Description/Story:
Abban Sojoji Book 1 Complete Hausa Novel Document Written By Hafsat Bature (Boss Bature)
Description
Hannu tasa ta toshe kunnenta saboda ta gaji da jin masifar da Buzun maigadin yake ta surfa mata, “Ke wannan idan mayya ce kika kama mutun wallahi sai an yi da kyar za a samu magani.”
“Na she miki hajiya ba ta nan kullum sai kin zo, ba ki da zuciya ne kare ya lashe ko? Yarinya karama da ke sai taurin kan tsiya, da wasu kwala-kwalan idonki kamar na kwarton mazuru, kina kallon mutane da su ba kunya ko? Kai ga d’an iska!”
Dagowa ta yi a hankali tana kallon sa jin cin mutuncin da yake yi mata , idonta ne suka ciko taf da kwalla, kananun labbanta suka soma kyarma, tuni yanayin fuskarta ya canza.
Duk a tunaninsa yarinyar za ta mayar masa da martani saboda ya san yaran zamanin nan ba ka taba su su yi maka shiru, zuba mata ido ya yi kuri yana kallon ta. Gani ya yi tana ja da baya a tunaninsa tafiya za ta yi tabar wurin amma sai ta samu wuri a jikin bangon gidan ta tsugunna tare da kifa kanta a saman guiwowinta sannan ta soma rera kuka mai tsuma zuciya.
Tsayawa ya yi yana kallon ta, da alamun nadama a tattare da shi, har cikin zuciyarsa yake jin bai kyauta mata ba, yana Musulmi da shi ya gaza fahimtar yar karamar yarinyar da ke zarya kullum a bakin gate din gidan, bai taba tambayar kansa dalilin da yasa yarinyar take zuwa wurin ba. Ba irin korar karen da bai yi mata ba amma hakan bai sa gobe taki dawowa ba.
Jiki a sanyaye ya matsa inda take ya tsugunna a gabanta ya ce, “Kai kukan ya isa haka! Dago ka gaya mini mene ke damun ka me yasa kake zuwa kullum kana neman hajiya?”
Dagowa ta yi fuskar nan ta yi jaga-jaga da hawaye ga majina cikin shesshekar kuka ta ce, “Ina zuwa neman hajiya ne saboda na ji an ce tana taimakon ‘yammata ta sama masu aikatau ana biyan su kudi.”
Jim ya yi yana kallon ta kafin ya ce, “Kai ko mai yasa kake neman aiki karamin yaro da kai gidanku ba manya ne?”
Girgiza kai ta yi, “A’a babu kowa, ba mu da kowa, ni da ‘yan uwana ne kuma ba su da lafiya an kwantar da su a asibiti, kuna likita ya ce aiki za a yi musu, ba ni da kudin aikin saboda suna dayawa, shi ne nake so na samu aikin da zan yi ina samun kudin da zan tara a ayi musu aiki kada su mutu su bar ni ni kadai!” Karasa maganar ta yi tare da mayar da kanta kasa tana kuka.
Yanzu ya gane dalilin da yasa yarinyar ta nace sai taga hajiyar, a cikin zuciyarsa ya ce, “Baiwar Allah tana shikin damuwa karama da ita. Oh amma yana da tunani mai kyau!”
Riko hannunta ya yi tare da cewa, “Share hawayen ya isa haka, zan taimaka maka ka ga Hajiya, taso mu je ka zauna saman benchi ka ji.”
Mike wa ta yi ta bisa, a tare suka zauna saman bencin, jim suka yi na d’an wani lokaci kafin ya ce, “Ka yi shiru kaji ka daina kuka Allah shi ne gatan bawanSa ko mutun bai da kowa indai ya yi imani da Allah shi ne zai zama gatansa, ka shi gaba da addu’a ‘yan uwanka za su samu sauki har ku yi wasa da su.”
Murmushi ta yi saboda ta ji dadin maganarsa, hannu ya kai ya dauko ruwan bunun da yake dafawa a saman ‘yar butarsa, dama akwai karamin kofi guda biyu da yake amfani da su wurin zuba shayin.
Some of related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels