Labarai

Banfi Karfinta Ba Complete

Description/Story:

Yaroma Namijine! Complete Hausa Novel Document Written By Aisha Aliyu Garkuwa 

 

Description

🌹*_BAN FI K’ARFINTA BA_*🌹

 

🌺🌺🌺🌺🌺

 

 

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

 

 

*~❄We beare’s of soon golden We writer’s assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*

 

*Rubutawa*— Amina Hassan (Oum-Deedat)

 

*Hakk’in Mallaka*—(Oum-Deedat)

 

*Sadaukarwa*— Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k’auna ta gareki, k’anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.

 

*Godiya*—- Ga Allah subhanahu wata’ala daya bani rai da lafiya na rubuta maku wannan littafin mai dinbin fad’akarwa da nishadantarwa, yanda nafara lafiya ina rok’on Allah yasa in k’are lafiya.

 

*Jinjina*— ga ‘yan Golden Pen writers association Allah ya k’ara hada kanmu ya qara mana zaqin hannu ya bamu ikon rubuta abunda zai amfani al’umma baki daya.

 

*Matashiya*— wannan labarin qirqirarre ne banyi da niyyar cin zarafin kowa ba duk wanda ya ci karo da abunda yayi daidai dashi yayi haquri.

 

Page *_~1~_*

 

• ∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆•

 

Tsoro na Allah tsoro na muhadu dashi ahanya saboda ko ba komai dai ni nasan bana iya kallon cikin kwayar idanunshi,wani mugun kwarjini yakeman ta bangare guda kuma tsareni da idanunshi masu rikitar dani dayakeyi aduk lokacinda zamu hada hanya.

 

dukda an bashi shedar tinda ake dashi ba’a taba ganin miskili ta bangare guda kuma kamilin saurayi aduk fadin unguwar ba irin shi.

 

Unguwar da take cikeda ‘ya’yan masu kudi ‘yan gata, ‘ya’yan masu fad’a aji a fad’in Nigeria, da yawa yawansu ma ba a qasar sukeyin karatu ba ta wani bangare kuma sha’aninsu sukeyi da ‘yan matansu ‘ya’yan k’usoshin gwamnati irinsu amman duk da haka acikinsu Ya Ameen daban yake.

 

mata dayawa suna sonshi amman shi Sam basa gabanshi Aikinshi da kasuwancinshi kadai yasanya gaba, acewarshi har yanzu ba’ayi yarinyar dazai tsaya b’ata ma kanshi lokaci akanta ba, kai shi soyayyar ma gabaki dayanta bai yarda da itaba.

 

Menene abunso a jikin mace? Kullum tambayar da ya keyi ma kanshi kenan.

 

(Nidai nace bakaje hannu baneba lol🤣)

 

“”””””***************”””””

 

Ahankali nake takawa cikin natsuwata da tafiya ta mai ban sha’awa da burgewa, ni ahakan ma gani nakeyi sauri nakeyi saboda aiken da ummata tayiman kasuwa banaso na rasa adaidaita din da zai kaini duba da yanayin unguwar tamu, akwai drebobi har guda uku acikin tanqamemen gidan namu ko nace nasu amman dukda haka ummana ta haneni da shiga motocin domin kaini inda zani, a cewarta in tsaya matsayina na diyar mai aikin gidan mara galihu saboda gudun wulaqanci dukda cewa su drebobin ba zasu wulaqantani ba kasancewar mu dasu duk matsalar mu daya na wulaqanci da muke fuskanta daga matar gidan,

 

A wajen mai gidan da babban yaron gidan ne kawai muke samun sassauci amman ba daga su ba mudin da dabbobin dake gidan gonar bangare daya daga cikin gidan duk daya muke awajen iyalan gidan in kacire mutum uku rak cikin mutum bakwai daga cikin gidan watau Ya ameen Babban Dandan Gidan a maza, afnan watau autar gidan dashi kanshi kuma uban gayyar watau mai gidan Alhj Mustapha Dambulan

 

Ban aune ba naji nayi karo da mutum kasancewar saurin da nakeyi kuma da son kaucewa idanun drebobin saboda banaso su yiman tayin kaini din, lokaci guda kuma nayi baya zan fadi bankai ga kaiwa qasa ba naji an janyoni dakarfi har na fada faffadan kirjinshi da yake cike da haiba, lokaci guda dad’edd’en kamshin turarenshi da ke kara taimakawa wajen rikitar dani ya yiman sallama a hancina.

 

“Subhanalla” nace ina mai ja baya dasauri amman dukda haka damtsen hannuna na cikin nashi ba tareda ya sakeni ba,

 

“yi hakuri don Allah yaya…”

 

“Shiiii🤫” ya katseman hanzarin bashi hakuri da nakeyi, cikin isa da rashin son magana dinnan nashi ya bude baki dakyar yaceman “is ok ya wuce amman nan gaba ki dinga kula, bakyau ana tafiya ana tinani”

 

ya fada ahankali yanda nikadai zan iyaji dukda dai cewa dama haka yanayin maganar tashi take don in ba saninshi kayiba saima ka dauka maganar zuci yakeyi labb’anshi ke motsawa

 

Sakina yayi tareda zagayeni ya wuce kaman ma ba shine ya gama magana ba yanzu

 

Girgiza kaina nayi yayinda har yanzu ban koma normal ba bugun zuciyata ya qara gudu lokaci daya kuma ina kokarin daidaita numfashina domin ji nayi kaman ya wuce tare da numfashin nawa,

 

juyawa nayi nabishi da kallo har ya shige dan madaidaicin apartment din nashi da yake cike da kyau da qayatuwa a bangare guda na gidan.

 

Ci gaba nayi da takawa mamakin shi fal araina, na godema mahalicci na da ba aunty sauda ko nihal ce wannan tsautsayin ya faru akansu ba da na kade har buzuna,bani kadai ba ma har ummata da take cen tana masu iyakar iyawarta cewa zasuyi na bangajesu na daidaita kafada ta da tasu ubanwa ya haifeni,

 

oh “Allah ya soni” na fada afili ina mai sauke ajiyar zuciya daidai lokacin da na daidaita kaina ta gefen titi ina mai tafiya tareda waige waigen Inda zan hango abun hawa saboda inaso nayi sauri na amsoma ummana aikenta kada mukara yin laifi akan wanda mukayi dasafe wajen Hajiya matar gidan da muke aikatau.

 

 

_Muje zuwa Wannan shine mafari_

 

File Name   Banfi Karfinta Ba… Hausa Novel Doc.
Title   Banfi Karfinta Ba Complete
Author    Amina Hassan
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    17/07/2024
File Size    2 MB
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No
Download Ban Fi Karfinta Ba Complete Novel Document By Amina Hassan  

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button