Garin kano unguwar lamido cresent GRA.
Gidane babba daga gate din gidan kana shugowa zaka san gida ne na masu arziki, atsakiyar gidan akwai babbar bishiyar guava wadda tayi girma sosai tayi ma compound din rumfa, kyawawan yara ne su hudu suke buga kwallon wasa, dukkan su maza ne da alamu yan uwane saboda kusan kammanin su daya saidai biyu daga cikin yaran farare ne sauran biyun kuma baqaqe ne, kyawawa ne yaran bulbul don akalla bazasu wuce shekara bakwai zuwa tara ba kana ganinsu zakasan hutu ya zauna ajikinsu suna sanye da riga da wando na jeans,agefen su wani yaro ne zaune gefen wajen famfon da ake wanke motoci yana kallon su da alamu yana son ya shiga cikinsu amma sun hanashi yarone kyakyawa black beauty shima bazai wuce 10yrs ba yana da manyan idanuwa very innocent sannan yana da hanci wanda ya karama fuskarshi kyau irin na Fulanin asali saidai akasin fatar jikinshi chocolate color, daya daga cikin yaranne ya kalli inda yaron yake sannan yace ‘’kai salim zoka buga ball din”, aikuwa kamar jira yake ya taso da gudunshi yana zuwa dab da wanda ya kirashi ji kake bamm anbugo ball din saitin goshin sa nan take ya kwala karar jin zafi agigice ya durkushe kasa, sukuwa yaran me zasu banda dariya, jin kukanshi ya karade duka gidan yasa wata farar mata ta fito daga main entrance din parlour, ganin yaran atsaitsaye suna dariya yasa ta karaso wajensu, kallonsu tayi daya bayan daya, fararen yaran ne su biyu suka matso wajenta suna mummy mummy, kallonsu tayi sannan tace Khalil,khamis menene haka banace kuyi wasanku ku kadaiba, wanda aka kira da khamis ne ya kalleta yace ‘’mummy muna wasane saisu jabir sukazo sukace zasuyi munce masu bazamuyi dasu ba shine jalal yace wai ayi competition muna cikin yi sai jabir ya kira salim wai yaxo ya buga bayan ya taho shine ya buga mashi ball akanshi’’, kallon jabir tayi sannan tace ‘’kai daman baqin hali yayi maka yawa ka godewa Allah ba yarana ka bugama kwallon nan ba da wallahi sainaci uwarka”…
Download>>> Doctor Eesah Complete Novel
Jan hannun yayanta tayi fuu suka wuce parlor salim kuwa bawan Allah ko kallonshi batayi ba ta wuce cikin gida, jabir da jalal kuwa daukan ball din sukayi suma suka wuce cikin gidan, anan suka bar salim sai matse kwalla yake idanun shi duk sunyi ja goshinsa ya dan kumburo sosai don ba karamin bugu jabir yayi mashi ba. Yana nan tsaye wata yarinya wadda akalla bazata wuce shekara goma sha biyar ba kyakyawa ce fuskarta sak irin ta salim amma ita ta fishi dogon hanci, zubinta irin na sirarara ne, hannun ta rike da bucket din kaya da alamu shanya zatayi, juyawa tayi zata wuce hanyar backyard din gida domin anan suke yin shanyar kayansu jin sautin kuka yasa tadan juyo saitin compound din gidan, karaf idanunta suka sauka kan salim da ya tsugunna yana kwalla, kallonshi tayi da kyau sannan tace ‘’ Salim zonan,juyowa yayi jin muryar yayarshi salima, aguje ya taho wajenta, kallonshi tayi da kyau ganin goshinsa yayi qulu tace ‘’subhanallah salim meya sameka haka? Waye ya dakeka?
Download>>> The Governor Wife Book 1 Complete Novel
Kallonta shima yayi yace’’ ya salima ina zaune wajen famfo ina kallon su jabir suna buga ball shine yace nazo muyi ina zuwa ya buga min ball akaina, kallonshi tayi cikin tausayin kanin nata sannan tace ‘’Salim na fada maka kadaina wasa dasu bakaji kamanta abinda adda tace mana ko?, kasan ba son zamanmu suke ba acikin gidan nan nasu, kadaina kulasu kaji?’’ girgiza mata kai yayi sannan yace’’ toh ya salima bazan karaba. Hannunshi taja suka wuce backyard anan ya taimaka mata suna shanya kayansu data wanke, bayan sun gama ta kofar baya wadda take hade da kitchen din gidan suka shiga.
Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel
Wata yar budurwa ce ta juyama kofar kitchen din baya da alamu wanke wanke takeyi a sink din kitchen din tana tsaye, sanya take cikin doguwar rigar atampa kalar ja da ratsin yellow ajikin rigar wadda ta zauna dass ajikinta, kanta hulace kalar kayan jikin nata red, tanada diri sosai saboda kana ganinta ta baya zaka hango yanda mazaunan ta wanda suke dan girgizawa sakamakon juyin da takeyi wajen dauraye kayan wanke wanken, tanada irin shape din da ake kira da hour glass ko ace figure 8, tanada hips masha allah har ya rinjaye jikin nata don batada wani kiba sosai don doguwa ce, salim ne ya taho aguje gefenta ya tsaya a gefenta yace ‘’ adda na sannu da aiki’’ juyowa tayi tana kallonshi sannan ta kalli salima data tsaya gefen shi suna mata murmushi itama murmushin tayi masu…ina ganin fuskarta nace masha Allah, yarinya ce kyakyawa itama black beauty, chocolate color irin wankan tarwada dinnan ita baza ace mata choco ba ita baza ace mata fara ba sbd tafi salim da salima dan haske amma itama din tana cikin category din chocolate colors, hancin ta kuwa kamar har yafi na salim da salima mikewa wanda ya karama fuskarta kyau da annuri, tana da idanu manya manya round afuskarta wul wul dasu suna dauke da eyelashes zara zara,ga cikar gashin gira har yana nema ya hade, bakinta kuwa yana nan oval shape gwanin birgewa, batashafa komai ba a lebanta amma kamar an goga jambaki a lower lips dinta, ta wajen lip line dinta kuwa yadanyi baki ba sosai ba wanda ya karama bakin nata kyau sosai, itama akalla bazata wuce 19yrs ba, kirjinta daidai jikinta manya sannan batada wani tumbi sosai don doguwa ce sharr da ita amma akwai diri…….,
Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document
Murmushi kawai take masu saidata kara kallon salim sosai tukunna ta bude baki ta tace ‘’ ya Allah salim what’s wrong with your forehead?, shuru yayi sbd yana tsoron kar tayi mashi fada, salima ce tayi charaf tace ‘’ adda Amra wasa yaje zaiyi da wa’enchan mugayen yaran shine suka buga mashi ball ah goshi, na fada mashi ya daina zuwa wajensu yaqi ay gashi nan yajama kanshi”,….
Kallonshi wadda aka kira da amra tayi sannan ta tsame hannunta daga wanke wanken tace salim “I thought we’ve talked about this na fada maka kadaina zuwa wajensu sbd duk sanda ka rabe su sai sunyi maka mugunta kuma idan kayi kokarin ramawa kuma iyayensu su huce akanka dan Allah Salim ka rufa mana asiri kadaina zuwa wajensu, ka zauna kayi wasan ka kai kadai kaji ko”?
Download>>> Dr Bobby Hausa Novel Document
Girgiza mata kai yayi sannan yace “insha Allah adda bazan kara ba”,murmushi tayi mashi sannan ta jawoshi jikinta tace ‘’matso nan na gani dakyau’’ matsowa yayi sannan ta jawo shi sosai tadan duqa ta fara lailaya mashi goshin nashi, bakinshi ya bude zai fara ihu ganin salima na neman buge mashi bakin nashi yasa yadan runtse idanun shi, ahankali amra ta fara mulmula mashi har saida goshin ya koma, matse kwalla yayi sannan yace adda akwai zafi sosai kaina ya fara ciwo”, kallon salima tayi sannan tace ‘’ salima kije daki akwai Panadol acikin drawer na dressing mirror ki bashi yasha ya kwanta kafin akira sallah dhuhr”,..hannunshi salima ta ja suka wuce cikin gidan, ita kuma amra ta cigaba da wanke wanken.
Karanta>>> Abban Sojoji Book 2 Complete Novel
Saida ta tabbatar ta gama wanke duk wani plates da tukwane da akayi using na breakfast din safe tukunna ta share kitchen din, ko’ina saida taga yayi tsaftsaf sannan ta fito da vegetables daga fridge domin daura lunch, wanke vegetables din tayi a sink sannan ta aje su ah kitchen island domin fara yayyankawa, anatse ta fara yanka su red bell pepper dasu carrot anatse cikin qwarewa take yin komai saida ta gama tukunna ta daura tukunya akan gas, fito da tafashen nama dasu blended kayan miya tayi daga fridge tukunna ta fara soyawa, cikin mintuna kadan ta kammala beaf sauce dinta sannan ta juye acikin warmars, bayan ta gama ta daura couscous dayake yanada sauqin dahuwa bata wani jima ba ta gama sannan ta fara yankan su salad da cabbage dasu carrot saidata gama tukunna ta faara preparing salad…cikin nutsuwa ta gama komai ta gyara ko’ina sannan ta fita da warmers din,..ahankali take tafiya har ta iso dining area wanda baida tazara sosai da kitchen din, dining ne babba mai dauke da chair goma sha biyu, kujerun ajare suke colorn black and gold, gefenshi wani babban console ne shima black and gold Sai wata katuwar artificial flowers by the corner wadda ta karama wajen kyau saidan dispenser babba daga gefe,anatse ta fara jera komai tsaftsaf gwanin birgewa, saidata tabbatar ta gama komai tukunna hankalinta ya dawo jikinta sauka tayi daga stairs din dining din ta wuce sitting room, babban parlor ne sosai irin na gidan manyan mutane yasha ado sosai shima yana dauke da kujeru black da ratsin gold tsakiyar parlor kuwa wani qaton carpet ne gold babba sosai sai wani katon center table shima yasha adon kayan alatu na zamani gefen kujerun kuwa wasu shegun side stools ne masu kyan gaske na wood, agaban parlorn kuwa wata tapkekiyar tv ce wadda take akunne an saka tashar nickelodeon da alamu yaran gidan ne suke kallo daga bisani suka tashi suka bar parlorn da tv din akunne , ahankali ta wuce wajen tv station din sannan ta kasha switch din, bayan ta rage hasken chandelier parlor din, komawa tayi hanyar dazai sadaka da kitchen daga gefe akwai wani corridor wucewa tayi harta karasa dakuna biyu ne a wajen suna facing juna, daki daya ta tunkara sannan ta wuce bakinta dauke da sallama, dakine mai dan girma aciki kuwa dan matsa’kaicin gado ne mai dan girma sai karamin carpet atsakiyan daki daga ciki kuwa toilet ne aciki sai yar wardrop a gefen wajen shiga toilet din, anatse ta shiga ciki, juyowa salima tayi wadda take zauna akan kujerar dressing mirror din su mai dauke da dan turare da mai na shafawa da roll on kallonta amra tayi sannan tace ‘’an fara abinda aka saba ne’’
Karanta>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel – Aihausanovels
kallonta salima tayi sannan tace ‘’ adda wallahi har allah allah nake Monday tayi mu koma school zaman dakin nan ya ishe ni wallahi donma allah ya taimaka wannan zane zanen da nakeyi yana dauke min hankali,”..kallon book din hannunta amra tayi sannan tace ‘’our future architect muga yau me kika zana’’ …karban book din hannunta amra tayi sannan ta fara kallon book din….
Title | Auren Katin Kasa |
Book Type | Txt |
Live On | Aihausanovels |
Released Date | 2 July 2023 |
Author | QueenMarh |
Uploader | Mr. Aihausa |
Phone No: | 08032542629 |
Group |
Domin Sauke Littafin Sai Ku Danna Inda Aka Saka Download Here