Tsaki Jalila tayi, taje ta dakko trolley tafara zuba kayanta, A daren Jalila taje tasamu dadyn Hanan tace masa zata koma gida jibi saboda sunkoma makaranta, daddy beji dadi ba yacewa Jalila da kansa ze maida ita gida.
‘yan gidansu Hanan sunji babu dadi batun tafiyar Jalila, sun mata Alheri sosai, Inna ma taji babu dadi, tace itama wataran zatasa akaita kano gurin Jalila, ranar da Jalila zata koma tun safe tagama shirinta tsaf, karfe goma na safe daddyn Hanan da kansa yasa Jalila a mota ya tafi kai Jalila gida, suna tafe suna hira.
Jawwad yayi duk yadda zeyi ya hana Jalal tafiya amma wannan karon Jalal ya dage, yayi rantsuwa yace seya tafi sannan yaki gayawa Jawwad hakikanin abunda akayi masa a gida, Jawwad ya tafi gidansu Jalal yasamu daddy bayan sun gaisa yace
“daddy me akayiwa Jalal ne yace in yatafi baze sake dawowa ba, bansan me akayi masa ba”
Nan daddy yagayawa Jawwad abunda yafaru. Jawwad yace
“Amma daddy meyasa kake zargin Jalal akan wannan, daddy zan iya rantsuwa da Alqur’ani Jalal baya neman mata, koma wacece sharri take masa daddy”
“Jawwad se daga baya naga nima ban kyauta masa ba, ka bashi hakuri, yadena fushi da daddyn sa, amma kokana da masaniyar dalilin dayasa Jalal ya tsani Ilham, ko tayi masa wani abun ne?”
Jawwad yayi Jim sannan yace “A’a daddy nima bansaniba, ban san metayi masa ba”
“Anya kuwa Jawwad zan yadda bakasan komai ba?”
“daddy dagaske nake bansan komai ba”
“to shikenan, amma Jawwad dan Allah kahana Jalal tafiyar nan, nasan yana fushi dani, amma karya tafi ya bar daddyn sa”
“Insha Allah daddy zanyi kokarin yin hakan”
Jawwad ya tashi ya fita, tun lokacin da Abba yayiwa Jawwad zancen kai kudin Auren Naja yake rashin lafiya amma be gayawa kowa ba, ga kuma tension din Jalal, yakoma daki ya tarar Jalal yanata hada kaya, ya zura masa ido, yarasa mema zece masa, kansa ne yake sarawa sosai ya kwanta akan doguwar kujera ya lumshe ido, yanata sakawa yana kwancewa.
Nana tasan da dawowar Jalila dan haka tanata murna, tana shirye2 itakuma Naja so take Jalila ta dawo ta kuntata mata rai.
Karfe biyu na rana Su Jalila suka iso kano, Nana ta fito ta taresu ta rungume Jalila suka dinga murna, Abba baya gari, ya tafi da Maama lagos, kwanansu uku da tafiya, dan haka Jalila ta budewa daddy sitting room ya zauna.
Nana ta dauki kayan Jalila ta shiga dasu cikin gida, ta kawowa daddy ruwa da lemo da Abinci.
Duk abun nan, Jawwad besan su Jalila sun dawo ba, Jalila da kanta ta tafi part din Jawwad tana shiga palourn sa ta tarar da Jawwad a kwance akan kujera ya lumshe ido Jalal kuma yasa TV a gaba amma sam ba tv yake kallo ba tunani yakeyi.
Sallama Jalila tayi, sallamar tata ce ta dawo dashi daga dogon tunanin da yakeyi, be taba zaton kafin ya tafi zega Jalila ba, seda suka danyi seconds suna kallon kallo, dauke kanta tayi ta nufi gurin da Jawwad yake kwance,
“Yaya Jawwad” ta kira sunansa amma be amsaba, hannu takai ta dafa goshinsa yayi zafi sosai da sauri tace “Subhanallah” dan girgiza shi tayi,
A hankali ya bude ido yana kallonta murmushi yayi mata yace “Baby saukar yaushe haka ba Labari?”
Cikin kulawa tace “Yaya Jawwad baka da lafiya ne haka”?
Mikewa yayi zaune yace “kai amma nayi murna da dawowarki, munyi missing girkinki da kiriniyarki”
“Yaya Jawwad keep jokes aside ka rame sosai baka da lafiya, nakira layinka baka dagawa, Hanan ma ta kiraka amma bata shiga, yanzu daddyn Hanan ne ya kawoni, yana son ganinka”
Jawwad yace “Shikenan bari inje”
Jalal ya kalli Jawwad yace “dagaske baka da lafiya? Meyasa baka gayamin ba?”
Jawwad yace “meye Amfanin gaya maka banida lafiya? Kaika gayamin dalilin dayasa zaka bar kasar nan? se dazu daddy ya gayamin abunda yafaru, kuma matakin da kake shirin dauka shine ya dace? Gaba daya hankalina a tashe yake Jalal, ni bakasan a matsalar danake ba, gashi kaikuma da maganar dakazomin, gaba daya hope din iyayenka akaina yake, bakaga magiyar da daddy yakemin akan kar inbari ka tafi ba narasa yadda zanyi ba dole rashin lafiya ta kamani ba, gaba daya narasa meyake min dadi” gaba daya tausayin Jawwad yakama Jalila
Jawwad Ya mike ya fice a dakin ba tareda Jalal yace masa uffan ba, Jalila ma bayan Jawwad tabi.
Ba karamin tausayi Jawwad yabashi ba, shikansa yana tunanin yin rayuwa ba tareda Jawwad ba, amma yana daga cikin dalilansa na son barin kasar nan yanaso Jawwad yasamu kwanciyar hankali, ya karbi Aiki ya hutawa ransa dawainiyar daya dingayi masa tsawon shekaru a ganinsa wannan ce kawai hanyar dazewa Jawwad halaccin abunda yayi masa.
Jawwad yaje gurin daddy, sun dan dade suna magana da Jawwad sannan yayi musu sallama yatafi.
Tunda Jalila ta koma gidan Naja take habaici tana yada magana
“ko anki ko anso, koda dariya koda kuka seta Auri Jawwad, Jawwad ba mijin kafura bane”
Jalila tabawa banza ajiyarta, duk yadda Naja taso ta tsokani Jalila, Jalila taki kulata.
Bayan daddy ya tafi, bayan la’asar Jalila ta tafi dakin Jawwad domin tana son yin magana dashi matuka, dakin ta shiga da sallama amma bakowa a palourn, bedroom dinsa taje tana knocking sannan ta bude dakin, ta hango Jawwad yayi rigingine ya lumshe ido kaman me bacci, sallamar Jalila ce tasashi ya bude ido, mikewa yayi zaune a hankali tareda kakalo murmushi yace “Babyn Ummi, ya gajiyar hanya? Na zata by now kina can kina hutawa”
“ina batun hutawa Yayana ba lafiya, ya jikin naka?”
“lafiyata fa kalau”
“A’a ni ban yadda ba ina zuwa”
Jalila takoma cikin gida ta hadawa Jawwad tea ta kawo masa, ya karba ya shanye yace “Nagode Jalila”
“meye kuma na godiya? Yaya Jawwad magana nakeso muyi da kai”
Gyara zama yayi yabata dukkan Attention dinsa Jalila tace
“Yaya Jawwad meyasa ka amince da Auren Naja?”
Ajiyar zuciya yayi ya danyi shiru sannan yace “Jalila Maama ta takura na rasa yadda zanyi ne”
“Yaya Jawwad, tun tasowarmu bantaba son wani sama da kai ba, amma ganin Hanan tana sonka, kuma Maama bata son Alkarmu tare, banason tayi fushi da kai, bana son ta fadi wani mummunar kalma akanka dazeyi tasiri a rayuwarka, Yaya Jawwad ba dan nadena sonka nakoma gefe na zuba maka ido na barwa Hanan kai ba, ina ganin kona barka Hanan zata maye maka gurbina, Amma meyasa zaka yadda da Auren Naja, Na tabattar Abba besan komai game da Wacece Naja ba, ita kanta Maama akwai abubuwan da bata saniba game dasu Naja” Jalila takarasa maganar idonta taf Hawaye,
“Yaya Jawwad, Hanan zata shiga damuwa sosai, tana maka so bana wasaba shiyasa na yadda da soyayyar da Hanan take maka ne dan samun nutsuwa da daidaituwa tsakaninka da mahaifiyarka, amma meyasa zaka Amince da Auren Naja?”
“Jalila bijirewa Auren Naja ze kuma jawomin wata damuwar ne, Har Yanzu Maama takasa gane Yaya mairo ba kaunarta take ba, ta riga ta zigata idan nace banason Auren nan komai ze iya faruwa, Amma ni kaina bana son Auren nan Jalila, Jalila na hakura da kene kawai saboda nasan idan har na Aureki bazaki samu kwanciyar hankali da nutsuwa ta fannin dangin mahaifiyata ba, Jalila bayan tafiyarki Maama ta kirani akan maganar Auren tace Abba zemun zancen Auren muddin na bijire nace ke nakeso” sekuma yayi shiru yakasa cigaba
“Ina jinka bakomai karasa”
“Jalila Maama cewa tayi muddin na bijirewa maganar Auren Naja nannunawa Abba ke nakeso bata yafemin ba”
Zare ido sosai Jalila tayi, ta danyi shiru sannan ta girgiza kai
“Yaya Jawwad ka kwantar da hankalinka kayita Addu’a komai zezo da sauki Insha Allah, Allah ya ganar da Maama, Amma zaka iya Auren sister na ko Yaya?”
Shiru yayi bece komai ba
“Yaya Jawwad nida Hanan duk dayane, tana sonka sosai Zata kulamin da kai yadda yakamata, Insha Allah zanyi duk kokarin da zanyi amma bana son kacigaba da damuwa”
“To Babyn Abba na dena Insha Allah”
“Yawwa Yaya Jawwad dina, kamanta da wannan batun gaba daya, Mutum managarci kamarka be dace da mace irin Naja ba, kadena damuwa kar ciwo yakama ka”
Gyada mata kai yayi yana murmushi. Jalila ta mike ta fito daga dakin tanajin wasu Hawaye, harga Allah tana kaunar Yayan ta a zuciyarta babu macen dazata so tarasa managarcin mutum kamar Jawwad, harzata fita ta hango abu akan center table, dan haka ta dawo da baya ta tsya tana dubawa.
Jalal yana dakinsa yakuma tattar dukkan wani abu dayake bukata, ya hadesu guri daya sannan ya fito ya tafi cikin gidansu, dakin daddy ya tafi ya tarar dashi yana Aiki akan system dinsa.
Daddy na ganin Jalal ya ture system din yana murmushi
“Welcome my son”
“Thank you dad”
Jalal yasamu guri ya zauna sannan yace “Daddy naga bazan iya tafiya ba tareda nayi maka sallama ba, ina kaunarka fiye da tunani dukda kamin abunda bazan manta ba, amma bazan iya rabuwa da kai ta har Abada ba, daddy duk inda zan kasance a fadin duniya muna tare, Dubai zan tafi zamu dinga haduwa in kaje can, zan dinga zuwa Nigeria saboda wasu mutane, Amma Mummy taje ta riki Ilham a matsayin yar data haifa “
“My son nibana farinciki da wannan tafiyar taka, nafison ka kusada mahaifiyarka, Jalal idan katafi ba idon kowa akanka babu mece maka bari, bam san wace irin Rayuwar zakayi a can ba, Dan Allah Jalal
” Ya isa haka daddy karka rokeni dan Allah 🙏, Mummy bata sona bata kaunata, bata son farinciki na kanta kawai tasani, damuwarta ce kawai damuwa damuwar wani bata ta bace, daddy kasan yadda zuciyata takemin idan nasan cewa uwata na raye amma bana tareda soyayyar ta saboda wani dalili nata, kalli Rayuwar danakeyi saboda son zuciyarta, daddy Jawwad yayi yayi yaga nakoma mutumin kirki amma abu ya gagara, Amma wani dalili da ban taba tunani ba yana kokarin sani in rabu da shaye2, daddy idan har na cigaba da zama a kasar nan Mummy tanamin abunda takemin to bana tunanin bakin ciki ze bari in rabu da shaye2″ Hawaye sosai Jalal yake kaman mace
Jalal yakamo hannun daddy ya rike a cikin nasa, Sannan yadanyi murmushi yace “Daddy na kasan wani abu? Inada Ajiya a Nigeria bazan iya barinta gaba daya ba, in kaga nabar Nigeria gaba daya to Ajiyata na dauka, kamin fatan Alkhairi daddy na”
Yana gama maganar ya sumbaci hannun daddy ya sakeshi ya juya ya fice, daddy yarasa abunda yake masa dadi, idan Jalal bayaji ta wani fannin baya ganin laifinsa saboda tabbas rayuwarsa cike take da kalubale daban2.
Jalila takoma daki sukayi waya da Hanan amma batace mata komai akan Batun Auren da za’ayiwa Jawwad ba, sannan tacigaba da kokarinki kwantarwa da Jawwad Hankali tareda bashi karfin gwiwa,
Jalila sam taki kula Naja, ta maida ita kamar wata mahaukaciya, tayi zage zagenta da habaici amma Daga Nana har Jalila sukaki kulata.
Ilham ta shirya takuma zuwa gidansu gurin ummanta, domin din yadda sukayi da malaminsu,
“Ilham malam ya tabattar min Jalal baya neman mata, Sannan aikin da’akayi masa har yanzu yana nan ajikinsa, amma akwai matsala”
Da sauri Ilham tace “matsalar menene kuma?”
“Malam yace aikin da’akayi masa ya rage tasiri akansa, saboda akwai wanda yake ta kokarin rusa komai”
Girgiza kai Ilham tayi tace
“Umma wallahi wannan yarinyar ce da na nunamiki a Asibiti, hatsabibiya ce ta gaske ni Jalal yaciwa mutunci agaban iyayensa yace ya tsaneni ya tsani me sona”
Zare ido Umman tayi “Yatsaneki ya tsani me sonki dan Iskanci, kan bala’i ai wallahi daga shi har khadija basu isaba senaga abunda ya turewa buzu nadi”
“to ai Umma ba wannan bama, akan case din nan na zargin yana neman mata, yace kasar nan ze bari wai inyaso Mummy ta rikeni ni ta haifa bashi ba”
“Yabar kasar nan saboda me? Ke Ilham akwai aikifa baki kirin agabanmu, idan yaron nan ya tafi be Aureki bafa? Ita khadija me tace?”
“me kuwa zata ce ranar kaman ze rufeta da duka”
“tsinanniya ni dama ya daketa ta mutu in yaso yakare rayuwarsa a prison”
“Ahha umma akan me? Ta mutu akaishi prison bamu mallaki dukiyar damuke Hari ba?”
“to ai Ilham tsawon zamanki a gidan nan ba wani kokari da kikeyi, ace duk wannan shekarun ko kallon kirki baya miki sema tsana”
“to Umma yazanyi? Ni tun farko sonayi inyi me gaba daya kowa ya huta, kuma kiris ya rage amma ina shegen taurin kaine da shi kamar dutse ne a kirjinsa ba zuciya ba”
Umma ta numfasa tace “Munyi maganar da maman Yaseera, tacemin akwai wani malaminta a can Nijar, munyi da ita zanje ta rakani shima mu jarraba irin nasa Aikin mugani”
“to Amma Umma tayaya? Kasar fa ze bari”
“Dan ubanki kije kiyi duk yadda zakiyi, ki lallabashi in ta kama hada kuka akan bakya so ya tafi, ni nama rasa dalilin dayasa ya tsaneki haka wallahi, keba muniba to kodai yasan abunda mukeyine?”
“Haba dai yaza’ayi yasani? Ni dai Umma dan Allah ki kai Sunan yarinyar nan kawai intakama a kasheta, dan wallahi yanzu ba zargi nake ba, na tabattar ita yakeso”
“tayaya kika sani?”
“Umma ninake ganin abunda nake gani, wallahi Umma idan kinga Jalal ya tabani to bisa kuskure ne, koda wasa baya bari ya tabani, bama ni kadaiba kinsan halinsa bayason mata su rabe shi, amma ganin idona naga ya rungumeta, itakuma makirar tsinanniya tayi luf a kirjinsa, Allah ka dai yasan abunda sukeyi wallahi na tsaneta kamar mutuwata, kuma bakiga yadda baban Jalal din yake mutunta ba, keba shi kadai ba har Mummy bakiga yadda take mata ba”
Jinjina kai Umma ta shiga yi sannan tace
“kyaleni da ita, zata gane kuskurenta, nasan yadda zan bullowa lamarin zata gane bata da wayo, kafin inje gurin malamin, zan gayamiki yadda zakiyi kowa se ya tsaneta”
Haka sukayi ta hirarsu su saka wannan su kwance wancan.
Jalila kullum dare setayi salla takaiwa Allah kukanta haka take raba dare, gata gwana gurin yawan tilawar Alqur’ani, shiyasa Jalila ta yadda da duk wani abu da take aikatawa a rayuwarta take Nasara tasan dogaro ga Allah, riko da ibada da nacewa Alqur’ani shine matakin dukkan wata Nasara a rayuwarta, duk abunda ta tinkara setaga bayansa, ta taba duk wanda takeso komai matsayinsa amma babu abunda ze faru da ita, ta yadda da dukkan abunda ta roki Allah intaga bata samu ba to lokaci ne beyiba, ta yadda wannan shine matakin Nasararta a rayuwa wadda Umminta da akewa kallon tubabbiyace ta dorata a wannan tafarkin.
Tunda Jalal yace zeyi tafiyar Nan Mummy hankalinta yakasa kwanciya, gashi tasan yadda Jalal yakejin haushin nan nata baze saurareta ba, Amma yazama dole Jalal ya Auri Ilham dan cikawa Saudat Alkawarin ta wannan ne kawai abunda zatayi ta wanke laifin ta a gurin Saudat.
Mummy tayiwa daddyn Jalal magana akan yayi wani abu ya hana Tilon danta tafiya ya yabarta amma amsar daya bata ta mata ciwo
“da lokacin danake miki maganar ki hakura da tafiya karatu kikula da tilon danki da kinji magana ta da koba duka ba ko yaya da Jalal yaji maganarki, ko kin manta watansa bakwai kika dena bashi Nono, a wata bakwanma se lokacin da kika gadama, niba abunda zan iya ki kyaleni”
Ba karamin ciwo maganar daddy tayi mata ba amma ba yadda ta iya.
Ilham ta shirya taje dakin Jalal don jarraba ganin ko ze saurareta amma kusan ya kwashe komai nasa dake dakin nan se abunda ba’a rasa ba, tasan yana gidansu Jawwad dan tunda abun nan ya faru yakoma can dan haka ta bishi can gidan.
Jalila ta kaiwa Jawwad Abinci amma baya nan, se Jalal a palour, bata kulashi ba ta shiga tana gyrawa Jawwad bedroom. Tagama ta fito palour yana zaune inda Tabarshi yana daddana waya, ta fito tazo ta zauna a teburin dake gabansa, tana fuskantar sa, dagowa yayi ya kalleta, kallon dayake mata dukta tsargu, basarwa tayi tace
“Abokin Yaya wai dagaske tafiya zakayi?” A ranshi yace lallai yarinyar nan sekace bata san sunansa ba, nikam nace ai kaima haka kake cemata kanwar Jawwad 🙄,
Sauke idonsa yayi sannan yace “Kafin kiyi tafiya ai nagaya miki ko?”
“Aini ban zaci dagaske kake ba” dagowa yayi yana kallon ta karo na biyu yace “na taba yimiki karyane? Ko Ba kya son in tafine?”
“to inma ka zauna mekake karamin inka tafi hutunane ai, dan ba karamin wahala nake sha saboda kai ba, da inka tafi na huta banga abunda kayiba balle inji haushin ka, amma ni Su Mummy nake dubawa da Yaya Jawwad”
Ilham ce ta shigo dakin da Sallama Amma abunda ta gani zata iya kiranshi da mummunan gani, Amma ta dake tunda sulhu take nema, gaba daya suka daga kai suna kallon Ilham, tattara nutsuwarta ta boye damuwar ta ta tako a hankali tazo gaban Jalal ta tsuguna tace “Yaya gurinka nazo”
Bece mata uffan ba itama Jalila bata tashi daga gabansa ba, Ilham tace “Yaya Jalal san girman Allah dukda kace baka sona, dan Allah karkayi tafiyar nan, bana son ka tafi, Mummy ta shiga damuwa sosai bata iya cin Abinci se kuka takeyi dan Allah kayi hakuri nikaina zan shiga damuwa sosai, Jalal so fa ba karyane ba ni ganin gilmawarka a cikin gidanma ya isheni farinciki amma bansan dalilin dayasa kake kina hakaba “
Wani kululun bakinciki ya tokarewa Jalal rai a fusace yace ” dalla malama ki tashi kibani guri, ai bakinku daya Mummy karkinemi ki rainawa kanki hankali, bana sonki bana kaunarki kifita daga rayuwata tun kafin inyi miki Illa, babu wanda ya isa ya hanani tafiya ba kukan Jini ba ko Hawayen karfe zatayi ba ruwana, ta manta sanda nake mata magiya take tafiya tana barina, lokacin danake matukar bukatar ta, kinga dalla bacemin daga nan ko in ballaki” yakarasa yana zazzare ido gaba daya jikinsa bari yake
“wai dan Allah wace irin zuciya ce da kai, baka yafiya baka mantuwa, koma metayi maka ai ita takawowaka duniya, tana sonka shiyasa bata so ka tafi, Yaya Jawwad ya dena zaman gidan nan saboda bayason ya dinga tuna zakayi tafiyarka ka barshi, kalli yadda Ilham take kan gwiwoyinta tana kuka amma kai ko a jikinka meye hakane?”
Kafe Jalila yayi da idanuwansa da ita kanta wani lokacin suke bata tsoro, gashi yakara hade rai sosai.
Wani bakinciki yakara tokare kirjin Ilham kamar zuciyarta ta fito waje.
A hankali yafara motsa baki yace
“Wallahi idan har banyi tafiyar nan ba to bana raye, ba ruwana da halin da wani ze shiga saboda babu wanda ya damu da halin da nake ciki” yafada yana kallon kwayar idon Jalila
Kawai sukaga Jalila tana dariya, wadda ke matukar kara mata kyau tace
“to shikenan Ai seka tafi in gani” ta mike tsaye takuma kallon sa ta kwashe da dariya seka dawo, karka fasa tafiya naga ta inda zaka tafi ai, kekuma Ilham na dawo koki dawo da abunda kika dauka kokuma inzo da kaina”
Kawai ta juya ta fice ta barsu a zaune suna mamakin maganar ta.
Mikewa Jalal yayi ze fice yabar dakin Amma Ilham ta mike ta sha gabansa
“Haba Jalal yanzu bazakaji magiyar
danake maka ba, dan Allah Jalal kayi hakuri, karkayi tafiyar nan, zan shiga mugun yanayi dan Allah Jalal, wallahi ina sonka, tunda kuruciya ta har kawo I yanzun”
“Ke waini sa’an wasankine? Wallahi koki matsa ko in tattaka ki”
Ya tureta gefe ya fice Abunsa, Abun duniya duk ya dami Ilham, Jawwad ne kadai ke iya sarrafa zuciyar Jalal wani lokacin, yanada matukar kafiya da taurin kai, gaba daya tunanin ta ya kwace.
Jalila takoma cikin gida ta tattara abubuwan dazata bukata dan gobe in Allah ya kaimu zata koma makaranta,
Karamar wayartace ta cika dakin da ringing, Jalila taga bakuwar lamba ta share tacigaba da Aikinta, amma still aka cigaba da kira har kusan karo uku, seda ta danyi tsaki sannan taja wayar tasa a kunnenta
Ajiyar zuciya akayi sannan akace “Masha Allah, kin karyamin record bana kiran mutum sama da sau biyu, komai tsananin bukata ta kuwa, Amma ta dalilin son danake miki har sau hudu ina kiranki”
Sarai ta ganeshi amma ta maze tace “ko zan iya sanin da wa nake magana”
“Ohh am sorry dear, bankoyi miki sallama ba, balle mugaisai nafara miki surutu, Ahmad ne”
“Ok Allah sarki yakake ya gida ya iyali”?
“Alhamdilillah queen, kin tafi bako sallama, ban san zaki koma kano ba ai”
“Aikam abune na gaggawa ya tasomin, in ban manta ba ranar agabanka aka kirani”
“Hakane fatan kowa da komai lafiya”
“lafiya kalau, ya na baroku?”
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
“komai lafiya amma kintafi kin barni da kewarki, duk lokacin danake wani abu kona rufe idona ke nake gani Jalila, kitemaki zuciyar maraya” ya karasa maganar cikin sigar magiya
“Kai karka bada maza mana, yanzu idan abokan Aikinka sukaji wannan aise suyi Maka dariya, babban soja kaman kai kana haka akan mace, macenma wata ‘yar yarinya”
Murmushi yayi yace
“Jalila ai babu wani batun namiji ko soja in ana maganar fage irin na soyayya, ba ruwansa da matsayinka, girmanka ko mukaminka, ba ruwansa da na birni kona kauye, dan haka kidena wani batun maza”
“hmm Wannan bayani haka yakamata ka bude makaranta ka dinga bada darasi”
Murmushi yakumayi yace “Tunda haka kikeso ai se ayi, kece director mukuma dalibanki”
“Tab aini bansan komai a wannan harkar ba”
“Ahh haba dai?”
“dagaske nake fa”
“Aikam zan koyardake yadda yakamata”
“to shikenan seda safe, gobe in Allah ya kaimu zanje school”
“hakane hakan yayi kyau, Allah yabamu alkhairi, zamu hade a dreams zanbiyoki har kano kan shinfidarki”
Murmushi Jalila tayi “Allah yabamu Alkhairi”
Ta katse wayar ta danyi murmushi, can ta hango Nana ta shige bargo ga uban zafi se wani kashe murya take ba’ajin abunda take cewa, Jalila ta mike ta yaye bargon, Nana ta hada gumi amma ko zafin bataji saboda tana soyewa da Mahmud, Jalila tace “Allah ya shiryaki”.
Ilham ta dade tana Nazarin me Jalila take nufi da Jalal baze tafi ba, danta fara karaya da lamarin Jalila yarinyar sekace Aljana idan tayi niyyar abu setayi shi.
Jawwad sam yaki kula Jalal gashi gobe in Allah ya kaimu karfe biyu na Rana ze tafi, yanzuma da Jawwad yadawo daga sallar isha’i daki yayi tafiyarsa ya kwanta, Jalal yabishi dakin ya zauna kusa dashi yace “Haba nawan yanzu fushi kake dani haka?”
Mikewa zaune Jawwad yayi yace
“Jalal dan Allah ka kyaleni, kace zaka tafi gaka nan ga hanya seka dawo”
“Jawwad nima inajin abunda kakeji a ranka, A tunanin ka rabuwa da kai abune me sauki a gurina, shekaru Ashirin da bakwai muna tare idan ban manta lissafin ba, Jawwad tafiyata shine samun saukinka, kaima ja maida kai karasa gina rayuwarka, bazan iya barin Nigeria gaba dayaba saboda ku biyu daddy zamu dinga haduwa a can dubai dashi”
“Jalal wannan ba uzuri bane ba, ni na gaba gayamaka na gaza da kai menakeyimaka na wahala, Allah ne ya hada jinina da kai bani da dan uwa Namiji kaidin nan dai tare muke faduwa mu tashi tsawon wannan lokacin, sannan lokaci daya kace Zaka barni tayaya zanyi farinciki Jalal”
“Am sorry Jawwad nasan babu dadi, kuma kana tunanin Wace irin Rayuwar zanyi a inda zanje, Jawwad Ina kokarin dena shaye2, A sanadinka a tsatsonka nasamu me haskamin bakar hanyar danakebi, dama lokaci dayawa kadaici da bacin rai dakuma miyagun abokai kesani kara kaimi gurin shaye2, Amma yanzu an janye miyagun abokai daga jikina, Jawwad idan na tafi inason in koma makaranta “
Sa sauri Jawwad ya kalleshi yace” dagaske kake? Da kanka kake fadin zaka koma Makaranta? “
” Kwarai kuwa zankoma Insha Allah “
Rungumeshi Jawwad yayi yana cewa” naji dadi dan uwana amma naso ace kana nan kusa dani, Amma dukda haka ni zan dinga biyoka Dubai din”
Kasan zuciyar Jalal ba wata makaranta kawai dan hankalin Jawwad ya kwanta ne
“kobakazo bama nizan dinga zuwa akai2”
Haka suka cigaba da hira.
Da wuri Yau Jalila ta shirya manu driver ya kaisu makaranta, ‘yan ajinsu Jalila sunyi murnar dawowarta nan aka dinga nunawa wanda basu santa bama, hatta malaman dasuke tsangwamarta suke ganin bata iya komai ba tabasu mamaki kwarai dagaske, saboda ba’a mata tambaya ta amsa a Aji, se lokacin data ga dama take zuwa lectures, wataran ma bata Attending, bata handout sedai in malami zeyi lectures ta dakko jotter, idan malami yayi ba dai2 ba bazatayi shiruba setayi magana, wannan bakin nata kesawa a koreta daga Aji, Akwai malamin da har test ya hanata yi, Amma a haka babu wanda yake da points dinta a kaf department din nan, hakika wasu mutanen ‘yan baiwa ne, shiyasa har Abada karka wulakanta mutane dan kowa baka san irin baiwar da Allah yayi masa ba. Ba iya dalibai ba hatta malamai sunyu mamakin Jalila ce takeda wannan kwazon.
Amma ita Jalila abunda yafi daukar hankalinta be wuce yadda har yanzu ake surutu akan abunda yafaru da Saleema da mahaifinta, Saleema ta warke amma bata iya shiga cikin mutane dan gaba daya ta dena zuwa makarantar, Sameera kam da farko ta tausayawa kawarta abunda yasameta Amma daga baya tunda aka sakesu daga police station tacigaba da abunda takeyi.
Jalila a ranta ta dinga jin anya kuwa ta kyauta abunda tayi, yanzu tayiwa Saleema dalilin dena zuwa makaranta, ta kunyata ta a idon duniya itada mahaifinta, Amma data tuna abunda Alhaji Kabir ya aikatawa Jalal, dakuma yadda ya dinga takuramata se yayi lalata da ita, da yadda ita kanta saleema suka addabi makarantar se taji hakan shi ya dace dasu.
Tun safe Jawwad ya bar gida sukayi sallama da Jalal yabar gidan.
Wajen sha biyu na rana Jalal yagama shirinsa tsaf, ya tsaya ya duba passport dinsa don yasa a karamar Jakarsa, Amma passport yace daukeni inda ka ajiye, ya duba ya duba amma be ganshi ba, hankalin sa ya tashi sosai ya duba kayansa be ganshi ba, gidansu yatafi ya duba dakinsa amma be barshi acan ba, yana kokarin fita daga dakin ne Mummy ta shigo dakin.
Ya tsaya yana kallon ta,
“Yanzu Jalal tafiya zakayi ka barni, laifina har ya kai ka kauracemin gaba daya, Haba Jalal koba komai nifa mahaifiyarka ce, kai kadai nake da baka tunanin halin dazan shiga inka tafi ka barni?”
Maganganun Mummy sam basuyi tasiri a zuciyarsa ba, seda yabari tagama gaba daya, kawai yaraba ta gefenta ya fice, danshi mugun haushin ta yakeji.
Mummy tarasa abunda yake mata dadi, ta zauna ta rushe da kuka a gurin, Abunda yakara bawa Jalal haushi be wuce yadda yana fitowa yakuma cin karo da Ilham ba, itama magaiyar take masa amma yai biris yai ficewarsa.
Jalal yayi duk tunanin daze yi amma ya rasa inda Passport dinaa yake, wayarsace tayi kara alamar sako ya shigo, Abuda ke cikin sakon ne ya razanashi sosai yasashi mutuwar tsaye wai an soke visa dinsa.
“Why!!!? Ya fada da karfi ji yayi yana neman ya fadi jikinsa na rawa, yanemi guri ya zauna ya dafe kai yai shiruu to laifin meyayi aka soke masa visa haka? Shidai yasan a Dubai be taba zuwa yayi laifi ba, Meyasa haka kodai Jawwad ne ya dauke masa passport, kai yasan Jalal beze masa hakaba Anya ba daddy ne yasa aka soke visa ba.
“Seka tafi in gani Ai, naga ta inda zaka tafi”
Maganar Jalila ya tuna, “to Amma tayaya Jalila zata iya sawa a soke masa visa, wata sani babba haka dazata saka ayi masa haka? Koma ita ta dauki passport dinsa, kai baya tunanin Jalila zatayi haka”
Amma dayayi shiru ya tuna irin gwaramar data hadawa Jeje da Alhaji Kabir abun ya zarce hankalin sa. Aikuwa a gigice ya tashi ya fito ya nufi gidansu.
Zahra batazo makaranta ba sunyi waya da Jalila tace mata batajin dadi ne shiyasa batazo school ba, bayan sungama lectures din farko Jalila tafita neman abunda zataci, gashi tana son zuwa banki ATM dinta yayi expire, dan haka ta siyi Ruwan jarka da biscuit tasaka a Jakarta ta nufi banki dan taje ta dawo da wuri, wayartace tafara ringing kaman karta daga, ta daga setaji muryar Ahmad, gaisawa sukayi suka shiga hira, Ahmad ya iya hira ga ban dariya shiyasa Jalila take sauraronsa, gashi ya iya soyayya da tattali, tabar department tayi nisa tana tafiya da waya a kunnenta taji Anyi wani jakin parking a bayanta, tsayawa tayi ta waiga a birkice dan ganin wani me kokarin ne haka, Amma wanda taganine yasa gabanta dukan biyar biyar, Jalal ne babu alamun Rahama a fuskar sa, ya tamke fuska sosai kamar be taba dariya ba.
Addu’a ta shiga yi a zuciyarta Allah yasa kar yayi mata tijara a bainar nasi. Ahamd yanata magana a waya amma shiru, Takowa yashiga yi yana nufota, yayinda ita kuma tarasa abunyi, ta kame a guri daya tana zare ido, yana zuwa yasa hannu ya janyo ta, ba musu tabishi ya bude gaban motar ya turata ya rufe, ya zagaya ya kunna motar yafizgeta a guje, tunda suka shiga motar bece mata uffan ba itama haka, Sedai tasaka hannunta ta rike kanta ta sunkuyar da kai dan tana matukar tsoron tukin Jalal, tukine na ganganci yakeyi kamar mara hankali.
Can Jalila taji yawan karar motoci ya ragu, A hankali ta bude ido taga sun doshi wani katafaren gida, yana zuwa masu gadi suka bude masa gate, ya shiga da motar yayi parking, se daga masa hannu sukeyi amma ko kula su beyiba,
bude motar yayi ya fito ya bude mata a tsawace yace mata “fito” ba musu ta fito yakuma fizgarta zuwa cikin gidan dabata san ko inane ba,
A can kasar zuciyarta tana ta Addu’a kuma tanada yakinin Jalal baze cuceta ba.
Suna zuwa wani tankasheshen palour, ya saketa ya kalli cikin idonta da yau ya raina fata take tsuma, a tsawace yace mata “Ina passport dina?”
“Ni ban dauka ba”
“Karya kikeyi”
“Niba karya nakeyi ba, ban dauka ba”
“Jaleela you are lying” jin yadda ya fadi sunan tayi ya tsarga tundaga kanta har kafarta.
“Nifa ba karya nakeba, dan Allah ka maidani, inada lectures fa”
“Ba abunda ya dameni bane, ni kika hana nawa uzurin kike gayamin kinada lectures, kibani passport dina”
“wai waya cemaka nina dauka? A ina zan ganshi?”
“keki gayamin jiya, kuma kika cigaba da rainamin hankali sena kakkaryaki, kibani passport dina ko in babbalaki”
“to Amfanin me zemaka bayan an soke visa?”
“Kekika dauka kenan? Ban abina tunda banaki bane, meyasa kikayimin haka? Akan me? Me nake tsinta a kasar nan banda bakinciki, Wace Rayuwa ce me Amfani nakeyi anan din, kowa yana kyamata da halayena babu soyayyar uwa a taredani ta fifita bukatarta akan farinciki na, se kokarin cusamin yarinyar dake neman halakani take, mahaifina danake da kwarin gwiwa akansa amma shike zargin ina neman mata, zaman menake a Nigeria banda takura da bakin ciki? Kowa kyamata yake akanme? Ba gara inje inda ba’asanniba inyi Rayuwata ba wanda yasanni ba, kibani passport dina” idonsa gaba daya ya koma Ja, jikinsa tsuma yakeyi.
Jalila ta fuskanci idan tayiwa Jalal rashin kunya yadda yake a fusacen nan ze iyayi mata ba dadi, dan haka ta kwantar da murya tace
“Shikenan is Ok, samu guri ka zauna zamuyi magana”
Cikin tsawa yace “bazan zaunaba, kibani passport dina”
“Idan baka zauna ba bazan gayamaka inda yake ba, Zauna tukuna”
Seda ya danyi jimm sannan ya zauna, ta zuge jakarta ta dakko ruwan da ta siya zata sha, ta bude ta mika masa, ba musu ya karba ze fara sha tace “Kayi Bismillah” seda ya dan harareta sannan yayi ya shanye ruwan se sauke numfashi yakeyi saboda bacin rai
“Kasan wani abu? Nina ga passport dinka akan center table na dauka, sannan nina saka aka soke maka visa”
Tsareta yayi da ido amma bece komai ba
“banyi haka dan inbata maka ba, nayi hakane dan sama maka mafita, kasan hukuncin me sabawa iyaye, muddin kayi tafiyar nan bada san ransu ba zaka iya samun matsala, Abokin Yaya laifin da mahaifiyar ka tayi maka wannan tsakanin tane da mahaliccinta, Amma abunda kake mata ba dai dai bane ba, kamata yayi ku zauna lafiya cikin hikima ka nunamata kuskuren da take aikawa, na baka misalai wancan karon daka kusa karyamin hannu, inkaji kaddarar wani zakaga taka ba komai bace ba, nima misali ce a gareka, na tashi ba mahaifi Allah ya karbi abunsa inada karancin shekaru, ga tsangwama saboda mahaifiyata daga baya ta musulunta, yanzu itama babu ita bansan a ina take ba, Natashi da kaunar Yayana, amma mahaifiyarsa batasona inaji inagani saboda kar mahaifiyarsa tayi masa baki na sadaukar da soyayyata na hakura “
Ta danyi shiru hawaye nabin fuskarta “ABDUL nasan dacin a tsangwami mutum amma kai da gatanka kana tareda iyayenka, kana da gata, suna kaunar ka wata kaddarace ta gifta dazaka iya gyarata, yau inka dena shaye2 ka gyara tsakaninka da Allah da iyayenka ze wuce kamar bakayi ba, nikuwa fa? Nasani ko Aure nayi se an gorantamin rashin dangin uwa, na ubanma waye Abba ne kawai, tare kuke da Yaya Jawwad kasan komai wani abunma ni bansaniba, Why Jalal, wanda yarasa iyaye yayi kuka, kai kana taredasu amma idonka ya rufe”
Sosai Jalila take kuka, yayinda jikin gogan yayi sanyi gaba saya, Jikin Jalal yayi sanyi matuka, kura mata ido yayi, yana tuno lokacin dasuke mata wasa shida Jawwad yana tuno abubuwa dasuka shude gaba daya tausayinta ya kamashi, handkerchief ya dakko a Aljihunsa, yana goge mata Hawayane yayinda taketa sheshaekar kuka kaman wanda akayiwa dole yace
“kidena kuka please”
“Ni kylaeni bazan dena ba din” tasa hannu a jakarta ta dakko passport din ta aje masa “ga passport dinka nan, seka dawo” tana kokarin tashi seji tayi yace
“Aina fasa” tsayawa tayi tana kallonsa
“Eh dagaske nafasa”
“Meyasa kafasa?”
“da farko kin dakukemin passport, kuma kin lallaba kinsa an sokemin visa daya zan tafi?”
“Kayi hakuri nasan kaji ba dadi abunda nayi, amma zaka iya nema na wani kasar katafi”
“Nafasa amma ya akayi kikasa aka soke visa na”
Ta goge hawayenta sannnan tace “daddy Hanan nagayawa ranar dazamu dawo, shine yace kar indamu zssa a soke”
Jinjina kai yayi ya danyi shiru tace
“nika tashi ka maidani”
“Saboda me?”
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
“Saboda haka nace, meyasa zaka kawoni inda ban saniba, ga gidan bakowa ni gaskiya ka maidani”
“hmm hakane nan inda baki sani bane, zan maida ke amma sekin gama kukan, nan gidanmu ne na gadon kaya inda aka haifeni, inda nayi rayuwa me dadi, dukda ba me dadi ce yadda nakeso ba, amma nayi Rayuwa dani da Jawwad daddy Rayuwa me cike da jin dadi” ya mike tsaye yace ‘ina zuwa”
Ya hau kan benen ya dan jima sannan yafito da wata Jaka a hannunsa duk ta danyi kura, yadawo yasamu guri ya zauna, har yaje ya dawo Jalila bata dena kukan datake ba, yasa hannu ya dan karkade Jakar sannan ya bude zip din, wasu uban hotuna ne aciki masu tarin yawa, yasa hannu ya debo wasu, ya mikawa Jalila, tasa Hannu ta karba tafara dubawa a tsanake, fuskarta sharkaf da hawaye amma hoton farko data gani yasata yin murmushi, Jalal ne da Jawwad suna kanan basufi shekaru biyar ba sun zazzaro ido suna sanye da kaya iri daya, haka ta dinga kallon hotunan tana dariya, galibin hotunan hada Umminta a ciki kan wani hoto taje, Jalal ya nutsu ya dauki wata Jaririya yana kallon ta,
Tace “Wannan wacece? Kanwarka ce”
“gata nan dai kalleta baki gane wace ba?”
Jinjina kai tayi alamar Eh, karba yayi yakuma duba wani yabata yace “wannan fa” itace batafi shekara biyu ba Idonta duk hawaye Sunsata a tsakiya
Ba karamin dariya hoton yabata ba “Wannan ai nice”
“wancan ma kece ai”
“to a ina kasamu wannan hotunan haka”
“Abee yanada camera da, shiyake mana hotuna in aka wanko daya abawa Ummi daya abani nake tara nawa, wasu kuma a gurin ummi na karbesu, wasu hotunan bani dasu suna gurin Ummi”
“lallai ka iya Ajiya”
Nan tadinga kallon hotunan, har hoton Iyayen Ummi akwai seda ya nuna mata, gaba daya ya manta da fushin dayakeyi, ita kuma ta manta tanada lectures
kan wani hoto ta kai, Ummice a jiki da Abeenta, sunsakata a tsakiya duk sun kalleta suna murmushi, ta tsaya ta zubawa hoton ido, sekuma Hawaye ya shiga zubowa daga idonta kuka sosai
Jalal yai kuri da ido yana kallon ta, hannu yasa ya zare hoton
“Bani tunda kuka zakiyi, ban hotuna na”
Cikin kukan tace “yi hakuri na dena”
“baza’a hakuran ba, bani nan”
Yasa hannu ya tattare su, rikewa tayi “dan Allah kabari in karasa”
Yana kokarin fizgewa ne hotunan suka zube a gurin, idonta ne yakai kan wani hoto dayasa taji hantar cikinta ta kada.
Da sauri ta dauki hoton tace “Wannan wacece?”
Karba yayi ya duba sannan yace “bakisan wannan ba? Kakarkuce wadda ta haifi su Abba”
“Wannan ai kakar su Hanan ce”
“kamar yaya?” ya tambayeta cikin rashin fahimta, nan ta kwashe komai tagaya masa na zuwanta bauchi jinjina kai yayi yace “masha Allah, nina san wannan kamar da kuke ba’a banza ba, tabbas abunda kakar Hanan tagaya miki haka yake, Sun baro garinsune saboda hari da ake kaimusu, amma yanzu karkiyi saurin fada, Abba yakamata kifara samu da wannan maganar, ya dade yana bincike ko Allah zesa yasamu wani daga dangin iyayensa, tunda basu san kowa ba daga family dinsu, Inna kawai suka sani da baba”
“Allah yasa gaskene Su Hanan ‘yan uwan su Abba ne, inda suke sunada yawa sosai estate ne guda gaba daya family dayane”
“‘ yan uwankune Insha Allah, bari in mayarda hotunan nan se in maida ke”
Ta gyada masa kai ta jirashi ya mayar ya dawo, ya kalleta yace
“muje ko”
Ta wuce gaba ya biyo ta abaya ta tsaya ta wigo ta kalleshi “dan Allah karkayi wannan tukin, dan Allah” bece komai ba ya bude motar ya shiga, itama budewa tayi ta shiga ya kunna motar, aka bude masa gate ya fita, masu gadi nata daga masa hannu amma yayi musu banza,
“Suna maka magana amma kayi musu banza ba dadi fa”
“to mezan musu? Ko sokike in sauka in tsaya ina surutu?”
“A’a bahakaba at least ko daga musu hannu kayi”
Be kuma kulataba ya cigaba da tukinsa,
Sarkar wuyansa ta kalla, sekace ba ďan musulmi ba, “Kafasa tafiyar dai ko?”
“baki yadda dame na fada bane?”
“A’a ni banceba, Amma dan Allah kadena yi wa Mummy abunda kake mata, dan Allah”
“Waike ba Adda tagaya miki komai game da rayuwata ba mekikeso inyiwa Mummy?”
“Bahaka bane ba, inka mutu tana fushi da kai Allah ma zeyi fushi da kai, kila sanadiyar yafemata kaga Allah ya daidaita maka Al’amuranka, mutane zasu dena kyamarka”
“Anya Al’amurana zasu gyaru? Mutane bazasu taba sakin jiki daniba kowa ya riga ya gujeni se kalilan din mutane”
“Al’amuranka zasu gyaru inkaso mana”
“Ta yaya?”
“I will help you do that, sekowa ya dawo yana sonka”
“how?” ya tamabayeta a takaice
“Just believe me, you Can change, I will help you change your life, trust me”
Kallonta yayi sannan yai murmushi “I have trust you already, ko iya haka you bring a lot of changes in my world, Thank you”
“kasan wani abu daga lokacin da ka kasance tareda abunda kakeso lokacin kake kara samun nutsuwa da kusanci zuwa gareshi, Iyaye abun sone, dakana kokarin ka manta abunda Mummy tayi maka ka kyautata mata wataran zaka manta da komai”
“bazan manta ba kuma ni yadda take kara cusamin Ilham ke batamin rai”
“wai me Ilham tayi maka haka?”
Kallon Jalila yayi irin kin rainamin hankali
“kinsan komai amma kina rainamin hankali, lokacin dana kwanta a Asibiti kikace musu ina bacci, sunsaki baki itada mahaifiyarta naji duk abunda suke cewa kuma kina tambayta me tayimin bansaniba”
Dauke kai tayi ta danyi murmushi.
Suna shigowa bakin layin suka ga wani dattijo yanata tattare ledojin da suka dan bata layin, da Sauri tacewa Jalal ya tsaya
“me zakiyi?”
“Kaga dattijon can zamu tsaya mu gaisar kaimasa Alheri”
“saboda me?”
“Maganar me mukayi dazu, you want change”
Hade rai Jalal yayi “Wannan mutumin ba irin zagin dabemun ba farkon fara shaye2 na”
“kayi hakuri ka nuna masa ka manta please”
Jalal yaja motar suka karasa inda dattijon yake suka gaisa sukayi masa sannu da aiki, sannan Jalal ya dakko dubu daya ya bashi yasa hannu ya karba ya dinga godiya sannan suka wuce,
“Kiduba Ajiyata dana gaya miki”?
Ya jefo mata tambayar, Jalila bata son rigimadsa tasan intace Ilham ta dauka fada zasuyi dan haka tace
“Wace Ajiyar fa?” ta tambayeshi irin ta manta din nan
Ya gano so take ta raina msa hankali dan haka ya kyaleta yayi parking Akan idon Ilham Jalila ta fito daga motar Jalal.
Ilham aranta tace “dama tazo dazan bakantawa Jalila insa a tsanate” dan haka Ilham da gudu ta shiga cikin gida tana kwalawa Mummy kira ta samu Mummy a daki idonta yayi Ja saboda kuka tana lazimi
“Mummy wallahi Jalal bashida mutunci bashida Imani, duk yadda kikayi kina kuka bakyason ya tafi seda ya tafi, gashinan a banza mace tasashi ya dawo yafasa tafiyar, wallahi gaskiyar daddy Jalal neman mata yakeyi”
Cikin rashin fahimta Mummy tace “Ke bangane me kike nufi ba”
“Mummy Jalal yadawo be tafi ba saboda Jalila”
“Kamarya saboda Jalila?”
“Oho musu dai, wallahi gashi can shida Jalila sun dawo, saboda ita yafasa tafiyar”
“ke ya akayi kikasan saboda ita yaki tafiya?”
Ilham ta gyara zama tace “Mummy nifa shiru kawai nakeyi, Allah kadai yasan abunda nake gani a tsakaninsu, bana son yawan bata miki raine”
A fusace Mummy tace “Ilham bana son shirme da shashashanci, kimin bayani yadda zan gane, ban fahimci ke kadai kika san abunda kike ganiba kimin bayani”
“Wallahi Mummy ba tun yauba akan yarinyar nan bakiga rashin mutuncin da takemin ba, kuma wallahi ita take ziga shi yakemiki wani rashin mutuncin, har dakinsa take zuwa gurinsa, Allah kadai yasan me sukeyi”
Mummy tayi shiru tace “lallai yarinyar nan makira ce, agaban idona take bude baki tacewa Jalal mara tarbiyya, Ashe itama mara tarbiyya ce, tunda take biye masa suna lalacewa, wallahi bata isaba dole in nesan tata da dana, dan bazan zuba ido yana ta’amalli da itaba, akan me na yadda da ita ina mata kallon mutuniyar kirki amma zatayi min haka? Gaskiyar dsddynsa yana neman mata kenan inbahakaba uban me take zuwayi dakinsa, kema banda rashin mutunci ubanme ya hana ki gayamin abun tun farko”
” Mummy dan Allah kiyi hakuri, kawai nidai bana son ki tayara da hankalinki ne a zatona zan iya shawo kan abun, tunda naga abunda yafaru yau kalli banbamin dayake miki dankice kar ya tafi, Amma dayake akwai abunda sukeyi ai baze iya hakura ya tafi ba, yanzu ki kwantar da hankalinki kawai dai kiyi kokari ayi mana Aure da shi a wuce gurin “
” Ke kina batun inyi kokari ke wani kokarin kikayi?, tsawon shekaru kina gidan nan amma kinkasa janyo hankalin sa, Amma kanwar kanwarki wannan ‘yar yarinyar hartasan taja hankalinsa duk taurin kansa, da uwar me tafiki? Niba ina nufin ki zubar da mutuncinki ba amma abun ya dauremin kai, ace har taci mutuncinsa agabana amma dayake bashida zuciya har tasamu kusanci dashi fiye dani da kema gaba daya Kinga tashi kibani guri ni raina ya gama baci”
Ilham ta mike ta fita tana zunbura baki, Amma dai tayi Nasara tunda har Mummy tafara daukar zigarta ta harzukata haka yanzu saura next plan dinta.
Jalila ta tsaya ta kalleshi tace “to ni zan shiga gida, Amma kabawa daddy hakuri”
“Hakurin me zan bashi? Jiya da daddare ya tafi U.K ai”
“to Mummy fa?”
“mezan mata, akanta nake kokuma wani abun nayi mata? ”
“Ohh God kanada taurin kai, Just recently kace you want change, kuma yanzu kana wata magana, she’s your Mother, komene halinta kuwa, Aljannarka tana karkashin kafarata, ko kanaso kashiga wutane?”
Tayi masa tambayar kaman tana tambayar karamin yaro
Kallonta yayi amma bece komai ba
“Kadinga zuwa inda take, kayi hakuri da duk yadda take, kadena bata mata rai, kaji dan gidan daddyn sa, your Mum is so kinda, she loves you, you have to show her love too, batun Ilham kuma babu dadi kace baka son mutum agabansa kaji”
Tai maganar tana murmushi sannan ta shige gida.
Sumar kansa ya shafa yayi murmushi shima.
Gida ya shige yayi wanka ya ci Abinci ya tafi gurin Jawwad, Jawwad na ganinsa yafara dariya “mutanen Dubai ya akayine?”
Jalal ya dan hade rai “naga alama da hadin bakinka kanwarka tasa aka hanani tafiya”
“niba hadin bakina, amma nasani daddyn Hanan tagayawa, tun a lokacin nasan za’a soke visa dinka, amma nayi shiru ban gaaya maka ba, Amma ya akayi kasan itace tasaka, ina fatan zakayi hakuri karka hukunta ta”
“Hmm Jawwad kenan, yarinyar nan nasan halinta sarai, tun ana gobe zan tafi take dariya tace taga ta inda zan tafi, kaga inba itaba babu memun haka, akwai abunda tayi da har yanzu yake bani mamaki shiyasa akwai abubuwan da idan tayi bazan mamaki ba. Sannan yazan mata ta riga tayi, ban mata komaiba tare muka dawo ma”
Murmushi Jawwad yayi yace “zoka bani Labari, yaushe kuka dena fada ne? Ya akayi ka sakko da wuri haka? Nazata inka gano itace semunzo ban hakuri kar a hukuntata hukunci me tsanani”
“ta fini gaskiya ne, a da dinma abubuwan da take fada akaina gaskiya take fada, nina nake fadan rashin gaskiya, sedai tafiya tsiwa a gadarance take gayamin magana abunda yake harzikani kenan”
“to yanzu fa?”
“Bansaniba babana kasani agaba se antayamin tambayoyi kake, sekace EFCC, kaje ka tambayeta mana”
Dariya Jawwad yayi tareda dan jan kunenen Jalal dake cin Abinci ta sigar wasa yace “Allah ya huci zuciyarka ranka ya dade nidai tunda baka hukunta taba kagama min komai”
Murmushi Jalal yayi sannan yacigaba da cin Abincin sa.
Sunata hirarsu shida Jawwad gwanin sha’awa,
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
Naja tana gaban mudubi, tasha kwalliya kaman zata gasar rawa, duk tabi ta tsuke jikinta, ta feshe jikinta da turare se taunar chewing Gum takeyi
Nana tace “Ehemm su hajiya Naja ko anyi sabon kamune wannan wanka haka?”
“bawani Sabon kamu, gurin Masoyina zanje tunda shi bezoba ai gara inje inda yake”
Jalila kallin Naja take kawai dan ba karamin tausayi take bata ba yanzu, rashin sani yafi dare duhu, da Jalila zata fadi wani abu data rusa duk wannan rawar kan da farincikin Naja har karshen rayuwarta, abunda ita kanta Najar bata san dashi ba “Allah ka kiyayemin Yaya Jawwad dina ka tsaremasa Imaninsa tareda dukkan Musulmi, dan a wannaan shigar da Naja tayi tana wannan masifaffen Kamshin indai Lafiyayyane namijine da wuya ya iya shallake wannan mugun tarkon na shedan.
Nana ko cewa tayi” kekam dan rashin aji dan yaki zuwa ke sekije inda yake, Sannan kalli shigar ki bata daceba kayan sun matseki”
“A’a ke kyaleni, A haka zanje irin wannan shigar da ita ake kama zuciyar masoyi kuma tana kara kusanci da kauna”
Itadai Jalila batace komai ba har Naja ta fice, sedai girgiza kai datayi tana cigaba dayiwa Jawwad addu’a.
Jalal yagama cin Abincin sa ya dakko system dinshi yana dubawa yace
“Jawwad next month fa zaka tafi Abuja gurin Aikinka”
Da sauri yace
“Saboda me?”
“Saboda nima haka na shirya maka kafin intafi, dan haka seka tafi”
“haba Jalal meyasa, Abba na kokarin bude mana store ne muyi ruining dinsa da kanmu kaga base nayi aikin gwamnati ba mun huta”
Dan tsurawa Jawwad ido yayi a ransa yace “mezanmaka a rayuwa Jawwad in biyaka kauna da alherinka, Sarai Jawwad yasan Jalal yanada tarin dukiya a kasa, Amma bayason ya kashe masa zuciya kar ya nemi na kansa”
“Kaga idan ka tafi nika barni da harkar kasuwancin zanyi mana, Amma seka tafi fa”
“Amma Jalal hakan……
” Salam Alaikum “
Muryar Naja ta katsesu gaba daya suka juyo suna kallonta
Wato har wani pink take saboda tsabar bleaching, saboda daganin wannan farin banata baneba, ga gaba daya dakin ya gauraye da kamshin turarenta tareda karnin mayukan da take Amfani dasu, tasaka riga da skirt na material dasuka kama jikinta matuka duk saman kirjinta a waje.
Dauke Kai Jalal yayi, yacigaba da danna system dinsa
“Masoyina gurinka nazo fa”
Tai maganar tana kokarin zama a kusada Jawwad, Jalal kam mikewa yayi ya shige bedroom din Jawwad, yana tunanin meyasa wasu matan basuda kunya basu san ciwon kansu ba, ace mace budurwa kaman wannan amma tana nanikar namiji haka ba kunya ba tsoro, hakama Ilham take masa wani lokacin, To Amma meyasa ita Jalila bata haka? Shidai yasan ba ruwansa da mata hasali yana gudun taba macen daba maharramarsa ba, Amma ita Jalila bayajin komai dan ya tabata, yana jin kaman hakan shi a gurinsa ba laifi bane, sannan duk lokacin da hakan tafaru a tsakanin su yana ganin matukar tsoro da rikicewa a idonta. Haka yacigaba da zancen zuci yanata tunani daban2.
“Haba masoyin, Meyasa baka zuwa inda nake Yaya Jawwad, wallahi banajin dadin abunda kakemin sam baka nunamin soyayya”
Matsawa yayi daga kusada ita yace “Naja soyayya daban Aure daban a yanzu keba halalina bace ba meyasa zakimin irin haka? Ke ko kunya ta bakyaji ne haba Naja kidinga kama kanki mana”
Matsowa takumayi jikinsa tana kashe murya tace
“meye wani kama kai, Aurena fa zakayi dan Allah kasaki jiki ka nunamin soyayya haba Jawwad” takai hannu tana shafo fuskarsa
Gaba daya jikin Jawwad rawa yakeyi Tsaki yayi yana kokarin mikewa, tunda ya fuskanci bazata ganeba
Riko hannunsa tayi tana kokarin Rungumeshi, A fusace ya hankadeta kasa yana kokawa da numfashi,
Tashi takuma yi tace “bazanyi zuciya ba” sekace mayya take kuma shanye ido kamar tana maye, ta rungume shi.
“Ke!!!” ya daka mata tsawa a fusace wadda seda yasa Jalal fitowa a sukwane yayi jifa da ita
“ki tashi kibarmin dakina, Allah ya shiga tsakanina dake ban taba aikata mummunan sabo ba bazan fara akanki ba, get out from my room ko in illataki” idon Jawwad yayi jawur jikinsa yana rawa, gaba daya ta kasa gane dama Jawwad yana fushi haka? Jalal ya karaso ya rike Jawwad yace
“Jawwad kyaleta yi hakuri, calm down”
“bazanyi hakurin ba ka kyaleni, wallahi takuma zuwarmin daki sena bata mamaki, bata san a bisa umarnin Maama zan Aureta ba, in bahakaba me zanyi da ita? Me take dashi daza’a kalla a ce wannan mace tagari ce ya dace a Aureta? Itada mahaifiyarta sun shiga sun fita sun rabani da kanwata shekara da shekaru suna uzzuramata suna bata mata rai suna cimata mutunci, na hakura, ance sena Aureta na hakura nayi biyayya, be isheta ba seta nemi tasana aikata laifi me muni”
Kallon Naja Jalal yayi, kaddai ace wannan yarinyar ya yadda ze aura, Amma Jawwad hakurin nasa yayi yawa. Naja ba karamin mamakin abunda Jawwad yayi mata tayi ba, ita babban mamakinta bata taba ganin yana fada ba, saboda tasan mutum ne me kunya da kawaici.
Jalal yace “Naji kadaiyi hakuri”
“bazanyi hakurin ba Jalal”
Jalal yace “da nine da yanzu kacemin masifaffe, haba dan uwa Aliyu Haidar zakin Allah, katangar sikari na Hanan kowa ya jingina da kai seya lasa, fari me farar aniya kai a cikin masu sunan ma na dabanne kayi hakuri” Jalal yana lallaba Jawwad ne saboda yasanshi be iya fushi ba, seya shafe shekaru be fushi ba amma idan yayi abun baya kyau.
Naja tace “kagama duk masifunka, wallahi nidin dai ni zaka Aura kuma zaka gane baka da wayo, bari Maaman ta dawo zaka gane ka taka tarkon mace.
Jalal ya hanashi magana, suka kyaleta a gurin yaje ya dinga rarrashin Jawwad, ana haka Hanan ta kira wayar Jawwad, Jalal yai murmushi yace “kaga ka daga wayar nan ayi maka kalamai, zaka huce”
“A’a ka kyaleni, am not in mood”
Aikuwa Jalal ya daga wayar suka gaisa yace “Hanan ga mutumin naki, Amma ransa a bace yake fa”
“Subhanallah dan Allah wayakai min zuciyarsa bango har akasamin shi fushi, dan Allah ka bashi wayar”
girgiza masa kai Jawwad yayi alamar baze karba ba
“kiyi hakuri, baze karba ba fa, ransa a baci yake”
Hanan a shagwabe tace “Shikenan tunda baze karba ba amma zuciya ta bazataji dadi ba, Allah kuka zan tayi duk daren nan, wallahi har naji tawar zuciyar tafara nauyi”
Ai tuni Jawwad ya zare wayar a hannun Jalal yasa a kunnensa yace
“Hello Hanan kina jina?”
“haidar dina me akayi maka?”
“wani little issue ne, kuma yanzu komai yayi settling”
“little issue baze bata maka raiba”
“ki manta kawai, kar inga abunda yasamin ke kuka”
Jalal yaji Jawwad ba kunya anataya masa kalamai agabansa. ya minstili kafar Jawwad yace “dan rainin hankali kawai”
Jawwad yai murmushi
Jalal ya daga masa hannu ya wuce gida.
Yanayin maganar Hanan kaman Jalila, tuno moments dinsu yayi dazu dayake ta dage bilhakki tana masa fada, da yadda take da ido idan batada gaskiya murmushi ya dingayi shi kadai, har ze kwanta ya tuno maganganun Jalila game da Mummy.
Mikewa yayi ya nufi cikin gidan, babban palourn Mummy yasa hannu ya bude kofar. Salla takeyi yanemi guri ya zauna, rabonsa da dakin nan harya manta yana jiranta yana sake2 a zuciyarsa mema ze ce matane?.
Ta idar tagama lazimi, ba karamin mamakine yakamata ba ganinsa a part dinta
Ta kalleshi tace “Lafiya kuwa? Ashe baka tafi ba, uwarka wadda tafini, wadda take baka abunda bana baka ka fasa tafiya saboda ita.
” Wakenan? “