LABARINA (Zango na biyar, kashi na uku)
Sabon shiri, sabon salo, sabuwar fikira.
Shirin ya yi gamon katar tare da afkawa hannun gwanaye ta fuskar rubutu. Wato irin abin nan da ake ce wa komai na babba, daban ne.
Marubuta 1: Nasir S. Gwangwazo, Yakubu M. Kumo.
Marubuta 2: Siddika Habib, da Sidiya Sidiya.
Labari: Aminu Saira
Ɗaukar nauyi- Sarkin waka
Ba da umarni– Aminu Saira
Kamfani- Saira Movies.
Manyan Taurari:
Sumayya
Lukman
Presido
Ummi
Sarkin waƙa
Baba Dan’audu
Baba Rabiu.
Wani Maigidan Haya Ya Kori ‘Yan Hayansa Saboda Yadda Suke Adddabansu Da Kukan Dadi Idan Suna Jima’i
Masu Amfani Da GBWhatsApp Suna Cikin Hatsari
So Makaho Ne: Wata Zuƙe kiyar Baturiya Yayi Wuf Da wani Dan Nigeria
Matsayin da Na ba Mahaifina na Gida, Shi na bai Wa Adam Zango – Jaruma Tumba Gwaska
An Haramta Wa Yan Fim Saka Kayan Yan Sanda A Fim
Yadda Rayuwar Jaruman Hauwa Waraka Ta Koma Bayan Daina Saka Ta Film
Masha Allah: Bidiyon Hafsat Idris (Barauniya) A Gidan Aureta
1. Idanun Maimuna sun yi matuƙar rufewa game da lafiyar Sumayya.
2. Alhaji Ɗan gaske ya zama tsanin saita Shirin zuwa tsantsar wa’azantarwa da nuna darajar mahaifa. Fita ta huɗu.
3. Wacce irin soyayya ce tsakanin Lukman da Ummi? Kamar kishi, kamar raha, kamar soyayya?
4. Samun uba irin Alhaji Ɗan gaske wajen son ɗa kuma ƙoƙarin ɗora shi akan turba ta gaskiya abin alfahari ne ga kowanne ɗa. Amma da alama kamar Aliyu bai fahimci ni’imar da Allah ya yi ma shi ba.
5. Tawagar juyin juya hali ta kankama a gidan Yari.
6. Makauniyar soyayyar Lukman ta rufe ma shi idanu, yana ta tafka kura-kurai a zamantakewarsa da ahalinsa.
7. Wanne mataki Aliyu zai dauka ke nan a gaba don ganin Sumayya ta samu lafiya?
KURA-KURAI:
1.Ban san a wacce duniyar ake neman aure irin na Presido ba, ko ba komai suruki ai ya wuce wasa. Duk da cewa shiri ne ƙirƙirarre, amma kalaman Aliyu ga mahaifin matar tasa kamar yadda yake iƙirari suna yin nauyi. Ya kamata ya sassauta.
2. Zuciya da riƙo irin na Maimuna game da Rabiu sun yi tsauri da yawa, duk da cewa ya yi mata laifi. Ya kamata a samu zuciyar musulunci, ” Matar na tuba…”
Labarina wata katafariyar makaranta mai ɗauke da manyan darussan rayuwa ababen koyi. Gefe guda kuma akwai raha da barkwanci da kalamai masu sanyawa a dara ko ba a shirya ba. Labarina na cikin manyan shirye-shirye masu dogon zango da ake yayi kuma yake daukar hankalin masu kallo.
Mubarak Abubakar Saulawa
16-9-2022.