Hausa novels

Wace ce ita Chapter 70 Hausa Novel

WACECE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy🌹

SEVENTY📍

Wani iri yaji aransa hangota dayayi tana kuka, sai suratai take baya dai jin abinda take cewa, cikin sanyin jiki ya karasa cikin dakin ya zauna a bakin gado yana facing dinta….
Ji tayi kamar ana kallonta ta dago sukayi ido hudu dashi, tana ganinsa ta mike a tsorace zata bar dakin, da sauri ya ruko hannunta ya mai da ita dama jikinta babu karfi, fashewa tayi da kuka tashin hankali na bayyana karara akan fuskarta still tana kokarin kwace hannunta ta gudu, tausayi ta bashi sosai har besan sanda yasa hannu ya fara goge mata hawayen ba amma me makon hawayen ya tsaya sai ma kara karfi dayayi….
Matso da fuskarsa dab da tata yayi a hankali yace;
“Stop crying baby girl!”…
Ai sai taji kamar ya tunzurata, hawaye ya balle mata kamar famfo….
Rintse ido deen yayi yana jin babu dadi aransa, he can’t believe wannan uban kukan da take duk shi ya jawo, tabbas mami tayi gaskiya datace be kyauta ba da bai rufa mata asiri ba, daya rufa mata asiri da yanzu bata cikin wannan halin da take gashi har drip yaga alamun ansa mata, sai dai ko wanene baze iya controlling kansa a lokacin ba, babu wanda ze iya daukan irin wannan abun a lokaci daya…..
Kara motsa da fuskarsa kusa da nata yayi har hancinsu na gogan na juna, kallon kyawawan lumsassun idanuwanta da hawaye ke zuba kamar da bakin kwarya yayi, da jikekken gashin idonta da yake sheki me ban sha’awa saboda kukan data sha, tsigar jikinsa ne ya tashi saboda tozali da jajayen lips dinta da yayi, sunyi jazur dasu kamar ya cinyesu…..
Wasu sababbin hawaye ne suke sake silalowa akan fuskarta da suka sashi kara rikicewa, batareda tinanin komai ba ya dora harshensa akan fuskarta, a hankali ya fara lashe mata hawayen making sure he is super gentle yanda wasu bazasu sake zubowa ba, ya shiga yawo da tongue dinsa ko ina na fuskarta kamar wanda yake lasan sweet….
Dib ta nemi hawaye ta rasa damshin tongue dinsa da yake smooching fuskarta dashi na ratsata, ga kamshin turarensa daya cika mata hanci saboda kusancin da suka samu, kokarin bude idonta tayi yayi saurin dora bakinsa a gurin, dole ta maida idon ta rufe, kissing din idonta ya farayi wildly yana emphasizing akan gashin idonta, wani iri taji a jikinta har zazzabinta na neman dawowa sabo, deen kuwa hankali kwance ya maida fuskarta kamar wani ice cream ya lashi chan ya lashi nan, kokarin janyewa tayi saboda yanda jikinta ya fara rawa amma ya hanata ta hanyar cupping face dinta tightly, karshema ya fara kissing ko ina na fuskarta insanely kamar wani zautacce….
Sai da yaga jikinta na rawa sosai sannan ya janye da kyar yana ruko hannunta, kamar jira take ya saketa jikinta ya daina rawa, sake cupping fuskarta yayi murya chan kasa ko fita bayayi sosai yace;
“I’m sorry baby girl”….
Banza ta masa tana jin wani mugun haushinsa aranta, su gama mata wannan uban dukan shikenan sai yazo ya lashe mata fuska ya bata hakuri tace ta hakura? Inaa…..
“Believe me I wasn’t in my right senses da hakan baze faru ba, I’m really sorry pretty”…
Dauke kai tayi tana turo baki irin bata yarda ba dinnan….
“Ko baza kiyi hakuri ba please talk to me”…..
Ya fada yana kokarin juyo da ita ta kallesu, juyo da ita yayi ya shiga dukan kirjinsa da hanunta yana fadin;
“Ki rama if it will make you feel better”….
Sai kuwa ta fara dukan nasa da karfi harda hadawa da yakushi, ido kawai ya zuba mata yana kallonta ita a dole ramawa take abinda batasani ba shi dadin dukanma yakeji dan ji yake kamar ana dora masa audiga a jiki saboda laushin tafin hannunta…..
Sai da tayi son ranta sannan ta janye tana maida numfashi, sake kamo hannunta yayi yace;
“Ki dai kara zaki fi jindadi”…
Dake bata da wayo sai ta cigaba da dukan nasa tana hurting kanta, sai da karfinta ya kare sannan ta janye hannunta tana bata fuska tace;
“Ni na gaji”…
Dariya yayi yace;
“Ohk, toh sannu”….
Shiru ne ya biyo baya na yan sakanni kafin deen yace;
“Fatima!”….
Dagowa tayi ta kallesa mamaki dauke akan fuskarta because it’s unlike him ya kira sunanta kai tsaye, tasan kuma saboda sunan mami ne, ko umm bata kiranta kai tsaye bare shi…..
“I know you’re surprised that I call you with your real name, saboda kisan mahimmancin zancen da zan miki ne!”…..
Be bata izinin cewa wani abu ba ya dora da tambayar da yasan inba amsarta ya samu ba baze kara samun nitsuwa a rayuwarsa ba;
“Tsakaninki da Allah meya faru a gidansu khaleel? Waya cire miki kaya ko ince meyasa kika cire kaya? And meyasa jikinki yake miki ciwo?”….
Kwabe fuska tayi memakon ta fada masa abinda ya tambayeta sai cewa tayi;
“Nima sai ka fadamin abinda yasa kabawa waccen stranger din numberka”….
“Okay zan fadamiki, but answer my question please”…
“Ni sai ka fara fadamin sannan”….
“Okay I gave her a wrong card”….
Bude ido tayi tace;
“Dagaske?”….
Gyada kai yayi yace;
“Eh, now tell me what transpired between you and him”….
“Babu komai, I only tell him to get me some nighties because I can’t sleep da kayan jikina”…..
Gyada kai yayi yace;
“When he get you the nighties sai me ya faru?”….
“Shikenan, I changed and sleep”….
“Tsakaninki da wa?”….
“Allah!”….
“Jikinki da yake ciwo kuma meya samesa?”….
“Sanyi AC ne ya min yawa, so it started affecting my body”…
“Then meyasa naga jacket din danasa miki da veil dinki a parlour shi kuma rigarki a other room dinchan, does it mean a parlour kuka fara cire jacket sai kuka karasa bedroom kuka cire rigan?”.
Deen ya jeho mata tambayar yayinda komai yake kokarin dawo masa sabo, kasa jurewa ya jira abinda zata ce yayi ya dafa kafadarta cikin wata iriyar murya ya shiga girgizata yana fadin;
“Just tell me nothing happen, tell me sanda kika cire kaya baya nan, tell me he didn’t even see a pinch of your hair, dan Allah kice min babu abinda ya faru fatima”….
Rikicewa tayi ganin yanda yake girgizata, a tsorace tace;
“Babu abinda ya faru, ba a gaban shi na cire ba, he didn’t touch me”….
Wani kakkarfan ajiyar zuciya ya saki yanajin wani sanyi a ransa, be damu da ko karya ta masa ba shi dai kawai bayasan jin negative abu dan za’a iya samun matsala…..

“Boddi ko gaisawa bazaki bari muyi ba”…
Cewar abby da zuwansa gidan kenan kamar yanda sukayi da umm ze zo da safe, a guest parlor ta sameshi ko gaisawa basuyi ba ta fara masifa wai asan yanda za’ayi ita fa dole su aurar da baby tee….
“Ai ba gaisuwa na kirawo ka muyi ba, ya ina gayamaka abinda ya dace ayi and you’re making me look stupid”….
Kallonta yayi murmushi na subuce masa yace;
“Waya koyawa boddi na masifa haka?”….
Wani irin kallo ta masa tace;
“Karka kara kirana da wannan sunan, in bazaka iya kirana jamila ba, call me doctor”…
“Boddi look at me!”….
Ya fada babu alamar wasa a fuskarsa…
Kamar bazata kallesa ba ta dai dago sukayi ido hudu dashi, sai taji duk wasu maganganun data tanadar masa sun makale mata a makoshi, dauke kai tayi batace komai ba…..
“Now this is my boddi that I can punish with my eyes, sannan ki sani har duniyar nan ta nade bazan iya dena kiranki da wannan sunan ba”…..
“Idan kuma nayi aure fa?”….
Ta katsesa tana kin hada ido dashi…
“Saidai in bana duniyarnan kenan amma wallahi da raina ba zaki auri wani inba ni ba, na gwammace mu zauna a haka duka babu aure da in barki ki auri wani, kinsan waye muhammad akan abinda yakeso ba sai na miki tini ba”…
“Wannan kuma matsalarka!, I won’t even waste my time discussing this with you saboda babu wannan a agenda dina, now back to kan yarka, na fadamaka abinda nakeso ayi, kuma dole sai anyi period!”…..
Kada kai yayi cike da nitsuwa yace;
“Atleast ki min bayanin komai yanda zan fahimta, meyasa tayi hakan then sai mu san abunyi”…
Mikewa tayi tace;
“Na riga na fadamaka step din da yarka ta dauko, and inaso kayi abinda ya dace a matsayinka na ubanta, in ma bazakayi ba ni zan dau mataki da kaina, just don’t come back and start questioning my doings”….
Tana gama fadin haka ta ficewarta….
Kiran sunanta abby ya shigayi tayi banza dashi tayi tafiyarta….
Tashi yayi ya fita daga parlourn ya nufi parking space, securities dinsa na ganin tawowarsa suka bude masa mota ya shiga, har driver ya shiga zeja motar abby yace ya dan bashi space, ya kuma fadawa sauran suma su dakata, yana fita abby yayi dialing number bappa saboda yasan shi kadai ze iya shawo kan lamarin dan yanda boddi ta dau zafi koshi baze iya da ita ba, a bi abu a sannu kuma taki….
Da sallama bappa ya daga wayan, amsawa abby yayi sannan suka gaisa a mutunce, bappa ya sake yiwa abby ya karfin jiki kafin ya tambayesa ko lafiya dan yasan ba kasafai abby ke kiransa ba….
Abby be boye masa komai ba ya fada masa iya abinda yasani ya kuma fadamasa yanda sukayi da umm yanzu…
“Haka jamilan tace?”
Cewar bappa yana kada kai…
“Eh bappa, ni damuwata daya taki tsayawa ta min bayani yanda zan fahimta mu san abunyi, tace dai dole abi yanda takeso, dan allah bappa ka mata magana tayi hakuri mu nitsu abi komai a sannu, nasan kai kadai zata saurara shiyasa nace bara na kiraka”..
“Yanzu saboda shashanci bazaka iya tsawatarwa mace ba? Shikenan sai abinda tace za’ayi? Toh barni da ita zanyi maganinta”….
“Ayi hakuri bappa, nagode sosai, Allah ya kara girma…..

Saida sukayi nisa sosai da gidan sannan khaleel ya cewa me mashin din daya daukesa ya kaisa nearest hotel ya kwana dan Allah ya gani ba ze iya komawa gida a darennan ba, gani yake kamar ze tarar da deen a cikin gidan….
A daidai wani motel me mashin din ya saukesa, karban number me mashin din yayi yace dan allah gobe yazo ya kaishi gida sai ya bashi kudinsa gabadaya saboda yanzu be fito da kudi a jikinsa ba sai credit card dinsa kawai da yake aljihunsa, ba musu ya bashi number sannan sukayi sallama ya tafi….
Shiga cikin motel din khaleel yayi yana dan kalle kalle dan gani yake kamar deen ze zo ya samesa anan, dadi daya ma yaji saboda yasan deen bazeyi tinanin yana karamin guri haka ba, atleast he’s safe….. Card dinsa yayi using ya biya kudin daki sannan ya shiga ya rufe kofa, sai a lokacin yaji ya fara dawowa cikin hayyacinsa, zama yayi yana tinanin wifey dinshi, ko tana lafiya yanzu?, Allah yasa mugun yayanta be mata wani abu ba, tabbas in ya mata wani abu sai ya dau fansa, addu’a ya cigaba da mata har bacci barawo ya sacesa, bashi ya farka ba sai karfe takwas na safe, kallon agogo yayi yaga ya balakin makara ya fada toilet da sauri ya dauro alwala, yana idar da sallah ta fado masa a rai, gashi babu waya a hannunsa bare ya kirata yaji halin da take, waje ya fita yana jiran zuwan me mashin din, comteplating ya fara ko yaje gida ko kuma yaje gidansu baby tee yaga halin da take ciki tukunna, a haka har me mashin din ya karaso ya samesa…..

“Your temperature is so hot zahrah”..
Deen ya fada yana janye hannunsa daga kan goshinta….
Kamar zatayi kuka tace;
“Baku kuka dukeni ba”….
Hannunsa ya dora akan lips dinta softly yace;
“Shhhh don’t cry pretty, we’re so sorry, bazamu kara dukanki ba”….
Turo baki tayi a shagwape tace;
“Toh ba umm tace sai tamin aure ba”..
“Kwantar da hankalinki wasa takeyi, I will make sure na wankeki a gurinta, kema kuma ki bata hakuri kice mata bazaki sake ba, kinji ko?”….
“Toh”….
“But wait, meyasa kika je gidan ma?”….
“Ba kai bane nace bazan bawa yarinyar number ba shine ka kunyatani kabata”….
Sakin baki yayi yana mamakin shirme irin na baby tee, ashe bata da wayo har haka?…
“Toh shine sai ki rasa inda zaki sai gidansa, why not ki dawo gida?”….
A hankali tace;
“Bazan kara ba”…
“In kika kara ma babu ni babu ke, ko mami bazata kara kulaki ba, infact dukan da za’a miki sai yafi na jiya”….
Kwabe fuska tayi tace;
“Ba kace ba zaka kara dukana ba?”…
“Ai bani zan dukeki ba, wasu zamuyi hiring su miki shegen duka, ni kuma kinga banaso ana taba lafiyarki, so please karki sake kinji yar kanwata?”…..
Gyada kai tayi, yaja hancinta yana murmushi….
Tea ya tafi ya hado mata ya lallabata tasha dakyar sannan ya bata pain relieve ya kuma sake mata allura….
Sai da yaga bacci ya dauketa sannan ya fita daga dakin….
Karo suka kasa ci da mami data tawo zata shigo dakin, da sauri ya matsa ya bata hanya…
Harara me rai da lafiya ta masa sannan tace;
“Uban me kake nema bayan muguntar da kuka mata jiya kai da uwarka?”….
“Babu komai mami”…
“Kai dai kasani manufuki kawai me hada gurmi, na dai fadamaka ka fito da mata dan wallahi baza a mata wannan auren ita kadai ba, see in kaga dama ma karka fito da mata zan aura maka duk wacce naga dama, inka isa kuma ka saketa”…..
Sannan ta shige ta barsa a wajan…..
Juyawa yayi ya nufi dakin umm, sai da yayi knocking ta basa izinin shiga sannan ya shiga, dawowarta kenan daga gurin abby, gaisawa sukayi sannan yace;
“Umm magana nazo muyi”…
“Ina jinka saif”….
“Umm dan Allah ki janye maganar da kikayi akan baby tee, abun ba yanda kike tinani bane, wallahi she is innocent”….
Nunashi tayi da yatsa tace;

Yar Harka Page 1-10 Hot Romantic Hausa Novel

“Tashi ka ficemin daga daki!”….
“Umm please listen to me, it’s not what you’re thinking wallahi”….
“Ni kake gayawa it’s not what I’m thinking? Wato da kai ake batawa kuma kazo kace zaka gyara? Yanzu na gane duk wani tabaran da fatima takeyi harda kai a ciki! Haka zaka rike amanar dana baka? Toh bazan saurareka ba kuma sai nayi abinda nayi niya babu fashi, my friend get out of my sight!!”….
Fita deen yayi a hargitse, gabadaya sai yayi danasanin sanar dasu gaskiyar inda ya samota, gashi abu yazo ya kwabe masa mami kuma ta hada dashi, ga umm ta dage akan maganar aurenta da khaleel shi da yake kokarin ganin komai ya rushe, fita yayi daga part din ya koma nasa, zama yayi a sofa yana rike da kansa, innalillahi kawai yake maimaitawa yana kiran sunan Allah, ya dade beji kansa ya dau chargi irin na yau ba, ya dade beyi dana sanin abu irin wannan ba, ya dade beji hankalinsa a tashe irin haka ba, maganganun umm kadai sun tarwatsa masa nitsuwarsa bare a kaiga maganar da mami take masa na aure, shi ba auren da akace yayi bane yake damunsa a’a ita baby tee ce bayaso ta auri khaleel, a halin yanzu ya fahimci ma baya san ganinta da kowa bama khaleel ba, rasa inda zesa ransa yaji dadi yayi kawai ya dauko allurar bacci yayiwa kansa, wayarsa ce ya fara ringing kafin effect din allurar ta fara aiki akansa ya share kawai, kiran ne ya yawaita ya dauka da niyar sawa a silent kawai yaga number tayi capturing attention dinsa saboda special number ne, dauka yayi yasa a kunne yana sauraran ayi magana…
Cikin siririyar muryarta data kara lankwasawa tace;
“Hi handsome”…
“Waye?”…
Shine abinda deen ya fada yana kallon ceiling…
“Suhaima ce, the girl you gave your card at Payless Hypermarket tare da sister dinka”….
Dan jimm yayi yana kokarin tino ta, chan ya gyada kai yace;
“Ki turomin address din gidanku, zanzo gobe”…..
Zaro ido tayi unbelievably tace;
“Really? Dagaske zaka zo handsome?”…..
Kit taji ya kashe wayar, wani irin tsalle ta daka sannan ta turo masa address din murna kamar ze kasheta…..

Sosai ran umm ya kara baci da maganar deen, wai yaro karami ne zezo ya mata garinnan imagine! Ba kunya deen ya kalleta yake fadamata baby tee is innocent, ita batasan sanda ya zama haka ba, tashi tayi da niyar dauro alwala ta kaiwa Allah kukanta ta hango wayarta na vibrating, dauka tayi taga bappa ne….
“Jamila kin kyauta! Ku saurari zuwana gobe!”….
Abinda bappa ya fada kenan ya kashe wayarsa…..

Gabadaya babu wanda yayi bacci me dadi a gidan ranar, ita mami tana fama da baby tee da jikinta ya tsananta har saida ta sake kira akasa mata ruwa, umm kuma tana kan sallaya tana kuka tana kaiwa ubangiji kukanta, deen kuwa allura kawai yake dirkawa kansa amma saboda damuwar da yake ciki baya minti goma ya farka daga baccin, haka suka wayi gari da zuwan bappa da sassafe…..
Suna zaune su uku a parlour, da bappa da mami da umm, duk yanda sukayi bappa yaci wani abu yace shi ba wannan bane ya kawosa ba, kwata kwata babu lissafin shigowa abuja yanzu a tsarinsa amma dole yayi takakkiya yazo saboda yaga abubuwa suna neman tabarbarewa…..
Kallonsu yayi daya bayan daya sannan yace;
“Inaso ku bani hankalinku duka, magana zanyi me mahimmanci kuma ba me tsaho ba”…..
“Muna sauraronka bappa”…
Suka hada baki wajen fada….
Daure fuska yayi yace;
“Kun bani mamaki matuka musamman ke jamila da kike ganin babu wanda ya isa ya dakatar dake in kikayi niyar abu, ke kuma fatima ina sane da abinda kikeyi kema, amma duk ba lefinku bane lefina ne dana zuba muku ido na barku kuna zaman kanku kuna cin gashen kanku kuna abu kamar marasa mafada, toh nagama zuba muku ido, nima yanzu dole abi umarnina, ke fatima a wani dalili kike kin daukar wayan tsohon mijinki bayan yana neman sulhu game da aurenku, ke kuma jamila kinfi kowa ke gaki ishasshiya wato kince babu aure a tsarinki ko, toh duk baku isa ba! Sannan kince kin basa sati biyu ya aurar da yarsa toh kema sai ki shirya komawa dakinsa nan da sati biyun! Kema fatima haka dan babu wacce zan cigaba da zubawa ido tana zaman kanta!! ”….

TAKARI… Complete Document By Aihausanovels.com.ng

 

Back to top button