Zafafa 2023

Kwai Cikin Kaya Book 1&2 Complete Novel Document

Kwai Cikin Kaya Book 1&2 Complete By Billyn Abdull

Description/Story:

Kwai Cikin Kaya Book 1&2 Complete Novel Document

Written By Billyn Abdull

 

Description

………..Ko wacce kafar yaɗa labarai da ta yanar gizo labarinsu a wannan safiya ta laraba shine sace shahararren mai arziƙin nan *Alhaji Sadi kokino (ba giyar yaro ba)*.

A yanda labaran ke ta yawo an sace Alhaji Sadi kokino ne a daren jiya talata a filin jirgin sauka da tashi na babban birnin ƙasar. Abu mafi ɗaure kai ga wannan lamari shine ta hanyar da mutumin da yay garkuwa da shi ya ƙwamushe sa. Da yawan mutane da suka shigo jirgi ɗaya da Alhaji Sadi kokino sun tabbatar ma jama’a da lafiya lau ya sauka, harma ya gaisa da wasu tsirarun mutane da suka je tarbarsa. Sannan akwai wasu ƴan jarida guda biyu a filin jirgin da har suka ɗauki hotansa da gajeren bidiyo. Kowa ya shaida Alhaji Sadi lafiyar ALLAH ya shiga motar da ɗaya a masu gadinsa ya buɗe masa, sannan amintaccen direbansa yaja motar a gaban kowa. Sai dai a lokacin da motocin suka shiga harabar gidansa aka sake buɗe masa ƙofa dan ya fita sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye, a taƙaice dai Alhaji Sadi kokino yayi ɓatan dabo a hanyar dake tsakanin filin jirgi zuwa gidansa.

Zuwa yanzu dai jami’an tsaro sun bazu ta ko ina nemansa, tare da buɗe kunnuwa da idanu ko za’aji wani abu da ga bakin wannan mai ƙwamushe da ba’a san ta yanda yay siddabarun sace Alhaji kokino ba…

*____________________________________*

A yayin da masu yawun mai da yanda akayi ke kaikawo akan wannan ruɗaɗɗen labari suma talakawa ƴan bani na iya sai tofa nasu albarkacin bakin suke. Ko wane dandalin sada zumunta na yanar gizo ka shiga sai kace nace akeyi. A yayin da wasu ke jimamin lamarin wasu ALLAH ya ƙara suke faɗa, a wani gefen kuwa ma kai tsaye suke ƙaryata lamarin da dangantashi da farfaganda irinta manyan ƙasa ce kawai, ƙilama yana can kwance a gidansa lafiyar ALLAH.

Daga masu ƙaryatawa har waɗanda suka gaskata kowa yana da dalilinsa, dan kuwa a yanda ƙwamishen ya kasance dolene ya bada mamaki, musamman idan mukai dubi da jami’an tsaro da cctv cameras da ke zagaye da filin jirgin, ga haske ta ko ina tamkar rana.

 

Koma dai yaya abin ya faru lokacine zai bayyana mana hakan😟.

*___________________________________*

Kwance yake a bayan motar idanunsa a lumshe tamkar mai barci, lokaci-lokaci yakan ɗanja guntun tsaki tare da huro zazzafar iska daga bakinsa.

Duk da kasancewarsa gwarzo kuma jarumin mutum mai ƙoƙari da jajircewa a aikinsa kallo ɗaya zakai masa a yanzu ka hango tarin gajiyawa da ɗunbin kasalar dake tattare da shi.

Tsayuwar motar da buɗe murfin da akayine ya tilasta masa buɗe lumsassun idanunsa kaɗan tare da ɗago hannunsa ya kai dubansa ga agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun, kaɗan ya yamutse fuska yana sake huro iska kaɗan kafin ya sauke hannun da maida dubansa ga ƙofar motar da aka buɗe.

Tamkar bazai motsa ba sai kuma ya yunkura a hankali ya ja baƙar rigar sanyinsa jibgegiya dake gefe ya zura kafafunsa waje.

Da sauri wanda ke tsaye a gabansa da alama shine ya buɗe ƙofar yay azamar kai hannu zai amshi rigar sanyin yana sake ƙamewa alamar girmamawa.

Kansa ya girgiza masa ba tare da ya bashi rigarba, ya matse idanu kaɗan saboda sara masan da kansa yake na azabar ciwo, ya sauke numfashi kafin ya fito gabaɗayansa yana tura ƙaramar bindigar hannunsa a aljihun bayan wando.

Idanunsa da ke jajir ya ɗago yana saukewa akan matasan samari biyu, cikin hanzari suka ƙame tare da sara masa. Hannunsa na dama ya dinƙule kawai yay gaba ba tare da suma yace musu uffan ba. bishin sa sukayi a baya suma ba tare da sheresun da yay ya damesu ba.

 

Cikin nutsuwarsa ya iso wajen da ake buƙatar ganinsa, da ganin yanayin ɗakin zaka fahimci wajene keɓantacce na jami’an tsaro da sukan tattauna akan wani case ko shawarwarinsu idan sun tado musamman ta fuskar tsaro.

Ba tare da yay magana da kowa ba ya samu waje ya zauna, suma sauran waɗanda suka shigo tare wajen zama suka samu. Ɗakin yayi tsit, bakajin komai sai ƙarar AC da na fitar numfashi, sai kuma ɗan motsin da baza’a rasaba.

Wanda ke tsaye jikin allon bangon yana wani ƴan zane-zane ya ɗago fuskarsa a matukar murtuke yana kallonsu.

“Nasan kowa zaiyi mamakin wannan taron na gaggawa da muka kira, duk da dai dukkan tunaninmu zai iya tsayawa a waje ɗaya game da abinda muka wayi gari da shi na sace babban mutum irin Alhaji Sadi Kokino. Kamar yanda muka sani tun a daren jiya wasu a cikin jami’anmu suna a wajen domin binciko ainahin abinda ya faru, a yanzu hakama daga can muka tado ɗaya da ga cikinsu domin ya bamu bayanai dangane da lamarin, sannan musan mataki na gaba da zamu ɗauka kuma, dan yanzu dai ga agogo ya nuna ƙarfe 7:19am, na tabbata duk inda 8am tayi wannan labarin zai gama baje duniya ne, sanin kankune kuma mune jami’ai na farko da kowa zai maida hankalin ji da ga garemu, tun daga kan jama’ar gari zuwa ƴan jarida da iyalansa dama jama’ar dunaya baki ɗaya”.

A tare suka shiga jinjina kai alamar gamsuwa da bayaninsa.

Cikin gyara tsayuwa ya ke kallonsu, ya sauke idanunsa akansa da har yanzu hannunsa ke dafe da kansa, *“Jawaad!”*.

Jin sunansa da aka ambatane ya sakashi janye hannunsa tare da ɗago manyan idanunsa da ke a jajur ya sauke akan ogan nasa, cikin dakewar murya da ke tabbatar da shiɗin jarumine ma’abocin nutsuwa ya amsa da “Yes sir” tare da miƙewa tsaye yana ƙamewa.

Gaban allon ogan ya nuna masa da biron dake hannunsa.

Cike da kasala mai tare da nauyin jiki ya taka zuwa wajen, ya maido kallonsa gaba ɗaya zuwa ga sauran jami’an tsaron dake cikin ɗakin taron.

Cikin nutsatstsiyar muryarsa mai amo da saka razani ga abokin gaba ya fara faɗin, “Duk abinda zan faɗa game da wannan lamarin a taƙaice zai iya zama gaggawa, dan har zuwa yanzu da na baro filina jirgin da gidan Alhaji Kokino babu wani bakin zare da muka samu a kai sai surutai marasa makama, a cctv cemaras na Airport kuma lafiya lau Alhaji Sadi ya shiga mota tare da masu tsaron lafiyarsa. A ɗan nazarina ta wannan gaɓar ya nuna lallai mai satar yanada matuƙar wayo, kuma ƙwararrene mai aiki da ƙwaƙwalwa…”

Kowa jin jina kai ya shiga yi alamar gamsuwa da bayanin Jawaad da ke riƙe da kansa da ke ƙara ƙarfin sarawa na ciwo.

Wanine cikin waɗanda ke zaune a kujeru na musamman, alamun shima babbane yay gyaran murya tare da gyara abin maganar dake gabansa. “Wato bayanan JAY abin dubawa ne kam tabbas, amma ku wace shawara ce da ku a kan hakan?”.

Wani ne da ga can rukunin kujerun da Jawaad ya taso ya ɗaga hannu, damar magana aka bashi. Bayan ya miƙe ya ƙame sannan ya fara magana cike da girmamawa, “Yallaɓai ƙwarai maganar jay gaskiya ce, sannan ya kamata muma muyi shiri na musamman akan wanann case ɗin, dan inhar muka kuɓutar da Alhaji kokino ba ƙaramin daraja hukumar ƴan sanda zata sake samuba a idon jama’a”.

Tafa masa sukai, wanima ya sake ɗaga hannu aka bashi dama, shima goyon bayansa ya nuna akan maganar Jawaad. Bayan shi mutane biyu sun sake yin mubayi’a kafin wani ya tashi shikuma bayan an bashi izini, fuska a ɗaure yana wani hura hanci da fesar da iska yace, “Sam wannan shawarar tasa bata kan tsari, ya kamata ama ƙalubalancesa, tun a daren jiya bayan faruwar abin da mintunan da basufi goma ba aka turashi wajen shida wasu jami’an tsaro, amma ace babu wani bayani na cigaba da aka samu, bayan a ƴan mintunan da sukaje wajen bai kai nisan da za’ace shi mai ƙwamishen yayi nisa ba, kawai shi dai yace bazai iyaba sai a nema wanda zai iya kawai, inba hakaba ta silar wannan case ɗin to lallai hukumar ƴan sada tana tare da babbar barazana ta zubewar kima da sake saka shakku a zukatan al’umma a kanmu”.

Kowa kallonsa yake kawai, yayinda manyan suke jinjina masa kai da wasu a tsirarun sauran jami’an.

Jawaad kam ko motsi baiyiba balle ya kalli wanda ya gama bayanin, sai dai ya saki wani ƙasaitaccen murmushi da ya bayyana loɓar kumatunsa guda biyu kawai.

Ba karamin sukar zuciyar Qaseem Ali murmushin Jawaad yayi ba, amma ta wani ɓangaren ya ɗanji sanyi a ransa ganin maganarsa taso kawo ruɗani, dan sai ya zam kawunan jami’an tsaron yana neman rabuwa, wasu suna bin bayan Jawaad Abdul’aziz yusuf, wasu kuma suna bin bayan maganar Qaseem Ali.

Dan danan cece kuce ya fara yawaita a ɗakin taron har sai da aka tsawatar.

Murmushi Qaseem Ali ya saki ganin Jawaad ya dafe kai, sannan fuskarsa ta kuma ɗaurewa alamar ransa ya sosu, dama babban burinsa kenan.

Sai dai kuma sam tunaninsa bai sanar masa gaskiya ba, dan shi Jawaad surutun da ɗakin taron ya kaure da shine ya kuma saka kansa ƙarfin bugun ciwon da yakeyi sakamakon rashin samun isashshen barci da yay a daren jiya, ga ruwan sama da yay musu dukan tsiya jiyan da daddare, bayan dama ya koma gida a ƙurarren lokaci ne jiyan kafin ayi kiransa akan maganar sace kokino.

Tsitt ɗakin yayi bayan tsawatarwar da akayi, yanzu ma ɗaya daga cikin shugabannin ne yay magana.

“Duk wani kace nace bama buƙatarsa anan, kowa yasan wanene JAY akan ƙwazon aiki, ba wannan ne na farko ba da aka bashi irin wannan damar kuma ya magance ta, sai dai ko wanne irin case da ruɗanin da yake zuwa da shi, dan haka a wannan gaɓar mun naɗa Jawaad Abdul’aziz yusif matsayin wanda zai kula da wannan case ɗin, sannan mun saka Qaseem Ali matsayin mataimakinsa, kuna da damar haɗa rundinar jami’ai 30 da zasu taimaka muku, muna fatan zaku bamu gudunmawa ta haƙiƙa wajen fiddamu kunya ku kuɓutar da Alhaji Sadi cikin lokaci ƙankani da baza’a ga rauninmu ko gazawa ba”.

Tunda ya fara magana Qaseem yaji sunansa matsayin mataimakin JAY fara’ar fuskarsa ta ɓace ɓat, hakama magoya bayansa. Ga Jawaad kam bai ko ɗago kaiba balle musan yanayin da yake ciki.

Sun ɗan cigaba da tattaunawa kusan na awa ɗaya, wandda acikin awa ɗayarnan ba ƙaramin a takure Jawaad ya tsinci kansa ba, ana kammalawa ya nema izinin zuwa gida ya ɗan huta koda na awa uku ne.

Babu wani jan zance aka bashi dama, dan yanayinsa ya nuna buƙatuwa sosai na san hutun…..

*___________________________________*

Tunda Gimba yay fakin motar a harabar gidan ya buɗe idanunsa da suka sake masa nauyi da ƙyar, ba tare da ya jira Gimba ya buɗe masa murfinba ya buɗe da kansa ya fice, rigar sanyinsa ce kawai a hannunsa sai bindiga da ƙaramar wayarsa da ya fita da ita kawai.

A yanda ya shigo ya ga falon jiya yauma haka ya sameshi, yaja siririn tsaki yana haɗiye wani abu mai nauyi da ya tsaya masa a maƙoshi, zuciyarsa a matuƙar cinkushe ya ƙarasa sama inda nanne ɗakin barcinsa yake.

Kallo ɗaya yayma falonsa ya ɗauke kai, dan hatta da kofin da ya sha shayi a daren jiya yana a inda ya barsa, sam shi baima san wace irin mace ya aura ba, ƙazama ko ballagaza?. Takaici bai nemi shake numfashinsa ba sai da ya ƙarasa haɗaɗɗen bedroom ɗinsa ya sauke dubansa a kan lafiyayyen gadonsa da har yanzu take kwance, ta wani ƙudundune cikin lallausan bargonsa tana shaƙar barci. Tuni idanunsa sun sake kaɗawa sun koma jajur, yayinda jijiyoyin kansa suka sake fitowa raɗa-raɗa, yasan ko rantsuwa yay baza a bisa bashin kaffara ba akan Shuhudah batai sallar asuba ba.

Bai sake kallon gadonba ya jefa rigar sanyin akan sofa tare da zube wayarsa da bindigar saman tabirin dake shakanin kujerar da gado.

Duk da wani jiri-jiri da yake gani saboda yunwar da ke cin hanjinsa hakan bai hanashi nufar bayi ba dan ya samu ya watsa ruwa ko zai samo kan jikinsa……………✍🏻

*_Turƙashi, wannanfa shine Cakwakiyoyi ba Cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al’ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa ba’a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin ay.a da tsakkuwar zancena bayan mun tsunduma cikin labarin tsundum😉._*

_Ku kasance tare da ni Bilyn Abdull dan jin yanda wannan littafi mai suna a sama zai kasance, minene ma ma’anar *ƘWAI CIKIN ƘAYA!!?*, nasan wannan tambaya ce dake cikin zuciyoyin masu karatu baki ɗaya, wadda ni Bilynku kaɗai zan baku amsarta😚._

*Zata iya kasancewa cikakken buk ɗin sai bayan sallah ƙarama zaizo muku idan munkai da rai, idan kuma na samu dama koda ba kullum ba zanyi wasu pages kafin azumi insha ALLAH☺️🧐*⛹🏻‍♀️

Kwai Cikin Kaya Book 1&2 Complete Novel Document Txt

File Name Kwai Cikin Kaya… Hausa Novel Doc.
Title Kwai Cikin Kaya Book 1&2 Complete Document 
Author Bilkisu Abdul (Billyn Abdull)
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    07/11/2024
File Size    1.5MB
Format Size    TXT
Book Price    ₦300
Phone No   09032345899
Download Kwai Cikin Kaya Book 1&2 Complete Novel Document By Billyn Abdull

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

Book 1 👇👇👇

Book 2 👇👇👇

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button