Uncategorized

Mu Ma Yaya ne Page 1

 >>>>>>>>> MU MA ‘YA’YA NE  >>>>>>>>>>

Tana zaune a harabar gidan kan wani tudu ta yi tagumi tana kallon yaran da suke wasa a filin gurin, daga nan wasan yake nema ya zama fada. Ta taso da saurinta tana cewa. 

“Haba Muntari, ku bari mana”.

Ta shiga tsakanin su. 

“Haba Sa’id, na gaya muku ku daina fada a tsakanin ku, duk wanda ku ka gani a gidan nan dole mu hada kanmu mu zamo ‘yan uwan juna tunda ba mu da kowa sai junan namu”.

Muntari ya ce, “Ai Sa’id din ne ya fiya tsokana”.

Ta dafa shi, “Ka rinka hakuri, kai kuma Sa’id ka daina tsokana ka ji?”

Ya ce, “To”.

“To miko hannun ka ku gaisa”.

Ya miko hannunsa shima ya miko suka gaisa da junan su .

“Yauwa to kuje ku ci gaba da wasan ku kafin anjima mu shiga makaranta ko? “

Suka rike hannun juna suka tafi. 

Safiya ta dafa ta tare da cewa.

“Tunda na ga ban ganki a dakinmu ba na ce na san kina gurin zaman naki. Wannan guri kamar gado”.

Ta yi dariya, Safiya, ina jin dadin zaman wajen ne, ya fi dadin tunani, sabida iskar sa. 

“Ke kuma kullum tunani, yaushe za ki bar tunanin ne? 

“Safiya ina naga ranar daina tunani? Mutumin da baisan kansa ba, ban san wacece ni ba, to ina naga ta daina tunani?”

Safiya ta ce, “To du ba haka muke ba, ya zamuyi? Haka Allah Ya so ya ganmu, ba sai mu karba ba mu kuma yi masa godiya? 

Ummimi ta ce, Haka ne “.

Kukan da taji ne daga can dakin yara ya sa ta yi zumbur ta mike da saurinta har tana cin tuntube ta shiga dakin, ta dago shi.

“Saddik ka tashi ka ga ka jike jikinka da fitsari ai dole kayi kuka Saddik saboda kaikayi”.

Ta cire masa kayan ta yi masa wanka, ta matse kayan ta shanya. Ta duba ta dauko masa wasu kayan ta sa masa, ta karbo masa koko a kofi ta zauna tana bashi yana sha. Wasu suka farka duk kuka suke yi suna neman agaji.

Ta ajiye Saddik din ta kama tashin Maman dakin mai kula da su.

“Mama, ki tashi kinga duk sun farka”.

Mama ta ce, “To ba zaki tashi waccan Maman ba sai ni? Ko ni kadai ake biya albashin?”

“Yi hakuri Mama, itama yanzu zan tashe ta”.

Ta juya kan daya Maman wadda itama aikinta ne kula da yaran.

“Mama ki tashi, kinga gaba dayan su sun tashi”.

Itama Maman ta tashi tana mutstsike ido.

“Ashe rana tayi? Tun daga Sallar asuba da na koma bacci ban san garin ya waye ba, ina ragowar ‘yan uwan naki? Ba sai ki kirawo su ba mu hadu mu gyara kananan”.

“Suna can suna shirin makaranta, nima sauri nake yi, bari naje na dauko musu kokon a kicin kafin mu gama yi musu wankan”. Ta fita da sauri.

Mama ta kalle ta cikin tausayawa, ita ce kawai take iya zuwa ta taimaka musu da yaran marasa baki, su ragowar sun fi son ‘yan wadanda suka fara tasawa, sun san ba sa kashin kwance ko fitsari bare su wanke musu.

Ummimi ta dauko koko fari kal da aka yi masa damu mai kyau, sai dai sukari da bai ji ba ta zuzzubawa yaran a kofunan su, ta sa musu murfaye masu hudoji yanda za su rinka zuka ba tare da sun bata jikin su ba, kamar dai fida.

Mama ta yi musu wanka, daya Mamar tana shafa musu mai, Ummimi ta rinka sa musu kayan su tana danka musu fidar kokon su a hannun su. Sai da ta ga sun gama da shirya yaran ta yi saurin tafiya dakinsu ta yi nata shirin ta shiga makaranta, har an fara yi musu darasi.

Da yake Ummimi tana ganin kamar karatu shi ne gatanta a nan gaba, don haka ba ta sake ko wasa da shi. Tana da matukar kokari da basira, komai aka biya mata ta dauke shi a kanta.

Haka bangaren Islamiyya, ba ta wasa, ta san duk litttafan nan su Ahlari, Kawa’idi, Hadisi da dai sauran su. A Alkur’ani kuwa yanzu su na izu arba’in da biyu, kuma karatu suke yi mai kyau ba na zuku ba.

Yanda kullum take kara yiwa Allah godiya kenan, yanda ta zo a haka bata san kowace ce ita ba sai Allah Ya sa rayuwar su ba ta wulakanta ba, sun sami ingantaccen ilimi mai kyau. Yanzu tana shekara goma sha shida, tana aji biyar a sakandire.

Ummimi kyakkyawar yarinya ce fara kal da ita ga ta da sanyin hali. Tana da tausayi, ga ta da raunin zuciya, abu kankani sai ya sa ta kuka. Gashi dai itama tashi ta yi ta tsinci kanta a gidan marayu, ba ta san wace ce ita ba, ba ta da Wa ko Kani na jini. Amma duk yaran da suke cikin gidan marayun ta rungume su, ta zame musu tamkar Uwa.

Da ta ji yaro yana kuka za ta taho wajen sa ta rungume shi tana rarrashin sa, idan yunwa yake ji ta samo masa abinci ta bashi ya ci.

Kusan kullum sai ta yiwa yaran wanki, ba ta so ta gansu da kaya masu datti, duk da dai gwamnati da masu kudi su na kawo musu tallafi sosai, amma ba komai ake basu ba, ma’aikatan sun fi kwashewa su kaiwa iyalan su. Duk da dai ba kowa ne ke da son zuciyar a cikin su ba, daidaiku ne, kuma su ma sai sun faki ido su ke samun damar kwasar tallafin da ake kawowa yaran.

Shi yasa yaran duk sun fi sabawa da ita, don ba ta gajiya da hidimar su. Shi yasa duk wanda yake rigimar sa sai dai ya nufo Ummimi, ita ce mai rungumar su ta rarrashe su, ta kuma samo musu abinda suke bukata na daga ruwa ko abinci, ko dan biskit, ko alawa, tunda duk ana kawo musu.

Ummimi ba su san ko ina ba, domin rayuwa suke yi iya cikin gidan kawai. Karatun su na boko da Islamiyya duk a ciki suke yi.

Ranar Asabar ba su da makarantar boko, Ummimi sai ta tafi office din shugabar ‘yan rainon na su ta yi mata shara. Tana goge-goge ne Hajiya Hadiza ta shigo, ita ce shugabar ta su, ta ce.

“Sannu Ummimi”.

Ta durkusa, “Mama, ina kwana?”

“Lafiya lau Ummimi, ya ku ka tashi? Ya kannen na ki?”

“Lafiya kalau muke”.

Ta mike ta ci gaba da goge-gogen ta.

Masinjan ta ya shigo da sallamar sa,

“Ranki ya dade ga baki kinyi.

“To Malam Iliya, su shigo.

Malam Iliya ya koma ya shigar da su, maza ne guda biyu daya yana rungume da jariri, dayan kuma yana janye da wata mata tana ta masifa tana cewa.

“To ka sake ni mana, ina ruwanka da ni? Ka cika ni ka daina ja na”.

Ya kai hannu ya kwada mata mari, ya jawo ta cikin office din.

Mama ta ce, “Subhanallahi! Lafiya Malam ka ke dukan ta?”

Mutumin ya ce, “Ai Hajiya wannan da ki ka gani matsiyaciyar mata ce, ya cancanci ayi mata ma fiye da hakan”.

Kinga ni dan Adaidaita sahu ne, na biyo ta unguwar can kasancewar shiru babu mutane a gurin, sai na hango kamar mutum ya tsuguna shi ne na sauka gefen hanya na kashe babur din na lallaba a hankali, shi ne nai ta jin kukan jariri, ina zuwa gurin sai naga wannan ‘yar banzar matar ta tsuguna ta haka rami ta saka dan jinjirin nan a ciki da ransa da komai tana zuba masa kasa a kansa za ta binne shi, shi kuma yana ta tsala ihu. Shi ne na sa kafa na hankade ta, ta mike tana kokarin guduwa na tado kafarta ta fadi na take ta. Na ciro dan na riko ta ina jawo ta tana turjewa, sai Allah Ya hadani da mutumi nan shi kuma yana tura kurar ruwa, shi ne yaga yanda take turjewa ta ki ta taho yake tambaya ta me ya hadamu, duk na gaya masa, shi ne ya kwada mata mari ya karbi dan ya bar kurar ruwan nasa a can muka taho”.

Hajiya Hadiza ta ce, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!”.

Ta dauki waya tana bugawa D.P.O na ‘yan sanda, ta ce.

“Yallabai, wani kes ne anan office dina wanda abin ya fi karfina sai kun shigo ciki”.

Da kansa ya ce gashi nan, don jin me yake faruwa?

Ummimi kuwa tana tsaye rike da duster da take goge-gogen sai kuka take yi tana yiwa matar nan wani irin kallo na tsana.

Ummimi ta zo ta karbi ‘yar daga hannun mutumin nan dan ga ruwa ta rungumeta a jikinta tana kuka. Ta kalli Hajiya Hadiza ta ce.

“Mama, nima haka tawa Uwar ta yi min ko?”

Hajiya Hadiza ta girgiza kai ba tare da ta ce komai ba.

Sai a sannan mai jegon ta dago ta kalli Ummimi da take rungume da ‘yarta, sai a lokacin ta ji hawaye ya zubo mata a idonta. Daidai lokacin da D.P.O ya shigo shi da wani kurtun dan sanda da kulki a hannunsa.

Mama ta dau dubu biyu ta bawa dan Adaidaita sahu ta ce su raba da mai kurar ruwan, suje su dau babur dinsu da kurar ruwansu kada a sace musu, daga baya sa dawo su ji yanda aka yi. Suka fita suma suna godiya.

Hajiya Hadiza duk ta mayarwa da D.P.O yanda maganar take. Ya dakawa mai jegon tsawa ya ce.

“Ke karbeta ki bata nono ta sha”.

Mai jegon ta karbeta ta sa mata nono a baki, nan da nan yarinya sai ta kama sha, ta yi shiru.

D.P.O ya ce, “Yan iskan yara, kuna kananan ku kun bata rayuwar ku, kuyi cikin shege, ku yi ta yar da shi. Ba ku ji kunyar yawo da shi ba sai kun haihu ku zubar da ‘ya’yan ko ku kashe su, kenan ku ke jin kunyar yawo da su. To bata nonon ta sha, za mu mika ki a kotu a kokarinki na kisan kai, kinga za a daure ki, daga karshe ki yi zaman bursin na dundun dun.

Kuma ‘ya dole ki shayar da ita, kinga kin jawo muku rayuwar gidan bursin kenan ke da tatsitsiyar yarinyar da bata ji ba bata gani ba.

Mai jegon nan tana budar baki sai ta ce.

“Alhamdu lillahi, na godewa Allah da Ya kubutar dani bisa mummunan halin da nake ciki. Hakika na kara yiwa Allah godiya da Ya san duk inda bayinSa suke, Ya ke kuma tallafa musu duk sanda suke cikin mawuyacin hali. Tunda har zan samu inda zan tsuguna na rayu da ‘yata kowanne irin kunci ne zan iya jurewa. Haka Allah Ya so ya ganni, ya kuma kaddaro min”.

Mama ta ce, “Kin san kaddarar ne har ki ka kasa hakuri da abinda Allah Ya dora miki kike kokarin yin kisa?”

Ta girgiza kai, “Ba kisa zanyi ba”.

D.P.O ya ce, “Karya aka yi miki kenan?

“Ba karya suka yi min ba, abinda suka tarar da ni ina yi kenan, amma nima dole ce ta sa ni.

Mama ta ce, “Dole kamar yaya? Yi mana bayani muna jin ki.

Ta ce, “Ni sunana Surayya, bani da Uwa, amma kafin Uwata ta rasu ni ‘yar gata ce ta kin karawa, domin Babana da Babata ni kadai suke da ni.

Iyayena ba ‘yan nan garin bane, ‘yan kasar Mali ne, duk shekara muke zuwa can kasar ganin gida. Saboda Allah Ya yi Mahaifina Alhaji Atiku wajen neman abinsa anan yake, kuma ya samu rufin asiri da dukiya daidai gwargwado.

Duk da gatan da Iyayena suke bani hakan bai sa na sangarce ba, domin Iyayena sun yi kokari wajen inganta tarbiyyata, sun bani ilimi na boko da na Arabiyya.

Muna rayuwa ni da Iyayena mu uku, wata rana Mamana ta tashi da amai da gudawa na lokaci daya, ba ta kwana ba Allah Ya karbi ranta. Mun yi kuka sosai ni da Babana.

Lokacin da aka share makoki muka je can kasar su Babanmu, a nan suke jin mutuwar Mamana, su ma sunyi kuka na rashinta, inda dangin Mahaifiyata suka nemi da ya basu ni, ya ce su yi hakuri ba zai iya ba. Na sa dangin ma sai da suka nemi ya bar musu ni, ya ce, a’a. Hakaa su ka rabu da shi ya taho da ni.

Muna zaune ni da shi a gidan da wata tsohuwar mata da take yi mana aiki tun Mamana tana da rai, sai mai gadinmu. Na ci gaba da zuwa makaranta ta, lokacin ina aji hudu a sakandire.

Wata rana Babana ya ce min ai aure zai yi, zai samar min sabuwar Mama. Nai ta murna ina cewa, Allah Ya sa kamar Mamata take mu ci gaba da rayuwar mu cikin jin dadi.

Babana ya yi aure, ya auri wata mata Hajiya Sarai, ina kiranta da Mama. Sai dai ita ba irin Mamana ba ce, saboda wannan tana da fada, ga ta miskila ba ta dariya, don ni tsoronta ma nake ji, don in ta daka min tsawa sai na firgita.

Gaskiya ba na jin dadin zama da ita, amma ba ta yanda zan iya gayawa Babana domin koyaushe tana tare da shi, ko meye ma sai dai ya gaya min a gabanta ko ni na gaya masa a gabanta.

Watan Babana uku da aure ‘yan fashi suka shigo gidanmu suka nemi ya basu kudi, duk ya tarkata ya basu da mukullayen motocin sa guda biyu. Duk wani abu nasa mai amfani wanda dukiya ce, to sun kar e shi. Amma sai suka dora masa bindiga a wuya suka ce ya fadi wasiyyar sa ta karshe, domin za su kashe shi.

Na saka kuka ina cewa, “Ku taimaka min kada ku kashe min shi, shi kadai ne da ni, ban san kowa ba a garin nan, kuma bani da kowa. Don Allah ku yi hakuri kada ku kashe shi”.

Babbansu ya ce, “Yi shiru ‘yar kyakkyawa, kema muna nan tafe kanki, don a lissafin mu har da ke”.

Ragowar suka daddaure Babana, a gabansa yana kara yana fincike-fincike suka toshe masa baki, katon nan ya yayyagemin kayan jikina ya yi min fyade a gaban Mahaifina.

Ina ji Abbana yana yin wata ajiyar zuciya, duk da haka suka sakar masa harbi a kafada, ya yi wata kara dai-dai lokacin nj kuma na suma, sai farkawa nayi na ga ‘yan sanda a zagaye da mu ana kokarin dauke Babana za a kaishi asibiti. Ni kuma wata makociyar mu ce ta gyara ni, saboda matar Babana ta bi shi asibitin.

Babana bai mutu ba yana ta shan bakar wahala, ga barbi, ga harbi, ga ciwon zuciya da ta buga a lokacin da yaga katon nan ya yi min fyade.

Watan Babana shida a asibiti aka dawo da shi gida, kwanansa biyu da dawowa matarsa take gaya masa wai ai ciki ne dani.

Ya ce, “Wane irin ciki?”

Ya kira ni yake tambaya ta, na ce, “Wallahu nima ban sani ba, naga dai ciki na yana girma, kuma ina jin motsi”.

Ya ce, “Ba kya yin al’ada?

Na ce, “Tun lokacin da nayi wankan tsarki dan fashin nan ya yi min fyade, tun daga wannan jinin ban kuma gani ba”.

Babana ya dafe zuciyarshi yana salati yana wata irin shakuwa, na gigice na tafi dauko masa ruwa ina kuka, kafin na zo har ya mutu. Na yi ta ihun kuka na ina tumami, matar Babana tana kallona kawai.

Ni dai ban san lokacin da aka yi masa jana’iza ba, domin suma nayi sai bayan kwana uku ma na san inda kaina yake.

Haka na ci gaba da zama da matar Babana cikin halin kunci da wahala, ga yarinta, ga nauyin ciki, ga maraici. Don ta mayar dani ‘yar aiki, ni ce shara, wanke-wanke. Ni zanyi girki, amma sai dan abinda ta sammin. Ga tsohon ciki, haka zan side ba tare da na koshi ba.

Dai dai da ruwa in har zan sha ya isheni, sai dai idan na faki idonta.

A haka shekaranjiya ciwon nakuda ya kamani, ina ta murkususu ta zo tana zagina, ban fito nayi aikin gida ba, da taga yanda nake ta ce.

“Nakuda ‘yar nan? To bazan zauna na ga wannan kazantar ba, bari na bar miki gidan, sai dai idan kin haihu ki san duk inda ki ka  bata a gidan nan kin gyara, don bana son karnin haihuwa”.

Ta fice ta bar ni a wannan hali ina ta fama juyi, tun ina iya ambaton Allah har bakina ya kasa furta wata kalma, sai a zuciyata nake ta nanata Inna lillahi wa inna ilaihir traji’un, da kiran Allah Allah.

Cikin hikimar Ubangiji sai ya turomin tsohuwar da ta yi mana aiki, zuwan matar Babanmu ta kore ta. Cikin taimakon Ubangiji baiwar Allah nan Allah Ya bata ikon tallafa min haf na haihu.

Tsohuwar nan ta sa ruwa ya yi zafi, duk ta gargasa min jikina. Ta dumama min abincin jiya da ta gani a kicin din, ashe da abincin ta barni na kwana da yunwa, kuma na  tashi da nakuda. Shi ne dalilin da yasa ashe na galabaita sosai.

Iya ta gyara wajen fes, sai gashi da na ci abincin ta yi min wanka ta gargasa min jikina, na kwanta na samu bacci sosai.

Iya ta yiwa yarinyar nan wanka ta nade ta a zannuwana, domin babu riga ko daya da za a sa mata.

Iya dai tana ta zaman jiran matar Babana ta dawo ta tafi har ta fara gyangyadi bacci kuwa ya kwashe ta.

A takaice dai matar Babana ba ta dawo ba sai da safe tare da wasu manyan Alhazai su na dudduba gidan, ban san ko cinikin me suke yi ba, naji dai suna ta lissafin kudi.

A ranar ta kwashe komai nata ta yi tafiyarta ba tare da ta ce min wani abu ba.

Iya ta tafi tun jiya da daddare, ni kadai na kwana a gidan nan, sai yau da safe wadannan Alhazan suka zo suka ce min.

“Ke me kike yi ne ba ki tafi ba?

Na ce, “Ina zani ni da gidanmu?

Daya Alhajin ya ce, “Ai yanzu ba gidanku bane, domin Hajiya ta siyar mana da shi mun biyata kudinta, ta kuma bamu takardun gida kin gansu nan. To don haka maza ki hada shirginki ki fice ko muyi mimi wulakancin da ba ki taba zata ba.

Abin da ya fado raina fyaden da ‘yan fashin nan suka yi min har na samu ciki, sai naji tsoro kada su yi min hakan na samu wani ciki , shi yasa kawai na goyo yarinyar na fito ba tare da na dauki komai ba.

Tun safe nake garari na rasa gurin zuwa ga kishirwa, ga yunwa, shi ne na samu waje na haka rami na saka yarinyar na rufa zani akan ramin na sa dutsuna a bakin ramin, kan dutsunan nake zuba kasar. Ni manufata runfa na yiwa yarinyar saboda rana, ina so na dan kwanta na yi bacci na dan huta, shi ne mai Adaidaita sahun nan ya ganni ya kama dukana yana cewa zan kasheta, ni kuwa wallahi ba zan iya kashe ta ba tunda na san ita kadai ta ragemin a duniya, tunda dangina sun yi min nisa.

Wannan shi ne labarina na gaskiya, idan kuma karya nake aje can unguwarmu a tambaya.

D.P.O ya ce “Wacce unguwa ce?

Ta gaya masa, ya ce.

“Tabbas ba karya kike yi ba, domin lokacin da abin ya faru kimanin wata tara da sati biyu kenan a hannuna kes din yake, wanda har yau maganar tana kotu ana kokarin  binciko ‘yan fashin. Kuma abinda muke zargi ma shi ne, da sa hannun wannan matar Baban naki ‘yan  fashin suka shiga gidan naku har suka aikata   miki fyade suka  kuma kashe  Mahaifin ki”.

Surayya ta kara fashewa da kuka, Ummimi da ke ta faman  kuka ta sunkuya ta dauki ‘yar ta ce.

“Kawota kada ta fadi”.

Ta dauketa ta sa ta a baya ta goya, D.P.O ya ce.

“Kina ganin ya za a yi da ita? Tunda dai duk kinji matsalarta, ni kuma na tabbatar  da gaskiya ta fada, domin kes dinma a hannuna yake  kamar yanda na gaya miki.

Ta ce, “Hakane, to  ai duk gaba  dayansu Uwar da ‘yar duk namu ne, tunda  gidane na marayu   da wadanda ba su da kowa sai Allah. Tayi zamanta ta ci gaba da karatunta tana rainon  ‘yarta,har Allah Ya sa ta samu miji tayi aure, sai mu hadata da mijin  suje can kasarsu a nemi danginta.

D.P.O ya  ce, “Hakane, mu kuma za mu ci gaba da neman   matar na n don  tuhumarta.

“To D.P.O, Allah Ya taimaka.

“Amin”.

Ummimi, jeki ki samo mata abinci”.

Ta ce, “To”

Ummimi ta tafi da saurinta, ta yi sa’a an gama abincin su na rana. Tuwon shinkafa ne da miyar kubewa (ehem dadi kenan).

Katuwar malmala ce, amma da Surayya ta karkace sai da ta cinye ta tas, ba Ummimi da take yarinya ba, dai dai da Hajiya Hadiza sai  da ta bata mamaki  wajen cinye wannan tuwo. Lallai ta san cewa yarinyar ta horu da yunwa.

Ummimi  ta  bata danta ta tafi  dakinsu don ta shirya  ta kuma ci abinci, saboda  lokacin shiga Islamiyya   ya kusa. Ta bar Surayya a  office Mama tana  cike mata takardu.

Ummimi tana shiga dakinsu Safiya ta tare ta tana cewa.

“Ke kuwa Ummimi me kike yi a office din shugaba? Yau kin dade”.

“Kin sanni Safiya da son sanin abu, wai koni ma zan gano ta yaya aka kawo ni gidan nan, duk da har yanzu duk kaunar da Mama take yi mi ta ki ta ce min komai a game da yanda Uwata ta yar dani aka tsinto ni. Yau kuma Uwa da ‘yarta gaba daya muka samu kari”.

Safiya ta ce, “Ikon Allah, ai ita wannan yarinyar za ta taso cikin jin dadi tunda tana tare da Uwarta. Ummimi addu’a zamu yi tayi, sai kuga in da rabo Allah Ya sa mun hadu da Iyayenmu kafin mu mutu”.

Ummimi ta ce, “Ai kuwa duk ran da muka hadu sai na ce Umma me yasa ki ka yi cikina ki ka yarda ni? Ba ruwankj da wacce irin rayuwa da yanayi zan shiga, ke dai kina can kina bin son zuciyarki”.

Safiya ta ce, “Fada ki ke yi Ummimi, ina za ki ga fuskar da za ki gaya mata hakan ma? Ba sai ta yarda ta karbe ki ma a matsayin ‘yar ba tunda gudunki take yi? Ai mu irinmu da kika ga Iyayenmu suna yar da mu gudunmu suke yi, suna gudun abin kunya kada ace suna da shegu”.

Ummimi ta ce, “Ni wallahi da zan ga Babar tawa ma cewa zanyi Umma na yafe miki, don Allah ki rungumeni ko sau daya ne naji dumin ki, na ji irin kaunar nan da ake ji tsakanin ‘ya da Uwa”.

Safiya ta ce, Allah Ya s Iyayen namu suna raye mu gansu ko da sau daya ne”.

Ummimi ta ce, “Amin.

Suka gama shirin su suka ci abinci, suka shiga Islamiyya.

Surayya kuwa duk aka gama cike wa’yansu takardu, Mama ta yi kiran wata sabuwar Mama da aka kawo saboda kula da yara ta ce.

“Ga yarinya nan da danyen goyo, ki dubi Allah ki tuna da ranar sakamako ki kula da yarinyar nan, ki yi mata bikin haihuwa, ki kula da ita sosai da ruwan wanka. Za a rinka bata abinci mai kyau daboda mai jego ce. Ki kula da ita kamar ‘yar cikin ki.

Kaddarar rayuwa ce ta fada mata, kada ki dubi albashin da gwamnati take baki, a’a hangowa kanki babban sakamako da yake can yake jiraki a ranar lahira saboda aikin da kika tsaya kika yi mai kyau na taimakin yaran da ba su da kowa da kuma marayu.

Mama sabuwa ta ce, “Na karba, in Allah Ya yarda komai kuma zanyishi bisa amana. Allah Ya taramu a ladan.

“Amin”.

Ranar Lahadi da hantsi Ummimi ta shimfida musu babbar tabarma a gindin eata rungujejiyar bishiya da take kallon office din Mama shugaba. Ummimi ta tara kananan yara a kan tabarmar tana ta yi musu wasa irin na cankulato-cankulato da su lugulugu ta nuna, yaran suna cikin nishadi. (uhm ni Ridwan har na tuno da yarintakata)

Sa’id ya ce “Yaya Ummi, kiyi mana tatsuniya mana mai dadi”.

Ta ce, “Kai Sa’id kasan tatsuniya karya ce, ba zata amfane ku da komai ba”.

Surayya ta yi sallama ta zo ta zauna, Ummimi ta yi saurin karbar babyn da take sunkufe a cikin kayan sanyi, ta ce.

“Surayya, ba Mama ta ce jego kike yi ba, sai kinyi arba’in za ki fara fitowa?”

Surayya ta ce, “Au! Idan ana jego ba a fita?

“Ba haka naji Mama ta ce ba”.

Dai dai lokacin da Mama Sabuwa ta karaso wajen tana cewa.

“Au Surayya fitowa kika yi na dawo dakin sai na tarar ba kya nan? To ga dumamen tuwo da na karbo miki tashi muje ki ci. Ummi kawo ‘yar, sai sunyi arba’in za su fara fitowa.

Ta ce, “To.

Ta mika mata “yar, suka koma daki.

Muntafi ya ce, “To Yaya Ummimi kiyi mana tarihi mai dadi.

Ta ce, “To bari nayi muku tarihin matan Annabi (S.A.W).

Saddik ya kama kuka yana miko mata hannu, ta dauke shi ta barr masa biskit ta bashi, ta rabawa yaran biskit ‘yan biyar-biyar da Mama ta aiko musu da shi yanzu.

“Bari na fara yi muku daga tarihin Nana A’isha, aurenta da fiyayyen halitta Annabi Muhammad (S.A.W).

Annabi (Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Ya samu wani tsawon lokaci bayan rasuwar Nana Khadija kafin Ya sake maganar wani aure, a sannan ne dattijuwa Khaulatu Bint Hakim ta je wajen sa ta ce, “Ya Ma’aikin Allah, naga duk ka rame saboda rashin Khadija”.

Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ai don ta kasance Uwar ‘ya’yana ce, kuma mai kula da gida”.

…Shafi na 35 an samu matsala babu komai a jiki.

.shafi na 36…… Allahu Akbar! Idan Allah Ya nufi abu to sai Ya kawo sanadinsa.

To Allah Ya kaddara wannan Aure sai Ya sanya Khaulatu ta zamo ita ce sanadi.

A Hadisin da Bukhari da Muslim da Turmuzi suka rawaito daga A’isha, ta ce, “Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “An nuna min hoton ki a cikin darare uku a cikin baccina, Mala’ika Jibrilu ne ya ke nuna min ke a cikin koren yanki na alharini, sai ya kance wannan matarka ce, sai na ce, idan daga Allah ne to Zai tabbatar da shi.

Don haka aure ba tilas bane, kada wani ya zaci hakA saboda karancin shekarunta. To ko kadan ba haka bane, don kuwa abin da Nana A’isha ta rinka nunawa bayan daurin auren ya tabbatar da irin kaunar da Nana A’isha take yiwa mijinta. Ga dai abinda A’isha Uwar Muminai ta rinka cewa.

“Manzon Allah bai aure ni ba har sai da Jibrilu ya zo masa da hotona, ya ce wannan matarka ce duniya da lahira. A lokacin ina ‘yar yarinya, ina daura tufafin harfu. Yayin da ya aure ni sai Allah (Subhanahu Wa Ta’ala) Ya sa min kunyar sa.

Wannan Hadisi ya tabbata cewa Nana A’isha tana son mijinga, don da bata bata son shi da bata rinka jin kunyarsa ba.

A yayin da take sanye da tufafin harfu, zani ne na fata wanda ‘yan mata su ke daurawa a waccan lokacin kafin ayi musu aure.

Yanda aka yi bikin aurenta Nana A’sha ce da kanta ta ba da labarin yanda aka yi bikin aurenta a Hadisin Bukhari da Muslim, inda take cewa.

“Manzon Allah (S.A.W) ya aure ni ina ‘yar shekara shida, sai muka isa Madina muka sauka a unguwar Banil Harsi binil Khazraj. Sai Mahaifiyata Ummu Rummana ta je ta kwallamin kira a lokacin ina wasan lilo ni da kawayena. Sai na je wajenta ina ta faman nishi, ban san abinda take nufi ba, sai ta kama hannuna har sai da muka je kofar gida, sannan ta dakatar dani, yayin nan numfashina ya lafa, sai ta samu ruwa ta shafa min a fuska da kaina, sannan ta shigar dani gida. Sai ga matan Madina a gidan, sai suka ce.

“Shigo, Allah Ya sa kin shigo cikin alkhairi da albarka da kyakkyawan arziki”.

Sai ta mika ni gare su, sai suka gyara ni. Ba zato sai naga Manzon Allah (S.A.W) a yayin nan lokacin hantsi ne. Sai ta mika ni gare shi, a sannan ina da shekaru tara”.

Ya zo a wata ruwayar cewa, a lokacin da Ummu Rummana ta mika Nana A’isha ga Annabi, sai ta zaunar da ita gabansa, ta ce, “Ga Iyalinka nan, Allah Ya sanya maka albarka a game da su, su ma ya sanya musu albarka a game da kai.

Nana A’isha ta ci gaba da cewa, “Sai matan suka fita, Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yana tare dani a gidanmu ba a yanka rakumi ko akuya ba har sai da Sa’adu bn Mu’azu ya aiko mana da wata gidauniya, aka kuma aiko mana da kwaryar Nono, Manzon Allah (S.A.W) ya sha, sannan ya miko min nima na karba na sha ina mai cike da jin kunya”.

Daga nan sai aka dauki Nana A’isha aka kaita zuwa gidan Annabi.

Kada ku zata irin wannan, a’a daki ne kwaya daya aka gida mata a kusa da Masallacinsa (S.A.W). An gina shi da tubalin kasa, aka yi masa rufi da zangarniyar dabino, sai aka sanya masa tabarma daga cikinsa, aka dora katifar fata akai wacce aka cusawa zarbar dabino a ciki. Sai labulaye da aka sanya a kofar dakin. A sannan daga dakin Nana Saudatu sai nata dakin kawai. Daga baya duk wadda Annabi Ya aura sai a gina mata nata dakin, har suka kai dakuna tara duk a kusa da Masallacin sa.

Tsananin soyayyar Nana A’isha ga Annabi (S.A.W).

Allahu Akbar! Nana A’isha ta nuna wa Annabu tsantsar soyayya da kauna ta gaskiya, saboda soyayyarta gareshi shi yasa ta yiwa sauran matan sa zarra wajen yi masa biyayya. Ta san yanda zata yi masa abu cikin lallashi da dadadawa, kuma tana tsananin kishin sa, ba ta yarda koda da kiftawar ido wata ta sha gabanta ba a wajensa (S.A.W).

Akwai wata rana da tayi masa karar kanta yana ciwo, sai ya jata da wasa yana cewa, “Damuwar me zaki yi? Idan da za ki rigani mutuwa kinga da sai nayi miki wanka, na saki a likkafani, na yi miki sallah, na binne ki.

A take a nan sai soyayyarsa ta sa kishi ya motsa mata, ta ce, “A yiwa wata dai, na rantse da Allah da haka za ta faru ba abinda zai hana ka angwanci da wata a dakina.

Allahu Akbar! Kunga wannan ya nuna mana irin soyayyar da Nana A’isha take yiwa mijinta. Saboda son da take yi masa tafi so ta zauna da shi da ta rigashi mutuwa ta shaki kamshin Aljannah.

Allah Sarki Uwar Muminai, ashe abin da take gudu na rabuwa da shi ya kusa, don ba su dade da wannan maganar ba bayan ‘yan kwanaki Annabi (S.A.W) Ya rasu ya barta da begensa.

Annabi ya so Nana A’isha fiye da sauran matansa saboda kyawawan halayen ta, domin Allah Ya yi masa nuni da ita.

Wannan ba abu ne wanda yake a boye ba, domin Mala’ika JIbrilu shi ya zo da hoton ta har sau uku yana yi masa bushara da auren ta.

Kuma ya tabbata a Hadisi Allah Yana saukar da wahayi ga Annabi (S.A.W) yayin da yake cikin mayafi daya da Nana A’isha.

Sannan kuma ga yanda Allah Ya kare ta a cikin suratul Nur, ya karyata wadanda suka yi mata kage”.

.

“Ummimi! Ummimi!.

Ta yi firgigit ta amsa kiran da Mama shugaba take yi mata, Maman ta ce.

“Ba kwa jin yunwa ne? Yau ba za ku ci abinci ba? Me kike ce musu ne?

“Mama tarihin Nana A’isha nake yi musu shi yasa kika ga sun nutsu ni kawai suke sauraro.

Mama ta ce, “Ai hakan yana da kyau, ki dauko muku abinci ku ci, sai ku yi shirin shiga Islamiyya. Su Saddik kananan kuma sai ku mika su dakin su”.

Ta ce, “To Mama”.

Ta dauko musu abincinsu a kula, Saddik ya debo musu ruwan sha, Sa’id ya daukk babban faranti da suke cin abincin a ciki.

Ita kadai ce ta ke iya cin abinci da yaran, saboda duk yawanci sa’o’inta da wadanda suka girmeta saboda sun ga sun girma sun san ciwon kansu, sun san su waye su, to sai su tayi ta killace kansu su rinka damun kansu da tunani da damuwa har sai an raba su da gidan, wasu a hadasu da mazan gidan ayi musu aure, wasu kuma idan wasu mutanen suna so in an tabbatar da kyan halinsu a basu.

Ummimi ta hada kan yaran maza da mata ta zuba abincin a babban faranti suka sa hannu suna ci a babban faranti suka sa hannu suna ci tana bawa kananan a baki, sai da gaba daya suka koshi. Tana wanke musu hannu wata mata ta tsaya dan nesa da su, wasu Hajiyoyi suka fito su biyu manya manya da su, daga ganinsu sun ci sun koshi, nera ta ratsa su, sun ta kallon yaran har suka shuge office din shugaba. Ba jimawa suka fito suka nufo waje  yaran, lokacin Ummimi tana hada kansu za su tafi dakunan su don su yi shirin shiga Islamiyya.

Hajiya Hadiza shugaba ta ce, “Ku tsaya.

Ummimi ta ja ta tsaya da yaran cikin sanyin jiki, domin ta san kwanan zancen.

Shugaba ta ce, “Ga yaran nan, bari a hado ragowar”.

Daya Hajiyar ta ce, “A’a, ai akwai wadanda suka yi mana anan ma, ni ba din takardar shaidar izinin daukar maza muka karbo ba ai da wannan ‘yar budurwar zan dauka.

Mama shugaba ta ce, “Ai wannan tawa ce, ba na bawa kowa. Mutane da yawa sun so su dauka na ki yarda.

Daya Hajiyar ta ce, “Ke kuma awa da kike da ikon hana daukan wata yarinya anan? Kada ki manta daga sama muka zo karba, a can muka nemo izini kuma aka amince mana daukan yara biyu maza, da munce da mace babu abinda zai hana mu daukar wannan ‘yar budurwar.

Ita dai Shugaba Hajiya Hadiza ta yi musu shiru ba tare da ta ce komai ba.

Daya Hajiyar ta ce, “Hajiya Rabi, wanne za ki dauka ne?

“Ai ni wannan dan farin yaron zan dauka, ke fa Hajiya Kulu?

“Ai ni wannan chocolate din zan dauka.

Suka nuna Muntari da Sa’id, Mama ta ce.

Sa’id da Muntari ku zo za a debe ku”.

Gaba daya suka rukunkume Ummimi suna kuka.

“Wayyo Yaya Ummi, kada ki bari a rabamu, mun fi son zama da ku, mun fi so mu fita gaba daya da ke mu koma gidajen mu tare. Don Allah Mama kada ki ba da mu ga kowa, kada a rabamu da Yaya Ummi.”

Ita kuwa Ummimi kuka take yi sosai kammar rantaa zai fita, duka ragowar yaran suma sai suka hau kuka. Itama kanta shugaba Hajiyaa Hadiza sai ta kama hawaye.

Hajiya Kulu ta ce, “Yau naga sabon salo hura wuta da tusa. In banda abinku ‘yan samari mene ne na kuka ku da Allah Ya ‘yanta ku kuka samu sababbin Iyaye? Za mu debe ku mu inganta rayuwarku da jin dadi, da ilimi har ku manta cikin kuncin da kuke”.

Hajiya Kulu ta ja Sa’id, Hajiya Rabi ta ja Muntari, “Taho dana, ni na san rikon ka da zanyi ba zaka taba yin nadama ba”.

Su Ummimi suna kuka su ma su Muntari suna kuka, suna ji suna gani aka zuba su a mota aka tafi da su.

Ko da Ummimi ta shiga Islamiyya kasa fahimtar komai ta yi saboda kukan da take ta faman yi.

Ko da aka tashi dakin su ta shiga ta kwanta, zazzabi kuwa ya rufe ta.

Safiya ta shigo ta ganta a kwance, ta zo ta zauna a kusa da ita, ta dafa ta.

“Ummimi, me ya same ki ne yau kike ta faman kuka gashi har kin haddasawa kanki zazzabi?

Cikin kuka Ummimi ta ce, “Damuwa ce”.

Safiya ta ce, “Haba Ummimi, yau muke a cikin damuwar ko jiya da haka kawai za ki daga hankalin kanki har ki jawowa kanki lalura? Ca nake ko yaushe ke kike gayamin cewar mu rinka yin hakuri da jarrabawar da Allah Ya dora mana, Yana sane da mu, wata rana sai labari?

Ummimi ta tashu zaune da kyar ta ce, “Sabo, sabo shi ne babban tushen da ya haifar min da damuwa. Ashe da gaskiyar mutane da suke cewa sabo ake yiwa kuka ba mutuwa ba”.

Safiya ta ce, “Me yake faruwa ne? Ni fa ban san ko meye ba.

Ta ce, “Safiya, a yau an rabani da Sa’id da Muntari, wasu Hajiyoyi ne sun zo sun kwashe su”.

Safiya ta dafe kirji, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Kinga irin abinda nake gudu ko? Shi yasa tun lokacin da nayi sabo da ‘yan biyu yaran nan kyawawa aka kawo su kamar su daya, muka dauki son duniya muka dorawa yaran nan, lokaci daya wani mutum ya zo ya ce bai taba haihuwa ba yana son yaran a bashj aka bashi ‘ya’yan nan, ga shi yanda muka saba da su aka kwashe su aka barmu da ciwon rabuwa da su. Shi yasa tun daga lokacin na daina sakin jiki da yaran, don kada muyi wata shakuwar a kuma zuwa a raba mu na kuma shiga damuwa. Ki rinka janye jikin ki daga yaran nan, kin san ba duka ake bari su girma a gidan nan ba, dole wasu ana kwashe su, to kinga shakuwa da su din duk ranar da aka rabu abin ba zai yi dadi ba”.

Ummimi ta ce, “Wallahi ni da mutuwa ma suka yi da sauki, don na san sun koma ga Ubangijin mu kowa ma ita yake jira, dole wata rana zamu koma gare Shi. To wannan ba a san su ba, ba a san ko su waye ba, ba a san daga ina suke ba. Da sunyi sha’awar daukan yara sun biyo ta sama sai a rinka ba su yaran nan, idan an ba da su babu wani wanda yake bi daga baya ya ga ina aka kai su? Ko kuwa inda aka kaisun wanne irin zama suke? Ko wacce irin kulawa ake ba su? Duk fa babu mai bibiya bare ya san zaman da suke yi.

Ko da yake ko meye ya faru da mu haka Allah Ya kaddara mana, haka Ubangiji ya shirya mana rayuwa, kuma Iyayenmu su ne mujazar komai da suka jefar da mu”.

“Haka za mu ci gaba da hakuri da rungumar kaddara kafin nan gaba mu ga yanda Allah Zai yi da mu”.

.

.

Yau amaryata Ummimi ta ce inyi posting kadan, domin tanajin kishi idan nayi da yawa masu suna Zainab da Zulaihatu suna karantawa.

.

Back to top button