Novel Document

Rashin Haihuwa Complete Document

Description/Story

Rashin Haihuwa Complete Hausa Novel Document Written By Ouummey

 

Description

😭 *RASHIN HAIHUWA*?

 

_(Ƙaddarar wasu matan)_

 

Na

💝💖* Ouummey* 💞💕

 

Wattpad @ouummey

 

 

Godiya

Da sunan Allah me Rahma me jin kai, dukkan Godiya ta tabbata ga Allah SWT Ubangijin talikai, me kowa me komai da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi me suna a sama cikin koshin lafiya, ina addu’ar Allah ya bani ikon gama shi kamar yadda na faro ya sa mu amfana da duk wani darisin cikin sa, kuskuren cikin sa kuma Allah ya yafe min.

 

*Jan hankali*.

This book is a total work of fiction, suna, gari kasa ko wani abu daga cikin labarin in aka yi rashin Sa’a yayi daidai da naki to fa arashi ne, ban rubuta wannan littafi dan cin mutunci ko wulakanta wani ba face dan ganin yada ce in fito da virtues din matan da rashin haihuwa yasa ake yi wa kallon kaskantattu, wulakantattu ko marasa amfani, a guji yanke wani abu ko juya min labarin ta kowace siga dan tabbatar da zaman lafiya, kamar yadda na faɗa wannan labarin ƙirƙirarre ne bisa fasaha da baiwar da Allah ya bani tare da yin duba ga rayuwar mu da abubuwan dake faruwa cikin wasu gidajen auren.

 

*Dedication*

*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu’ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sai dan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.

 

______________________________________

______________________________________

 

_Free Chapter One_

 

 

Tun daga kasa har sama nake karewa kaina kallo ta cikin tafkeken madubin da ke girke a dakin baccin nawa, babu ta inda na hango wata makusa ko kasawa a tattare da ni, hakan be wadatar da ni ba sai da na sake ɗagowa na sake sako duban tun daga kan yalwataccen gashin kai na bakikirin dake kwance kan kafadu na, a hankali na sauke duba na kan matashiyar fuska ta dake cike da tashen kuruciya, ba wai na budurtaka ba a’a na shekarun tashe ga iri na da muke kan wannan mataki, zagayayyar fuskar ta ɗauke take da wadatattun idanun da Allah ya ƙawata ta dasu, farare tas masu haske da matukar daukar hankali, ban tsawaita ba na sauko kan dogon karan hanci na da ya dada wa fuskar kyau bayan idon, hanci na ba siriri bane zut ɗin nan yana da dan fadi kadan da yasa ya zauna das kan fuskar, kyakkyawan ƙaramin baki na me ɗauke da madaidaitan lips da basu cika karanta ba haka kuma ba manya bane, a hankali kuma na lumshe idona na buɗe tare da sakin kyakkyawan murmushin da ya bayyana jerarrun haƙora na da basu kasance farare ba sedai milk ne masu kyau da suke samun kula a ko yaushe.

 

Cikin wani irin yanayi na girgiza kai na wani abu na tsirga min cikin raina na sunkuyar dashi kafin cikin karfin halin da na saba yi na bude na cigaba da surveying jikina, a kan cikakken wuya na idanuna suka sauka wanda ke dauke da wasu layi haka ko guru guru zance, cikar kirjina dake fisgar hankali na maida kaina farin ciki na ratsa ni, shafaffen ciki na da bashi da alamar ɗagawa balle in aje tumbin da wasu daga cikin sa’anni na ke korafi dashi suke kuma sha’awar lafewar cikin nawa sai dai gare ni hakan shine ciwo mafi girma ga rayuwa ta dan babban burin na a wannan duniyar be wuce in farka in ga cikina ya tasa kamar kowace mace da Allah ya albarkace ta da arzikin haihuwa ba.

 

Da kyar na haɗiye wani mugun miyau ina janye duba na daga wajen na maida kan faffaɗa kuma cikakken kugu na wanda shine abu mafi daukar hankali a jikina gaba ɗaya, nikaina yana daya daga cikin halitta na da nake alfahari dashi dan shine kadai abu ɗaya da ya rage min da ya riƙe ni a gidan aure na ya kuma sa nake da yar ragowar kima a idanun mijina wato surar da Allah ya min, ban tsawaita ba na karasa kan kafafuna dake wadace da jan lalle wanda bana rabo shi, lallen ya zauna daras kamar a kai a aka ƙirƙire shi, yadda ya haska farar fata ta kuwa abin ba’a ce wa komai.

 

Babbar ajiyar zuciya na sauke dana gama karewa kai na kallo kafin cikin sanyin jiki na dauki kwalbar turaren da tuntuni shi ne zan shafa amma na tsaya kallon kaina kamar bakuwar kan nawa, zazzagwa nayi a hannu na na shiga shafe lallausar fata ta dashi lungu da saƙo sannan na aje, wata na kuma ɗauka itama na murza a hannun na shige shafe wasu wurare masu mahimmanci a jikina, ina yi ina yan tunane tunanen da suka zame min jiki a duk lokuta irin wannan.

 

Ringing din wayata dake aje kan bedside drawer yasa na dawo hankali na sosai na shiga shiri da sauri dan nasan ba kowa ke kiran ba se oga, na dade da sanin ya tsani jira musamman daga gare ni kamar yadda yake faɗa min times without number sai too ifdai nikuma ya riga ya zame min jiki musamman a kwana kin nan.

 

Kayan bacci na ciro masu kyau, laushi hadi da daukar hankali na zura ina tattare gashi na waje ɗaya na kama shi cikin ribbon, duk da na shafa wasu turaren kafin sa kaya ba hakan ya hanani sake fesa wasu ba wanda suka sa take dakin ya cika da sassanyan kanshi na me ratsa zuciya wanda nake amfani dashi kadai lokacin da zan je ga oga.

 

Waya ta na ɗauka na kashe batare da duba komai ba dan bani da lokacin hakan me ni na can na jira na kuma san tuni ya cika yayi fam se nayi rarrashi.

 

Seda na sawa kofa ta key dan gudun matsala da jan magana sannan na wuce upstairs inda nan ne turakar me gidan take, seda nayi Knocking tare da dan dakatawa sannan na tura ƙofar a hankali ina me yin sallama cikin daga murya dan ankarar da na cikin dakin cewa gani nan fa tafe.

 

Nasan zaku yi mamakin wai na tsaya knocking ni da dakin mijina da addini ya bawa damar shiga wajen sa duk sanda naso haka kuma ganin sa cikin kowane yanayi halak ne gare ni, to ba komai yasa nayi hakan ba face gujewa haduwa da ɓacin rai, a irin wannan yanayin na kan ci karo da mabanbanta takaicin da kan hanani bacci wasu lokutan yayinda wasu lokutan kuwa nake hana zuciya ta damuwa ko da kuwa taso yin hakan.

 

Ajiyar zuciya nayi hango shi zaune ken bed Yana danna waya, cikin tafiya ta me daukar hankali da kuma karin wasu salo dan sace zuciyar oga na kai gefen mirror ɗin sa na aje yar jakar kayan hannu na sannan na karasa gare sa wanda tun shigowa ta da yayi min kallo ɗaya be sake yi ba.

 

Cikin jikin sa na shige ina manne masa kamar wata cingum na sanyaya murya dan nasan nayi laifi haka kuma na shagwaɓe fuska cikin fatan samun lagon sa

 

“Am sorry zuma naaa, na tsaya shirya maka kaina ne ta yadda zaka mori daren ka cike da annashuwa da farin ciki, ayi min afuwar dadewar da nayi plsss”.

 

Na karasa ina kai hannuna cikin ƙirjin sa ina masa waiwayi cikin salon da nasan baze iya jurewa ba, kamar yadda na sani kuwa lumshe idon sa yayi tare da rike hannun da ke yawo jikin nasa kana ya bude su ya zuba kan fuska ta

 

“Kullum se kince ayi miki hakuri kuma ba haka ze Hana gobe ma ki sake ba, na kasa gane meye matsalar ki Khadijah, ke ba da ba ba jikan da zaki fake da kula da shi ba amma ko mariya dake goyo ba zata faɗa miki kawo uzuri ba, Allah ya sani kin fara kaini bango dan na fara gajiya da uzurorin ki marasa kan gado da bakya rasa na bayar wa kullum”.

 

Daga jikin nasa da nake kwance na lumshe ido zuciya ta na motsawa, ba se Salees ya tuna min da cewa ban taɓa haihuwa ba, ba se Salees ya tunatar da ni bani da tsuntsu bani ga tarko ba dan hakan abu ne da bana taɓa mantawa ko da kuwa acikin mafarki ne.

 

Sanin shiru na wata matsalar ze jawo yasa na daure rashin daɗi na na bar shi iya cikin raina yayinda a zahiri na ɗago na sumbaci bakin sa ina tabbatar masa insha Allah ba zan kara ba wanda hakan yayi tasiri gare shi dama kuma be fiya riko ba, cikin zakuwa da natsuwa ya shiga birkita nutsuwa ta da salon sa masu tafiya da ruhi na suke kuma karamin kaunar sa a ko da yaushe inda nima tuni na biye masa muka fada cikin wata duniya me wuyar bayyanuwa, seda duk muka sami nutsuwar da ta dace kafin muka shiga wanka dan yin shirin kwanciya.

 

Ko a cikin toilet din ma be bar ni haka ba dan se da yayi neman maganar sa san rai kafin muka wanko jiki muka fito, cikin sanyin jikin gajiyar da ya tara min na maida kayana tare da hayewa kan gado na lafe ina sauke numfashi yayin da gefe ɗaya nake mamakin rashin faruwar lamarin da ya zame mana jiki cikin watanni ɗaya zuwa biyu da suka wuce.

 

Ban kai ƙarshen mamakin ba sautin kukan yaro ya fara ratsa kunne na, tun ina jiyo wa kasa kasa har ya fara ƙarfi alamun ana nufo dakin ne, cike da takaici na tsurawa kofar dakin ido cikin jiran faruwar sabon mu, dukan kofar aka shiga yi kamar a filin yaki wai kuma hakan da sunan knocking ne fa ake yi, daga kwancen da nake ban motsa ba naga tashin sa daga kokarin kwanciyar da yake yi kusa da ni ya bude dakin yana ɗan haɗe rai.

 

“Ka gan shi nan yaki yin shiru, nayi nayi wallahi se kuka yake har na rasa yadda zan masa, ni yadda yake yi ne ma yafi bani tsoro kalli kaga se wani miƙewa yake kamar ze shide”.

 

Ai oga se ya nemi haɗe ran da ya ɗan yi ya rasa ya kai hannu cike da hanzari ya karbi dan ya shiga riritawa, kamar abin shiri yaro maimakon yayi bacci ko yayi shiru ba se ma karawa kukan sa karfi da yayi hakan kuma ya sake dugunzuma hankalin uban duk yabi ya tashi dan Allah ya zuba mishi so da kawa zucin yaya, ko dan ya dade kafin ya same su ne?.

 

Iya shaka na shaka domin dai a yau na gaza yiwa mariya da Salees uzuri, ba dan komai ba sedan saboda ba yau hakan ya fara faruwa ba, abin kamar ya zame mata sabon da take jin dadin sa ni kuma ya zama sabon da ke taɓa zuciya ta da sani cikin ɓacin rai.

 

“Amma dai kasan wannan shiga hakki ne ko, yaya muna kwance kawai zaka bude wa wata daki hakan kuma duk be yi ba se an hana ni bacci, shin shima hutun nawa ya zama abin bakin ciki da hassada ne ko kuwa me?.

 

Wani kallon Salees ya shiga yi min me kama da na mamaki ko kuwa na zallar takaici ne, kafin kuma yayi magana tayi caraf ta riga shi

 

“Kiyi haƙuri Khadijah, Amir ne ban san me ke damun sa ba kwana biyu, ko kuwa har ya gane uban sa ne oho, kinga har mun kwanta amma yaron yace be san zance ba kuka har na rasa yadda zanyi dashi shi yasa na kawo masa ko ze yi shiru dan mama tace yawan barin yaro yana kuka ba lallashi na jawo masa matsalar ƙwaƙwalwa da kuma ciwon zuciya”.

 

“Kinga dan Allah dakata ba dake nayi magana ba ki bari shi da nake dashi ya amsa min, zuma naaa da kai fa nake magana”.

 

A irin fusacen da Salees ya kalle ni abin seda ya girgiza ni dan kallo ne me shaida Allah ya soki bana kusa da ke

 

“A sani na dai ke ba kurma bace kin ji me tace ko?”.

 

A yadda nakai geji nima hakuri na ya kare dan haka na bashi tawa amsar da fusatacciyar murya kamar yadda ya min

 

“Shine nace ina buƙatar sanin me kake nufi da ni ne dan wallahi sedai ko ta fita da yaron daga dakin nan ko ni na fita dan ba za’a dinga hanani bacci ana samun ciwo a banza ba”.

 

“Aikuwa sedai ke ki fita dan da dai dakin uban sa ne cikin gidan uban sa, kinga kuwa maganar a fitar dashi ma ai bata taso ba”.

 

Kuriii na masa da ido ina kallon sa yadda ya fadi abinda ya faɗa hankali kwance, ban san me yasa murmushi ya zabi wanzuwa a fuska ta ba a lokacin duk kuwa da tsananin ɓacin da rai na yayi

 

“Amma dai kasan nima ina da gidan uba ba daga sama na fado ba ko Salees, so ba daga daki ba ko gidan kace in fice ma yanzu se in tafi ai”.

 

“Mtsww, Ni dai ban ce ki fita daga gida ba sedai in Kuma ke kika so, daki dai nace ki fita dan yaro na ba inda zeje, ke ban da ma rashin imani kina kallon irin kukan da yaron yake yi ko tausayin sa ba kiji ba balle mahaifiyar sa da duk hankalin ta ke tashe se wani soki burutsu kike yi, ko da yake ai baki san ya rainon da yake ba tun da baki taɓa yi ba dole ki ga kamar karya ne”.

 

A wannan gaɓar kam tuni idanu na suka tara ruwan bakin ciki, ɓacin rai da kuma wani irin rauni dake tasowa tun daga can karkashin zuciya ta, ban kuma cewa komai ba na sauko daga gadon tare da ƙarasawa inda na aje jakata na ɗauka ina nufar hanyar fita daga dakin dauke da alwashi me girma cikin raina.

 

Kan bed na faɗa ina sakin kukan da nayi dauriyar riƙewa, wani irin kuka me fitar da sauti sosai jikina na rawa, kallo ɗaya me imani da tausayi ze min yaji zuciyar sa ta motsa, Allah ya sani na dade da gajiya da zaman auren Salees, ba dan na daina son sa saba, ba dan bana son cigaba da rayuwa dashi ba, sai dan in aka cigaba da tafiya a haka lallai zuciya ta na gab da bugawa, in Kuma haka be faru ba na tabbata jinina se yayi yawan da saukowar sa se Allah, yanzu haka ina mamakin yadda ko yaushe nayi gwajin bp nake samun negative result dan a irin damuwar da nake ciki hawan jini shine cuta mafi kankanta da ɓacin ran gidan Salees ka iya haifar min……………….!.

 

_*Ba zan gaji da fada muku ba haka ba zan gaji da tabbatar muku da ba gazawa ce ta sa Allah ya kaddare ku da rashin haihuwa ba face jarraba irin tasa da yake yi dan gwada karfin imanin duk wanda yace yayi imani, da zafi, da ciwo, da damuwa, da rauni amma in akaa daure tabbas rabon me girma ne kamar yadda Allah da kan sa yace yana kunyar matan da basu taɓa haihuwa ba, Allah ya bada masu albarka inda rabo, in Kuma babu Allah ya azurta ku da dauriya da karfin iya jure wannan ƙaddara*_.

 

 

Rashin Haihuwa

File Name   Rashin Haihuwa Hausa Novel 
Title   Rashin Haihuwa
Author    Oummey
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    29/10/2024
File Size     218.kb
Format Size    TXT
Book Price    Free
Phone No
Download Rashin Haihuwa Complete Novel Document By Ouummey

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button