Description/Story:
Kwankwason Jimina Complete Novel
Written By Nana Hafsatu (Mrs Xoxo)
Description Of Kwankwason Jimina Complete Novel
YANKIN BUNZA…
Mutanen da suka fara zama a yankin bunza makera ne da suka tashi daga garin GAFA domin neman kasa mai arzikin zinare, wacce za su sarrafa su yi karfe da ita mai ado..
Mutanen sun yi dace da samun kasar mai kunshe da sinadarin zinare, sannan kuma mai albarkar noma da ruwa da dazuzzuka da za a iya yin farauta…
Wajen ya kuma kasance mai matukar tsaro kasancewar akwai manyan duwatsu da tsaunuka, da mutane za su iya hawa su fake idan an kai musu hari, Duwatsun su ne dutsen BUNZA da GAFA da FANNAU da SARBO da DENTEKA
Akwai kuma koguna daban-daban da suka kewaye yankin, da suka hada da kogin Lawuna, da kuma kogin Nakare.
Hakan ya sa mutane da dama suka ringa yin kaura zuwa yankin domin zama…
Daga cikin mutanen da suka fi shahara cikin wadanda suka fara zama a yankin akwai wani jarumin makeri da ya iya kera zinare ana cewa dashi BUNZA, kuma sunansa ne aka sanya wa garin na BUNZA..
Dutsen BUNZA wanda girmansa ya kai murabba’in kilo mita 634,209, watau kwatankwacin kashi 52 cikin dari na girman jihar baki daya.
Yankin BUNZA ya hada da hamadar GAFA mai cike da tsaunika..
Mafi yawancin jama’ar yankin amce larabawa ne na Lebanon wanda ibtilai ya same su a daruruwan shekaru aka kwaso su zuwa kasar nijeriya. A ka kuma sauke su a yankin na BUNZA…Nan suka hayayyafa suka tara zuri’ah, akwai kuma barebari, Fulani da kuma Hausawa..
Yankuna da dama ne suka taru don shiryawa yadda zaa ci yankin BUNZA da hari. Domin yankin nada tarin arziki na zinare da suke hakowa. Kasashen da dama sun bukaci da yan usulin yankin su sayar musu da sansanin don mallakar wajen. Mutanen BUNZA suka ki amincewa da hakan…
Hakan yasanya yankuna dadama suka hada karfi da karfe suka kaiwa garin BUNZA hari. Suka kashe na kashewa suka farfasa duwatsun suka haqe suka kwashe zinaren. Sai babban uslin dutsen yankin na BUNZA shine bai karasa fasuwa ba daga gefe basu lura ba maharan. Suka ci garin da yaki suka kyale su.
Harin da aka kaiwa yankin BUNZA ba karamin rasa rayuka da arzikan tattalin yan garin sukai ba. Zuriya dadama sun mummutu. Wasu sun bar yankin sun gudu. Yayinda wasu da aka kwashe wa arzikin su nan take wasu suka futa hayyacin su. Wasu Suka samu tabin kwakwale da sauran su…
Bayan tafiyar lokaci mai tsawo….yankin BUNZA a yanzu babbar sana’ar yankin itace cinikin gishiri da dabino, sai dai a shekarun 1970’s harkar bude ido ta zama wata babbar sana’ar yankin…
Amman duk da hakan al’adar yankin ta na nan ‘ya’ya mata basa karatun boko. Mazan ne keyi kawai… Suma da sum dan tasa za’a dakatar dasu sun daina sai su koma noma da sauran aiyukan karfi na gado.
Dan karatun da sukayi amfamin sa shine idan masu yawon buda idanu suka zo yankin. Kuma basa jin hausa ko fullanci ko larabci to sai yaran su mazan suyi mu’amala da su ta yaren turanci..
Haka zalika matan da sun dan tasa sun fara girma sai a aurar da su ga mazaje. Suma mazan ba Kuma masu shekaru bane. Dik Yara ne wadanda Suka dara matan da shekaru kadan.. Ba Kuma son ransu ake basu ba.
Al’adar itace namiji zai nome gona acikin kwanaki kadan. Ya yinda macen zata dinga zuwa bingi/tekun ruwa don debo ruwa a manyan bokitai ta kai gidan surukai. Har sawu goma duk kwana daya.
Kuma tsakanin tekun da inda gidajen yan yankin yake akwai tazara sosai a tsakani… Amman duk wannan uban wahalar da ake sha kowane yaro da yarinyar sai sun cikace hukuncin sannan a daura musu auren dole. Hakan Kuma zaka hakura… Domin KADDARA!! KOWA DA IRIN TAASA (Free book dina)👌
Mai karatu kada na isheka/ki da ratattako takaitaccen bayani game da yankin na jihar BUNZA… Bara mu tsunduma cikin labarin don jin yadda kowane bangare zai kasance…
Amman Kafin sannan bari na Kara maimaitawa Mutanen yankin BUNZA. Kyawawan asaline musanman zuri’ar:
HAMIDNIYYA LEBANON
Zaune Nawraah take akan yar katifar ta. Hannun ta rike da biro da paper tana rubuta ABCD da manyan baki.
Amnah ta shigaa dakin da sauri. Tana karkada mata hannu. Hakan yasa Nawraah daukar littafin da sauri ta cusa shi karkashin katifa biron Kuma ta boye shi acikin hular kanta.
Sai zare idanu takeyi. Kalo daya zakai mata kasan batada gaskia. Ta tsiri riko hannun Amnah tana ce mata………
File Name | Kwankwason Jimina… Hausa Novel Doc. |
Title | Kwankwason Jimina Complete Novel |
Author | Nana Hafsatu (Mrs Xoxo) |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Rich Vs Poor Story |
Published Date | 31/10/2024 |
File Size | 400KB |
Format Size | TXT |
Book Price | 500 |
Phone No | 09166221261 |
Download Kwankwason Jimina Complete Novel By Nana Hafsatu (Mrs Xoxo)
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.