Karfe A Wuta Chapter 29 By Ayshercool
Da kallo suka bi jauhar, ganin yadda take yi musu kuka wiwi, wani gandiroba ya ce “Koma tsallake, idan ki ka gama kukan, sai ki tafi”.Ta juya ta kama hanyar tafiya, tana ji a ranta kamar duk duniya, babu wanda ya kaita rashin sa’a.Sannu a hankali yake tunkaro gate ɗin fitowar, zuciyarsa cike da mamakin yadda aka sake shi, dan bai san ma zai fita ba, sai yau ɗin.Tsayawa yayi bayan ya fito daga cikin gate ɗin, ya lumshe idanunsa sakamakon hasken ranar da ya ji ya yi wa idanuwansa yawa, sannu a hankali ya cigaba da buɗe su, har ya ji hasken yayi dai dai da abun da idon nasa yake buƙata.Kamar an kira sunanta ta waiwayo, ta hangoshi a tsaye, shi ma ita yake kallo da mamaki, ba ƙaramin kashedi ya yi wa su liti ba, a kan kar su kuma ɗaukarta su kaita in da yake.Da sauri ta nufo shi, ta kasa tsayar da hawayenta ta na wata irin ajiyar zuciya ta ce “Har na ji daɗi, da suka ce mini, ba za su sake ka yau ba”Yayi shiru yana kallon ta.Ƙare masa kallo take yi, an yi masa aski an aske masa sajensa da gemunsa, sai ɗan kaɗan da ya fara fitowa, idanunsa sun washe yayi haske, saboda babu kayan shaye-shaye a nan, sai dai ya rame sosai.Kallonta kawai yake yi, kamar wata baƙuwar halitta, sai dai bai yi mata magana ba.Tayi ajiyar zuciya ta ce “Mu tafi?” Ya jinjina mata kai yayi gaba.Ta ɗaga ƙafarta kenan takalminta ya tsinke, ta durƙusa ta cire takalmin ta ce “Takalmina ya tsinke” ya kalli ƙafarta sannan ya dubeta, ƙafarta busu-busu, duk yadda ya santa da gayu, ko ba ta gaya masa ba, ya san tafiyar ƙafa ta yi.Ta tsayar musu da abun hawa suka hau, sai dai har suka je in da za su sauka, duk surutun da take yi, ko sau ɗaya bai tanka mata ba.A titi suka sauka, saboda kuɗin motar ba zai isa a shiga da su har ƙofar layin ba, har ta yi gaba, ya janyota ya cire mata takalmansa ba tare da ya ce komai ba.Ta ce “A’a ka saka kar ka taka wani abun”.Kallon da yayi mata, ya sanya ta yin shiru, ta saka takalman kamar zata tashi sama a kansu suka shiga layinsu, kamar ta taka rawa, master ya fito.A falo ya zauna, ya kashingiɗa ya lumshe idanunsa, ta shiga banɗakinsa, ta haɗa masa ruwa mai zafi, ta ce “Master ga ruwan wanka na kai maka” bai yi mata musu ba, ya tashi ya tafi, kafin ya fito ta jera abinci a falo, ya yi wankan ya fito falo, ya tarar da abinci, yanayin yadda yake cin abincin ya tabattar mata da yana jin yunwa sosai duk da dama can acici ne.Yana so yayi mata magana, amma ya rasa me zai ce mata ma, ya gama ci ya tafi ɗakinsa ya kwanta, dan surutunta ya fara takura shi, duk da yayi kewar abubuwa da yawa a tare da ita, sai dai yadda yake jin zuciyarsa a cunkushe babu daɗi, ya sanya shi jin surutunta ya gundure shi.Allah ya taimaketa, ya wuni a ɗaki, bai fita ko ina ba, tun da ya dawo.Hafsa kuwa ta samu abun yi, dan tun da Allah ya sa ta mallaki lambar wayar Alhaji mu’azzam, take kiransa a waya, da sunan rarrashin sa a kan rashin jauhar, tare da ƙoƙarin sake ɓata jauhar ɗin a wurinsa.Mahaifiyarta ta sake miƙewa wurin shige-shige a kan Allah ya tabattar da lamarin aure tsakanin hafsa da Alhaji mu’azzam.Cikin ikon Allah, idan ta kira shi, yana amsawa ba ya yi mata wulaƙanci ko makamancin haka, hakan ya sa ta cigaba da ƙoƙarin cusa kanta cikin hikima da kissa.Sannan suka yi ƙoƙarin rufe wa mama duk wani abu da yake faruwa, ba ta san halin da ake ciki ba.Kasancewar Al’amin ya fito ya dawo gida, ya sanya jauhar yin isashshen baccin da rabonta da shi, tun kan a rufe shi, dan bayan sallar asuba da ta kwanta, ba ta farka ba sai goma saura.Ta fito tsakar gida da sauri, ta fara aikace-aikace, ta dafa tea ta soya dankalin hausa.Ta dafawa Al’amin ruwa a heater, ta je ƙofar ɗakin ta tsaya tana sallama.Ƙasa-ƙasa ya amsa, ban da yana da buɗaɗɗiyar murya ma ba za ta ji ba, ta shiga tana sake yin wata ta ce “Ina kwana master” “Lafiya ƙalau””Ban san ka tashi ba, yau na makara da na fara kawo maka ruwan wankan ai, bari na haɗa maka” ta haɗa masa, yanzu ma bai yi musun yin wankan ba, ya tashi ya shiga banɗakin.Ɗakin fes yake, amma ta din da karkaɗe karkaɗe, da goge-goge, ta kunna turaren wuta, ta fito masa da kaya ta saka musu turare.Ya gama ya fito, jikinsa yana ɗigar da ruwan wanka, ya ɗauki dogon wando ya saka, ya zube mata wanda ya cire a kan katifa ya fito.Kallo ɗaya tayi masa ta kawar da kanta gefe ta ce “Ba ka saka rigar ba, na fito maka da ita ma”.”Ba na buƙata, wandon ya isheni”.Jauhar ta ce “To ai kar ayi sallama, a ganka a haka”.”Ki koma ɗaki idan ba zaki iya kallona a haka ba” yayi maganar yana zama.Ya kalleta ita ma yau ba hijjabi a jikinta, doguwar rigar material ta saka, mamaki yake yi, yadda ta yi duhu, ga wani uban ƙashin wuya da ya fito mata, tayi rama sosai da sosai, ashe jiya dan ya ganta a cikin hijjabi ne ya sanya bai gane ba, sai ya ji ransa babu daɗi.Ta haɗa masa abincin ta miƙa masa, ya ɗauka zai kai baki ta ce “Bisimillah” a zuciyarsa ya maimaita sannan ya fara ci.”Askin nan da aka yi maka, ka yi kyau, sai dai ban so aka aske gemun ba gaba ɗaya”Idan ba gizo idanunta suka so yi mata ba, da murmushi zai yi ya shanye abun sa.Ta tanƙwashe ƙafarta ta sake cewa “Sannu master, a prison ɗin ma duka ake yi, na ga bayanka duk shaidar duka. Wallahi ba zan taɓa yafewa wanda suka yi maka sharri ba, ban taɓa shiga tashin hankalin da na shiga ba, na san baka ta’mali da wannan abar, sauran ma zaka daina wataran in sha Allah” tayi maganar hawaye na cika mata ido.”Kun kusa gama exams ko?”Jin yayi magana ya sanya ta saurin ce wa “Eh, cikin azumi zamu gama in sha Allah””Allah ya taimaka””Amin na gode, baka tambayeni kwaɗinka da ƙadangaru ba?”Ya rausayar da kai ya ce “Ai naki ne ba nawa ba” hakan yayi da kammala cin abincin.Ta ce “Alhamdilillahilazi aɗa’amana haza, warazaƙatana min gairi haulin minni wala ƙuwwa, Ubangiji Allah ya ciyar da mu na anjima” tayi maganar tana tattare kwanukan.Kafin ta dawo ya ɗauki pillown kujera ya kwanta.Ta je gabansa, ta durƙusa ta kai hannunta goshinsa ta ce “Wai haryanzu kana zazzaɓin ne?”Ya girgiza kai alamar a’a.”Master duk ka yi wani iri kamar an canza mini kai” duk lokacin da ta danganta shi da ita, sai ya ji wani abu a ransa da bai san Menene ba.Yana daga kwance ya din ga miƙa, yana ɗan banƙare kafaɗunsa zuwa bayansa.”Ciwo bayanka yake yi ne?”Ya gyaɗa mata kai alamar eh.”Bari na ɗaukko man zafi na shafa maka zaka ji daɗi, naga wani raunin bai gama warkewa ba”. Ya jinjina mata kai, sai dai bai buɗe idonsa ba.Ta je ta ɗauko man, ta dawo ta zauna a bayansa, tana shafa masa a hankali.Ta ce “Juyo” ya gyara kwanciyar sa a hankali, jikinsa wasu wuraren duk shaidar yankan wuƙa, bayan tabon duka.Haka kurum zuciyarta ke raya mata, kai hannu kan gashin da yake kwance a ƙirjinsa, da sauri ta rintse idanunta ta kawar da wannan tunanin ta kira sunansa.”Master””Mmm?” Ya amsa idonsa a rufe.Ta ce “Ka na jina?””Mmm”A ɗan shagwaɓe ta ce “To ka kalle ni, magana zamu yi fa”Ya buɗe idanunsa a kanta, take ta sunkuyar da kanta, saboda wani irin nauyi da kwarjinin da idanun nasa suka yi mata, a tunaninta ta daina jin tsoron sa, ashe haryanzu da sauran rina a kaba, yayi mata shiru yana kallonta yana jiran tayi maganar, sai dai ta kasa.Gaba ɗaya sai ta diririce, ta kasa maganar sai cigaba da shafa masa man zafi a wuri ɗaya a kafaɗarsa.Hannunsa ya saka ya cire nata, ya karɓi man zafin ya ajiye, ya ce “Ya aka yi?””Dama sonake na ce dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mini, na yi sanadiyar shigarka wahala, duk laifina ne da ban gaya maka an kawo maka saƙo ba, ka yi haƙuri mantawa na yi ka yafe mini dan Allah””Idan naƙi fa” yayi maganar very serious.Cikin damuwa ta ce “Please dan Allah ka yi haƙuri””Zan duba, ki je ki yi karatunki saboda exams” ta jinjina kai ta tashi, tsakar gida ta fita ta hau wanke-wanke, ta ɗaukko kayansa da ya cire, da wanda ya dawo da su daga prison, ta jiƙa su dan ta wanke.Wasila maƙwabciyarta ce tayi sallama, kasancewar ƙofar ba a rufe take ba, jauhar ta ce “Anty wasila sannu da zuwa ga kujera””Yauwwa jauhara, ashe mai house ya dawo, jiya na ji halimatu ta ce ta ganku, na zata sharrinta ne ma, na zo ɗazu tun takwas da rabi, na yi ta bugu baki buɗe ba na ce bari na tafi, su jauhar ana can jikin miji an liƙe ba a tashi ba”Jauhar kawai ta yi murmushi tana fatan Allah ya sa bai jiyo ba, tun da yana falo a kwance.Ta ce “Jiyan ya fito, ban samu na shigo na gaya muku ba ke da maman halimatu”.”Allah sarki jauhar, kin sha wahala shikenan kuka ya ƙare, ki daina anty wasila ba ki san me nake ji ba, zuciyata kamar ciwo take, Allah dai ya bar wannan ƙauna, zuciyar ya daina ciwo ko?”Dariya kawai jauhar take yi ta ce “Ta daina””To ai da kamata yayi, da ki ka san zai fito, ki yi magana ayi gyare-gyare a gyara masa turaka, ki zo na baki kayan maman nihal Anty maryam, na sanmiki kayanta ki gwada ki ji, ai ba kya yi shiru ki zauna haka ba” (Ga mai buƙatar jarraba kayan maman neehal sai ya tuntuɓeta ta wannan lambar 0706 677 4630).Wasila ta din ga sakin layi, sai da jauhar ta ce “Anty wasila yana nan fa, yana falo yana jinki”Tayi ƙasa da muryarta ta ce “Na shiga uku, kuma ki ka bar ni nake ta zuba, amma baki kyauta mini ba”.Ta durƙusa ta kwashi takalmanta cikin sanɗa, ta fice, jauhar ta din ga dariya, ta rufe ƙofarta, sai dai ita ma shiga falon ya gagareta, saboda kunyar abun da wasila ta din ga faɗa, dan ta san halinsa, sai ta sakankance, bacci yake yi, ta ga idonsa biyu.Ta jima tana raɓe-raɓe kafin ta shiga ɗakin, baccinsa yake yi, sosai take jin tausayinsa, yanayin yadda yake miƙa ma, kawai ya tabbatar mata da zaman gidan kaso bai yi masa daɗi ba.Tana ta dirzar kayansa, ta ji an yi wani irin fito a waje, sannan aka buga mata gate, ta saka hijjabi ta buɗe ta ga su walid.Ta ce “Yaya walid, ina wuni””Madam dama mutumin nan ya fito baki sanar mana ba? Sai yaran da muka saka gadinki ne suka faɗa mana”.”Dan Allah ku yi haƙuri, na san zai neme ku, bacci yake yi ne”.Liti ya ce “Ko dai ki ka ɓoye shi ki ka hana shi fitowa”Ta ce “A’a na isa? Ban hana shi fitowa ba, ina dai roƙon Allah ku bar mini shi, na san dole dai zai zo in da ku ke”.Walid ya sake wani irin fito, tana waiwayawa ta ga har ya zira riga ya fito.Saroro ta yi ta tsaya tana kallon sa, ya ƙaraso, zai raɓata ya wuce.Jiki a sanyaye ta ce “Fita zaka yi? Ban gama ganinka ba fa”Kallonta ya yi, ya raɓa zai wuce ta ce “Dan Allah Master kar ka sha komai, ko ka je in da ake aikata laifi, dan Allah” maganar da tayi, har hawaye ya cika mata ido.Bai kulata ba ya fita, gaba ɗaya sai ta ji garin yayi mata babu daɗi, duk da tana cikin shauƙi, da farincikin dawowarsa.Tana jin shewar su walid, da suka ganshi, ta ja jikinta, ta koma ɗaki, aikin ma ta kasa cigaba, kawai ta saka kuka, kasancewar shi ne kaɗai abun da take yi, ta rage damuwarta, sai kuma tsananta ambaton Allah.Tun wannan fitar da yayi, tun tana saka ran dawowarsa, har ta cire rai, dan har magariba ba ta kuma saka shi a idonta ba.Tayi ta addu’a a ranta, Allah ya sa yana lafiya.Har bayan goma na dare, ta kasa kwanciya, sai sha ɗaya da wani abu, ta ji yana rufe ƙofa, ta fito falo da sauri, ya shigo yana haska fitilar wayarsa, gaba ɗaya falon ya gauraye da warin wiwin da yake yi, jikinta yayi sanyi ta kasa yi masa magana, yadda yake tafiya ya tabattar mata da a buge yake, ya wuce ta ya tafi ɗakinsa.Ta nemi wuri ta zauna a wurin, ta haɗa kai da gwiwa, ta din ga kuka ƙasa-ƙasa, ta tashi ta nufi ƙofar ɗakinsa ta leƙa, ɗakin duhu, sai dai tana hango hasken wutar jikin sigarinsa, ta juya ta koma ɗakinta, ta ji tana neman sarewa, kamar Allah ba zai karɓi addu’arta a kan sa ba, da sauri ta din ga istigfari, ta nemi wuri ta kwanta.Da safe da ta tashi, ba ta ko nufi ƙofar ɗakinsa ba, sai da ya fito ya tarar da ita a falo, tana shirin dutse.Cikin girmamawa ta ce “Ina kwana””Lafiya ƙalau” ya zauna a kan doguwar kujera, ta ce “Afuwan kar ka ga ban kawo komai ba, wallahi ba kuɗi a hannuna ban girka komai ba”Bai yi magana ba, sai kamar bayan mintuna goma, ya ɗauki wayarsa ya ɗan danna ya saka a kunnensa. “Kawo mini bredi da lipton, kayan tea dai na dubu biyu, kawo mini gida ka karɓi kuɗin”. Ya ajiye wayar.Jin wayar da ya yi ya sanya ta tashi ta ɗora tea, kasancewar da wuta ta ɗora a heater.Tana cikin kwashe tea ɗin, ya fito ya je ya karɓo kayan shayin, ya ajiye mata a ƙofar kitchen.Ta ce “To, Allah ya saka da alkhairi”Ta ɗauka ta dudduba, da yabi ta ita, iya buredi da sugan ya isa, sauran kuɗin ko taliya sa saya, ta ɗauka ta soya ƙwan, ta kawo kayan karin.Shikaɗai ta haɗawa ta koma gefe, ta cigaba da shirinta.”Wannan shirirtar ta fi ki karya kumallo?”Ta girgiza kai ta ce “Ba na jin yunwa ne, zan karya amma”.Gaba ɗaya ba ta walwala, duk surutun nan ma da take yi masa, yau bakinta shiru, ta kunna mp ɗin ta, ta ajiye a gefe, tana saurar radio, ana ta zancen za a tafi yajin aiki, saboda tsadar rayuwa da rashin ingantacciyar rayuwa ga ma’aikata.”Amm Angela ki ke ko?”Tayi murmushi ta ce “Ko ‘yar madara ba” tayi maganar cikin ƙoƙarin ɓoye damuwar da take ciki.”Koma dai wanne ne, magana ce da ni”Ta ce “To” ta ajiye kayan abun da take yi, ta fuskance shi, amma ba ta yadda sun haɗa ido ba.”Kalleni, idan ina magana na fi son ki kalleni, ki daina sunkuyar da kai”Kallo ɗaya tayi masa ta sake sunkuyar da kai ta ce “Ba zan iya ba ne, wani abu nake gani a cikin idon naka da yake bani tsoro””Kin kusa daina gani, wata shawara na yanke a kan zamanmu, ni wannan yawan koke-koken da ki ke yi, da wahalar da ki ke sha ba na so, jin sa nake yi kamar wani nauyi a kaina, kuma ni gaskiya ba zan iya daina wasu abubuwan ba, ina saka ki a damuwa da matsala sosai, ga rayuwar ki a cikin hatsari, duk saboda ni. Kina takura rayuwata sosai da sosai, nima kuma ma san ina takura ki dan haka na yanke shawarar kawai na sauwwaƙe miki, ki koma gida Allah ya baki wani mijin ki yi aure, ni ba na buƙatar mace a cikin rayuwata”.Tun da ya fara maganar, ta ji kamar an jona mata shocking, zuciyarta ta din ga bugawa da wani irin sauri, ta rasa me ma za ta ce.Sai da ya kammala tsaf, sannan cikin ƙarfin hali ta kalleshi ta kawar da mai ta ce “Wannan ne tukuicina kenan? Baka buƙatar mace a rayuwarka, nima ƙaddara ce ta kawo ni in da ka ke, na zata idan na jure na cigaba da yi wa baba biyayya, na yi biyayyar aure, komai zai wuce, zan ci riba, amma yanzu na fuskanci ni ce mara sa’ar, ko ina ba a buƙata ta, yanzu tozarta maraicina shi ne ka ga ya dace da ni, har ya sanya ka ce ba zaka yafe mini ba jiya? shikenan ka bani a rubuce na kai wa baban, na gode master, amma duniya da ba a yafiya da mu zo i yanzu ba, na san nayi maka kuskure amma na baka haƙuri, amma ka sani idan ka sake ni, ka tozarta maraici” ji tayi numfashinta ya yi wa ƙirjinta nauyi, kawai ta tashi jikinta na rawa.Tsananin fargaba da tashin hankalin maganar da ya gaya mata, ya sanya period ya zo mata ba shiri, har jikinta ya ɓaci, dama sauran kwana ɗaya ya zo.Har tayi maganar ta gama, ba ta kalleshi ba ko sau ɗaya.A ransa ya din ga maimaita ;idan ka sake ni, ka tozarta maraicina. Ita a tunaninta abun da ya faru ne ya sanya ya ce zai rabu da ita? Marainiya ce kenan? Ya tambayi kansa a lokaci ɗaya ya bawa kansa amsa da no wonder.Sai kuma jikinsa yayi sanyi, shi wannan wahalar da take sha, ya ɗauka za ta yi murna da abun da ya ce, kawai ya basar ya kwanta.Sosai ta din ga kuka, a ɗakinta, tana tunanin wane irin baƙin jini ne da ita haka? Duk yadda take haƙuri tana lallaɓa auren nan, amma ya yi mata wannan sakayyar, take ta fara tunanin wane irin zama zata koma ta yi a wannan gidan na su, da suke nuna mata ƙiyayyarsu a fili?Da ƙyar ta shiga banɗaki ta gyara jikinta, ta fito zauna a ƙasa ta cigaba da kuka.Bayan ya gama abun da yake yi, ya fice ya bar gidan.Kanta ne ya fara ciwo, ga numfashinta da yake ta barazanar ɗaukewa, ga wani irin azababben ciwon mara da yazo mata da zazzaɓi duk a sanadin tashin hankalin maganganun Al’amin.Yaya saifu kuwa tun da ya dinga bibiya, aka tabattar masa da an saki Al’amin, hankalinsa ya kwanta, ya so ya je gidan nata ya tabattar amma har ga Allah ba ya ƙaunar shi, duk da sau ɗaya ya taɓa ganinsa, ranar ɗaurin auren a masallaci, kawai a jikinsa yake jin azabatar da jauhar yake yi, dan ba zata faɗa bane kawai.Al’amin kuwa, su walid suna ta hirar irin tashin hankalin da matarsa ta shiga, da aka kai shi prison, da irin aiken da ta din ga yi masa da kayan amfani yana prison.Gaba daya sai ya tafi lissafin yanzu idan ya saketa, to abinci fa? Amma shi duk da haka gani yake hakan ne mafita, wannan tashin hankalin da take shiga idan ya shiga cakwakiya, sai ya ga kamar yana shiga hakkinta da yawa, kuma a idonta yake ganin damuwa idan ta ganshi a halin maye.Da daddare da ya dawo, yadda ya fita ya bar kayan karin kumallo, haka ya dawo ya tarar da su, ba ta taɓa ba, sai yayi tunanin ko wani abun ta ci, dan haka ya ƙarasa hallake buredin da ƙwan, ya shige ɗakinsa ya cigaba da busa hayaƙi cikin nishaɗi.Washegari ya din ga zaman jira, ya ga ta fito ta yi abun karyawa, amma shiru, gashi bayan sallar asuba ya yi shaye-shaye dan haka yunwa yake ji sosai.Ganin har sha ɗaya ba ta fito ba, ya sanya ya fice, sai dai kuma yajin aiki ake yi, da ƙafarsa ya tafi unguwar su, wurin su Walid.Yau ko tsintsiya jauhar bata ɗauka ba, tana ta fama da kanta, da la’asar ya dawo, ya sake tarar da gidan yadda ya bar shi.Gaba ɗaya sai gidan yayi masa wani iri, ya kwashe kwanukan da ya karya da su jiya, ya fara tunanin ko fushi tayi, shi ne ya sanya taƙi yin shara a gidan.Yana tsaye yana kallon falon, ya ɗaga kai ya ga ta fito daga ɗakinta, kamar fuskarta ta kumbura.Ya tsaya yana kallonta, ya ga tana ɗaga ƙafa da kyar a hankali.Kawai ta yanke jiki ta faɗi a wurin, a sukwane ya yo kanta, ya ɗagata.ta motsa da ƙyar, hannu ya saka ya juyota jikinsa sosai, wani irin hucin zafi jikinta yake fitarwa, ta ɗaga idonta da ƙyar ta kalle shi, idanunta sun yi ja sosai da sosai ta mayar da su ta lumshe.Hankali tashe ya ce “Menene?””Kaina ne zai fashe” tayi maganar hawaye na bin gefen fuskarta, kafin yayi magana, jikinta ya hau karkarwa, haƙoranta na karo da juna, idonta na neman juyewa saboda zafin zazzaɓi da matsanancin ciwon kai.Ɗagota yayi sosai ya ce “Ki na ji na?” Ta ɗaga masa kai da ƙyar.”Zan je in samo abun hawa, mu je asibiti””Yajin aiki ake yi, ka manta?” tayi maganar a galabaice.Sai yanzu ya tuna, dan da ƙafa ya je yawonsa ya dawo, ƙungiyar ƙwadago na jagorantar yajin aiki da kuma zanga-zanga domin janyo hankalin gwamnati a kan wasu haƙƙoƙin ‘yan ƙasa.”Na sani, yanzu zan dawo” Ba tare da ya san in da zai nufa ba, ya kwantar da ita kawai ya fita, a ransa yake jin idan ya bar yarinyar nan da ciwo, bai yi wa kansa adalci ba.A titin unguwar, ya ga wani ɗan adaidaita sahu, ya tsayar da shi ya ce “Malam mara lafiya zaka ɗaukar mini”Mai baburin ya ce “A’a yi haƙuri ba aiki na fito ba, ba ka san ana yajin aiki ba ne maigida?””Ana yajin aikin amma ka fito da babur?””Eh na yi wani uzuri ne, gida zan koma”.A ɗan hasale ya ce “Mara lafiya zaka ɗaukar mini”Shi ma a hasale mai baburin ya ce “Na ce ba zani ba, ana dole ne? Ka nemi wani mana”A fusace ya daki tayar gaban adaidaita sahun, mai napep ya waro ido ya ce “Malam meye haka?”Kawai ya shiga bayan adaidaita sahun, ya zare wuƙa ya ce “Bi cikin layin nan, ko na zaro hanjinka yanzun nan da russia” tsit mai ɗan sahun yayi, ya bi layin tare da yin sarandar ƙwace masa baburin ma zai yi.A ƙofar gidan ya saka shi yayi parking, ya sauka ya ƙwace mukullin babur ɗin, ya shiga cikin gidan da shi.Ya ɗauko hijjabinta ya saka mata.”Master”Ya kalleta ba tare da ya amsa ba, ta ce “Yi haƙuri, na saka wahala””Ki yi mini shiru”Ta ce “To” ya ɗaukkota kamar matacciya, ya shiga da ita napep ɗin.Ya ciro mukullin ya miƙa wa mai baburin ya karɓa yana cunkusa fuska ya ce “Megida amma ka san yajin aiki ake yi, ina zan kai ku? asibitin gwamnati babu aiki”.Al’amin ya ce “Ko ma wane asibitin ne mu je”Kamar wata ‘yar kyanwa, haka ta kwanta luf a jikinsa, da suka hau kwalta, sai sanyin da take ji ya ƙaru, dan haka ta ƙara shigewa jikinsa, jikinta na ta rawa.Wani Asibitin kuɗi ya kai su a gadon ƙaya, Al’amin ya cilla masa dubu ɗaya, ya rungumi jauhar ya shiga da ita.Ba a taɓa ta ba, sai da ya biya kuɗin file da komai, sannan aka fara yi mata abun da yakamata.suka shiga wurin likita, aka tambayi sunanta, ya manta surname ɗin ta da ya gani a invitation ɗin su, dan haka ya ce a saka mata Zahra Al’amin, shekaru ya ce bai sani ba, sai kintata akayi, aka tura su yin gwaje-gwaje.Bayan sun dawo,ikitan da ya duba ta, yayi ta mita malaria tayi mata mummunan kamu, ga ulcer kuma ga jininta ya hau.Al’amin ya ce “Malam ba lissafi ko masifa zaka yi mini ba, ayi mata abun da yakamata kawai” yanayin yadda yayi maganar, ya sanya likitan gane waye shi.Sai dai Al’amin yayi mamakin jin an ce jininta ya hau.Likitan ya ce “Tana da aure ne?”.”Eh”Likitan ya ce “Ayi gwajin ciki, kar mu yi treatment da ka”.Al’amin ya ce “Babu ciki”Likitan yayi saroro yana kallonsa.”Malam ni ne mijinta, babu wani ciki, ka yi sauri a fara yi mata abun da yakamata, tana ta murƙususun ciwo. Ko ba ka yadda ba? Al’ada take yi, ko kuna ganin cikin kwana ɗaya ne ko biyu?”Likitan ya ce “Ikon Allah”Jauhar duk da tana fama da kanta, wata irin kunya ta rufeta, ya aka yi ya san tana period ma.Tana ta yinƙurin amai, sai dai babu komai a cikinta, aka ce ya samo mata wani abun ta ci, kafin a fara treatment.Ya fita ya sayo uwar gurasa mai nama, da ruwa ya kawo mata.Ya zo ya tarar, an saka mata ruwa, da allurai.Ya kalli fuskarta, bacci take yi sosai, tana iya ƙoƙarin ta a kan sauro, kar ya cije ta, ba ita ba har shi, da magariba ta yi za ta hau rufe ko ina tana kunna maganin sauro.Abun da bai sani ba, tsananin damuwar da ta shiga bayan kama shi, da maganganun da ya gaya mata jiya ne suka haifar mata da ciwon.Sai dai babbar damuwarsa, hawan jinin da aka ambata.Sai wajejen magariba, ta ɗan samu afuwa.Wajen isha’i aka sallame su, suka yi mata wasu allauran, aka ce masa maza ya kaita gida, alluran suna kashe jiki.Duk kuɗin jikinsa sai da suka ƙare, suna fitowa harabar asibitin, jikinta ya saki ta tafi zata faɗi, ya riƙeta da ƙyar suka fita, sai dai gaba ɗaya titin babu ababen hawa.Ganin sai tangaɗi take yi, kuma bashi da wata dabara ya sanya, ya ɗaure ledar magungunan ta, ya ɗaga ta ya saɓa a bayansa, ya ɗauki takalmanta ya riƙe a hannunsa, ya zagaya ya bi lunguna.A din ga yi ana sauke hakki, idan baki saya ba 0009450228 Aisha Adam jaiz bank Ayshercool 08081012143
