshi,da sauri tasa hannu ta kar6e kofin,Tasa abaki tana sha,abun ya bashi mamaki,kaf ta shanye tea din,
“Bari na baki abaki….naga hannunki na kerma ”
A Æ™ule tace”Zanci dakaina,”bata jira ya Æ™ara magana ba,ta sanya hannu ta bude plate tana cin abincin da kanta,natsuwa yayi yana kallonta,yadda take moving lips É—inta wurin taunar abuncin ba Æ™aramin yanayi take jefa shi ba,bawan Allah ya kafe ta da ido yana kallonta,a tsiyace take cin abinci,kafin ta haÉ—iye wani ta tura wani abakinta,Har ce mata yayi taci a hankali karta shaÆ™e,Amma ko sauraronshi batayi ba,Ita burinta ya tashi ya tafi shiyasa take sauri ta gama cin abincin yayi mata allurar koya tafi ya bata wuri,

Bayan ta kammala cin abincin ,ta miÆ™a mashi hannun sai kace ba ita bace wannan me tsoron Allurar ba,Yau dai yaga abubuwan ban mamaki atattare da ita,ajiye tray É—in yayi,Kafin ya É—auko sirinjin allurar,ya tsira mata a cikin jijiyar hannunta,Tsabar raÉ—aÉ—i yasa ta runtse idanuwanta,tana fidda sauti”Wash Allahna,”Lumshe idanuwanshi yayi a yayin da yake kallonta,A hankali ya zame allurar daga hannun, ya ajiyeta,Magungunan ya shiga miÆ™a mata,ta dinga turasu abaki tana korasu da ruwan dake hannunta acikin kofi,

Bayan ta kammala shan magungunan Ya tattarasu ya mayar acikin ledar,ya É—auke sirinjin allurar da sauran tarkacen Ya mike ya nufi dustbin ya zuba su aciki,
Komawa yayi gefen gadon ya zauna yana kallonta,har lokacin babu annuri akan fuskarta,So yake ya bata hakuri akan abunda yayi mata ba,data ga ya ƙura mata ido,Sai ta rufe idanuwanta tamkar maiyin bacci,ba zato ba tsammani taji saukar kiss ɗinshi a saman neck ɗinta A harzuke ta buɗe idanuwanta,tamkar zata rufeshi da fada,Amma sai ta kasa,

Yana ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,Wayarshi dake ajiye cikin trouser pocket dinshi ta soma ringing,da sauri ya lalubo wayar tare da cirota Ya duba mai kiran nashi,
Abbansu ne,picking call É—in yayi kafin ya kara wayar a kunnanshi,tunkafin yayi sallama,Muryar abba ta katse mashi hanzarinshi,
“Kana ina ne”?
Kallon sehrish ya É—anyi,ta kawar da idonta gefe,
“Nazo duba jikin reesh ne,”
Abba yace”Okey,Dama ammi ce ke son ganinku”
Hakanan Yaji gabanshi ya faÉ—i rass,

Some of related Hausa Novels

 

(ga duk mai buÆ™atar Littafin Abban Sojoji from book one to 3,Yayi mun magana,Sannan idan mutun nada tambaya dangane da littafin nan shima yayi mun magana,Saboda masu yaÉ—a jita jita,Da kuma mahassadan dake kokarin 6ata mun suna,its better mutun ya tunkareni idan ma tambaya gareshi,Su kuma munafukan dake kokarin shiga gonata Allah Ya basu sa’a,tamkar taki suke agare ni)

 Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 122 Complete Novel

 

Back to top button