Novel Document

Miskili Ne Complete Novel Document

Miskili Ne By Momyn Fareesa

Description/Story:

Miskili Ne Complete Hausa Novel Document Written By Momyn Fareesa

 

Description

……misalin k’arfe 6:17 pm”fahad shariff ne zaune a parlourn gidansa”yana sanye da wondo 3quater fari k’ar da farar t shirt”gabansa laptop ce yanata danne danne”sai k’amshi turaren sa me dad’in gaske ke tashi Acikin k’ayataccen parlourn nasa”yayi kyau fuskarsa nata shek’i tayi fiyau da ita gwanin burgewa,sbd d’azun yaje Ammasa Aski”gaba d’aya hankalinsa na kan laptop d’in”yatura red lip nasa na k’asa cikin bakinsa yana tauna”Ahaka mus’ab da yarinyar da baba ladi suka shigo cikin parlourn da sallama”ba tare daya kallesuba ya Amsa da k’yar”baba ladi tabi parlourn da kallo tana girgiza kanta ,Aranta tace lallai Ana kashewa k’asa kud’i”mus’ab ya zauna gefensa dukda basufi 40 minit da rabuwa ba Amma saida yace”Abokinah barka da hutuwa”baba ladi kuwa hannun yarinyar ta kama suka zauna kan carpet tana fad’in Alh Ina wuni?”ya d’auki kusan second 5 kafin ya juyo ya kalleta anutse yace”Ina wuni baba?”pls ki kirani da sunana karki samu damuwa”wancan shine d’akin da zaku zauna qkwai komai ciki”ga kitchen shima”yafad’a yana yiwa yarinyar kallo d’aya ya d’auke kansa”sabuwar doguwar riga ce abaya Ajikinta”wacce Ayanzun mus’ab yaje da rigar yabama baba ladi tabata ta canza”yadda rigar ta Amshi jikinta kuma ta yafa mayafin zaka zata batada wata matsala”da Alama time d’in datake hayyacinta tanada nutsuwa da kamun kai.dan ta nutsu sosai tama k’i kallonsa”baba ladi kuwa godiya tayiwa shariff ta mik’e tsaye rik’e da ledar kayanta ta nufi d’akin”itama yarinyar kamar tana jira ta mik’e tsaye da nufin ta bita….K! shariff yadakatar da ita”raba Ido ta farayi tanaso ta wuce Abinta”bakya jine?zonan kiji mezan fad’a miki” yakirata cikin k’asaitacciyar muryarsa me dad’in sauti ga masu sauraronta…pls kasan fa ba sunanta tasani ba bazata gane kiranta kakeyi ba”cewar mus’ab Ahankali”banza sheriff yamasa ya rufe laptop d’in gabansa ya maida dubansa gareta”suka had’a Ido! haka nan yaji k’irjinsa ya buga lokaci guda”wanda yayi mamakin meyasa yaji hakan?”saiya basar yasakar mata harara yamata Alamar tazo da hannu”itadai tana tsaye hawaye cike da idonta ta kallesa ta kalli mus’ab”wai meye zata maka daka matsa sai tazo?”tamkar bazai tanka mus’ab ba”cike da gadara yace”idan tazo zaka gani”bema rufe baki ba ta iso Ahankali gaban table d’in ta aza dogayen hannuwanta masu Jan kalle ga yatsu a saman laptop d’insa “Azatonta Abin wasa ne”wata rikitacciyar tsawa yadako mata yana saka hannunsa ya ture hannayenta”ta rintse Ido jikinta na rawa”yaja tsaki yana kai hannunsa gefen veil d’inta”kasancewar saku saku yake saiya zame”kusan rabin gashin gaban kanta yafito”da k’arfi ya murd’e mata kunne yana fad’in daga yau zaki koma tab’a Abinda babu ruwanki dashi?”k’ara ta saki yacika kunnan yana jan tsaki,yayinda mus’ab ke kallonsu kamar tv”sharif na yatsina fuska yace”zaki mun shiru ko saina mareki ne?inaso kisani kika mun k’azanta babu ruwana da baki hayyacinki zaki sani ne!kin shigo kinata kallon mutane baki iya gaisuwa bane?”…..eh ni ban iya ba”tsaki yakoma ja”Agundure yace”daga yau sunanki *Amaan* idan na kiraki ki Amsa! tashi kibani waje”Aikuwa tana tashi da gudu ta nufi d’akin da baba lady ta shiga”wanda mus’ab na ganin yadda jikinta ke juyawa ya kauda kai yana mamakin halin Abokin nasa”Ajiyar zuciya ya sauke kafin Anutse yace”Ina baka shawara kabi yarinyar nan Ahankali,ko kuma Amaan d’in daka saka mata zance?”banza shariff yamasa ya maida hankalinsa wajen TV”dan gaba d’aya har mus’ab d’in haushinsa yakeji “shi kuwa be damu da shirun daya masa ba yaci gaba da cewa”idan kana tafiyar da ita da tsawa da hantara zata dinga jin tsoronka tana maka kallon mugu”sannan bbu kyautatawa kenan idan kamata haka”karka manta Amana Aka baka ita”idan tsohuwar nan fa ta lura kana kyararta tasanar ma mlm fa?”me kake tunani zai d’auka?….look mus’ab! kasan dai ba’a tursasani ko?”so what da duk Abinda kowa zai d’auka A kaina ne?”idan kuma na cire hannuna kanta banida damuwa da hakan sai kaje ku k’arata kaida ita”iya Abinda yafad’a kenan ya mik’e tsaye kamar zai tashi sama ya haura upstairs….sosai ran mus’ab yab’aci”sai kawai ya mik’e tsaye ya fita daga cikin parlourn”dama daga waje yayi parking d’in motarsa “kasancewar dama shariff ya sanar masa ya sallami ma’aikatan gidan sbd beson saka Ido”Akuma d’azun da mus’ab d’in zaije d’aukar su shariff ya sanar masa yayima baba ladi bayanin yadda zasu rayu Agidan “beson k’azanta,zata yimusu break fast da lucsh itada yarinyar”mus’ab d’in kuma yamata bayanin komai….. Amaan na shiga d’akin ta fad’a jikin babah ladi tana kuka”menene kuma yafaru?”ba hamma bane”kuma yace”sunana Amaan”d’an murmushi baba ladi tayi tana shafa kanta tace”to shikenan daga yau duk wanda yace miki Amaan ki Amsa da na’am”sannan kidena yawan kuka da wannan guje gujen idan bakiso kuyi fad’a da yayanki”kuma kidinga sallama duk inda zakije”dato ta Amsa tana sauke Ajiyar zuciya sai kuma tace”wai hamma yace”bana gaida mutane”to daga yau ki dinga ce masa Ina wuni”idan da safe ne kice masa Ina kwana?”yanzun ki tashi ga bayi nan kiyi Alwallah kamar yadda na koya miki idan na fito sai muyi sallah”dato ta Amsa ta tashi tsaye ta wuce bath room….sheriff kuwa da takaicin Amaan da mus’ab yayi Alwallah ya tafi masjeed”be dawo gidan ba sai bayan sallar isha’i yamusu take aways guda biyu na Abinci me rai da lafiya”dukda komai na bukata ya Ajiye d’azun da suka baro gidan mlm”yanzun kayan sawarta yakeso zuwa gobe ya siyo mata”suna zaune a parlourn Amaan na kallon TV”babah ladi ta latso tashar da sukeyin Tum & Jerry”kasancewar ta iya Amfani da romote”Ahankali yayi sallama”tun kafin ya rufe baki Amaan tace “hamma Ina wuni?”batare daya kalletaba yace”lafiya qlau” ya matsa ya mik’a mata ledar hannunsa”ta Amsa tanata kallonsa “shi kuwa bema kalletaba anutse yace”baba ladi zan wuce gidan Ammi da safe zan dawo insha Allah “babu wata matsala zan rufe gidan”idan zaku kwanta ku kashe hasken ko Ina”dato ta Amsa sukayi sallama”Atare sukaci Abincin suka k’oshi “baba ladi nata koya mata Abinda take ganin yaka mata ta koya”sai wajen tara da rabi na dare sukayi shirin kwanciya bacci…..

File Name   Miskili Ne… Hausa Novel Doc.
Title    Miskili Ne
Author    Momyn Fareesa
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Love Story
Published Date    02/03/2024
File Size    400Kb
Format Size    TXT
Phone No   08100084251
Download Miskili Ne Complete Novel Document By Momyn Fareesa

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button