Labarai

Dabi’ar Zuciya Complete Document

Description/Story:

Dabi’ar Zuciya! Complete Hausa Novel Document Written By Safiya Abduallahi Huguma 

 

Description

*DABI’AR ZUCIYA*

_FREE PAGE_ 01

 

 

Rana ce sosai wadda ta qwalle daga kowanne sashe na sararin subhana zuwa fadin filin duniya iyakar hangen dan adam,wadda take bada tsananin haske da kuma zafi,irin zafin dake sanyawa kowanne mai rai wala mutum ko dabba neman mafaka da zai samu inuwa da zata hutashshehi ta kuma dauke zafi da radadin da ranar ta haifar tun daga gangar jiki izuwa qwaqwalwa.

 

 

A irin wannan lokacinne ummukulsum ke tafiya cike da bacin rai da wani irin fushi,yarinya matashiya,wadda gaba daya shekarunta ba zasu haura sha biyar kacal a duniya ba.

 

 

Baqa ce ita,ba irin wuluk din nan ba,saidai tafi chocolate colour duhun fata,tana da yalwar gashin kai dana gira,madaidaicin baki da matsakaitan idanuwa,tana da baiwar fararen idanuwa,haqoran bakinta milk colour ne masu qyalli,madaidaicin baki da matsakaiciyar haba wadda ta qawata shape din fuskarta,a taqaice ummukulsum na cikin mata masu matsakaicin kyau.

 

 

Zafin da take ji a zuciyarta yafi wanda takeji a tsakar kanta sanda ranar ke kwadarta,idanunta cika yake da hawaye tana ta qoqarin maidashi,saboda sam batason tayi kukan,mutum ce ita mai jumuri da dakakkiyar zuciya,wanda wasu suka fassara hakan da tsananin taurin kai da kuma baqin hali.

 

 

Tana tafe tana hadiye abinda ya dunqule mata a wuyan,tana kuma duban yadda hanyoyin layukansu ya dade qwal babu jama’a,da alama kowa ya nufi gona,wadanda kuma basu da gonakin zuwa ko basu da abinda xasuyi cikin gonar sun tafi sabgogin gabansu.

 

 

Hannun hagunta ta kalla sanda take gab da gota wani siririn lungu,saita yanke shawarar tabi tanan din,don zaifi mata saurin isa gida,duk da ba kasafai ta fiya son bin lungun ba saidai dole,hatta da mahaifiyarta wani lokaci takan ce su haqura da bin hanyar,saidai a yanzun tana son isa gida da wuri ne,don ta baro mahaifiyar tata tana dakon dawowarta.

 

 

Ko tsakiyar lungun batayi ba ta soma hangota,asiya,’yar uwarta ta jini,wadda suke ‘ya’yan maza zar ita da ita,da mahaifinta da nata mahaifin uwa daya uba daya suke.

 

 

Ci gaba tayi da nufosu yayin data kafesu da idanuwa tana kallonsu.

 

 

Ita da ayuba,daya daga cikin matsan qauyen wadanda suke ji da tashen samartaka,ta gefe guda kuma sukeji da tashen rashin kunya,rashin ganin girman kowa,iskanci rashin tarbiyya da badala iri iri,saidai duk da wannan halayya tasa kusan babu wanda yake iya bugar qirji ya qalubalanceshi,shi din ko kuma daya daga cikin abokansa,sakamakon mahaifinsa ya kasance mai abun hannunsa cikin fadin qauyen,ta daya gefan kuma,mahaifiyarsa qanwa ce ga mai garin garin nasu,hakan ya sanya yake iya aikata dukkan abinda yaso,ya kuma taka dukkan wanda yaga dama,cike da gadara da kuma ganin karensa yakai tsaiko.

 

 

Asiyan na sanye da uniform na makarantar boko,makarantar da suka sha gori baqar magana gami da habaici kala kala a kanta,makarantar da ake mata wani kallo na musamman,aka dora dukkan buri na ci gaba kyautatuwa da gyaruwar rayuwar asiyan ita da duk wanda ya jibanceta a kanta.

 

 

Gefe daya ayuba ne tsaye gab da ita,kamar zasu shige jikin juna,magana suke da juna,saidai ba zata iya jin abinda suke fada ba,sakamakon ‘yar tazarar dake tsakaninsu,sosai ranta ya sake baci fiye da dazun lokacin da ta hanhi ayuban ya kama hannun asiyan ya riqe cikin nasa,wannan ba shine karon farko da taga asiyan cikin wani yanayi da yayi kama da wannan ba,saidai babu wanda ta taba furtawa bayaga mahaifiyarta,kuma har yau har kwanan gobe itace mutum daya tak data taba shaidawa abinda idanun nata ya gani,wanda daga bisani data fuskanci mahaifiyar tata batason dukka wata magana daya danganci wannan sai ta daina gaya matan,saidai a kullum kwanan duniya,duk sanda zata ga asiyan a yanayi irin wannan,tana jin ciwo sosai cikin ranta,tana jin baqinciki,amma ita din babu yadda zatayi da ita,saboda bata da wani iko ko qarfi wajen yanke hukunci cikin al’amuranta,haka taci gaba da takawa harta iskesu,ta kuma rabasu ta wuce ba tare data ce da kowa cikinsu komai ba,yayin da asiya da ayuban suka bita da kallo,har sai data kusa bace musu sannan suka dauke dubansu daga kanta lokaci guda

“Yar gidanku ta ganmu asy,kina ganin ba zata kai maganar gida ba?” Baki ta tabe tana gyara tsaiwarta sannan ta dubeshi

“To saime don ta ganmu?,zancan kai magana gida bata taba ba,don ba yau farau ba” wani duba yayi mata,a zahiri yayi kama dana burgewa dana qauna,saidai can qasan ransa yana taɗinta shi daya

“Ashema fanko ce,ballagaza,bani kadai ma kenan na saba latsawa ba,bari na saki jiki kawai na kwashi rabona,indai kudi ne matsalarta ta samu”, da wannan zancan zucin ya jefeta da murmushi,wanda ya sanyata itama ta maida masa martani.

 

 

Tana gamutsa wadan nan abubuwa guda biyu cikin kwanyarta ta fuskanci gidansu,gidan da kullum tsanarsa ke qara darsuwa cikin ranta,ana cewa da uba ake ado,itakam anan ta qalubalanci wannan karin maganar,a nan a bigiren da take….tana ado ne da mahaifiyarta ba wai mahaifinta ba,hausawa na cewa gida mai dadi…banda nasu gidan,bata hangi wani dadi nutsuwa ko kwanciyar hankali dai dai da qwayar zarra cikin nasu gidan ba,batasan yaushe ne zasu kalli gidansu suji farinciki kwanciyar hankali ko alfahari dashi ba.

 

 

Duk da cewa babu lallai a iya jiyota amma bakan bai hanata yin sallama ba sanda take shiga gidan,saidai kamar yadda ta zata ne ba’a jiyota din ba,har sai data qaraso babbar harabar gidan nasu mai yalwa sosai,kamar yadda mukasan gine ginen gidaje na ‘yan uwanmu ‘yan karkara,sashen dake hannun damanta,wanda aka gewayeshi da dangar kara saboda a rabashi daga kasancewa wani yanki na babbar harabar gidan ta nufa,tana iya jiyo tashin sautin qarar redio daga daya sashen dake hannun hagunta,yake kuma kallon nasu sashen,wanda shikam yafi nasu,don ko babu komai ya samu ariziqin katangar bulo na jar qasa kamar yadda ilahirin ginin gidan yake.

 

 

Sallama ta sakeyi karo na biyu,kusan a tare suka amsa mata,mata guda biyu qarqashin rumfar buni dake a tsakar gidan nasu,zaune suke saman tabarmar kaba,matashiyar da batafi shekara sha hudu ba,da kuma mahaifiyarsu wadda nata shekarun zasu kai arba’in,saidai idan bakayi mata mallo na tsanaki ba,zaka tsammaci tafi hakan,sakamakon hudowae furfura saman baqar sumar kanta,wanda hakan yake da nasaba da yanayi da hali na rayuwa.

 

 

Tana dosu su amma hankalinta yana ga ‘yar qaramar rumfa da suka tayar suke girki a cikinta,qamas take,ba’a hura wutar kara da sukanyi amfani da shi ba,hasali ma tukwanen a kife suke gaba daya a wanke qal kamar yadda ta barsu a dazun,alamu na nuna mahaifin nasu tunda ya fita bai waiwayosu ba kenan?,saita dauke kanta ta qarasa saman tabarmar da suke kai ta zauna,zuciyarta na qara dagulewa da baqin ciki.

 

 

“Har kin dawo?” Mahaifiyar tata ta jeho mata tambayar,idanunta ta soma saukewa saman ciwon dake saman qafarta,wanda a kullum yake dada rami,qafar tata tana sake kumbura,kowanne dare zuwa wayewar gari na duniya da wannan ciwon take kwana cikin zuciyarta tana tashi,tana jinsa tamkar a jikinta yake

“Ta yaya umma zaki tsammaci dadewata dama a wannan gidan?” Ta fada sautin muryarta yana nuna alamu na fushi.

 

 

Tsam mahaifiyar tata ta daga idanunta tana dubanta,ta wani fannin tana nazartar yanayin fuskarta na wasu sakanni,saita sauke boyayyar ajiyar zuciya,sannan ta kira sunanta a hankali

“Kaltume…..wannan gidan dai da kike magana a kanshi mahaifiyata a cikinsa ba wani ba kin manta ne?” Saita dauke idanunta daga kan ciwon karon farko tun daxun data zuba mishi idon,kamar wanda hakan zai taimaka mata wajen janye ciwon daga qafar mahaifiyar tata

“Na sani umma,na sani,amma saidai kiyi haquri umma,saboda bakina bazai daina fadar maganganu makamancin wadan nan ba,saboda shine gaskiya kuma ainihin abinda yake cikin zuciyata,matuqar ba zata daina ba itama….matuqar ba zata canza ba,nima banajin zan canza umma” sosai ta sake kafeta da ido,sannan ta buda baki a hankali tace

“Kaltum……”

“Kiyi haquri umma” tayi hanzarin fada ba tare data bari umman ta sake cewa komai ba,ajiyar zuciya umman tata ta sauke,sannan ta janye idanunta daga fuskar diyar tata,ta sani cewa kaltum yarinya ce mai fushi idan aka tabata,tana da zafi,tana da fushi idan aka tabata,saidai tana da tausayi da kuma sauqin hali a wasu lokutan.

 

 

Shuru ne yaci gaba da ratsawa tsahon wasu mintuna,sannan ta bude baki a sanyaye tace

“Ya kukayi da ita?”

“Kamar kullum kuma kamar ko yaushe,yau ma abinda ta saba tayimin,na samu kawu labaran….yaji maganar da mukeyi da ita,ya dauko kudi zai bani amma ta saka hannu ta karbe,tace ba zai bayar ba,idan ma an baki a gindinmu da babanmu kike qarewa…..wai umma me yasa ayi bata sonki?,anya kuwa mahaifiyarki ce da gaske….?” Wani kallo ta jefawa kaltum,wanda ya hanata qarasa fadar abinda tayi niyyar fada din,saidai duk da haka labarin abinda ya farun data shaida mata ba abinda ya hanashi tasiri saman fuskarta,duk da cewa wannan ba shine farau ba,ta saba da dade da sanin wannan dabi’a ta mahaifiyar tata,har kusan ya zame mata jiki,amma ta kasa sabawa,duk sanda wani abu mai kama da wannan ya faru sai taji zafin hakan har cikin zuciyarta.

 

 

“K’nnnnn” habiba qanwarta wadda ke xaune tun dazun gefan mahaifiyarsu ta fada,ita din mutum ce mai tarin haquri fiye da kaltum,bata da yawan magana,tana da sanyin hali tamkar na mahaifiyarsu,saidai duk da haka ita din ma abun na damunta matuqa da gaske,yana ci mata tuwo a qwarya,saidai bata fiya tankawa ba,amma idan hira ta tashi tsakaninta da ‘yar uwarta wani lokaci takan fada.

 

 

Kallonta kaltum tayi,iya saman fuskarta kawai tasan itama ranta ya baci,ci gaba da maganar tata kuwa tasan bashi da wani alfanu,hakanan bazai haifar da da mai ido ba,don haka ta sauya akalar zancanta zuwa neman mafita

“Yanzu umma ya za’ayi kenan?” Shuru nadan sakanni tayi kafin ta amsa mata

“Babu komai,zanci gaba da nema kawai har Allah yasa a samu,idan ban samu din ba….zanci gaba da amfani da wannan maganin muga abinda Allah zaiyi” shuru kaltumen tayi tana hadiye wani yawu mai tauri,saita kalli sashen da suke girki wanda yake a bushe ba girki babu alamarsa,ta maida dubanta ga umman

“Baba bai dawo bane har yanzu?,naga baku dora komai ba” kamar ba wata tambaya tayi mai muhimmanci ba haka umman tata ta bata amsa

“Bai dawo ba,amma nasan yana kan hanya in sha Allahu” miqewa kaltum tayi,saboda ba abinda ranta ke sakeyi sai baci,tasan umman ta fada ne kawai,umman ta fada ne saboda ta bashi kariya a idanunsu,bayan babu wata kariya data rage masa da zai samu a idanuwansu,ya gama wargaza komai,ya kuma gama kwancewa kansa zani a kasuwa,don ba zata iya tuna sau nawa ta fita tayi kitso ta dawo ta kawo kudin sukaci abinci dashi ba,to kuma me yayi saura?.

 

 

Buta kawai ta dauka,har zata wuce bayan gida ta juyo ta dubi umman tasu

“Umma ina bilal ya shiga ne?”

“Bai jima da fita ba kika shigo,yacemin zaije wajen dan bala,yace kamar akwai aikin da zasuje yau” kai kawai ta gyada,bacin ranta yana sake ninkuwa,bilal da gaba daya bai cika shekara sha biyar ba amma yasan dukkan wata wahala ta duniya,yaro ne da gaba daya kamar baisan ciwo ko dadin jikinsa ba,Allah ya zuba masa tausayin mahaifiyarsa da son ‘yan uwansa,dukkan wani aiki da za’a kirashi na wahala bilal ya iyashi,kama daga kwabin bulon qasa,aikin gini,kwasar qasa,haqar masai ko rijiya,kai hatta da kiwon dabbobi idan mutum nada buqata zaije ya karba yayi masa,burinsa kawai a biyashi kudin,burinsa kawai su samu abinci suci,tun yana aikin wahala ya dawo gida yayi jiyya har ya saba.

 

 

 

File Name   Dabi’ar Zuciya… Hausa Novel Doc.
Title   Dabi’ar Zuciya Complete
Author    Aisha Aliyu Garkuwa 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/07/2024
File Size    1.15 mb
Format Size    TXT
Book Price    Paid
Phone No
Download Dabi’ar Zuciya Complete Novel Document By Safiya Abdullahi Huguma 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button