Uncategorized

Adon Dawa Complete Hausa Novel

ADON DAWA Complete Hausa Novel Written By Mammy Kabeer

Posted by Ai Hausa Novel
Price ₦300
Category Hausa Ebooks
Uploaded On 30 Dec, 2022
Upload Time 8:29 pm
Hits 218 Views
Author

Writer Group

Novel Genre

Comment No Comments

Daji ne mai cike da tarin bishiyu,dogaye  masu yawan gaske,hakan yasa ta wani bangaren na dajin yake da duhu da sarkakiya,wani gurin kuma zaka ganshi akwai wadatar haske.

Dajin yana da matukar girma,wanda ke dauke da halittu kala-kala.baka jin komai sai sautin kukan tsuntseye kala daban -daban.

Kasancewar yanayine na damuna,hakan yasa dajin yayi lub-lub dashi,gaba ɗaya bishiyu dake cikin dajin sunyi ganye koraye shar dasu kwanin sha’awa.

Wasu daga cikin ganyayyakin har ruwa zakaga yana diga daga jikinsu,alamun raba.

Kai tsaye zamu iya cewa dajin yana da yanayi na ban tsoro,wanda bazaka taba tsammanin akwai wata halittar dan Adam dazata iya rayuwa cikinsa ba.saidai hakan bai hana dajin kyau da kawatuwa a idon duk wanda ya kalleshi ba.

Akwai birrai da yawa cikin dajin,sannan ana tunanin akwai mugayen namun dawa dake rayuwa cikin dajin.

Can gefe guda na hango wasu bishiyu kusan guda goma,acure guri ɗaya,kamar wanda aka hada kansu,suna da tsayi amma ba kamar sauran ba,da alama dai kamar yankesu akayi.

Daga kaina nayi ɗan kallon iyakar tsayin bishiyun,saidai ga mamakina wata bukka na hango asaman bishiyun nan ɗonono,da alama kuma akwai mutum dake rayuwa cikin wanann bukkar. Dan kuwa kana iya hango abubuwa irinsu kwanuka,abin zuba ruwa,daga gefe kuma ga wani guri mai tudu wanda ke nuna alamun gurin kwanciyane.

Daga can gefen bishiyun nan na hango wata yarinya tsugunne gaban wata yar korama dake dauke da ruwa mai kyau da haske,gefenta kuma zagaye da yan kananan shuke shuke,yarinyar ta juya bayanta,kuma ba kaya ajikinta,dan daga ita sai wani dan karamin towel data ɗaura shi asaman ƙirjinta,da alama dai wanka take,dan kuwa ruwa take diba tana watsawa ajikinta.

Ahankali yarinyar ta mike tsaye tare da tattare uban gashin daya zubo gadon bayanta ta nannadeshi kamar gammo. sannan ta janyo wani dan zani ta  daure kan nata dashi.juyowa tayi ta fara tafiya cike da kuzari atare da ita. Ta nufi jikin bishiyar nan.

Masha Allah !!!shine abinda bakina ya iya faɗa,sakamakon arba da kyakykyawar fuskar yarinyar da akalla shekarunta zasu kai sha takwas,doguwace mai matsakaici jiki,bazamu iya kiranta da Siriya ba,sannan bazamu ce mata mai jiki ba kai tsaye.tana da kira mai kyau da ɗaukar hankali, daga kasanta abaje take sosai,tana da hips,sannan tana da albarkatun kirji,jikinta shar shar yake,ita ba bakaba kuma ba fara ba,irin choculate colour ɗin nance.

Tana da rawn face,dauke da madaidaicin hanci mai kyau,idanunta dara dara ne  farare tass dasu,bakinta dan karami,mai dauke da pink lips,ataƙaice dai zamu iya cewa kyakykyawar yarinyace ta gani afada.

Hankali kwance take takawa cikin ɗan sauri ta nufi saman bishiyar nan, abin mamaki tana zuwa naga ta kama bishiyar cikin wani irin salo da kwarewa ta fara hayewa kamar wata biranya.kawai kama jikin bishiyar take tana ɗan tsalle sai kaga tayi sama.

Cikin abinda bai wuce dakika biyar ba naga ta haye saman bishiyar nan.

Zama tayi tare da janyo wani abu mai kama da akwati,saidai kuma da itace akayishi.

Budewa tayi tare da ɗauko wani irin kaya masu kama da fatar damisa ta sanya ajikinta.riga ce doguwa,wacce duka duka bata wuce iyakar gwaurinta ba.sai wani wando irin skin tite dinnan shima iya gwuiwa,gashinta ta ware tare da ɗauko wani mataji mai ƙarfi dan da alama da katako akayi shi.

Taje kan tayi sannan ta rabashi gida biyu ta daure.bayan ta kammala daure kan nata,saita dauko wani ƙaton zani ta  lulluɓa ajikinta,ga mamakina saina ga ta tada sallah,saidai kuma haka tayi sallar nan gwauri a waje,kuma akwai kurakurai sosai  cikin sallar.tana idarwa ta cire zanin sannan ta dauko wata ƙatuwar kwari da baka ta rataya awuyanta, sannan ta dauki wata yar karamar wuka,ta soke jikin rigarta,inda ta janyo wata jela jikin rigar ta daure ta abaya.kanta ba ko dan kwali haka ta kama bishiyar nan ta sauko kamar yadda ta hau.

 

Download

Click the below button to download, pls in case you get trouble trying to download kindly drop a comment.

Download any type of hausa novel which include Hausa Love, Adventure, fiction, Fantasy and other genre Hausa Novel paid and free and read them in confort of your zone at ArewaBooks.Com

DOWNLOAD NOW

 

Author’s Contact

  • Name : Saratu Kabir
  • Wattpad Handle : @
  • Nick Name : Mammy Kabeer
  • Whatsapp Number : 08067072477
  • Nationality : Nigeria
  • Email :
  • Group : Elegant Writers Association

The Book is not free

Back to top button