Description/Story:
Karfe A Wuta Complete Novel
Written By Ayshercool
Description Of Karfe A Wuta Complete Novel
Tsit ƙaton falon yayi, ba ka jin sautin komai, sai ƙarar gudun AC.
Sai mutanen falon da suke tsaye sun yi cirko-cirko, kamar masu jiran wani sakamako.
Wata matashiyar budurwa ce, durƙushe a kan gwiwoyinta, fuskarta ɗauke da wani yanayi na tsantsar damuwa, da tashin hankali, fuskarta tayi sharkaf da hawaye.
“Yanzu sakamakona kenan a wurinki? Irin wannan sakamakon shi na cancanta daga gare ki ko?”
Cikin ƙulewa wata babbar mace ta ce “Dama wani sakamako ka ke saka ran samu daga tsintaccaiyar mage? Ai ba za ta taɓa mage ba, abun da na din ga ankarar da kai kenan, tun a shekarun baya, amma ka kasa ankarewa, yanzu ta nuna maka ita ƴar kunama ce”
Budurwar ta yakice gumin da yake tsatstsafo mata, ba tare da nadamar abubuwan da suke gudana ba a ƙasan ranta, a zahiri ta ce “Ba mummunan sakamako bane ba, abun da ka tarbiyantar da ni a kai ne, gaskiya ita nake tsaye a kai, bani da niyyar cutar da kowa a gidan nan, kowa aikinsa yake yi, yakamata ayi mini adalci, ba a goyi bayansa a nuna ni ce nake kan ƙarya ba, a bari nima na yi nawa aikin”
Cikin tsawa ɗaya matar ta ce “Har wata gaskiya ce da ke…..
Dattijon ya ɗaga mata hannu ya ce “Ya isa haka, tashi ki je, ba na ko son ganinki, ki je ki yi abun da ki ke ganin ya dace da ke”.
Cikin rauni da tashin hankali ta ce “Abba, ba ka son ganina ka ce?”
“Eh mana, idan har ki na gudun ɓacin raina da fushina, dole ki ba wa ɗan uwanki duk wani cikakken haɗin kai, domin gudanar da aikinsa yadda yakamata”
Cikin matsanancin tashin hankali ta ce “Amma Abba ni kuma menene makomata…? Yakamata a ji ta bakina Abba”
Bai tsaya sauraron mai za ta ce ba, yayi gaba zai bar falon. Cikin matsanancin tashin hankali, ta riƙe ƙafarsa ta na fashewa da kuka.
“Haba Abbana, me yayi mini saura a duniya, idan har zan rayu ka na fushi da ni, ka yi haƙuri zan yi abun da ka ce in sha Allah” tuni hawaye ya cigaba da wanke mata fuska, tsantsar nadama da damuwa suka mamayeta, ta din ga kuka da sheshsheƙa kamar ta shiɗe, amma ya fizge ƙafarsa ya yi gaba.
Yana barin falon, tamkar mutanen falon za su cinyeta ɗanya, haka suka yo kanta sa surutu, kowa da abun da yake faɗa.
Tashi ta yi tsaye, ta goge hawayenta, cikin ko in kula, ita ma ta bi wata hanyar ta bar musu falon, cikin sigar kwa ci kanku.
Ɗakinta, ta shiga ta buɗe drower, ta fito da wasu takardu ta zube su a kan gado, ta kunna system ɗin ta da take caji a gefen gadon, lokaci guda kuma ta ɗauki wayarta tana dannawa.
Jin motsin mutum a bayanta, ya sanya ta waiwaya da sauri.
A tsaye ta ganshi bakin ƙofa, fuskarsa babu walwala balle annuri.
Mayar da hankali ta yi, za ta cigaba da danna wayarta, ya tako zuwa gabanta, ya tsaya ya ƙare mata kallo sannan ya ce “Kin shirya aikata abun da aka umarce ki ko kuwa?”
Cikin hanzari ta tari numfashin sa ta ce “Ban ce shirya ba, kuma ba zan shirya ba, daga nan har gaban abada, ka fita ka rabu da ni”.
Cikin matuƙar mamaki yake bin ta da kallo, “Yanzu duk kukan da ki ka yi, ƙarya ki ke yi kenan?”
A hasale ta ce “Ina ruwanka, idan ma kukan ƙarya ne ko na gaske, ka yi aikinka in yi nawa, kar ka sake yinƙurin shigar mini aiki, idan ba haka ba komai yana iya faruwa, wallahi ba zan fasa abun da na yi niyya ba, idan kuma ka cigaba da takura mini, zan baka mamaki”
Hannu ya saka, ya ɗagota daga kan gadon ya ce “Menene zai faru, wani irin mamaki zaki bani? Me zai faru nake son ki gaya mini. Kina da hankali kuwa? Kin san doka amma kina taka ta yadda ki ke so? Da me ki ke taƙama ne haka?”
“Doka ko? Ni iya takata na yi, kai kuma cin zarafinta ka ke ƙoƙarin yi, ka ƙyale ni babu ruwanka da ni, ka yi naka aikin na yi nawa duk wanda yayi galaba shikenan. Idan ka ga dama ka je ka sake gayawa Abba abun da duk yayi maka a kaina, wallahi babu gudu babu ja da baya, ban fara dan ina saka ran dainawa ba, ba tare da na yi nasara ba” hankaɗata yayi kan gadon, yana wani irin huci, zuciyarsa na yi masa zafi, yayi wata irin ƙwafa yana bin ta da kallo. Cikin hanzari ya fice ya bar mata ɗakin, saboda idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi mata abun da ba shikenan ba. Ta yinƙura ta tashi zaune tana haki, tana kallon ƙofar da ya fita.
****
Tsaye take a gefen wani gini, tana ƙarewa harabar kotun ido. Yadda aka cika harabar da manya da ƙananan motoci ne, ya sake tabattar mata da manyan shari’oi za a gudanar a yau.
Ta din ga kallon agogon hannunta, tana kallon gate shigowa harabar kotun.
Motar gidan yari ce ta shigo, aka yi parking ɗin ta, sai dai tsayuwar motar babu daɗewa wata danƙareriyar motar, ta shigo harabar kotun.
A ƙalla an kai mintuna goma da parking ɗin motar, sannan aka buɗe bayan motar, wata mata ta fito, sanye cikin coat.
Mutanen da ke harabar wurin, suka nufeta, wasu suka karɓi jakarta, ana ta yi mata fadanci, cikin girmamawa.
“Ya Allah kai ne Allah, kai ne buwayi gagara misali, Ubangiji da babu wani kafinsa, kuma babu wani a bayansa. Allah na san mutanen nan sun fi ƙarfina ta ko ina, amma kaine abun dogaro na, na san ba za ka bani kunya ba. Allah sun fi ƙarfina ka fi mini ƙarfinsu. Allah ka yi mini kunfayakununka a kan shari’ar nan, hasken gaskiya ya shafe duhun ƙarya, duk da ina da masu goya mini baya, amma Allah goyon bayanka nake buƙata” ta jima a tsaye tana karanto addu’a, tare da yi wa Allah kirari.
A hankali ta furta “What a hectic trial, Ubangiji ka iya mini” cikin nutsuwa, ta fara taka takalminta mai tudu, ta nufi shiga cikin kotun, da takunta mai kama da na ƙasaita, shigarta ta lawyoyi tayi matuƙar yi mata kyau, tana tunkarar ƙofar shiga, zuciyarta na tsananta bugawa,tana fatan Allah ya shiga lamarin ta.
****
Ƙofar famfo kano state.
Ƙarfe goma saura mintuna goma na dare, tuƙi yake yi cikin sauri, saboda yadda fasinjar da ya ɗaukko take azalzalar sa. Duk saurin da yake yi, mita take yi masa, a kan ya ƙara gudu.
Yanayin kwalliyar da ta yi, cikin baƙin material, fuskarta ta sha make-up, zai tabattar maka daga wurin biki take.
Ta kalli agogon hannunta, kamar ta fashe da kuka ta ce “Mai napep, ka yi wa girman Allah ka yi sauri”
Ya ce “Wai dan Allah hajiya yaya ki ke so na yi ne? Haba babata duk saurin da nake yi, ki yi haƙuri mana mu tafi a sannu”.
A ƙule ta ce “Ban gane babarka ba, wani irin wulaƙanci ne wata babarka, na yi maka kama da tsohuwa ne?”
Yayi murmushi ya ce “A’a, ai ku mata duk in da ku ke iyaye ne… Katse shi ta yi ta hanyar cewa “kuma sai aka ce na haifi kamar ka? Ai sai a bari na haifa tukuna, a yanzu na haifi kamar ka, ai tawa ta ƙare a duniya. Ko yayarka ka ce mini ka cuce ni, balle babarka. Ni dai ka ƙara sauri, yau na san kashina ya bushe, sai an yagalgalani da masifa a gida yau. Aikin banza, ƙawayen amarya ƴan wahala, mun gama wannan wahalar a ɗauke ta a mota an kai ta gidanta, mu muna fama a titi. Mu ma Allah ya kawo lokaci, ace ga miji ga mota”
Ya waiwaya ya kalleta yana murmushi, a fusace ta ce “Lafiya malam?”
“A’a Allah ya baki haƙuri”.
Kafin su ƙarasa in da zata sauka, ta ciro masa kuɗinsa, su na zuwa in da za ta sauka, ta miƙa masa, ta sauka tayi cikin layinsu da gudu a kan takalminta mai shegen tsini, ko wahalar gudun ba ta ji.
Mayafinta da jakarta a hannu, ta tura gate ɗin ta shiga ta na haki.
Wani matashin saurayi, yana tsaye a harabar gidan hannunsa riƙe da waya, ya kalleta ya ce “Daga ina ki ke?”
“Biki” ta bashi amsa kai tsaye.
“Za ki ci ubanki kuwa, Major yana nan ido biyu, tun ƙarfe takwas ya dawo yake tambaya ko kin dawo, gashi kin kashe waya ke ga ƙwararriya”
Cikin ta yayi wata ƙara saboda tsoro “Allahumma inni as’aluka afuwa wal afiya, yau na kaɗe” ta ƙarasa maganar tana nufar cikin gidan.
Cikin sanɗa ta shiga falon, sai dai tana shiga, ta fara tozali da dattijon zaune a kan kujera 3 seater, ya sanya ƙofar shigowa falon a gaba, da gani babu tambaya ta san ita yake jira.
Tsayawa tayi ƙyam da takalmanta a hannu, da jaka da mayafi, kamar ta juya da gudu ta koma.
“Daga ina?” Yayi mata magana cikin dakakkiyar muryarsa.
Cikin rawar murya ta ce “Abba, wurin biki”
“To juya ki koma in da ki ka fito”
“Ai an tashi” tayi maganar kamar ta fasa ihu, dan tuhumar Abba babu daɗi.
“Dama haka mu ka yi da ke? Ki fita ki je ki yi zamanki? Ki dawo mini gida bayan goma, sai ka ce ki na zaman kanki?, koma ki kwana a in da aka yi bikin”
“Dan Allah Abb..”
“Get out, kar ki kuskura ki yi mini magiya. Duk gidan nan babu mai bani ciwon kan da ki ke bani Arfa, koma in da ki ka fito ba ki da wurin kwana a cikin gidan nan yau” da gudu ta juya ta fita saboda tsorata da ta yi.
Ta koma harabar gidan, a ƙasan zuciyarta ta ce “Na shiga uku, ni ake kora kamar wata karya, yanzu idan gidan mijina ne, ba sai dai ya gama bala’in in shige ɗaki na bar shi ba..
Ba ta gama tsinkewa da lamarin ba, sai da major ya kulle babbar ƙofar shiga cikin gidan.
Ta zube kayanta, ta tafi famfon harabar gidan, ta dinga wanke fuskarta, ta wanke kwalliyar fuskar gaba ɗaya, ta koma ta zauna jiran tsammani ko Allah zai saka Abba ya buɗe mata ƙofa.
Samarin gidan suka fara fitowa daga BQ, suna shimfiɗa a harabar gidan, za su yi kwanciyar zafi. Sai wulaƙanci suke yi mata, suna yi mata Allah ya ƙara, suna kyararta, kamar wadda ta aikata wani gagarumin abun kunya.
Ganin ba ta da mafita, ta laluba ta samo tabarma ta shimfiɗa, ta yi kwanciyarta dan a gajiye take sosai.
Tsakar dare, ta yi juyi, ta ji babu kowa a kan gadon sai ita kaɗai, mamaki ya kamata, ta kalli agogon wayarta, biyu da rabi na dare.
Tasowa ta yi ta fito nemansa, sai dai ga mamakinta, ta tarar da shi a ventilation ɗin saman bene, ya zauna a kan kujera ya saka harabar gidan a gaba, hannunsa riƙe da ɗan ƙaramin Alqur’ani yana karantawa.
“Lafiya dai?” Tayi maganar cikin mamaki.
Ya waiwaya ya kalleta ya ce “Lafiya ƙalau”
“Amma me ka ke yi a wurin nan, a wannan uban daren? Na zata tuni ka kwanta, na fito na duba falo baka nan”
Cikin ko in kula ya ce “Kar ki damu, ki je ki yi kwanciyar ki, Arfat ke punishment”
Cikin takaici matar ta ce “To ta na punishment, sai kuma kai ka zo nan ka zauna, ka hana idonka bacci?”
Yayi murmushi ya ce “Ko na kwanta ba zan iya rintsawa ba, ki yi kwanciyar ki kawai” tamkar ta yi tsaki, haka ta wuce shi ta ƙyale shi, tama tunanin yaushe ƙarshen wannan lamarin zai zo?.
Haka ya kwana a zaune, yana gadin harabar gidan, duk wanda yayi juyi cikin mazan nan, yana kallon shi.
Yana ganin yadda Arfa ke ta juyi, sauro ya dame ta, sai da ya ji tamkar ya sauka ya samu abu ya rufe ta, amma ya ƙyale ta.
Asubar fari, ya yi alwala, ya sauka ƙasa domin tafiya masallaci.
Samarin na jin takunsa, suka din ga tashi, idan ba haka ba, ya tashi mutum da carbi.
Ya na zuwa in da take kwance tana bacci, ya tsula mata carbi a ƙafafuwanta.
A razane ta tashi tana rarraba ido.
Bai ce mata uffan ba, ya yi gaba ya fice.
Tana ganin ya fita, ta tattara komatsanta, ta shiga cikin gidan, sai soshe-soshe take yi, saboda uban sauron da ya cije ta.
Cikin ɗakinta ta shiga, ta watsar da jakarta da sauran kayan a kan gadonta, ta jona wayarta a caji.
Ta tuɓe kayanta daga ita sai underwear. Wata matashiyar budurwa da aƙalla za ta ɗan girmewa Arfa ta fito daga banɗaki, ta kalle ta, ta ce “Arfa, ke kuwa a ina ki ka kwana? Har sha ɗayan dare ba ki dawo ba” banza tayi mata, ta taho fuuu ta kusa bangajeta, ta shiga banɗaki. Ta girgiza kai kawai ta shimfiɗa sallaya.
Da ƙyar ta yi sallar asuba, sai soshe-soshe take yi, tana idarwa ta ɓingire ta hau bacci a wurin.
Sosai take baccinta, dan ta gaji sosai, ga baccin jiya sam bai yi mata daɗi ba.
“Nabila!Nabila!!”
Tsaki tayi tare da jan “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, menene, wannan wane irin kira ne dan Allah?”
“Abba ne ya ce, ace miki yana fatan kin ajiye aiki ne, da ki ka kwanta kina bacci haryanzu ba ki fita ba”da sauri ta buɗe idonta, gaba ɗaya ta manta yau Monday.
Kamar korarriya ta tashi, ta afka banɗaki, a gurguje ta wanke bakinta, tayi wanka, ta fito ta shafa mayuka, da turaruka ta shirya cikin uniform.
Ta saɓa coat ɗin ta a kafaɗa, ta ɗauki jakarta ta goyo, ta sanya takalminta, tayi waje tana kunna wayarta.
Ta shiga kitchen, ta buɗe fridge ta ɗebi lemuka ta zuba a jakartab, da abun da ta ajiye da wanda ba ta ajiye ba, duk ta kwasa ta zuba, ta zuge jakar ta fito falo.
A falon suka yi karo da wata matashiyar mata, matar ta kalli Nabila ta ce “Ma’aikaciya ko mahaukaciya, kalleki kamar korarriya Nabila, zaki fita aiki amma ki ka kwanta ki na kwasar bacci abinki”.
Nabila ta ce “Anty, the whole barrister ki ke cewa mahaukaciya?”
“Yo banda shirme, kalleki kamar an hankaɗoki, ke wannan wane nutsatstsen ne ma zai ce ki tsaya masa shari’a?”
Nabila ta ce “I will fill a lawsuit against you, what you did is deformation of character, the whole barrister Anty ki ka zaga”
“Wuce ki tafi kafin na make ki ni? Idan suka kore ki daga wurin aikin, ai kya nutsu” Nabila ta sake kwasa da gudu a kan takalmanta kamar ba budurwa ba.
Mai aikinsu ta tarar a famfon harabar gidan, tana wanke-wanke.
“Shalelen Abbanta, yau kamar kin makara”
Ɗaga mata hannu kawai Nabila ta yi, kowa ya ganta sai yayi magana, ta kalli hanyar benen Abba, kamar ta je ta gaishe shi, amma ta fasa ta san yadda ta makaran nan, sai ya zaunar da ita yayi mata faɗa, ga laifin jiya ga na yau, kuma ta san sai ya haɗa har da na waccan shekarar yayi mata, dan haka tayi wuf ta fice waje.
Duk irin vibration ɗin da wayarta take yi, ba ta ɗaga ba sai da ta zauna a cikin adaidaita sahu, sannan ta ɗaga kai wayar kunnenta.
“Wai Nabila wani irin wulaƙanci ne, nake ta kiranki ki ka ƙi ɗagawa?”
Nabila ta ce “Ke ban son tijara, kin wuce aiki ne?”
A fusace mai maganar ta ce “Ban sani ba”
Nabila ta yi dariya ta ce “Sorry masoyiyya, ki fito titi gani nan” tafiyar mintuna sha biyar suka yi, suka iske wata matashiyar budurwar a titi, sanye cikin doguwar rigar abaya, ta kama adaidaita sahun ta shiga tana hararar Nabila.
“Sorry sumy, kar ki fashe dan Allah”
“Wallahi kin fusata ni Nabila”
“Shiyasa na ce ki yi haƙuri ai, ya gidan ya su mama?”
Sumayya ta ce “Suna lafiya ƙalau, meyasamu fuskarki? Na ga kamar ƙuraje”
Nabila ta rausayar da kai ta ce “Ke bari, the whole me, jiya Abba ya saka na kwana a haraba, sauron nan na cikin flowers suka yi idi a kaina”
Sumayya ta waro ido ta ce “Wai da gaske?”
“Zan yi miki ƙarya ne? Wallahi dattijon nan ya ce wai na koma in da na fito ya rufe ƙofa. Aikuwa na din ga tsinewa amaryar nan, na baro ta a gidanta cikin nishaɗi da farinciki, ni kuma na afka tashin hankali, kamar ni degree holder, Abba ya rufewa gida. Yanzu dan Allah da a gidan mijina ne, da ba sai dai yayi masifar ya gama ba, babu wanda ya ji ya gani? Ai Abba ya tozarta ni jiya. Sai so ake a ga fuska a tuhume ni, ko ayi mini rashin mutunci a gidan nan, kin san gidanmu Allah ya wadata mu da munafukai, ni kuwa na haɗe rai”
Sumayya ta ce “Allah ya ƙara, ke uwar gwaninta, har da kai amarya, banda uban anko da ki ka yi mata. Ina mai tabattar miki ke da ganinta ta tako gidanku, sai wani ikon Allah”
Nabila ta ɗan yi shiru ta ce “Ku ma fa haka ne, kin san wani abu, ba hassada nake yi wa amira ta yi aure ba, amma kalli na fita kyau fa, na fita komai amma amira ta shige daga ciki, ohh ni Nabila, duk kyan nan da dirin nan yadda ki ka san na je na haye kan high table ɗin nan ayi da ni ranar dinner. Ba ma wannan ba duk wannan gayun da kwalliyar ban yi saurayi a bikin nan ba”
Sumayya ta ce “Ki je ki ɗorawa ranki jarabar son aure, ki ƙi focusing a kan career ki, ni ko a jikina na san lokaci ne, kuma tun da ba yawon iskanci nake ba, duk wadda ta yi mini gorin aure sai na ci ubanta, shekarun namu nawa ne duka da za a addaba mana”
Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce “Ba haka ba ne Sumayya, we have a different backgrounds, ke kin san me nake nufi, wallahi ƴanci nake so Sumayya, ko ta halin ƙaƙa”
Sumayya ta ce “Kar neman ƴanci ya kai ki ga halaka, duk ina samarin naki ne to?ba wanda zaki tsayar?”
Nabila ta yi tsaki ta ce “Bar matsiyata, daga ƴan wahala sai ƴan iska. Sai dai duk wanda ya zo hannuna sai na ci rabona ayi baran-baran. Na daina wahalar son mutum, daga ƙarshe yayi breaking heart ɗina, ya ci bulus. And also haryanzu ban samu spec ɗi na ba kin dai gane”
Sumayya ta ce “Au ke yanzu har wane zaɓe-zaɓe ki ke yi?”
Nabila ta ce “To ana raba mai rai da motsi ne? Iya wuya akwai abun da zuciya take so, kuma ni na fi son namiji mai kumari sosai. Irin wanda zaki ganshi ingarman namiji mai cikar zati. Beside fuskar namiji ba gemu, ai sunansa sumayya, ni kuma daga dattijai, sai marasa gemu, sai kuma ƴan wahala, ni matashi nake so, ba kuma yaro ba”
Sumayya ta ce “Au sunana ne ma abun kwatancen iya shegenki ko, to ki je dan kanki. Mai napep zan sauka a nan, za ta baka kuɗin”
Nabila ta ce “Ke uban waye ya ce miki ina da kuɗi?” Tuni Sumayya ta sauka, ta bar Nabila.
Nabila ta yi ƙwafa ta ce “Zamu haɗu ne, zaki ga wulaƙanci”.
***
A hankali yake buɗe jajayen idanunsa, a lokaci guda kuma yana lumshe su, tamkar mai shirin yin bacci. Sai mirgina kansa yake yi, yana sake lumshe manyan idanunsa da suka koma jajaye matuƙa.
Tamkar an jefo shi, haka ya faɗo ɗakin, yana rarraba ido.
A hankali ya ɗaga kai ya kalli wanda ya shigo ɗin, ya mayar da kansa ƙasa ya sunkuyar.
“Allah ya taimaki oga…” Bai amsa ba kawai ya buɗe tafin hannunsa ya miƙa masa.
Wata baƙar leda ya ciro, ya ɗora masa a hannun, sannan ya ce “Sai dai Oga ba a samu da yawa ba, ƴar kaɗan ce, cinnaku sun yi wa kasuwar ƙawanya, shiga da fitar kaya na bayar da wahala, da ƙyar na samu wannan wurin wani ɗan inyamura, ina ga wuri zan canza, saboda kamar ana son yi mini cune”.
Bai ce masa uffan ba, ya kwance ledar, ya fito da kwalin wata allura pack guda, mai ɗauke da ampoule na allura guda goma.
Sirinji lamba biyar ya ɗauka, ya din ga fasa alluran yana zuƙa, sai da ya cika sirinjin, sannan ya miƙe hannunsa.
Ya ɗaga kansa ya kalli matashin da ya kawo masa allurar, bai ce masa komai ba, matashin ya bar ɗakin.
Ya mayar da idonsa kan hannunsa, ya yana kallon jijiyoyin da suka kwanta ɗoɗar a ƙarƙashin fatarsa, suka yi ruɗu-ruɗu, manya da ƙanana.
Ya dubi guda ɗaya, ya huda ta da sirinjin hannunsa, ya fara bawa kansa allurar sannu a hankali. Sai da ya zuba ta duka, sannan ya yi jifa da sirinjin, ya sunkuyar da kansa ya na jiran Sakamakon hukuncin da ya ɗauka.
Sai dai kusan mintuna goma sha biyar, bai ji abun da yake so ba, sai wani irin nauyi da kansa ya ƙara, idonsa ya din ga yi masa yaji, ya rintse idanunsa amma bai ji alamar abun da yake so ba.
Abu kamar wasa kansa ya din ga wani irin sarawa, ƙirjinsa yana zafi. Ya dafe kansa da hannunsa bibbiyu yana jujjuyawa tare da rufe idanunsa.
Ihu ya fara yi iya ƙarfin sa yana taƙarƙrewa, yana girgiza kansa, saboda yadda yake jin kansa tamkar zai yi bindiga.
Da gudu suka shiga ɗakin, suka fara ƙoƙarin danne shi, amma ya yi ihu ya watsar da su baki ɗaya ya cigaba da kururuwa.
File Name | Karfe A Wuta… Hausa Novel Doc. |
Title | Karfe A Wuta Complete Novel |
Author | Ayshercool |
Group | Ai Hausa Novels |
Genre | Romantic Story |
Published Date | 01/11/2024 |
File Size | 270KB |
Format Size | TXT |
Book Price | 1000 |
Phone No | 08081012143 |
Download Karfe A Wuta Complete Novel By Ayshercool
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.