Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 105 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

💋💋💋

 

Kwance yake asaman doguwar sofa mai mazaunin mutun ukku,da alama bacci ne ya É—auke shi,daga shi sai gajeran wando ajikinshi,

Sautin bugun Æ™opar falon ne ya farkar dashi daga baccin da yake yi,tun kafin ya buÉ—e idanuwanshi yace”Who is Knocking!”
From ouside the door yaji an ce”Afternoon sir!Kunyi bakuwa ne tana a waje tana jira,”
“Ka sanar da ita cewa Matar gidan bata nan,”har lokacin bai buÉ—e idanuwanshi ba,

Jim kaÉ—an har ya koma baccin nashi,Yaji an sake kwankwasa Æ™opar,rai a6ace yace”Sergeant!”
“Am Sorry sir,matar ta nace akan tana son yin magana da matarka Laila,”
Guntun tsoki General Ishaq yaja kafin yace”Let her Come in,”

“Okey,Sir,”

A Æ™ule yake dama sam Æ™awayen Laila ba burgeshi suke yi ba,duk yawancinsu irinta ne,masu mugun hali,’

Kwankwasa kopar yaji anyi,muryarshi a kasalance yace”Who is knocking”
“Hajiya Rabi’atu ce,Æ™awar Laila,”har cikin dodon kunnanshi ya jiyo daddaÉ—ar muryarta,sai gashi ya buÉ—e idanuwanshi,Saukowa yayi daga saman Sofa É—in da sauri ya nufi bedroom É—inshi dake a upstairs,Jim kaÉ—an yadawo jikinshi sanye da Jallabiya,

Hannu yasa tare da buɗe mata ƙopar,tun kafin ma ya kalleta,Wani irin daddaɗan ƙamshin turare mai ratsa sassan jiki da sanyaya zuciya ya daki hancinshi,from down ya soma kallonta,Highhills ne a ƙafarta,Jikinta kuma na sanye da Code lace milk colour riga bubuce ajikinta,ta aza mayafin asaman kafaɗarta,duka hannayenta da wuyanta na sanye da sarƙar gold,light make up ne akan fuskarta

Also Download Banana Island Book 1 Hot Romantic Hausa Novel Complete Document

Koda General Ishaq,ya yi arba da kyakkyawar fuskarta,farat É—aya ya waye ta,
da niyyar rashin mutunci ya buÉ—e Æ™opar,Amma sai gashi yana sakar mata murmushi,A wayance yace”Hajjaju ko”?
Mayar mashi da martanin murmusin tayi tare da É—aga mashi kai alamar eh,
“Ina fata ban takura maka ba,dama na shigo garin naku ne,Shi ne nace bari na leÆ™o mu gaisa da Æ™awar tawa,nata trying layinta amma akashe I don’t why,nashiga damuwa,”
Matsa mata hanya Ishaq yayi”mu shiga daga ciki mana,sai muyi magana”
“Toh”ta amsa mashi tare da bi ta gefenshi ta nufi cikin palourn,Shima yabi bayanta,Sai Æ™ara bin ta da kallo yake yi,from head to toe,wankan lace É—in da ta É—auka ba Æ™aramin tafiya yayi dashi ba,musamman da ta kasance dirarrar mace,

Wuri ta samu saman 2 seater ta zauna,Ishaq ya zauna saman 3 seater,
A tsanake ta soma magana bayan sun gaisa”Am Lailan tana ciki ne”?
“A’a,bata nan fa,bata sanar dake bane”?
“No Bata sanar dani komai ba,ai na faÉ—a maka ina ta trying layinta a kashe,”magana takeyi tamkar bata son motsa la66anta,dama hajjaju anji wayewa,ishaq kuwa sai Æ™ara kalleta yake yi,
“bazan 6oye maki ba,Zancen gaskiya mun rabu da laila,Ni banma son inda take ba ayanzu ha….”bai Æ™arasa maganar ba ganin yadda ta zabura ta miÆ™e tsaye tana faÉ—in”ka rabu da laila”?
Murmushi Ishaq ya É—an yi kafin yace”Calm down ur mind,koma ki zauna,”
Muryarta tamkar zatayi kuka tace’haba Ishaq,taya zaka ce mun in zauna?zaman me zan yi kuma,bayan ka rabu da laila!amma gaskiya banji daÉ—in wannan maganar ba,”
Zuba mata ido yayi yana kallonta,sai da ta kai Æ™arshen maganarta,sannan yace”pls ki koma ki zauna,I will explain to you,”
Fuskarta aÉ—aure ta koma ta zauna tare da cewa’wlh Ishaq ka bani mamaki,sam ni baka yi mun kama da irin mazan dake sakin matansu ba,meyasa zaka yiwa laila haka?idan ma laifi tayi maka,at least kodan saboda Hafsat ai bai kamata ka rabu da ita ba”
..shiru ya É—an yi batare da yace komai ba,har sai da ta hasala,ta soma Æ™oÆ™arin miÆ™ewa”Ni zan wuce,dama saboda Laila nazo,tun da kayi mana tsiyar taku ta maza,banga amfanin zama na ba,”
“Pls kada ki tafi,i will explain to u as i said,”Yanayin yadda ya furta maganar kamar akwai damuwa atattare dashi,hakan yasa ta gyara zamanta,tare da cewa”ina sauraronka,”
..”Ban cika son ina faÉ—in sirrikan matata ba,kuma bana É—aya daga cikin mazajen da suke fallasa sirrin dake tsakaninsu da matayensu,so kamar yadda kika ce,banyi maki kama da mazajen da suke sakin matayensu ba,inaso ki ci gaba da yi mun wannan kyakkyawon zaton,Sam ni a tsari na babu sakin mace,kuma ke shaidace!kinsan wacece laila,kinsan halinta,bakowani namiji bane zai iya jure zama da mace irinta ba,amma haka ni na daure na rufe idona na zauna da ita,bayan duk irin Girman laifukan da take yi mun,Laila ta kaini maÆ™ura ne,shiyasa har na zartar mata hukuncin saki……..”Anan Ishaq ya kwashe dukkan Abunda ya faru tsakaninshi da laila game da irin Zaluncin da ta yiwa Æ´a’Æ´an Uncle É—inshi ya sanar mata,
Saboda tsabar tashin hankali,Hajjaju ta shiga zabga salati tana faÉ—i “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!Dama su Sehrish Æ´a’Æ´an Abusufyan ne?”
Cike da mamaki Ishaq yace”Dama kin sansu ne”?

Karanta>>> Zurfin Ciki Book 1-4 Complete Novel Document

“Nasan su mana,Ae ni ce silar tura ita Sehrish din aikatau a anan gidanku,Ashe dama jininku ne su?Ya salaaam,”ta Æ™arasa maganar tana dafe kanta da hannunta É—aya,
“Wlh Nayi danasanin rashin sanar dakai da ban yi ba,Nazo naga Hosana da Jahad,acikin gidan nan,tunda na kallesu dama nasan cewa suna cikin mawuyacin hali,bayin Allah,”
“Dama kinsan da zamansu acikin gidan nan?kuma baki sanar damu ba?bayan kinsan halin Æ™awartaki”?
Idanuwanta cike tab da kwalla tace”Wlh banyi dabarar yin hakan ba,Amma ae komai ya wuce,kuma wlh nayi murna nayi farin ciki sosai da kasancewarsu Æ´a’Æ´an Abusufyan,in sha Allah idan na samu zuwa can abujan zanje na kai masu ziyara,”
Sun jima suna tattaunawa akan su Sehrish,bayan sun kammala firar tasu ne,Hajajju tace”Yanzu,mu dawo kan laila,”da sauri Ishaq ya katse ta da cewa”karfa kice zaki bani shawarar in mayar da ita,”
Girgiza kai tayi”a’a ni na isa,kawai dai yakamata kayi zurfin tunani,banso ka yanke mata hukuncin saki ba,ka jima tare da laila,kodan albarkacin hafsat bai kamata ka rabu da ita,Ya kakeso rayuwar hafsat ta kasance babu uwa atare da ita”?tayi maganar tana kallonshi,
“Hajjaju kenan!hafsat ba Æ™aramar yarinya bace,ta mallaki hankalinta,ba zata yi maraicin uwa ba,zan iya sawa ayi mata transfer ta koma Abuja da aiki,in yaso sai ta zauna a wurinsu Abba,”

“Kai kuma fa?ba zakayi maraicin rashin mace atare dakai ba?nasan dole ka buÆ™aci kulawa,gashi gidan ma ko mai aiki babu,”tayi maganar tana Æ™arewa gidan kallo,
Wani ƙayataccen murmushi Ishaq ya saki,anzo wurin da ya fi so,
Jingina bayanshi yayi ajikin sofa É—in tare da cewa”kin faÉ—i gaskiya,ina buÆ™atar mace atare dani,musamman wadda ta iya É—aukar wankan lace,ta iya kashe É—aurin kallabi,Sai dai ina jin tsoran na sake yin aure,saboda matan ne basu da tabbas,”
“Ba duka aka taru aka zama É—aya ba,kada ka yanke hukunci akan abunda baka da masaniya akanshi,Dole akwai na gari kuma akwai na banza,shiyasa kafin mutun yayi aure yake da kyau ya tsananta bincike,Don ya sama ma Æ´a’Æ´anshi uwa ta gari,haka mu ma matan,”
Sam bata kawo komai aranta ba,tana kai Æ™arshen maganar ta É—auki hand bag É—inta tare da mikewa”Ni zan wuce,”bata jira amsarshi ba,ta nufi hanyar fita daga falon,
Da sauri Ishaq ya miƙe tare da yin hazarin shan gabanta,ba arziki ta tsaya tana kallonshi,
Marairaice mata fuska yayi”pls Kada kiyi mun haka mana,nasan kin fahimci abunda nake nufi,koda ban fito na bayyana maki ba,”ya É—an daka da yin maganar yana jiran amsarta,
“Sauri nake yi,dan Allah ka bani hanya na wuce,ae kasan alaÆ™ata da laila,So bai kamata kayi mun wannan maganar ba,”
“Ita laila É—in ciki É—aya kuka fito da ita ne”?yayi maganar tare da tamke fuskarshi,
Girgiza kai tayi alamar a’a,
“Ko akwai wani hadisi ko aya daya haramta wa namiji ya auri Æ™awar matarshi”?
Nan ma ta sake girgiza mashi kai”ko É—aya babu,Amma ae ana barin halas ko dan kunya,Ishaq idan ma da wannan manufar kazo mun,Ni bazan iya aurenka ba gaskiya,ba wai don ka ta6a auren Æ™awata bane,No kawai bana ra’ayin Æ™ara kasancewa da wani É—a namiji ne,”
“Koda ace ni ne”?yayi tambayar fuskarshi da alamun damuwa,shiru tayi bata tanka mashi ba,a qagare take ma daya bata hanya ta wuce,
Cikin sanyin murya yaci gaba da cewa”Na jima da dakon sonki acikin zuciyata,Yanzu ne nasamu Æ™warin guiwar sanar dake,ko alokacin baya nayi kawaici ne kawai don saboda nasan bazaki amince da soyayyata ba,Saboda Ƙawanccan dake tsakaninki da laila,Amma yanzu babu Laila,meyasa zaki haramtawa kanki Æ™ara yin aure ne?nafa san komai agame da rayuwarki,lokacin da mijinki yayi hatsarin mota tare da É—anki,hada ni cikin waÉ—anda suka halarci jana’izarsu,Nasan abun dole ya ta6a maki zuciya sosai,Amma Ya zakiyi?mutuwa ce kuma tana akan kowa….”
Tuni hawaye sun wanke mata fuskarta,cikin shessheÆ™ar kuka tace”Dan Allah ka bani hanya na wuce”daÆ™yar sautin maganarta ke fita,
“Zan baki hanya ki wuce,Amma kafin nan ki tsaya ki saurari maganata,kina buÆ™atar wanda zai maye maki gurbin mijinki,kuma ni ashirye nake dana zama madadinshi,zan baki kyakkyawar kulawa in har kika amince kika aure ni,ke kinsan wanene ni basai na faÉ—a maki ba,bazan yabi kaina ba,Amma nasan kinsan komai a wurin Æ™awarki laila,kuma nima a wurinta nake jin labarinki,”

Karanta>>> Wace Ce Ita (Who is she) Complete Novel

Natsuwa tayi tana sauraran kalamanshi,yayin da take ta wasi wasi acikin zuciyarta,
“Daga ni har ke,babu yaro acikinmu dukkanninmu mun mallaki hankalinmu,Ki amince kawai nasan ba zaki rasa manema ba,Ni late comer ne,Amma da shiri na nazo bada wasa ba,inaso na haÉ—a zuri’a dake,Yaronki da kika rasa,Zaki samu madadinshi atare dani…..”bazata iya jure sauraron kalaman Ishaq ba,da sauri tabi ta gefenshi da gudu ta buÉ—e kopar falon ta fuce tana kuka,Ya fama mata tsohon ciwon daya daÉ—e acikin Zuciyarta,

Jiki asanyaye Ishaq ya koma saman sofa ya zauna tamkar ya fashe da kuka haka yake ji,bai yi tunanin zata ƙi amince mashi ba,gashi tunda yayi arba da ita ya rasa natsuwarshi,

*Marshal Omar*

Abun ya ɗaure mashi kai!tunda ya shigo bedroom ɗinshi ya same shi kwance yana ta sharar bacci,Yaushe rabon daya ga Sgr yana bacci irin wannan,tun kafin mutuwar Junaid,wuri ya samu gefen gadon ya zauna yana ƙare mashi kallo,Har cikin ranshi ba ƙaramin daɗi yaji ba daya samu Sgr yana bacci,da alama tun da yadawo daga sallar Asuba yake kwance yana bacci,don bai cire jallabiyar jikinshi ba,

Zuba mashi ido omar yayi yana kallonshi,yayi hugging ɗin pillow sosai a ƙirjinshi,kasa tashin shi daga baccin Omar yayi,don bazai so ya katse shi ba tunda an samu baccin ya ɗaukeshi,don yafi kowa shiga matsananciyar damuwa akan rashin Junaid,da kuma Alƙawarin da sukayi ma mahaifinsu,

Motsi ya soma yi da la66ansa da alama mafarki yake yi,matsawa Omar yayi kusa dashi ya kasa kunne don yaji me yake cewa,Sambatu ne yake yi yana ambaton sunan Reesh,abun ya ɗaure mashi kai,instead yaji yana sambatu akan Halin da suke ciki kaman yadda yai tunani amma sai yaji yana ambaton sunan reesh,Wai ma sunan menene reesh ɗin nan?ya tambayi kanshi tare da kallon sama yana ƙokarin tunano inda yasan sunan,
Sai da yayi zurfin tunani sannan ya gane cewa sunan Sehrish ne ya maida reesh,
Ƙayataccen murmushi Omar ya saki,aranshi yace”shegen bisa na,Allah ya toni asirinka,Allah kadai yasan me ya aikata ma Æ´ar mutane jiya da har yake sambatu akanta,Haba no wonder!ba banza ba yake ta sharar bacci,mutumin da saboda tsabar tashin hankalin da muke ciki ko runtsawa baiyi amma yau gashi ya baje yayi É—ai dai saman gado yana ta bacci,”

Motsi Sgr ya fara yi alamar zai farka,slowly ya ɗan ware blue eyes ɗinshi ceiling ya fara kallo na wani lokaci,kafin ya wurga idonshi kan Omar daya ƙura mashi ido yana ta faman sakin murmushi,
Muryarshi da alamun bacci bai ishe shi ba yace”Bro,yaushe ka shigo?
“Ban jima da shigowa ba,nazo na taras da abun farin ciki,Na same ka kana ta sharar bacci,hankalinka kwance kamar kana cikin jirgi mai ya Æ™are,”
yatsina fuska Sgr yayi batare daya ce komai ba,
“Ka gama shan Æ™amshin naka,Nasan komai,babu abunda zaka 6oye mun,”cike da zolaya Omar yayi maganar,
“What are u talking about”?Sgr ya tambaya fuska a É—aure yana kallonshi,
Murmushi Omar ya saki tare da kashe mashi ido É—aya irin na Æ´an duniyan nan,
“Tell me,Wacece reesh da naji kana faÉ—i acikin baccinka”?
A hasale Sgr yace”bansani ba,Omar yaushe ka fara sa ido,”
Dariya Omar yayi tare da cewa”basa ido bane,its just a question pls ka faÉ—amun sunan wa naji kana faÉ—i acikin baccinka,”
Harararshi Sgr yayi”I don’t know,”
“Kada kayi tunanin zaka 6oye mun wani abu,saboda alamu sun bayyana ajikinka,”
Jin haka yasa Sgr yayi saurin kai hannunshi saman short É—in jikinshi,
A Æ™ule ya furta”And then so what Omar!,Yau ka fara gani ne”?a fadace yake magana,dama ance wai da bori ake naÉ—e tabarmar kunya,
Sosai Omar ya 6a66ake da dariya,daƙyar ya samu ya tsagaita da yin dariyar
“I know this is a normal thing,but akan ka ni ban saba gani ba,gaskiya in ma na ta6a gani to na yau dai na musamman ne fa,Kalli fa ka gani,Tayi tsaye ba ladabi ba biyayya…..”kasa Æ™arasa maganar yayi saboda dariyar da ta ciyoshi,Rai amatuÆ™ar yace Sgr ya miÆ™e daga zaune tare da kai hannu ya warci pillow ya wurga ma Omar asaman fuskarshi,da sauri Omar ya ruÆ™o pillown ya janye shi daga fuskarshi yana yi mashi gwalo,
“May be it needs a second round shiyasa taki relax,É—an rainin hankali,kayi ta shan Æ™amshi wai kai baka buÆ™atar mace a arayuwarka ko?Yanzun wannan menene? Yayi tambayar cike da tuhuma,
Sgr was speechless,Zuba mashi ido kawai yayi yana kallonshi without saying anything,

Karanta>>> Tabarmar Kashi Chapter 1 By Safiyya Huguma

Omar kuwa daÉ—in zolayar tashi yake ji,
“Tell me the truth!meya faru jiya da daddare atsakaninka da ita”? cizon tausasan la66ansa ya shiga yi yayin da yake kallon Omar,kamar ya shaqe shi Haka yake ji,
“Tunda bazaka faÉ—amun ba,Al’qur’an saina faÉ—ama Uncle ince ka fara taushe mashi É—iyarsa,ni ban ta6a ganin mara kunya irinka ba Allah,nan nan fa ka auri yarinyar nan don tayi maka aiki,Æ´an share share da goge,Ashe muka maida shashashu,””

“Is enough Omar!kana so ka 6atamin raina ko?U know why i married her,yarjejeniyace akan zatayi mun aiki,so this is also part of her work,” ya Æ™arasa maganar tare da saukowa daga saman gadon yana faman hura hanci,
Dariya sosai Omar keyi,hada kwantawa saman gadon Sgr É—in,Yau da jan faÉ—a yazo,
“Naji abunda kace,Amma pls kaga yarinya ce,Ya kamata ka dinga É—an riritata,kana tarairayarta kamar new born baby,don nasan halinka Allah,kullum fuska a É—aure,ita kanta bazata samu sakewa dakai ba,halan ma Æ™arfi kake nuna mata?shiyasa har take baka”?
Dakatawa Sgr yayi daga yin tafiyar da yakeyi,Omar ya Æ™ule shi a hasale ya juyo yana kallonshi……..
ÆŠaga mashi gira É—aya Omar yayi tare da cewa”what do u think if she becomes pregnant?kaga shikenan Abba zai samu little Junaid,hakan zai É—ebe mashi kewar Babynmu da muka rasa,”
Har cikin zuciyarshi yaji maganar Omar,shi kanshi Omar da yayi maganar sai da yaji wani iri acikin zuciyarshi,
Bai dai tanka mashi ba,ya shige cikin toilet tare da turo ƙopar ya rufe,

*Boss Bature*

A 6angaren Sehrish kuwa,bayan ta kammala shan kukan nata,Bacci ne ya É—auke ta acikin garden É—in yayin da take zaune asaman garden Chair É—in,ta aza kanta asaman table É—in gabanshi,

Kukan tsuntsayen dake shawagi a wurin ne ya farkar da ita,a hankali ta buɗe idanuwanta,tare da miƙewa zaune tana bin tsuntsayen da kallo,jikinta duk ya saki,kewar junaid duk ta baibayeta,daƙyar ta iya miƙewa tsaye ta juya tana tafiya iska na kaɗa sumar kanta,cikin gidan ta koma ta ƙopar da ta fito,ƙopar da idan ka shiga zata kaika direct corridor ɗin dakunansu,

Lokacin da ta ƙaraso bedroom ɗinsu,hannu tasa ta tura ƙopar ta shiga daga ciki,babu kowa da alama sun fita yin breakfast ne,

Rage kayan jikinta tayi,kafin ta shige cikin toilet don tayi wanka,almost 30 mins sannan ta fito daga ciki,jikinta sanye da white underwear É—inta,gaban wadrobe ta nufa tare da sanya hannu ta buÉ—e tana neman kayan da zata sanya,

Karanta>>> Furar Danko Chapter 1 By Billyn Abdul

Wata gown ce ta ɗauko,Doguwa Red colour mai bazar net daga ƙasanta,daga sama kuma hannu ɗaya gareta siriri,rigar ta haɗu sosai,sanya rigar tayi ajikinta ta zauna mata sosai tabi shape ɗin jikinta,saukko da gashin kanta tayi ta sanya hannu ta barbazo dashi ya rufe bayanta,gaban mirror ta koma ta zauna da niyyar yin kwalliya amma sai ta shiga tunanin wai ma wa zatayi ma kwalliya?

Tana cikin wannan tunanin wayarta dake ajiye saman gadonsu ta soma ringing,miÆ™ewa tayi jiki ba Æ™wari ta Æ™arasa tare da É—aukar wayar,ta duba sunan mai kiran nata,Ajiyar zucia ta sauke tare da picking call É—in ta kara wayar a kunnanta”Mommyna,kin tashi lafiya,”
On the other hand Aunty azeema tace”Lafiya lou Daughter Alhamdulillah,Ya kike ya gida!ya jikin Oumman taku?Abba ya sanar dani cewa taji sauÆ™i,harma kun dawo gida,”
. “eh,jiya muka dawo,”
“Allah sarki,to Allah ya Æ™ara mata lafiya,”
Ta amsa mata da Ameen,
“Inason magana dake ne shiyasa na kira,”jin haka yasa Sehrish ta samu wuri gefen gadonsu ta zauna tare da wayar manne a kunnanta,
“Mommy ina sauraronki,”
Hajiya azeema tace”Yawwa,dama inaso naji ya tsakaninki da Rafayet?
“Shiru sehrish tayi saboda kunyar da take ji,tuntuni taso ta fayyace mata abunda ya fara shiga tsakaninta da Sgr amma kunya ta hanata,
“Kada kiji kunyar komai,ki É—auke ni tamkar Æ™awarki aminiyarki,inaso ki sanar dani komai,”Acewar hajiya azeema don ta ganota,kunyarta take ji shiyasa tayi shiru bata tanka mata ba,
Cike da jin kunya Sehrish ta sanar da ita duk wani abu dake wakana atsakaninta dashi,
Lokacin da ta kai Æ™arshen maganar,tana jiyo sautin dariyar hajiya azeema ta cikin wayar,da alama abun ba Æ™aramin daÉ—i yayi mata ba,sai da tayi mai isarta sannan tace”amma Rafayet baida ta ido,in banda ma baturen mutun,ka auri yarinya don tayi maka aiki,kuma ka 6uge da neman biyan buÆ™atarka,’
Sunnar dabkai Sehrish tayi,gani take yi kamar Mommy azeeman tana agabanta ne,
“Am sorry fa,karki ji inata yi maki dariya,abunne ya sanya ni nishaÉ—i,kina ji na ko”?
É—aga kai sehrish tayi kamar tana agabanta”ina sauraronki Aunty,”
“Yawwa inaso ki natsu ki saurare ni,nasan kina jin tsoron Sgr sosai,saboda yanayinsa,Yawan É—aure fuska,rashin fara’a da sauransu,wannan tsoron shi nake so ki cire!
ÆŠan waro ido sehrish tayi hankalinta atashe tace”Aunty,taya zan daina jin shakkarshi”?
“Na farko dai mutunne kamarki,ba aljani ba,dole sai kin cire kunya idan har kina so kija ra’ayinshi agare ki,har yanzu fa Sgr baisan so ba,sha’awarki kawai yake yi shiyasa ya fara kulaki,koda ace ma yana sonki bazai iya gane hakan ba,har sai kin koyar dashi,”
“Amma Aunty taya zan iya koyar dashi soyayya”?muryarta sanyaye tayi maganar
“Yanzu Sgr ya fara sha’awarki,bazaiyi wasa dake ba,zaki ga canji atattare dashi,zai fara baki kulawa ta musamman kuma zai damu dake,ba don komai ba sai don saboda yasan cewa ta wurinki ne kawai zai samu natsuwa aduk lokacin da desire dinshi ta motsa,zai dinga tarairayarki ne yana baki kulawa sosae,ko tari kika yi zai tambayeki lafiya?Sanin cewa in fa baki da Æ™oshin lafiya,abun zai shafe shi ne shiyasa zai dinga tambayarki da zarar yaga canji atattare dake,daga yanzu inaso ki lura dakyau ki gano wurin da yafi ra’ayin ta6awa ajikinki,saboda ta hakanne zaki gane lagwansa,sannan a duk lokacin da zaki je part É—inshi,ki dinga É—aukar wanka kuma kada ki dinga sanya manyan kaya irin atampa ko shadda wannan sai za’aje unguwa,ko cikin gida,ki dinga sanya kayan da zasu bayyana surar jikinki,Yadda zai dinga ganin komai Zahiran har ya gaza samun kwanciyar hankali,amma fa idan zaki sanya kalar wannan kayan ki tabbatar da kin sanya hijab ajikinki saboda akwai maza agidan,daga baya idan kinje part É—inshi sai ki cire kina jina ko”?

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

“Eh,”ta amsa mata,
“Yawwa,nasan dai basai na Æ™ara tunasar dake ba,game da tsafta duk kina yin wannan,Amma shagwa6a fa kin ta6a jaraba yi mashi….”tunkan ta Æ™arasa maganar,Sehrish ta 6a66ake da dariya,
Hajiya azeema tace”Allah kuwa,bafa wasa nake yi maki ba,shagwa6a tana É—aya daga cikin abunda ke jan hankalin É—a namiji zuwa ga mace,da kuma salon magana,da tafiya,da sauransu,”
“Aunty azeema shagwa6a fa kika ce,babban yaya zan yiwa shagwa6a aikuwa da rabon insha Mari,”daÆ™yar ta Æ™arasa maganar saboda dariyar data zo mata,
Itama azeema dariyar take yi,sai da suka tsagaita da yin dariyar tukunna tace”Don kina jin tsoranshi ne shiyasa kike jin wani banbarakwai,ai ba wani abu bane,ko da yake kufa Majority É—inku kunya ke hanaku nunawa miji soyayya,ba zaku iya sakin jiki ku nuna ma miji Soyayya ba,ga kuma girman kai,duk da nasan ke baki da wannam girman kan,kunyar dai ce kawai da kuma tsoro,’
Murmushi kawai Sehrish keyi tana sauraronta,aranta kuwa tana aayyana abunda zai faru idan tayi kuskuren yi ma Sgr shagwa6a,
“Ki Æ™addara cewa,Sgr jinjiri ne aka baki shi don ki kula da rayuwarshi,komai kece zaki koya mashi,kamar soyayya da bai iyaba zaki iya koya Mashi,duk abunda kika saba mashi,to shima ko bai iyaba zai fara kwatanta yi maki ne,”sosai Aunty azeema ta shiga koyar da ita,Yadda zata jawo hankalin Sgr,suna cikin magana ta wurga idonta kan Wall Clock,sam ta manta bata kai mashi breakfast É—inshi ba,”
AruÉ—e tace”Aunty azeema,na manta ban kai mashi breakfast É—inshi ba”
“Okey,ki kwantar da hankalinki pls,Zamuyi Magana anjima,”
. sallama Su kayi da ita,jiki na rawa Sehrish ta koma gaban mirror,janbaki ta É—auko red colour ta murza ma la66anta suka ciza sosai,turarenta ta É—auka ta feshe jikinta dashi,
Komawa tayi gaban wardrobe ta É—auko babban mayafi ta lullu6e jikinta dashi tun daga saman kanta,

High heels ta sanya a ƙafarta launin rigar jikinta,ƙarasawa tayi tare da buɗe ƙopar ɗakin ta fito,tun kafin ta ƙarasa fitowa daga cikin corridor ɗin ta soma jin sautin ƙarar Cokula,alamar abinci suke ci,

Kamar karta fito haka ta dinga ji,batasan taya zata nufi part É—inshi ba,ga mutane a dining area kuma dole ne in zata gifta sai sun ganta har ma su nemi jin ba’asin rashin fitowarta cin abincin,

Daƙyar ta ɗaure,ta nufi dining ɗin kaitsaye,tun kafin ta isa sautin takalmanta yaja hankalinsu,gaba ɗaya suka ɗago suna kallonta
“Daugher!dama idonki biyu?amma shi ne baki fito kin ci abinci ba”?Abusufyan ne yayi maganar,
“Ni nayi tunanin ma ko bacci takeyi shiyasa banyi magana ba,”acewar Abba,wanda ya tasa plate É—in abinci agabanshi sam ya kasa cin abinci,har yanzu kewar junaid ke É—awainiya dashi,
“Ina kwananku,”ta gaisar dasu cikin girmamawa atare suka amsa mata,
Duka matasan gidan nan suka hallara,dogon table É—in mai mazaunin mutun 12,anan Abbansu yake tare da Mommynsu,Fawan,Irfan, Jabeer,Khaleed,sai kanal Yousouf tare dasu Talal,Najeeb da twins,

ÆŠayan table É—in kuma mai mazaunin mutun 6,Oummansu ce tare da Abusufyan sai su Jahad da Hosana,idan ka kalli fuskokin matasan gidan sai sun baka tausayi,don kuwa kamar anyi masu dole don suci abinci,musamman fawan jujjuya cokalin hannunshi kawai yake yi,har yau ya hana kanshi jin daÉ—i duk don saboda Junaid,

“Samu wuri ki zauna mana”Mommynsu Junaid ce tayi mata magana ganin ta tsaya atsaye kiÆ™am,
Sunkuyar da kanta ƙasa tayi,tana wasa da yatsun hannunta sam taƙi motsawa,
“Ki zauna mana baki ji ana magana ba”Abusufyan ne ya tunasar da ita,
Tafiya ta soma yi zata zagaya ta zauna,
“Ina azmee take ne?naga yau tunda ta jera abinci,bata fito tayi serving É—inmu ba kamar yadda ta saba,kodai bata lafiya ne”Abba ne yayi maganar cike da son jin Æ™arin bayani daga wurinsu
Abusufyan yace”Nima tun É—azu na lura bata a wurin nan,yakamata a dubo ta aji ko lafiya,”
“Bari naje na kirata,”Ko sauraron amsarsu batayi ba,dama so take ta gudu daga Dining area É—in,
Gudu gudu sauri sauri ta nufi corridor ɗin ɗakinsu,a ƙopar ɗakin azmee ta tsaya tare da sanya hannu ta kwankwasa ƙopar,kusan sau uku tana buga ƙopar,ana ƙarshe ne tajiyo muryar azmee daga cikin ɗakin tana tambayar wanene,

Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document

“Sehrish ce Aunty azmee,su daddy ne ke nemanki,Sun ji shiru shi ne suka ce a kirawo ki,”
“Okey,gani nan zuwa,bana jin daÉ—i ne,”
Tsayawa sehrish tayi a bakin ƙopar ɗakin har saida azmee ta fito jikinta sanye da hijabi,
“Aunty azmee ya jikin naki”?
DaÆ™yar ta iya buÉ—e baki”da sauki,ciwon kai ne,kuma nasha magani,”
“Allah ya Æ™aro sauki Aunty azmee,”ta Æ™arasa maganar tare da ruko hannun azmee cikin nata,suka kama hanyar zuwa dining É—in atare,

Lokacin da suka ƙaraso dining area ɗin,hankalin kowa ya dawo kansu,
“Oumma ga Aunty azmee nan,kallatta ki gani,itace muke baki labarinta jiya mai girka mana abinci”a wani slow abu ta wurga eyeballs É—inta akan fuskar Azmee,karaf idanuwansu suka shiga cikin na juna,Zumbur abu ta miÆ™e tsaye tana kallonta,kallon kamar nasanki,Itama Azmeen kallon Sani take yi mata,
Ganin sun Æ™urawa juna ido,babu mai magana acikinsu,yasa Abusufyan tanka masu”Ko kunsan juna ne”?
Girgiza kai abu tayi”a’a gani nake yi kamar na santa ne,tayi mun kama da wata dana ta6a sani arayuwata,Amma bazan iya tunawa ba,
“Aunty azmee kefa?kinsan Oumma ne”?Sehrish ce tayi mata tambayar,girgiza kai azmeen tayi”A’a nima dai kallon sani nake yi mata,kamar na ta6a sanin wata mai irin fuskarta,amma dai ba ita bace ba,sunyi kama ne”
Murmushi sehrish ta É—an saki tare da cewa,”tunda baku san juna ba,bari na gabatar da kowannanku,”
“Aunty Azmee wannan itace Oummanmu,mahaifiyarmu,”
Sannan ta nuna Azmee”Oumma ga Aunty azmeen da muke baki labarinta jiya,ba iya girki kaÉ—ai ta iya ba,tana da kyakkyawar zuciya,mutuniyar kirki ce ita,”
Murmushi abu ta saki tare da miƙa ma azmee hannu suka gaisa da juna,kowa fuskarshi ɗauke da murmushi,

Ajiyar zuciya Sehrish ta sauke,ganin hankalin kowa ya koma kansu yasa tayi saurin lalla6awa ta wuce kitchen,shaf shaf ta shiga haÉ—a mashi breakfast É—inshi,

“Sehrish ta faÉ—amun irin halarcin da kikayi mata,bansan da wasu kalmomi zanyi amfani dasu ba wurin gode maki,Allah ne kaÉ—ai zai iya saka maki”
Murmushi Azmee tayi”Ae duk yiwa kaine,na dauki sehrish tamkar Æ´ar cikina,”dakatawa ta É—an yi da yin maganar,ta mayar da idonta kan Abusufyan”ina tayaka murna sosai,Allah ya Æ™ara haÉ—a kan zuri’arku,”addu’o’i ta shiga yi masu suna amsa mata da Ameen,kafin daga bisani Abba yace”Samu wuri ki zauna,Ke ma Azmee daga yanzu bana so kina wannan tsayuwar,don yanzu kinfi Æ™arfin Æ´ar aiki a wurinmu,pls kada kiyi mun musu kamar yadda kika saba,”
Murmushi Azmee tayi tare da samun wuri a table ɗinsu Abusufyan ta zauna,Abu ma ta zauna,a tsanake kowa yake cin abincinshi,Abunda zai ɗaure maka kai,ya baka mamaki shine duk bayan ƴan mintina sai abu ta saci kallon Azmee,da alama dai tasanta ne,kuma tana ƙoƙarin tuna wurin da suka ta6a haɗuwa,itama Azmeen satar kallon nata take yi,kowa da abunda yake sakawa aranshi,
Fitowa tayi daga cikin kitchen É—in hannunta ruÆ™e da Æ™ayataccen tray,hannu bibbiyu ta ruÆ™o shi,cikin sanÉ—a ta wuce upstairs,direct ta nufi part É—in Sgr,a bakin Æ™opar shiga falon ta tsaya sallama tayi jin shiru ba’a amsa mata ba,yasa ta wuce ciki izuwa bedroom É—inshi,tana Æ™oÆ™arin shiga,tajiyo maganganunsu shi da Omar,kasa kunne tayi tana sauraronsu,
“Yanzu ya zamuyi?duk mun jefa kanmu cikin haÉ—ari,idan har Abba yasan cewa Æ™aryane ba kidnapping É—in su Junaid akayi ba daga ranar zai Æ™ullace mu aranshi,kuma girmanmu zai faÉ—i agaban Æ™annenmu ne,nayi regretting wlh,”Omar ne yayi maganar,a yayin da yake zaune gefen gadon,
“Omar,nima ina danasanin yin hakan,na shiga damuwa sosai,bansan ya zamu yi ba,remain just one week and some days,daddy tare dasu fawan jiranmu kawai suke yi mu kawo masu Junaid”yayi maganar ne yayin da yake tsaye gaban mirror yana gyara jikinshi dake sanye da Bathrobe,ga danshi danshin ruwa da alama bai jima da fitowa wanka ba,
Kowanne fuskarshi akwai tarin damuwa,abun ya tsaya masu aransu,
Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,
“Assalamu alaikum,”jin muryarta yasa suka tsagaita da yin firartasu,
“Who’s there”Sgr ne yayi tambayar
“Sehrish ce,breakfast ne na kawo maka”
Murmushi Omar ya fara saki,yana kallonshi,harara Sgr ya É—an wurga mashi,

Also Download FARRAH Hausa Novel Complete Document By Maman Shuraim

MiÆ™ewa Omar din yayi”kar na takura maka,bari na baka wuri,idan Mun haÉ—u zamuyi magana,”bai tanka mashi ba,Ya nufi hanyar fita daga É—akin,
Sehrish na ganinshi tayi saurin gaisar dashi”Ina kwana ya Omar,”
Fuskarshi É—auka da fara’a ya amsa mata”Lafiya lou,ina fata kema haka”.
“Ina lafiya,”daga haka ya matsa mata hanya ta wuce ciki,Shi kuma ya fuce daga É—akin,

A hankali take tafiya ta cikin mirror yake Æ™are mata kallo,A saman table ta ajiye mashi tray É—in,sannan ta É—an juya tare da kallon bayanshi,gaisar dashi tayi”Gm ya Rafayet,ka tashi lafiya,”shiru bai amsa mata ba,kamar bashi bane ya gama magana yanzu tare da Omar,

Juyawa tayi saÉ—af saÉ—af zata bar bedroom É—in nashi,
“Where are u going?kin kammala aikin ki ne?”
“A’a,naga kamar kana shiri ne,Zan jira a falo,idan ka kammala zan shigo daga ciki in yi aikin,”
A wani slow ya juyo tare da kallonta,adai dai lokacin itama ta waiwayo shi,
Har sai da gabanta ya faÉ—i lokacin da idanuwansu suka haÉ—u cikin na juna,
Da hannu yayi mata alamar ta dawo,kamar wadda aka zarewa laka,haka ta dawo daga ciki duk tasha jinin jikinta,ƙoƙarin gyara Mashi bedroom ɗin ta shiga yi,kamar daga sama taji ya cire mata mayafin jikinta,da sauri ta juya tana kallonshi
“Taya zaki ji daÉ—in yi mun aiki da wannan abun a jikinki”?
Shiru tayi batace komai ba,Sae Æ´an kame kame takeyi,
Jefa mata shi yayi asaman bayanta,”ki san inda zaki ajiye shi,”
Ruƙo mayafin tayi tare da ɗaure ɗamararta dashi kamar yadda ta saba yi,mayar da hankalinta tayi wurin gyara mashi gadon,
Cike da tsantsan sha’awarta yake bin jikinta da kallo,bai ta6a sanin kyawun launin ja ba sai da yayi arba da rigar jikin Sehrish wadda ta kasance Red colour,ga shi hannu É—aya gareta,Soft skin É—in bayanta mai matukar jan hankali sai fisgarshi takeyi izuwa gare ta,

Tana cikin gyaran taji motsinshi a bayanta,A firgice ta juya karaf suka haÉ—a idanu,Zazzare mashi kyawawan idanuwanta ta shiga yi,farare Æ™yal dasu masu É—auke da kwayar ido brown colour,ja da bayan da take Æ™oÆ™arin yi ne yasa ta kusa faÉ—awa saman gadonshi saboda ta Æ™ure mashi,da sauri ya cafko Waist É—inta da hannu É—aya ya janyota izuwa jikinshi,gaba É—aya yayi hugging É—inta so tightly,ta ko’ina Æ™amshin turarenta neman yi mashi illa yake yi yana Æ™oÆ™arin Zautar dashi,natsuwa Sehrish tayi yayin da kanta ke kwance luff asaman faffaÉ—an Æ™irjinshi,wannan daddaÉ—an Æ™amshin turaren nashi ne ke dakar hancinta,Gaba É—aya jikinta ya mace,
Moving hands É—inshi yayi tun daga kan Ass É—inta ya tarboshi,ya jinjina girman hips É—inta,slowly yayi sama da hannun zuwa cikin sumar kanta,sosai ya shiga murza gashin da yatsun hannunshi,tamkar yana yi mata susa haka ta dinga ji,ga wani irin daÉ—i mara misaltuwa,almost 5 mins ya rabata da jikinshi,Yayin da idanuwansu ke kallon cikin na juna kamar masu jin bacci,dawo da hannun nashi yayi saman Hips É—inta tare da pulling É—inta ya haÉ—e gabansu sosai,Ji yake tamkar kawai ya aiwatar da abunda zuciyarshi ke raya mashi,but this is not the right time da yake son wannan abun ya kasance,
“Meyasa baki gaishe ni ba”?da wata irin kasalalliyar murya yayi maganar,
Muryarta na kerma tace”wlh na gaishe da kai,tunda na shigo,”
“Haka ake gaisuwa?”?
Abun nashi ya fara É—aure mata kai,
Cigaba da magana yayi”Ni ba haka nake son ana gaishe dani ba,a kowani lokaci idan kika zo part É—ina,lemme teach u..”moving face É—inshi yayi izuwa gefen fuskarta,Ya manna mata kiss,side by side na fuskarta,slowly ya dawo da sweet lips É—inshi saman nata soft lips É—in ya haÉ—esu wuri guda,kissing É—inta ya fara yi,da niyyar ya koyar da ita yadda yake son ta dinga gaisar dashi,Boss man É—in sai gashi ya fara Hawa kan Network,sosai ya matseta ajikinshi,A susuce ya shiga sucking lips É—inta,Mayar mashi da martani ta shiga yi hakan yasa shi Æ™ara zaucewa,gaba daya ya sabeta izuwa saman gadonshi ya kwantar da ita,yabi kayansa ya turmushe,Zage zip É—in rigarta ya fara yi,Æ™ankame hannunshi tayi saboda bata kaiga fita hayyacinta ba,kuma ta jiyo motsin mutun a falo,a rude yake faÉ—in”feed me pls,i really need it,”hankalinta ba Æ™aramin tashi yayi ba,ya zauce gashi wani yana tunkaro É—akin,
Girgiza mashi kai ta shiga yi tana faÉ—in”Akwai mutun a falo,bazan iya ba,”
“I don’t care,just feed me,Æ™oÆ™arin sabule mata rigar jikinta yake yi,don ya samu yasha ko ya kore kishin ruwan da yake ji,don maÆ™oshin shi a bushe yake,
“Rafayet”!muryar Abbansu ce ta karaÉ—e kunnuwansu,jiki na rawa Sehrish ta janye jikinta daga nashi,A hanzarce ta diro daga saman gadon ta faÉ—a bayan labule ta 6oye,tana faman sauke ajiyar zuciya,
Kasa amsa mashi kiran nashi yayi numfashin shi na fita da wani irin huci huci,yayi Uban goho asaman gadon,Sumar kanshi duk ta rufe mashi fuskarshi,
Shigowa cikin bedroom É—in Abba yayi,yana kallonshi cike da mamaki yace”Rafayet baka da lafiya ne”?
DaÆ™yar ya iya motsa lips É—inshi”Am ok,”
Ƙarasa shiga cikin ɗakin Abbansu yayi tare da samun wuri ya zauna daga gefen gadon yana ƙare mashi kallo,Yaƙi yadda ya ɗago da kanshi,gudun kada Abbansu ya gano shi,Don kallo guda zai yi mashi ya shaida cewa wani abu ke faruwa,ga janbakin sehrish daya 6ata mashi chest ɗinshi,
“Rafayet,inason magana da kai game da Junaid,na kasa cin abinci ko isasshen bacci bana samu,Raina yana bani cewa kamar bazai dawo ba,idan har akwai abunda kuke 6oye mun kaida Omar dan Allah ku sanar dani,Don in fidda rai da dawowarshi,”
Gyara bathrobe ɗin jikinshi yayi,ya ɗaure igiyoyin jikinta,sai da ya fara daidaita natsuwarshi sannan ya miƙe daga zaune ya zuro da ƙafafunshi ƙasa,kallon juna su kayi shi da Abbansu,hankalinshi ba ƙaramin tashi yayi ba,Ganin hawaye asaman fuskar Abbansu,
“Daddy,don Allah kadaina zubar da hawayenka,before end of this month,in sha Allah daddy,zan sanar dakai komai,”
“Har yaushe ne zaku cigaba da samun ran dawowarshi?Idan mutuwa yayi ku sanar dani mana,na fara zargin hakan acikin raina,da ace kidnapping É—in Junaid akayi dagaske,Even one day bazaku bari yayi ba,batare da kun dawo dashi cikin gidan nan ba,Amma almost 3 Weeks Junaid baya a gidan nan?kullum Æ™ara samana ran dawowarshi kuke yi”miÆ™ewa yayi daga tsaye jikinshi na kerma ya soma tafiya daÆ™yar yake iya tafiya,har sai da yakai bakin Æ™opar sannan ya dakata da yin maganar ya juyo tare da kallonshi har lokacin bai motsa ba daga zaunen da yake,
Cikin sanyin murya ya Ambaci sunanshi”RAFAYET”
“Na’am Abba,”ya furta hakan yayin da yake kallonshi,jikinshi ya gama yin sanyi,
“In cigaba da sa ran dawowarshi ne?ko in fidda rai,”shiru Sgr yayi batare daya tanka mashi ba,Nazarin maganar shi ya shiga yi,muddin yace mashi ya fidda rai,to tabbas zai fahimci cewa Junaid ya mutu ne,
Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace”Am really sorry Abba,dan Allah ka bani time,zan baka amsar tambayarka,Amma ba yanzu ba,akwai wani investigation da nakeyi,Zan sanar dakai komai,”
GyaÉ—a kanshi yayi tare da kama hanya ya fita daga cikin É—akin,Yana juyo muryarshi yana fadin”Zan cigaba dasa rai,”
Sun jefa kansu cikin tsaka mai wuya,kifa kanshi yayi A saman mattress É—in,
Sehrish dake la6e abayan curtains ɗin sai faman shessheƙar kuka takeyi,tausayinsu ne ya kamata,ta jima tana kuka abayan labulen kafin ta fito tana tafiya izuwa gefen da Sgr yake a kwance,
Tsayawa tayi tana kallonshi,yatsun hannunshi sae kerma sukeyi kamar wanda sanyi ya kama,
A hankali ta furta sunanshi”Ya Rafayet,”
“Pls,Just Leave am not in the mood,”da gudun gaske Sehrish ta kama hanyar fita É—akin tana kuka,bata ji zafin maganarshi ba,

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Yinin ranar ko abinci Sgr baici ba,Yadda takai mashi kayan abinci haka ta kwaso su,bai ta6a koda Coffee ba,

After 5 days,bayan kwana biyar,wanda yayi dai dai da sati uku da kwana Biyu da rasuwar baby Junaid!!!!!saura kwana 5 ya rage masu su bayyanar da Junaid,komai ya gama hargitse masu babu wani sauran kwanciyar hankali da suke dashi,

Wuraren Æ™arfe 9 na dare,Suna kwance a É—akinsu,har lokacin Atare suke kwana da Oummansu,Har É—aki aka ware mata haÉ—aÉ—É—en bedroom amma tace ita tafi son ta kwana tare da Æ´a’Æ´anta,Su uku ne saman gadon suna bacci,Oummansu tare dasu Hosana da Jahad,Sae faman sharar bacci suke yi,
Sehrish kuwa sam ta gaza runtsawa,ta sanya damuwa sosai aranta,ta ɗaurawa kanta nauyin alhakin Ƙaryar dasu Ya Omar su kayi ma Abbansu,
Tana zaune saman sallaya bata jima da kammala yin nafilfilin dare ba,hannayenta ta É—aga saman tana addu’a,yayin da hawaye ke shararowa akan fuskarta,kusan minti 30 Sehrish bata dakata da yin addu’ar ba,sai da tayi mai isarta aÆ™arshe ta fashe da matsanancin kuka,da sauri ta sanya tafin hannayenta saman fuskarta ta toshe bakinta gudun kada sautin kukanta ya tashi su Oummansu,
A saman dardumar ta kwanta,tana ci gaba da yin kukan,taso ace zata iya taimaka masu sai dai babu halin yin hakan,tafi damuwa da Sgr don tun ranar da Abbansu ya ƙara tunasar dashi akan Junaid,ita shaidace bai ƙara cin abinci ba,Sai dai lemu da yake sha,babu bacci a idanuwanshi,kullum babu lafiya ajikinshi,duk yabi ya hargitse,

A cikin wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita,
_Sae da suka kammala hoton sannan ta lura da zoben diamond ɗin dake hannunshi,sae faman ƙyalli yake yi_
_Waro ido waje tayi alamar mamaki tace”wow junaid wannan fa,waya siya maka shi_
_Mommy azeema ce ta bani shi,dama É—azu na sanar dake cewa zan nuna maki gift din da takawo mun,to itace wannan_
_Ya ƙarasa maganar yana nuna mata zoben da Wrist watch din_
_Junaid sunyi kyau wlh,musamman daya kasance kaine ka sanyasu_
_Thank u reesh,sunyi mun kyau amman idan ke kika sanyasu sae sun fi yi maki kyau,bari na ciro maki su ki sanya,nafison su kasance a hannunki_
_cikin sauri tace mashi”no junaid that’s impossible,Auntynku azeema ce ta baka shi,muddin ta neme shi a hannunka bata ganshi ba zata nemi jin ba’asin inda ka kai su,kuma ma in banda abun ka junaid wannan ae irin naku ne!kamar diamond ne fa,nida ko zoben azurfa ban ta6a sanyawa a hannu ba,balle diamond_

A firgice Sehrish ta farka daga baccin da ya dauketa,mafarkin da tayi yayi matukar É—aure mata kai,Zurfin tunani ta shiga lokacin guda ta gane wannan zoben da Junaid ya ta6a nuna mata Shi ne tagani a É—akin Aunty azmee kamanninsu É—aya Sak!tabbas kuwa shi ne na Diamond wanda Aunty azeema ta siya mashi mai harafin *j*

Wata irin zufa ce ta shiga gangaro mata agafe da gefen fuskarta,tunani ta soma yi mai yakai zoben Junaid a dakin Aunty azmee?Yakai mata ajiya ne,?sam bata kawo komai aranta ba,Amma tunawa da tayi cewa junaid duk inda zaije zoben nan na ahannunshi wannan yasa ta fara kokonton wani abu,Zumbur ta miƙe daga saman sallayar ta nufi saman gadonsu,

Lalla6awa tayi ta haye saman gadon,saitin wurin da Jahad take a kwance,hannu tasa tana É—an bubbugata yayin da take ambaton sunanta a Hankali don kada ta tashi Oummansu,
“Jahad!jahad!”can cikin bacci jahad tajiyo muryarta,dakyar ta iya buÉ—e idanuwanta masu É—auke da bacci,ganin Sehrish yasa ta dan mike daga zaune”lafiya rishi?dama baki yi bacci ba?”
“Jahad duk ba wannan ba,wata tambayace nakeso nayi maki,A ranar da kuka fita tare da Junaid shan ice cream shin kin kula akwai agogon diamond da ring a hannunshi ko babu”?
‘Meyasa kikayi mun wannan tambayar Sehrish!So kike ki tayarmun da hankalina?Kinsan fa banaso ana tunamun mutuwar Junaid,”tayi maganar hawaye na zuba akan fuskarta
Arude Sehrish tace”dan Allah ki sassauta muryarki Jahad,bana so kowa yaji,nasan baki so amma dan Allah ki yi hakuri ki amsa mun tambayata,”
Shiru Jahad ta É—an yi da alama ta shiga zurfin tunani,kusan minti 5 kafin tace”Kamar naso naga zoben a hannunshi,Amma bazan iya tunawa ba gaskiya”
“Ko hoto baku É—auka tare dashi ba”?
Rai aÉ—an 6ace Jahad tace”haba Sehrish sai kace wata Æ´ar jarida,irin waÉ—annan tambayoyi haka?
“Nidai ki amsa mun tambayata,”a kule tayi maganar,
Ganin ranta ya 6aci yasa Jahad cewa”Am Sorry,munyi hoto da junaid,hada ma videos muka É—auka,Amma wayar bata a hannuna,Tana a wurin Ya Omar…..”tunkan takai Æ™arshen maganar Sehrish ta fuce daga cikin É—akin a fujajen.

Back to top button