Description/Story:
Matar Damisa Book 1 Complete By Asmeetah
Description
Wata tsohuwar Mata ce zaune a bakin bishiya, ta jingina bayanta a jikin bishiyar tana shafa sumar kan Yarinyar dake kwance saman cinyarta,
Yarinyar bazata wuce 20yrs ba, tana kwance kamar mai yin bacci taji uwar tana shesshekar kuka! A firgice ta tashi zaune tana fadin “Uma lafiya kuwa, meya faru dake?”
Cikin kuka Tsohuwar tace “Ayush inaso ki tayani neman gafarar ubangiji, na tafka babban kuskure a rayuwata, inaji ajiki na zan mutu, Ayush! Zan mutu ba tareda na nemi yafiyar Junaid ba”
Lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka mai kashe zuciya
“Uma Dan Allah ki daina kukan nan banso, banso na rinka ganinki acikin wannan halin,
Shin wanene wannan JUNAID din? Sannan mai kika Aikata masa haka har kike fad’in munanan kalamai akanki saboda shi? Cikin zubda hawaye Ayush take fad’in “Uma idan baki furta mun abunda ke ranki ba taya Zan iya temaka miki da Addu’a bayan bansan laifin da kika Aikata ba”
Cikin takaici da cije la66e Umma take kallon Ayush wacce itama Ayush d’in kallon Umman take,
“Ayush! Na tsani kaina, kema idan kika ji labarina na tabbata zaki tsaneni ne, Zan gaya miki Amma kafin nan inaso ki yafe mun Dan Allah” tana kallon Ayush cikin tausayawa.
Da mamaki a fuskar Ayush cikin kasalalliyar murya tace “ni kuma Uma? Nasan bakiyi mun komai ba, duk abinda kikayi mun nasan aciki soyayya ne, bazaki iya cutar dani ba Mamana, saboda haka na yafe miki duniya da lahira”. Murmushin takaici Umma tayi murya a sha’ke tace “Ayush a yanzu rayuwata batada amfani, a shirye nake dana mutu, sai dai Ina mai tausaya miki idan na mutu bansan halin da zaki shiga ba, Ayushh banida en uwa banida kowa, mutane gudu na suke saboda ban aikata abu mai kyau ba, hakan yasa laifi na ya shafeki kowa kyamar mu yake,” kinga can ta nuna wani ‘Dakin Kara sannan ta cigaba da cewa “nasan kinsan cewa nan ne ‘Dakin mu na kwana, tin kina jaririya muke wannan dajin! Kinsha tambayata cewa Ina BABANKI, SU WAYE EN UWANKI amma na kasa baki amsarki saboda kada ki gujeni, amma yanzu a shirye nake dana fuskanci duk wani ‘Kalubale”
Taja dogon numfashi murya Ciki-ciki tace “AYUSH”
Cikin Sanyin murya ta amsa “Na’am Uma Ina sauraronki” fuskar nan duk ya jagalgale da hawaye ga yayi jawur abunka da farar mace.
Ta cigaba da cewa “Ina so naga kinyi Aure kin haihu, Ayush kina da kyakykyawar zuciya, kinada tausayi, Sam bana fatan ki d’auko kalar halina koda da qwayar zarrah, sannan banaso ki d’auko…
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
Read / Download Matar Damisa Book 1
Proceed with your download by clicking the below button👇👇