Hausa novels

Kanwar Maza Page 74 Complete Novel By Ayshercool

Page 74

 

Usman ya yi ƙuri da ido yana kallonta.

 

“Yaya usy ba ka ce komai ba?”

 

“Ji nake kamar in kama ki in maƙure mini wuya ne”.

 

Cikin damuwa ta ce “Dan Allah ka yi haƙuri, ka rufa mini asiri”

 

“Ke dalla ware malama, ke yanzu duk zaman da ki ke yi, yake baki ci da sha, ya ɗauki nauyin karatunki, shirme kawai ki ke tafaka masa, zuwa ki ke kiyi masa ƙiri-ƙiri da ido, kamar gardi a cikin gida, ke kanki ba zaki taɓa waye ba, abun da aka koya miki baki san idan kin yi aure ki waye ba, sai kayan hauka da rashin hankali”

 

“Ni fa yaya usy ban gane me ka ke nufi ba”

 

Usman ya ce “Idan bai yi miki kiss ba, wata zai je ya yi wa a waje?”

 

“Yaya usy, ku fa ku ka ce mini haramun ne, Allah zai ƙona ni idan na yi”

 

“Kuma sai aka ce miki har da mijinki? Ai gara ya ƙara auren, kuma ba abun da zai hanamu raƙashewa da bikin, ki je ki yi ta shirmenki” Usman ya tashi ya bar kitchen ɗin.

 

Ta yi shiru tana tunani, ta yaya haka zai yiwu? Sun ce mata abu babu kyau, yanzu kuma an dawo an ce mata ya halatta ba tare da wani cikakken bayani ba. Ta basar da zancen ta cigaba da harkokinta.

 

Mai sunan baba kuwa rumaisa ta haɗa shi da assignment mai wahalar gaske, domin kuwa kasa sukuni yayi, maganar ta din ga damun zuciyar sa, ya din ga jin tamkar yayi tsuntuswa ya je ya ga Iman.

 

Da wayar mama, rumaisa ta kira Mahmud a waya, ta ce ya zo ya ɗauke ta, ta bashi adress ɗin gidan.

 

Yayyen ruma sun sha mamakin ganin Mahmud, basu san shi, ba sai dai wasu lokutan ta kan yi maganar sa.

 

Ya fi takawa sakewa da mutane wasu lokutan, dan haka nan da nan ya shiga cikin su Aliyu kamar sun saba.

 

Rumaisa ta ce “Daddy, ga Yasir, shi ne hacker shi ne ku ka yi waya da shi”

 

“Ki ka kuma ce mini hacker, ba zan sake yi miki wani abu ba”

 

Mahmud ya ce ‘Rabu da ita, ai ni da kai muke aikinmu” ta nuna masa Abdallah ta ce “Ga masterna a wurin zane-zane, da shi nake koyi, duk da idan na taɓa masa kayan zane, wataran ranƙwashina yake, amma a hakan Alhamdilillah na koya, dan haka shi zai yi mana zane, sonake kan papa ya dawo, mun gama komai”

 

Ya ce “Lallai team ɗin nan an haɗa manyan ƙwari a cikin sa, Allah ya dafa mana”. Mama sam ba ta san a kan me suke magana ba, bayan la’asar sosai, sannan ya ɗau ruma suka tafi gida.

 

Aikuwa ta sha faɗa a wurin laila, wai ta tafi gida, ba a kira takawa an tambayi izninsa ba, ruma tayi mata banza, irin kan ki ake ji ɗin nan.

 

Kusan sati guda, laila ta saka ruma a gaba, ta hanata sukuni, gashi ta yi ta mata magana da turanci, komai ruma ta yi sai ta ci gyaranta.

Ta hanata kwana tare da iman, tare suke kwana a ɗaki tare da ita, gashi ta kasa ta tsare ta hanata video call da takawa.

Abu ɗaya ne yake yi mata daɗi, kunun maman Khadija na sabaya da take sha safe da yamma, wannan kam tun da batu ake na ci, ruma tana jin daɗin haka.

Ban da wannan, duk wani wanke-wanke da gyaran fata rumaisa ba so take yi ba.

 

Rumaisa na zaune tana shan kununta, ita da sabir, dan idan suna sha, kamar ya shiga cikin kofin, ko zama ba ya yi, yana tsaye ayi ta bashi yana lashe baki.

 

Laila sai video call take da mijinta, ga mijin ya fara manyanta, amma ta shagwaggwaɓe, sai taɓara take, tana ce masa baby, suna wani abu mai kama da iskanci a wurin rumaisa.

 

Rumaisa har leƙawa take, ta sake kallon fuskar mijin, wai wannan gundumemen mutumin ne baby, ‘Taɓ sukumbiya, wai baby taɓ’ laila tana jin ta, taƙi kulata, su suke wayar amma ita take jin kunya.

 

Babu babban abun da yake bata mamaki, kullum da daddare sai sun yi video call, laila ta ɗau kwalliya kamar zata biki, ta sha ƙanan kaya, ta zauna a gaban waya ko system.

 

Yau kam da abun ya ishi kunnuwan rumaisa, ta saka hannu ta toshe kunnenta. Sai da laila ta gama wayar, sannan ta dubi rumaisa ta ce “Ba zaki iya ba ko, ni ƴar iska ce ni da mijina, shi ne ki ka toshe kunne?”

 

Ruma ta yi shiru. “Ban ce dole sai kin yi irin nawa ba, ni na yi shekaru a gidan aure, na saba da mijina sosai da sosai, ke nake fatan ki daina wannan shirmen, ki san me ki ke yi” ruma ba ta ji za ta iya abun da laila ke yi ba, a ganinta fitsara ce muraran, ga takura mata da take yi.

 

Da safe kan ta tafi makaranta, ta karɓi wayar iman, ta kira Adam voice call.

 

“Budurwata”

 

“Papa” ta kira sunansa a shagwaɓe.

 

“Ya aka yi?”

 

“Ni gaskiya wannan anty lailan ta takura mini, ta yi ta mini masifa, da na motsa ta yi mini faɗa, duk ta bi ta saka mini ido”.

 

Adam ya ce “Haba mimi, baki kira ni kin ji lafiayata ba, sai kawo mini ƙara, ke ma ta ce mini ba kya ji, taurin kai ki ke yi mata”.

 

“Yi haƙuri ya kake?”.

 

“Ban sani ba, tun da baki damu da ni ba”

 

“In ji wa? To yau saura kwana ɗari da saba’in da biyu ka dawo, calendar ce da ni, kullim sai na yi marking kwanakin da suka rage ka dawo”

 

Adam ya ce “Wow, lallai kin damu da ni sosai, take care, kar ki makara”

 

“Ni kar ka kashe”

 

“So ki ke ki makara a school ko?”

 

“Hmm ka san me?” “A’a sai kin faɗa”

 

Ji tayi kamar ta gaya masa zancen kunun da take sha sai kuma ta fasa.

 

Jin tayi shiru ya sanya ya ce “Akwai matsala ne?”.

 

“A’a”

 

“To ki shirya a kai ki school kin ji budurwata, sai mu yi waya anjima”

 

Ruma ta ce “Video call nake so mu yi in ganka, amma wannan anty lailan ta hana, duk abun da zai sani farinciki ba ta so”.

 

Ya ce “nima dokar nan ta isheni gaskiya, mutum da budurwasa a hanasu sakewa”

 

Ruma ta yi dariya ta ce “To saurayina, sai na dawo, kun gama taron yaushe zaka wuce karatun”

 

Ya bata amsa da “sai Allah ya kaimu jibi”.

 

Da ƙyar suka yi sallama, ta ajiye wayar ta tashi.

 

Wata irin kewar adam ce ke sake bijirowa rumaisa, ji take kamar sun shekara ba sa tare, tayi shiru tana tuna abubuwan da suka faru a tsakanin su, daga aurensu zuwa yanzu, a hankali ta yi ajiyar zuciya, ta tashi tana shirin makaranta.

 

Mai sunan baba kuwa tsayin lokacin nan, kullum sai ya ɗau wayarsa ya ji kamar ya turawa iman message, amma sai ya kasa, ya duba chats ɗin su, ko zai ganta online, amma ya ga sam ba ta fiye hawa online ɗin ba ma, gashi sai yana tsaka da jimami, da tunanin ya zai yi, Aliyu ya zo yana kashe murya yana waya da habiba, wanda ba ƙaramin ƙular da shi yake yi ba.

 

Mummy ba ta sake nunawa Mahmud fushi ko damuwa a kan abun da yayi ba, hasali ma taƙi yarda su sake ɗaukko zacen, kamar babu abun da ya faru, ta ƙarƙashin ƙasa kuwa, tana cigaba da shirin, sake rusa giwa, saboda ta yi alwashin sai baƙin ciki ya kashe giwa, in dai da ranta babu wani abun alkhairi da zai sameta, babban birinta yanzu bai wuce kassara rayuwar rumaisa ba, kasancewar ita ce babbar barazanar ta.

 

Ɓangaren Jamil ma, yana ta neman hanyar da zai yi magana da rumaisa, dan ya sha zuwa makarantar su, ya tarar da sidi yana tsaye yana jira, kuma alamu sun nuna babu wanda ya san adam yana zarginsa, dan haka so yake ya tutsiye rumaisa, ya ji me da me ta sani.

 

Baba uwani ma kullum zaman ɗar-ɗar take yi, a kan kar rumaisa ta tona mata asiri, dan tuni mummy tayi mata fata-fata ta sallameta.

 

Ammi na ta yi wa iman bayanin cewa Jabir ya ce mata, yana jira mai girma turaki ya dawo, wambai ne zai nema masa auren iman, kuma ya bata tabbacin cewa ya shawo kan hajiya Lubabatu ta amince masa ya nemi aure iman, kuma yayi mata zancen haɗa lefe ta ce masa wannan maganar su ce, su yakamata su tattauna.

 

Iman da ke shan kunun sabayar maman Khadija, dan ba a bar ta a baya ba, har ita ake sha, dan kuwa kogi bai ƙi daɗi ba, ta sunkuyar da kai tana sauraren ammi, ruma kuwa tana ta game a wayar ammi, kamar ba ta san me ake faɗa ba.

 

Ammi sai ta yi zaton kunya ce kawai irin ta iman, ya sanya taƙi magana, Nusaiba kuwa sai zaƙalƙalewa take yi, tana tsara yadda biki zai kasance.

 

Sallamar hajiya Lubabatu ce, ta katse musu hirar, Ammi ta amsa su kuma duk suka bita da kallo.

 

Ammi ta faɗaɗa murmushin ta, ta saka duk abubuwan da suka faru a baya, mussaman da Jabir ya ce mata ai ta amince da aurensa da iman, dan haka cikin murna ammi ta karɓeta.

 

Sai dai ta turɓune fuska ta ce “Giwa ba zama na zo yi ba, magana zamu yi dan Allah”

 

Ammi ta ce “To shikenan, ko zamu shiga daga ciki ne?”

 

“A’a ba wani daga ciki, magana zamu yi a buɗe a fai-fai. Wallahi giwa ki ji tsoron Allah, idan har kina son gamawa da duniya lafiya, mace sai tsabar son kanki a zuciyarki. Kawai kin juya mini tunanin ɗa, ki rasa da wanda zaki haɗa shi, sai auren ƴar tsintuwar ki, yarinyar da ki ka ce kin san iyayenta, ki ka gaza nuna su har rana mai kamar irin ta yau, kawai dan ki cuceni, wato sarauta ta bar gidanku, idan Allah ya yi jabir ya samu sarautar galadima, kin dai aura masa ita, dan ku mallake shi sai yadda ki ka yi da shi, wato kowa ya rasa, wanccan ba lafiya ce da shi ba, kin san ba sarautar zai yi ba, Mahmud kuma tun da Jamila ce ta riƙe shi, ba zaki bari abun arziki ya same shi ba, tun da ba ke yake yi wa kallon uwa ba, sai ki ka lallaɓa zaki aura mata ɗa na, to ba zai yiwu ba wallahi”

 

Ammi ta ce “Dan Allah ki yi haƙuri Lubabatu, ki fuskance ni, Jabir fa shi ya kawo kansa, ya ce yana son iman, ba ni na takura masa sai ya auri iman ba, kuma shi ne ya bani tabbacin lallai kin amince wa auren nan”

 

“Ni ina na san ana yi, ana ƙulla mini kitimurmura, ina ɗan sarauta ina auren shegiya da aka tsinto, wallahi ƴar tsintuwa ba zata samar mini da zuriya ba, idan ba haka ba a nemo iyayenta a nuna mini”

 

Tuni jikin iman ya fara rawa tana kuka, rumaisa kuwa ji tayi kamar ta mari iman, ba ta da kataɓus, da an yi mata abu sai kuka saboda tsabar shagwaɓa.

 

“Lubabatu shi ɗa na kowa ne, iman kuma ƴar ku ce, meyasa lallai sun kun nuna mini, iyakata ne?”.

 

“Ba wani ɗa na kowa ne, idan na kowa ne ki aurawa adam mana, ko dai sarautar ki ka ƙallafawa rai, sai kin mamaye komai, wallahi ɗa na yafi ƙarfin auren ƴar tsintuwa, baƙin halinki ne yake bibiyar ki da yaranki”.

 

Tuni rumaisa ta hasala ta ce “Wai jabir ɗin banza Jabir ɗin wofi, me aka yi aka yi wani Jabir munafiki da shi, ban da ƙaddara ta Allah, ki kalli iman ki kalli jabir ɗin mana, wani sololo kamar an mari ɗan akuya. Wai ku baku da wani buri sai ku zo kuna zagin ammi, me tayi muku?”.

 

“Ke rufe mini baki, ko na zo na talitseki, ƴar matsiyata ban saka da ke ba, sa’arki ce ni?”

 

Ruma ta ce “Wallahi talitseni, dai-dai yake da taka kan ɗan maciji, baku da magana sai ta sarauta, fir’auna ma ya mutu ya bar mulki, dan abun kunya, mijinki na can na jinya, ke da ɗan ki kuna nan kuna fafutuka a kan wata sarauta, wannan ne abun alfahari dan za a aure shi? Idan tsoho bai ji kunyar hawa jaki ba, wallahi jaki ba zai ji kunyar kayar da shi ba, ai ni idan mutum babban banza ne, bana ganin girmansa, tun ranar da muka je gidanki, ki ka ci mini mutunci nake ƙullace da ke”

 

Ammi jikinta har rawa yake, ta ce “Rumaisa ya isa haka, ku tashi ku shiga ciki” dan ammi ba ta taɓa ganin ruma tana asalin tijara ba sai yau.

 

Laila ta ƙaraso falo ta ce “Ammi su shiga ciki su je ina? Rumaisa kin yi mini dai-dai, ai asara na ga matar da ta wofantar da mijin da ya gatantata lokacin yana da lafiya, yana ƙasar waje yana jinya, tana nan tana shirme a gari, ita da ɗan ta mara tarbiyya.

Ƴar wahala, tun da na sanki Lubabatu baki da alƙibla daga ke har Mummy, shiyasa rayuwa ta ƙi yi muku yadda ku ke so, kuma albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da alƙur’ani, cigaba yanzu muka fara”

 

Ruma ta ce “Kuma in sha Allah, sai na dawowa da ammi Mahmud”

 

Laila ta ce “Dan Allah malama kwashi banzayen ƙafafuwan ki, da aka saba bin bokaye, a bar mana part, kar a zuba mana masifa”.

 

Hajiya Lubabatu ta nuna kanta ta ce “Laila har da su kaza a cin danƙo, ni ƴar riƙo za ta gayawa magana haka”.

 

“Ƙwarai ƴar riƙo ba, ko nima zaki ce mini shegiyar ne? Ke sa’a fa ki ka ci, Jabir yana girmamani, da wallahi ashar zan ɗuɗɗura miki, zaki iya fita”

 

Su biyun duk suka ƙureta da ido, ba wanda ya fi ɓata mata rai, irin cin mutuncin da rumaisa ta yi mata.

 

“Giwa a gabanki sirikarki suka ci mini tuwo ko, duk saboda wannan yarinyar, na faɗa ba zan bari ɗa na ya auri wannan yarinyar ba, da ban san asalinta ba, wanda ba na raba ɗaya biyu, ƴar gaba da fatiha ce, kuma zaku ga abun da zai biyo baya” ta fice tana huci.

 

Bayan fitarta, Ammi ta kalli laila ta ce “Laila mey…..”

 

“A’a Ammi, daga ni har rumaisa ba wanda yayi laifi, nima fa ba son aurenta da jabir ɗin nan nake yi ba, saboda duk wani abu da ya shafi mummy, bana ƙaunarsa na tsani matar nan kamar yadda na tsani mutuwata, ke kuma iman, idan aka kuma zuwa ana gaya miki magana, ki ka ɓare baki kina kuka, ubanki zan ci, sokuwa kawai komai kuka, bayan kin san larurar da ki ke ɗauke da ita”.

 

Jikin Nusaiba duk yayi sanyi, ita dai tana yi wa iman sha’awar auren jabir, amma halin mahaifiyarsa ne sai a hankali, kuma wani point da ruma ta kawo abun dubawa ne, mutumin da mahaifinsa yake ƙasar waje yana jinya, an bar shi shikaɗai sai mai kula da shi, tilon ɗan sa namiji kuma yana nan yana gararambarsa.

 

Sai dai ba a fi mintuna arba’in, da tafiyarta ba, wambai ya kira ammi a waya.

 

Suka gaisa, gabanta na faɗuwa, ko wani abun hajiya Lubabatu ta je ta kitsa masa, sai dai ta ji ya ce mata “Mun yi magana da jabir galadima, idan turaki ya dawo, zuwa ranar lahadi idan Allah ya kai rai, zamu kai kuɗin auren yarinyar wurinki iman wurinsa, ya ce mini kun gama magana, zamu sanya watanni biyu ne kawai auren”

 

Gaba ɗaya sai ta ji ya ɗaureta ta da jijiyoyin jikinta, ammi ta ce “To ranka ya daɗe, Allah ya tabbatar mana da alkhairi”

 

Laila ta ce “Lallai ma jabir munafuki ne, yana sane da uwarsa ba ta so, amma yake maganar kai kuɗi? Kodayake hakan shine dai-dai, ta auri jabir ɗin, mu ga ta tsiya, Allah ya tabbatar da alkhairi, ai Allah ya fi su”

 

Ammi ta ce “Subhanallah, Allah ya kawo mini ƙarshen wannan fitintinu, ni abubuwan ma sun isheni, Addu’a dai nake tayi, Allah ya shiga lamarin nan, bai kamata a hukunta jabir, da laifin mahaifiyarsa ba, tun da shi mutumin kirki ne”.

 

Ruma ko sunan jabir ba ta son ji, dan haka ta bar falon gaba ɗaya, ita zaman gidan duk ya isheta, gida kullum cikin tashin hankali da bala’i, an saka mutum ɗaya a gaba da masifa.

 

Harabar gidan ta fita shan iska, tana ta zazzagawa, tana kallon fulawoyi, ga sanyin la’asar, yanayin yayi mata daɗi sosai.

 

Daga sashin Mummy ta hango jamil, ta tsaya tana kallon sa, su kullum suna gidan nan, kodayake ba abun mamaki bane ba, tun da ƴan uwa ne, amma ita a wurinta duk wanda ya fiye zuwa wurin Mummy ba shi da gaskiya.

 

Ga mamakinta taga yana tunkarota, dan haka ta haɗe rai zata juya ta tafi, ya cimmata da sauri ya ce “Ɗan tsaya mana, yau Allah ya sa mun haɗu, magana zamu yi”

 

Ta ƙare masa kallo ta ce “Maganar me?”

 

“Magana a kan abun da ki ka cewa mjinki na kina zargina da kisan Aisha”

 

Ruma ta ce “Ba rami meya kawo rami,? Ni ban ce ka kashe anty aisha ba, kuma da mijina ku ke magana ba ni ba, dan haka babu ruwanka da ni”

 

“Amma ko menene ke ki ka kitsa misa, daga auroki ƴar mitsitsiya da ke, kin rikita mana zaman lafiya family”

 

“Dama can ba zaman Allah da annabi ku ke yi ba, kuma na faɗa ɗin, idan kana da gaskiya, maiyasa a da baku damu da anty aisha ba, sai yanzu kake damun baban sabir, wataƙila ma da kai ake haɗa baki ake ɓata masa suna”

 

Jamil ya ce “Kin san me ki ke faɗa kuwa?”

 

“Malam danginmu babu mahaukaci, ban yi gadonsa ba, kuma babu ƴan shaye-shaye”

 

Jamil ya ce “Ni fa jami’in tsaro ne, zan iya amfani da kakina wurin ladabtar da ke, da tursasaki a kan kiyi bayanin abun da ki ke ɓoyewa”.

 

“To meya hanaka yin hakan tuntuni? Ka yi mana, amma ka sani na san da batun saka sunan anty aisha, a matsayin magajiya da mai girma turaki ya yi, a kan filin sa, da wani kamfani da haɗin gwamnatin tarayya suka karɓa jingina, ake amfani da shi, ana bashi wani kaso, na kuɗi, wanda kai tsaye yake shiga asusun anty aisha. Ka ga idan baka kiyayeni ba, zaka tsinci talatarka a laraba”

 

“Wa..ww..waye ya gaya miki wannan maganar? Kenan adam saboda wannan maganar, ya fara tunanin ɗora zargin sace matarsa a kaina?”

 

Rumaisa ta ce “Kai ma kenan saboda ka wanke kanka daga zargi, ya sanya ka ƙirƙiri cewa ya kashe matarsa yayi tsafi da gangar jikinta?”

 

Mamakin rumaisa ne ya mamaye shi, ya ce “Kuma aka ce miki ni ne na yaɗa wannan maganar? Me ki ke nufi ne?”

 

Ruma ta yi murmushi ta ce “Ba ina nufin kai ne ba, kawai na yi tunanin, kowaye ya saka aka sace anty aisha, shi ne ya yi wa mijina sharri, ni ba ƴar sanda ba ce ba, amma ƴar baiwa ce, garkuwa da aka yi da anty aisha shiri ne, kuma idan ba ka da hannu, kar ka damu kanka, sai dai ita rayuwa, iyawa ce, abu ƙailalan zaka yi, ya jefeka cikin masifa a gaba, har ƙarshen rayuwarka, ka sani iya wuya ina bayan mijina, kuma kar ka sake tunkarata da wannan maganar”

 

Dafe kai Jamil yayi, ya ja da baya,gaba ɗaya ya ma rasa ta ina zai fassara maganganun rumaisa ne? Ta hargitsa masa zance cikin zance wace irin yarinya ce ne haka? Kamar ana controlling ɗin ƙwaƙwalwarta da remote?.

 

Lokacin da rumaisa ke daf da shiga sashin ammi, taga laila ta fito da sauri, ta yi wa sidi magana, akan ya kawo mota, zasu tafi asibiti iman ta suma.

 

Da gudu ruma ta shiga sashin ammin, iman na kwance a in da ta barta ɗazu tana bacci, ashe daga haka ta suma, ammi na ta magana amma shiru.

 

A gaggauce suka ɗauketa, tuni ammi zuciyarta ta karaya, saboda yadda jikin iman ya saki, kuma Ammi ta ɗora alhakin hakan a kan hajiya Lubabatu, da ta zo ta yi mata wannan cin mutuncin.

 

Ammi ta ce Rumaisa da Nusaiba su zauna a gida, ita da laila suka tafi kai iman asibiti.

 

Rumaisa ta kasa zaune ta kasa tsaye, lokaci lokaci ta din ga jan uban tsaki ta ce “Allah ya tsinewa babar jabir ɗin nan, da bata san darajar ɗan Adam ba, daga ita har shi wawan jabir ɗin, mara zuciya”

 

Nusaiba ta ce “Ya zaki din ga zaginsa, shikuma me yayi miki?”

 

“Ba ruwanki da ni, ai naga take-takenki, ke kike goya masa baya, ke ki aure shi mana” duk da Nusaiba ta girmi rumaisa sosai, dan ta girmi iman ma, amma haka tayi shiru ta kasa magana.

 

Sai dare laila ta dawo, suka tashi gaba ɗaya suna tambayar laila ya jikin iman ɗin.

 

Laila jiki a sanyaye ta ce “Da sauƙi, sai dai jini ya hau, zuciyar ta kumbura, amma ta farfaɗo ta samu bacci.”

 

Ruma ta ce “Anty laila dan Allah a fasa auren nan mana, ko dan ceto rayuwarta”

 

“Ai ni zan fi so yi auren nan, dan nuna mata iyakarta, kuma magana tun da ta riga ta je gaban wambai, rusata ba abu ne mai sauƙi ba, mutumin nan ba ayi masa wasa”.

 

Rumaisa ta rasa abun sa yake yi mata daɗi, ji take kamar ita ce a halin da iman take ciki.

Nusaiba ce ta shirya, ta tafi asibitin, dan taya Ammi kwana da iman.

 

Yau sai ga rumaisa da tashi cikin dare tana sallar dare, tana yi wa iman da yayanta addu’a, idan da alkhairi Allah ya sa mai sunan baba ya auri Iman. Dan ta san mai sunan baba, akwai zafi, amma mutum ne mai kyautatawa da tausayi, kuma ba ta taɓa ganin abun da ya damu da shi sosai bayan ita da mama ba sai iman.

 

Da gari ya waye, laila da rumaisa suka je duba iman, suka kai musu abinci.

 

Iman ta farfaɗo, amma ta yi pretending, bacci take yi, saboda ba ta son magana, dan numfashinta sama-sama take yin sa.

 

Ammi da Nusaiba suka koma gida, an yi sa’a ruma da anty laila an ɗan fara shiri, sannan laila ta sarawa tsagerancin rumaisa, mussaman jiya, da ga tsigalewa hajiya Lubabatu.

 

Wayar iman na hannun rumaisa, dan yanzu wayar kamar ta su ce su biyu.

 

Rumaisa ta kira mama ta ce “Mama dan Allah ki zo ki duba iman, ba ta da lafiya muna asibiti”

 

Mama a duk lokacin da ta ji an ce iman ba ta da lafiya, hankalinta yana tashi, mussaman da ciwonta yake mai hatsari.

 

Bayan ta gama wayar ta dubi laila ta ce “Anty laila”.

 

“Na’am”.

 

“Wai yaushe zan yi video call da papa ne?”.

 

Laila ta ce “Sai lokacin da ki ka fara bin umarnina”

 

“Anty laila dan Allah, so nake na ganshi”

 

“Kin fiye taurin kai ne, sai lokacin da ki ka fara yarda zaki yi abun da nace miki ba gardama”

 

“To me ki ke so na yi?”

 

Ta ce “Ba wannan ba ma, so nake mu bashi mamaki, sai kin fi haka kyau da cika, ke baki ga yadda jikinki ya fara yi ba ne”

 

Ruma ta ce “Na gani, kullum idan na je wanka ina dubawa, idan sun fara girma”.

 

Laila ta yi dariya ta ce “Ashe dai kina son su fito”.

 

“Wallahi ina so”

 

“To ki mayar da hankali da cigaba da shan kununki, bayan sabayar maman Khadija ma, akwai maganin maman ilham, shi kuma a iya fito da nono yake aiki, baya sanya ƙiba, haɗinta haɗi ne mai kyau ɗan mambila ita ma.

Rumaisa daga lokacin da mace tayi aure, zama bai ganta ba, shekaruna a ƙalla talatin da huɗu, amma kalleni kamar ƴar ashirin da biyar.

Bana zama, abu ba sai ya lalace ake gyara shi ba, garkuwa ake yi kafin ya faru, nan gaba kina haihuwa kina shayarwa, dole zasu ranƙwafa ko su zube, amma idan ki ka tattala su, ki ka kula da su, tsaf zaki yi ta haife-haifenki, ba tare da kin sirewa miji ba.

Kuma ba ina nufin ki je ki sai abun da baki san menene ba ki sha, ba haka nake nufi ba, duk abun da na baki kiyi amfani da shi, na san kyansa da ingancinsa, kuma na san da me aka yi shi.

Kin ga maman Khadija na ta haɗin kunu ne na sabaya, da yake gyara jiki, ya sanya ƙiba da gyara fata, kuma kowa na iya sha.

Ita kuma maganin maman ilham, akwai matan da suna da ƙiba, basa buƙatar yin ƙibar, gyaran nonon kawai suke so, ita maganinta haɗe-haɗe ne, na natural abubuwa, ba shi da side effect kayanmu ne na islamic da saiwoyi masu kyau, ake kawo mata daga mambila ta haɗa.

Ya ki ke gani, idan mutum ya haɗa garin kunun sabayar maman Khadija, da kuma maganin gyaran nono na maman ilham?

Rumaisa ita mace ba ta zama ba gyara, dan haka so nake ki cika kiyi kyau, kan dawowar takawa”.

 

Ruma ta yi shiru sannan ta ce “Ni fa na zata kawai amfaninsu a shayar da ɗa, ashe mutum gori ake yi masa idan bashi da su”

 

Laila ta ce “Sosai makuwa, shiyasa ake son gyarawar ai, kuma gori ba iya na mata ba, har na miji, wanda ya fi kowanne takaici ba, miji yayi miki gori dan baki da su, ko kin bari sun lalace”

 

Ruma ta sake gyara zama ta ce “To ita ma na maman ilham ɗin zaki sai mini?”

 

“Eh mana, mai ze hana? Ki din ga biyayya kawai, mun gama magana da ita ma”.

 

Cikin farinciki ta ce “Allah ya sa su fito kan papa ya dawo, kin san me? ce mini fa yake, wai nasa yafi nawa girma, wai nawa kamar girman wake, daga baya kuma wai kamar murfin jarkar faro”.

 

Ƙyalƙyalewa da dariya laila ta yi ta ce “Rabu da shi, kan ya dawo zai sha mamaki, sai ki rama. Ai tun da akwai kunun maman Khadija, da kuma haɗin maman ilham, an wuce wurin, kin wuce gori mutuniyar”.

 

“Allah ya sa anty laila, to zasu kai kamar na samha? Su Fauziyar nan, wai a dubi samha ta fini komai amma ya aureni, idan nawa suka fi nata, ai ba zai aureta ba ko?”

 

Laila ta ce “Wannan kuma effort ɗinki ne zai sanya, ya aureta ko ya fasa”

 

READ ƘANWAR MAZA PAGE 75 HERE


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button