Hausa novels

Wani Gari Complete Document

Description/Story:

Wani Gari Complete Document!  Novel Document Written By Khadeeja Candy

 

Description

*⚜️ …WANI GARI… ⚜️*

1️⃣

Baya baya ta yi ta lankwasa kamar za ta fadi sai kuma ta yi gaba tare da cira kafarta ta dama sama kafar da ta sha ado da fararen yayan wuri ta buga a kasa cikin tabon lakar ruwan saman dake sauka, ta mika hannayenta duka biyu sama ta ware karan dake hannayenta ta buga su da karfi har sai da suka yi kara, sannan ta fara juya k’ugunta yayan wurin dake daure a kwankwasonta suka fara kara, a take maza da matan dake gurin suka hau tafi, masu ganguna irin na itace suna dukawa sai ta rufe ido tana taka rawar da ta zame musu ta al’adar wanda aka saba gabatarwa sau daya a kowace shekara.

Wata siririyar busar sarewar ce ta rika tashi a tsakanin mazanjen da ke buga gangunan kidan, a take kowa ya fara rausayar da kai domin busa ce dake saukar da natsuwa da annashuwa tare da nishadin zuciyar duk wani mai saurarenta, ciki kuwa har da Sarkin Garin Garuk da yan majalisun masarautarsa da kuma fadawansa. Busar sarewa ce da babu inda zaka taba jin ta a duniya sai a garin Garuk. Ko a cikin garin babu wanda ya iya sarrafa halshe da numfashi ya busa sarewar sai Waira da dan’uwanta Eid, busar sarewa ce da Eid ya kirkireta da tsananin karfin tsafin da babu wanda zai iya busar sai shi da kanwarsa Waira, ita ma kuma saboda ya amince mata ne, busar sarewa ce da ta zama haramun ga jama’ar garen su kwatanta kwaikwayonta ma balle har su gwada yi.

Busar sarewar ce, ke kara mata kuzari da karfin taka rawar da take, yadda take lankwasa da murza kugunta sai ka rantse da Allah babu ƙashi ko daya a jikinta, ruwan saman da ke sauka yana ta wanke datti da tsananin daudar dake jikinta, domin walki ne daure a kugunta sai wani katon ganyen data daura a kirjinta ya rufe breast dinta da a yanzu suke girma, a tsakanin guiwowyinta zuwa kafafuwanta a sake yake, haka ma cibiyarta a waje take, ta saki gashin kanta dake cinkushe ya kwanta har kusan mazaunanta, kunnuwanta na sanye da yan kunnen mai karamin kokon kan karamin tsuntsu kamar yadda wuyanta ma yake sanye da sarkar kokon kan maciji.

Ranar yau rana ce ta musamman ba ga jama’ar garin kadai ba, har ga yar sarkin masafa kuma jikar sarkin masafa na garin Garuk wato Waira.
Ranar yau rana ce da suka kadaice domin yin bikin abun bautarsu, da kuma bauta masa a tsawon ranar har zuwa lokacin gudanar da wannan rawar da Waira take takawa, a al’adar mutanen garin sau daya suke bautawa abun bautarsu a shekara, a ka’idar bikin ko wace shekara da kalar yarinyar da ake zaba a bata damar taka rawa a biki, a bana ma an zabi Waira kamar yadda aka zabe ta a bara, saboda kwarewar da ta yi da kuma yadda ta iya bin salon busar tana motsa jikinta kamar wata hawainiya.
A irin wannan ranar ce kadai Waira take wanka, a irin wannan ranar ce kadai take raba jikinta da duk wani datti da kazantar da suke daukar shekara suna rayuwa a jikinta, wato sau daya tal Waira take wanka a shekara!

Waira matashiyar yarinyar ce yar kimanin shekara goma sha hudu, ya daya tilo a gurin sarkin matsafa na garin Garuk, kuma jika daya tak a gurin sarkin matsafa na garin Garuk, kuma ya daya tak mai jiran gadon sarauniyar matsafa na garin Garuk.
Waira kyakkyawa ce sosai irin kyan da karya mace take ta yi mata duba daya ta kawar da kai balle kuma namiji, fara ce fol irin farin nan mai kyau da ba kasafai kake samunsa a jikin fararen mutane ba sai zababbu, tana da yalwar gashin kai da ya cumuimuye da datti saboda rashin son wanka da tsabta, duk da yake gashi ba abun alfahari ba ne a gurin yan matan garin Garuk domin duk wanda ka duba kanta zaka ganta da gashi daga manya har yara, tun daga kan mazan ma sai wanda ya ga dama ya aske, balle kuma mata da suke ado da shi. Waira kyakkyawar matashiyar budurwa ce mai tasowa, mai tsananin farin jini a tsakanin mata sa’ainta masu tasowa, sai dai tsoron dan’uwanta wato cousin dinta Eid ya hana maza da yawa kusantar inda take. An yi ittifaki kaf a tahirin garin ba a taba yin kazamar yarinya irin Waira ba, ba kazanta ta bangarem abinci ko abin sha ba, kazanta a gurin tsabtace jiki, sam sam sam Waira bata son abun da zai hada jikinta da ruwa da sunan wanka sai a dole, kamar saukar ruwan sama ko kuma a inda ya zama dole sai an shiga ruwa sannan a wuce ta wani gurin, hakan ya saka ta shar’antawa kanta wanka sau daya a shekara, wato kamar dai yadda ake gabatar da bikin abun bautarsu a shekara bayan gama bikin take zuwa ta yi wanka, wannan ya saka ranar ta kara muhimmanci a gareta da kuma duk wani masoyinta.

Waira ita kadai ce mahaifiyarta ta haifa, wanda za ta gaji mahaifinta kamar yadda mahaifinta ya gaji kakanta, wato sarautar tsafin iya yan gidan kawai suke gadonta sai kuma jininsu, a ka’idar sarautar ba a nadawa sai saurayi ko budurwar ya kai shekaru ashiri, wannan ya saka aka ajewa Waira kujerar har sai ta kai wadannan shekarun. Sai dai haka be hana a fara koya mata tsafi da yadda ake yinsa ba da kuma saka mata shi a jikinta domin al’ada ta mutanen garin kowa da kalar na sa tsafin sai dai na wani ya dara na wani kamar yadda bahaushe ya ce ko Baba da Babansa.
Jama’ar garin Garuk wadansu irin mutane ne da ba su yarda da duk wani abu na cigaban zamani ba, tun daga kan tufafinsu har zuwa abincinsu da kuma mu’amalarsu ta yau da gobe, ba sa hawan mota sai dabbobi, makwancinsu da ginakinsu duk irin na mutanen da ne, Garin Garuk wani babban birni ne da a kimiyance za a iya kira shi da jiha, domin babban gari ne mai cike da albarkar noma da ruwa da tautsuna da itatuwa, jama’ar garin ba su yarda dan garin ya kawo musu bako ba face da sanin sarki shi ma kuma ba bakon da zai zauna zaman dindindin ba, haka ma ba su yarda jininsu ya auro ko a aura daga garesu ba sai jininsu, wato ba sa auratayya a tsakanin wata kabila sai ta su. Haramun ne dan wani garin da ba na su ba ya ji yana kaunar jininsu ma, balle kuma jininsu ya kaunace wani da ba na su ba.
Sai dai sun amincewa jama’ar garin fita waje gari domin shakatawa ko yin wani abun. Sam ba su yarda da maita ba, sai dai tsafi ya zama kamar ruwan da suke rayuwa da shi.
Ba kowa ne yake sha’awar leka wajen garin Garuk duk kuwa da kasancewar Sarkin Garin ya yarje musu, ciki kuwa har da Waira da ko bakin kofar garin bata sha’awar zuwa a yanzu, tun bayan da sarkin garin ya saka a saukar da tsafi a jikinta, sai aka iyakance mata iya inda take iya tafiya sakamakon lura da suka yi da yawan yawon da take da shi a cikin garin da kuma hawan tsaunuka da bishiyoyi kamar biranya, ko wane kalar itace da tsauni ta san yadda zata sarrafa shi ta hau, an fada mata an kuma jaddada mata idan har ta kurkura ta bar garin Garuk ba zata taba iya dawowa ba, rashin dawowar kuma yana nufin rasa rayuwarta.
Wasu daga cikin jama’ar garin suna fahimtar yaren wasu garuruwan cikin kuwa har da dan’uwanta Eid sai dai Waira bata jin wani yare sai na Gurtuk wato yaren garin Garuk, sai dai tana da karfin basirar fahimtar maganar mutane ko da kuwa bata jin yaren, kana tana da tsananin tsafin sanin abun da ya faru da mutum ko dabba a rayuwarsa ta baya, Waira yarinya ce mai tsananin shiga rai, hakan ya saka take da farin jini a gari, hakan kuma ya kara dankon zumunci da shakuwa a tsakaninta da dan’uwanta wato dan kanen mahaifiyarta Eid.
Eid handsome guy ne mai jini a jika, matashin da yalwar gashin kai ta kara masa kyau domin ya kan daure gashinsa ko ya sake shi kamar dai yadda mata suke yi, fari ne sai dai ba irin farin Waira ba domin ita ta fita dabam duk da kasancewar datti da daudar dake jikinta ya hana farin fatar nata haskawa da kyau, garuruwan da Eid be taba ziyarta ba a Nigeria kadan ne, domin ya kan fita garin Garuk yayi nisan zango ya bawa idanuwansa abinci sannan ya dawo.
Wani abu mai kama da wabi kakan Waira mahaifinta kadai ya haifa haka ita ma mahaifinta ita kadai ya haifa, dukansu sun mutu ne bayan samun magaji kamar yadda ita ma zata iya mutuwa bayan samun na ta magajin, ba al’adar tsafin ce a haka ba, al’adar zuri’ar da Waira ta fito ne a haka.

 

 

File Name  Wani Gari Hausa Novel Doc.
Title   Wani Gari
Author    Khadija Candy
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    24/10/2024
File Size    1.38mb
Format Size    TXT
Book Price
Phone No
Download Wani Gari Complete Novel Document By Khadija Candy

Click the below green button to read the novel online

READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button