Novel Document

Amaryar Zayyad Novel Document

Description/Story:

Amaryar Zayyad! Novel Document

Written By Rahma Kabir

 

Description Of Amaryar Zayyad Novel Document

Ƙagaggen labari ne, in kinga yayi iri ɗaya da labarinki ko wata ‘yar uwarki to arashi ne, amma banyi ko dan kowa ba sai dan in isar da saƙo da faɗakarwa cikin nishaɗi.

 

Gargaɗi

Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin ko kuma satar fasaha, ko a mayar mini da shi Audio a ɗaura min shi a wata kafa na media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, ban hanaku ɗaura labarina ba amma a barmin sunana tare da barin rubutuna yadda yake, da fatan za a kiyaye

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 

ZAINAB (Safna).

 

Tunda aurenta ya gabato ta samu kanta cikin yanayi na fargaba da tunanin abinda zai je ya dawo, samakon faruwar wasu al’amura a shekarun baya da suka gabata. A lokacin da aka saka ranar aurenta da Sadiq biki ya rage saura kwana goma Allah yayi masa rasuwa, Safna ta samu kanta cikin mawuyacin halin da ba zata iya misaltashi ba, da kyar aka samu kanta dalilin tsananta addu’a da mayar da lamuranta ga Allah, a haka har ta samu ta dawo dai dai ta dangana tare da karɓan ƙaddarar ta. Bayan wani lokaci ta kuma haɗuwa da Lukman tun tana ƙin bashi dama har ta sake masa suka fara soyayya, cikin ƙanƙanin lokaci suka shaƙu daga bisani kuma ya turo manyansa aka fara maganar aure, an kawo sadaki da komai na aure saka rana ya rage wanda iyayensa ne suka ce a basu lokaci su gama shiri kan a saka, kwatsam Lukman da kanshi yazo yace ya fasa aurenta sannan ya yace ya yafe komai da suka kawo, Safna a lokacin kamar zata yi hauka domin ta kamu da tsananin son Lukman fiye da yadda taso Sadiq, babban tashin hankalinta yadda yaƙi faɗar meye dalilin janyewarsa. Safna gata da kyau, ilimi, nasaba, natsuwa da tarbiyya bata da makusa amma kuma ƙaddararta yana ga aure, da kyar ta iya haƙuri da rashin Lukman wanda har hakan yaso jefata cikin wani hali, ta kusa kamuwa da ciwon zuciya, ga hawan jini ya yayi mata dirar mikiya da ƙanƙanin shekarunta, ga rashin barci da ciwon ulcer da yayi mata mummunar kamu saboda rashin cin abinci, haka suka dinga zaryar asibiti da kyar aka samu aka shawo kanta ta dangana, tun daga wannan lokacin ta haƙura da zancen soyayya bata kula kowa duk nacin mutum sai dai yayi haƙuri ya rabu da ita, gata da farin jinin samari amma haka ta shafe shawon shekara biyu bata saurarensu.

 

Wani lokaci da yayarta Anty Maryam ta haihuwa a taron sunanta, sai rikici ya ɓarke a tsakanin dangin mijinta da danginta wanda hakan ya jawo tashin hankali har aljanu suka dinga zubar da mata a ƙasa, ciki har da Safna ta zube numfashinta ya ɗauke tamkar babu rai, hankula sun tashi sosai dan kyar aka shawo kan matsalar, amma ita Safna sai da ta kwana biyu a sanƙare bata san inda kanta yake ba anata aikin ruƙiyya da hayaƙi, a hakane har aka samu aljanin yayi magana wanda ya tabbatar da shine ya ke haifar da matsala a maganar aurenta, duk da Sadiq lamarin yazo da ƙarar kwana, sannan ba wai ya auri Safna bane kawai bai yarda wani namiji ya raɓeta ba, da kyar aka samu ya tafi ta dawo hayyacinta, tunda aka fahimci ga inda matsalar ta take kuma itama ta fahimci lallai tana da matsala duba da yawan mafarkin ruwa ko tana tashi sama da mafarkin macizai ko tana faɗa da wasu halittu, tunda ta yiwa malamin da yayi mata ruƙiyya bayani yace In Sha Allah zata samu lafiya, ya bayar da magani wanda za ta soma amfani dasu. Alhamdulillahi wannan shine hanyar warakar matsalar Safnah dan an kwashe shekara biyu ana aikin magani kuma an samu nasara dan har Allah ya sa ta fara kula samari a lokacin shekarunta ashirin da huɗu a duniya, ganin suna niman su hanata sukuni yasa ta tsaida Zayyad a matsayin wanda zata aura duk da bata ƙaunar mai mata, amma soyayyarsa tayi mata dirar mikiya wanda ba zata iya haƙura dashi ba duba da shima yadda yake mugun ƙaunarta.

 

Ba zata mance haɗuwarsu ta farko ba lokacin taje shagonsa dake kan babban hanya tsakanin Gomna Road da kuma Badikko, taje siyo fulawa da kayan haɗin donot, da ta gama siyayyarta an saka mata a leda ta tsaya bakin shagon zata tare napep ta wuce gidansu dake ɓangaren Abakwa GRA, sai ga wani yaro ɗan makaranta akan keke yazo zai wuce, tsautsayi yasa shi raɓar gefenta saboda gosilon daya haɗu a gurin, nan ya fasa mata ledar fulawa ya fashe ya soma zuba a ƙasa, da azama Safna ta kamo rigar yaron wanda ya sashi dole ya tsaya, ta shiga yi masa masifa akan lallai sai ya biyata, yaron ya soma bata haƙuri amma taƙi saurarensa dan abin yayi matuƙar ƙona mata rai, haka mutane suka fara taruwa a gurin masu bata haƙuri nayi masu bawa yaro laifi suna yi, Zayyad dake shago yaji haniyar tayi yawa sai ya fito yana tambayar yaran shagonsa meke faruwa? suka sanar dashi sai ya ƙaraso inda su Safna suke ya shiga bata haƙuri yace shi zai biyata, ya amsa ledar ya bawa ɗaya daga cikin yaransa akan su sake yi mata awo, nan taro ya watse sannan Zayyad ya gargaɗi yaron akan ya riƙa kula da hanya yayi masa godiya ya tafi. Zayyad ya koma shago ya zauna yana hango Safna har aka gama zuba mata ta amsa ta wuce, wannan dalilin yasa tasan shine asalin mai shagon da take yawan siya kaya a gurinsu, shima kuma dalilin daya saka shi riƙe fuskarta kenan, da ta zo siyan abu yana jin muryanta yake ganewa zai fito ya tsaya har a sallameta ta wuce, a hankali ya fara jin wani abu yana ɗarsuwa a zuciyarsa game da ita, tun yana ƙaryata kansa har ya yarda da ya kamu da sonta, ita kuma tana yawan zuwa shagonsa ne tayi siyayyar kayan fulawa saboda sana’arta kenan harkan snacks, donot da samosa tafi yi dan ta iya sosai tana yin na taron suna ko biki ko wani sha’ani, bata yarda da zaman banza ba dan har a gida tana yin na sayarwa, in tayi da yawa takan ɗiba ta tafi dashi makarantar bokon da take koyarwa ta bayar a shagon makarantar ana saida mata, in ya ƙare a bata kuɗin shima mai shagon ya cire ribarsa. Wannan shine sanadin haɗuwarta da Zayyad wanda baiyi ƙasa a guiwa ba har sai da ya kafa gomnatinsa a zuciyarta ya samu gurbi, tun tana ƙi har saida ta amince masa har suka shafe shekara guda da watanni kafin aka saka lokacin bikinsu, gashi yanzu saura wata ɗaya a ɗaura auren. Kiran daya shigo wayar Safna shine ya dawo da ita daga duniyar tunani data shiga, ta sauke numfashi ta ɗaga kiran da sauri dan har ya kusa tsinkewa ta kara a kunne.

 

Wa’alaikum Salam ina yini Maman Ilham.

 

Lafiya lau Alhamdulillahi, ya shirye shirye?

 

Hmmm lafiya lau.

 

Amaryarmu kenan ki daina wani hmmm ko kunyata kike ji? Abinda mun riga da mun zama ɗaya, dama na kira ki ne akan ki tura mini hoton ankonki ina so Abban Ilham ya siya mini ne nima na shiga tawagar ango kar a barni a baya.

 

Ok ba damuwa anjima zan tura miki ta WhatsApp In Sha Allah.

 

To nagode Allah ya nuna mana bikin lafiya sai anjima ɗin.

 

Yauwa a gaida yara nagode.

 

Daga haka suka kashe wayar, Safna tabi wayar da kallo tana mamakin Rashida yadda ko kaɗan bata taɓa nuna mata kishin zata auri mijinta ba, shigowar Anty Shafa falon yasa ta aje wayar tana cewa.

 

Anty wai kinji matar Zayyad ce tace in tura mata ankon bikina zata yi.

 

Ikon Allah! tunda nake ban taɓa ganin mace mai sauƙin kishi irin matar nan ba, ina ce itace kwanaki ta rako shi zance.?

 

Eh mana ai zuwanta ya kai sau biyu, sai ta biyo shi ita da yara su zauna anan cikin gida su barmu muyi zance a waje, har sai mun gama zai kirata ta fito su wuce.

 

Allah mai iko, gaskiya in har auren nan ya tabbata ina kyautata zaton zaku yi zaman lafiya.

 

Wlh Anty shiyasa bana fargaba da zai haɗamu gida ɗaya, kuma su anty Maryma sai ƙorafi suke yi akan kar na yadda amma ganin yadda take yi mini yasa nake ganin babu wata matsala dan ya haɗamu gida ɗaya.

 

Ki kwantar da hankalinki ki tsarkake zuciyarki In Sha Allah za kuyi zaman lafiya. Yauwa anjima mai gyaran jikin zata zo sai ki zauna cikin shiri.

 

To Safna tace mata, Anty Shafa ta zauna tana bawa yarinyarta nono, sai ga umma da Anty Maryam suma sun shigo, nan Anty Shafa ke basu labarin matar Zayyad tace a tura mata anko, anty Maryam taja guntun tsaki.

 

Wlh matar nan ki yi hattara da ita ban yarda da wannan shige miki da take yi ba, bayan muna da labarin sam bata jituwa da dangin mijinta.

 

Maryam karki karyawa Safna zuciya ta karaya, in kin san ba zaki ƙarfafa mata guiwa ba to ki daina kawo irin wannan maganar bana so, tunda ta nuna mata haka ya tabbatar da Zayyad yafi ƙarfin gidansa ne, sannan kuma akwai zaman lafiya a tsakaninsu tunda har zance ta taɓa rakoshi.

 

Umma nima shi na gani ba tada matsala wlh. Ni damuwata ɗaya ne kar wannan auren ma a kuma samun matsala irin na baya a fasa.

 

In Sha Allah ba abinda zai faru Zayyad sai ya zama mijinki Ƙanwata, ai Alhamdulillahi anyi maganin jinnun jikinki kuma an samu nasara da izinin Rabbil Ka’aba.

 

Cewar Anty Shafa da murmushi a fuskarta, anty maryam tace.

 

Kina amfani da magungunanki ko? ba kya wasa dasu.

 

Eh ina yi.

 

Yauwa. Amma ya maganar aikinki? zai barki ki cigaba da yi ko.

 

Hmmm Anty nifa wlh na gaji da zarya a hanya, shekara kusan huɗu fa ina koyarwa kawai zan kama business ne dan Zayyad yace zai bani jali nayi sana’ar cikin gida.

 

Safna daɗi soyayya! ke har kin yarda da zancen sa ko, karki yiwa kanki sagegeduwa fa Allah.

 

To Anty Maryam yace baya son matarsa tana aiki nima kuma na gaji da aikin, tunda shi yayi alƙawari nasan zai cika mini In Sha Allah.

 

Allah ya kyauta yasa ba daɗin baki ya cika ki dashi ba.

 

Ke dai Maryam kowa yana son wannan auren amma naga ke sam ba haka bena gunki.

 

Umma wlh ina son Safna ta yi auren kwanciyar hankali ne saboda duk cikinmu babu wacce take da kishiya, amma ace ita zata auri mai mata kema fa ba kishiyar nan gareki ba.

 

Ƙaddarar kowa daban, ita haka Allah ya ƙaddara mata, ai duk cikinku zan iya cewa babu wacce zata kai Safna adawa da ƙin namiji mai mata amma da yake yana cikin jarabawarta gashi zata auri mijin wata kuma Allah saiya ɗaura mata sonshi a haka, ni bana son yawan ƙorafin nan ku bita da fatan alkhairi.

 

Cewar Umma data miƙe dan shiga ɗakinta, nan suka cigaba da tattauna maganar bikin dan dama abinda ya kawo su kenan, suna so ayi bikin Safna fiye da yadda aka yi nasu a baya, shiyasa bini bini suna gida sun haɗu dan maganar bikin.

 

Malam Abdullahi shine mahaifinsu sai Umma Raliya mahaifiyarsu, gabaɗayansu mazauna cikin garin Kaduna ne sai dai asalinsu mutanen zaria ne daga ƙaramar hukumar Lere. Abba ma’aikacin gomnati ne yana koyarwa a makarantar sakondari, Yaransu biyar Anty Shafa’atu itace babba tana aure a tudun wada yaranta biyar sai anty Maryam tana aure a maƙarfi raod yaranta uku sannan yaya Mudassir sai Zainab data ci sunan mahaifiyar abbansu ana kiranta Safnah, sai auta yusuf. Alhamdulillahi wannan zuri’a sun ginu bisa tarbiyyar addinin islama da karatun zamani, duk da Anty Shafa da Maryam a iya secondary suke tsaya aka yi musu aure, amma fannin islamiya kuwa koda suka iya aure saida suka haɗa karatun sanawiyyarsu wanda dukkan su suna koyarwa a islamiyar dake kusa da gidajen aurensu. Yaya Mudan ya haɗe Digree ɗinsa fannin electric engineering, yana da shagon sayar da kayan wuta bai tsaya jiran aikin gomnati ba, Safna kuma tana da deploma a fannin islamic studies daga nan kuma bata ɗaura ba, sai ta samu aiki a wani private school ta soma koyarwa ana biyanta, fannin islamiya ma ta gama Mutawassiɗa tana shirin ɗaurawa ne Zayyad ya fito aurenta shine ta dakata dashi, Yusuf kuma yana matakin kammala secondary ya sauke Al-Qur’ani, wannan shine takaitaccen tarihin familyn su Safna.

 

*****

 

Zayyad.

 

Yana zaune a office ɗinsa dake cikin babban shagonsa, wanda kayan masarufi yake sayarwa kuma babban dila ne dan har sari yana bayarwa, sannan akwai kimanin matasa biyar da suke aiki a ƙarƙashinsa. Wayarsa ce ta yi ƙara ya duba sai yaga yayansa Kamal ne da sauri ya ɗauka tare da yin sallama, bayan sun gaisa ya ce.

 

Yaya dama ina son zan kira ka riga ni. Batun kai lefe Hajya ta sanar dani wai kai dasu Baba Mamman zaku kai, wai yanzu haka ake yayi.

 

Eh ta sanar dani shiyasa ma na kiraka muji ya abin zai kaya, an sanar dasu Baba Mamman ɗin kuwa?

 

Ina ga ta faɗa musu, yanzu lokaci za a saka da za akai.

 

To Allah ya kaimu ina ganin ranar Juma’a zan shigo kaduna. Ya batun gidanka kuwa ka ƙarasa ginin?

 

An gama komai gyara kaɗan ya rage.

 

To madalla zan tura maka dubu ɗari biyar a cigaba da shirye shirye, amma da fatan Rashida bata ɗaga maka hankali ba.

 

Babu wata matsala dan sosai ta karɓi auren, baka ga yadda take hada hada ba da shirye shirye.

 

To Allah yasa ta ɗaure ya baku zaman lafiya, sai kayi ƙoƙari kayi adalci a tsakaninsu.

 

In Sha Allah, nagode yaya Allah ya saka da alkhairi.

 

Ya amsa da Amin kana suka yi sallama, Zayyad ya sauke ajiyar zuciya fatansa ayi bikin nan lafiya duk da yana da labarin faruwar matsalolin auren Safna na baya, hakan bai taɓa sashi fargaba ba dan yasan matar mutum kabarinsa, kuma yasan tana da matsalar jinnu basu ɓoye masa ba, fatansa dai Allah yasa zasu barsu su zauna lafiya, yadda yake matuƙar ƙaunarta baya jin akwai abinda zai hanashi kawo Safna gidansa, ji yake tamkar bai taɓa aure ba akan ta ne zai fara, ƙarin farin cikinsa yadda Rashida ta bashi haɗin kai da goyon bayan auren, shiyasa ya samu natsuwa yake gudanar da komai cikin kwanciyar hankali. Sai gabda magrib suka rufe shago ya shiga mota ya kamo hanyar gida.

 

Daya ƙaraso ya yi hon mai gadi ya buɗe masa ya shiga yayi parking yara suka rugo da gudu suka yi masa oyoyo tare da wasu yara su biyu maza baƙin fuska, ya kama hannun Aslam suka shiga falon, ga tv nan a kunne suna kallon wani tasha da aka sanya waƙoƙin Hausa sun cika volume ɗin ko sallamarsa basu ji ba, ganinsa ne yasa Anisa ƙanwar Rashida tayi saurin rage volume, Anty Wasila data rashe a ƙasa shirim ita ba kaɗan ba tayi saurin jawo ɗankwali ta ɗaura ta gaishe shi, ya amsa tare da yi mata sannu da zuwa dan ya shaidata yayar Rashida ce, ɗiyar wan mahaifinsu wacce mahaifiyar Rashida ta riƙe bayan rasuwar mamanta, Anisa ma ta gaishe shi ya amsa yana cewa.

 

Ganinki sai an cika form kin yi mata ƙaura a gidan nan kamar munyi miki laifi.

 

Makaranta ne ya ɓoye ni amma yanzu munyi hutu sai ka gaji da ganina. Tun ɗazu naso kiranka nace nazo gidanka ka tawo mini da abin daɗi dan nasan shagonka baya rasa kayan ciye ciye.

 

Da kin kira da na riƙo miki biscut, yasu mama da fatan kowa lafiya.?

 

Lafiya ƙalau.

 

Ta bashi amsa sai ya wuce zuwa ɗakinsa, ya soma rage rigar jikinsa sai ya isa gurin da yake aje flaks ɗinsa na ruwan zafi ya ɗaga yaji babu komai a ciki, yaja guntun tsaki ya koma ya zauna, shuru shuru yana jiran Rashida ta shigo bata shigo ba, dan lokcin daya shiga falon bata nan amma yasan zuwa lokacin tasan ya dawo.

 

_Rahma Kabir ce, da fatan zaku sake bina a cikin wannan tafiya mai sabon salo. Ina uwargida da amarya da masu shirin shiga daga ciki wannan ma tafiyarku taku ce, akwai sirrin zamantakewa da yawa a ciki kar ku bari a baku labari._

Amaryar Zayyad Novel Document txt.

File Name   Amaryar Zayyad … Hausa Novel Doc.
Title  Amaryar Zayyad Novel Document 
Author    Aisha Aliyu Garkuwa 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    07/11/2024
File Size    250KB
Format Size    TXT
Book Price    500
Phone No   09034940106
Download Amaryar Zayyad Novel Document Rahma Kabir 

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button