Novel Document

Mutallab Complete Novel Document

Mutallab Complete Novel Document By Nimcyluv

Description/Story:

Mutallab Complete Novel Document

Written By Nimcy Sarauta

 

Description

Jami’an tsaro ne ta ko’ina cikin kayan kaki ma bambanta, duk da cewa yammacin ranar lahadi ne a watan Fabrairu bai hana ta gane fuskarsa ba. Cikin tashin hankali jikinta na rawa da kyarma ta nufe shi tare da ƙoƙarin cakomo wuyan babbar rigarsa tana furta cewa “Shi ne, wallahi shi ne, daman na ce zan gano shi” a gigice mutumin dake ƙoƙarin shiga motarsa da aka buɗe masa ya yi baya yana mai ƙarewa matar kallo sosai sai dai ya kasa gano ko wace ita? Daga ina me kuma take buƙata.

“Wace ita?” Ya furta yana tambayar zuciyarsa tare da kallon gefe. “Wallahi shi ne, mugu azzalumi sai ka yi kuka, ka wulaƙanta ” Jin furucinta ya saka ƴan’jarida dawowa kan ta, suka fara tambayar “Kin san shine? Mene haɗinki da shi?” Kafin ta yi magana wani ya ce “Arrest her, ku kamata”

A hankali ya jingina da jikin motar can ya numfasa yana kallon yaronsa ya ce “Wace ce? Na santa ne? To me ya sa take abu kamar ta sanni?”

“Sir da gaske ta sanka bana jin ko mutuwa ta yi ta dawo zata manta fuskarka, kuma zamanta a raye yana nufin abubuwan da yawa dole a yi wa tufkar hanci, kar a bari ƴan’jarida su samu ganawa da ita, even your securites, wannan matsalar kai da kai ce kuma zata shafi kimarka” cike da mamaki ya yi ta kallon yaron nasa na tsayin sacanni da ƙyar ya cije leɓe ya ce “To ina na santa? Me ya sa zata zama damuwata?”

“Sir ita ce wacce ka saka aka kawo maka ita, wacce ka yi wa fyaɗe a lokacin…..,”

“Ya isa!” Ya ce yana jin jiri na neman ɗauke shi, ya dubi tarin jama’ar da suke wajan can ya yi murmushi yana ɗauke fuska sai kuma ya ƙurawa yaron idanu ya juya ya kalli matar ya gyatsine fuska ya ce “kuma ta kasance a raye ya haka? To a yi hanzarin toshe wannan ɓarnar ya zama kamar ba a yi ba”

“Amma me ya kamata a yi mata?”

“A yi mata allurar hauka, wacce ake yi duk shekara da wata wata kana a kaita gidan yari, life in prison har ta mutu. Bayan haukan zata mance komai, su ƴanƴan talakawa wama ya damu da su mutu ko su yi rai bata da wani mai tsaya mata kai mutuwa ma za ta yi” yana faɗin hakan ya shige mota. Tana takure a jikin ƙofar ɗakin da aka ajjiyeta idanunta ƙur a kan photonsa zuciyarta sai zafi take mata wani abu ya tsaya mata. Da sauri ta juya jin an buɗe ƙofa wani mutum ne sanye da farar riga ya rufe fuskarsa hannunsa riƙe da ƙaton sirinji iya ruwan allurar da ya yi ja abin tsoro ne, ta fara ja da baya amma a haka ya fincikota tare da yin cilli da ita,ta faɗi saman carpet bai tsaya jiran komai ba ya caka mata allurar a ƙashin bayanta wajan spinal cord ihu ta fara da birgima idanunta ya shiga ƙaƙƙafewa jikinta na sandarewa ta dinga buga kanta da jikin bango tana buge-buge a hankali jini ya fara fitowa ta cikin hanci da bakinta tabbacin allurar ta amshe ta za kuma ta yi aikin da ake buƙata a jiki da ƙwaƙwalwarta.

******
Cikin sauri suke tafiya a wani ɗan dogon lungu mai duhun gaske tsarin wajan gabaɗaya a ƙuntacce yake kamar zunubin gidan yari. Magana suke ƙasa-ƙasa ɗaya daga cikin su kuma yana duba agogon dake hannunsa tare da duba cikar lokacin fuskarsa a haɗe take sosai. Sai da suka kawo ƙarshen ginin suka tsaya ya ɗaga kai a hankali ya dubi saman da kansa ke taɓowa ya ɗan rusuna sai kuma ya dubi jami’in tsaron dake wajan ya yi masa nuni daya buɗe ƙofar. “Yes sir!”
Bayan ya sara ya ƙame ya buɗe ƙaton kwaɗon yana toshe hanci saboda wari da zarnin wajan. SP Gali ya kalli team ɗin nasa cikin bada umarni ya ce

“Ku jira nan, idan akwai damuwa zan muku alama na san dai he can’t do anything, ba zai iya komai ba” gabaɗaya suka jinjina masa kai tare da zagaye ƙofar fuskar kowannen su manne da baƙin gilas. A hankali Sp Gali ya tura ƙofar ya shiga yana durƙosawa saboda rashin girman wajan. Tunda kafin su ƙarasu wajan ya san da zuwan nasu har aka buɗe ƙofar tare da shigowa, yana durƙushe inda yake ya kifa kansa a ƙasa hannunsa dunƙule ya damƙe abu wanda tun kafin a kawo shi gidan abu yake a hannunsa, yin duniya yaƙi buɗe abun balle a san menene shi.

“Hey you!” Sp Gali ya ce yana saka ƙafa tare da buge ƙafarsa ganin yaƙi motsawa, tamkar gunki haka yaƙi motsi ya kuma ƙi ɗago kansa Sp Gali ya shiga kallon wajan ya rasa wanne irin hali ne da wannan yaron mai baƙar zuciya da taurin kai ya sauke numfashi cikin kwantar da murya ya ce “Ni idan na ce maka ina da tausayi na yi maka ƙarya, amma ka saka zuciyata karaya kana bawa kanka wahala kana bawa jami’anmu wahala. Me zai hana ka sauƙaƙa mana wahalar nan ka faɗa mana gaskiyar abin da ya faru a wannan rana kuma a wannan daren? Me ya sa ka aika abin da ka aikata? Ka kashe matarka, ka kashe ta har lahira kuma kaƙi magana shekara uku kenan kana wajanmu ka rainawa hukuma hankali da kotu, kai baka da zuciya ne dame kake taƙama saboda kana da tsari a jikinka ƙarfe ba zai ratsa naman jikinka ba, muna da kalolin azaba nau’i-nau’i amma gaskiya muke buƙata, ka amsa cewa ka kashe matarka a zaman kotu na yau shikenan sai a yanke maka hukunci daidai da zaluncin da ka aikata”

Har Sp Gali ya kammala maganarsa bai motsa ba, babu alamun zai ɗago kai balle ya tanka. Sp ya miƙa hannu zuwa hannun mutumin dake dunƙule da abu zai amsa a firgice ya ɗago kansa yana buɗe dara-daran idanuwansa akan Sp Gali sai da zuciyarsa Sp ta motsa saboda wani mugun jaa da idanunsa ya yi. Fuska ɗaure ya yi wa Sp kallon warning har lokacin bai yi magana ba dukkan naman jikinsa rawa yake kamar zai kaiwa Sp damƙa fuskarsa baibaye da gashi kansa ma cunkus yake ba’a gane kamanninsa sosai saboda cikar gashi.

Sp ya duba lokaci sai kuma ya shafa kai ya ce “SCORPIO” nan ma ya sake ɗago kai da sauri ya zubawa Sp idanu “Idan ka bari na gano cewa kai ne Scorpio….”

Ya cije baki yana miƙewa tsaye ya furta “Zan addabi rayuwarka, gwara ka zauna a iya wanda ya kashe matarsa da dai ka kasance kai ne Scorpio. Mene asalin sunan naka?” Ya tambaya yana juyawa kamar zai fita saukar gurnanin da ya ji ya saka ya yi saurin juyawa idanunsa ya sauka wanda ake zargi da kashe matar tasa yaga ya dafe kai da hannu bibbiyu yana jujjuyawa ya dinga haɗa kansa da bango cikin sauri Sp Gali ya ce

“Team” a guje suka shigo hakan ya saka ɗan ƙaramin ɗakin cika fuskar Sp ba wasa ya ce “Ku danne shi a karɓo abin hannunsa dole mu san mene babu mamaki zamu samu hujja a ciki” yana cewa haka ya fita yana amsa kira. Ganin sunyo kansa ya yunƙura gabaɗaya ya fisu faɗin ƙirji da damtse amma suka rufar masa sanin cewa sarkin yawa ya fi sarkin ƙarfi ya saka shi damƙe hannunsa da kyau yana ɓoye abun da suka karɓa, kokawa suke da shi ya dinga haɗa su da bango ya kama hannun ɗayan ya karya bisa dole suka fice a wahale. Sp ya saka wasu manyan mutane fito da shi suka ɗaure shi da ankwa tare da sarƙa tun daga ƙafa har zuwa kansa.

A harabar Criminal Investigation department CID aka tsaya dashi domin tafiya zuwa kuto a rana ta ƙarshe wanda ke nuna ko a sake shi, ko a kashe shi ko kuma ya tafi gidan ɗan’kande. Team guda ne masu matuƙar basira da ƙwarewa akan aikinsu team ɗin ya haɗa da wanda yake ɓangaren Legal section, Anti-human trafficking, Medical Staff, Legal services, NDLEA, FID Federal investigation department. Gabaɗaya idanunsu yana kansa kowanne yana karantar yanayinsa amma shi ko a jikinsa banda faratansa na hannu dana ƙafa da aka ciccire wajan gana masa azaba babu wani rauni a tattare da shi sai matsanancin baƙi da ya yi ya zama kamar mahaukaci saboda shekarun daya ɗauka a kulle daga kuto zuwa state cid zuwa Fid amma har tsayin shekarun bai buɗe baki ya yi magana da kowa ba, babu kuma wanda ya damu daya tsaya masa. Suna ta surutai ƙasa-ƙasa duk yana jinsu har sanda wani yake cewa “Babu hanyar da za a tilasta shi ya yi magana ne? Muna buƙatar muryarsa”

Sp Gali ya ce “Ina zargin wani abu game da matarsa daya kashe”

“Wanne abu? A binciken da mukai a wajan iyayen yarinyar tun farko ita ta nuna tana son shi, shi da ita class mate ne kuma age mate, tun suna shekaru 15 a secondary school suke soyayya. Me ya sa ya zaɓi ya kashe ta? Sun ɗauki shekaru tare bai taɓa yunƙurin rabata da duniya ba sai ranar da aka ɗaura musu aure? This is complicated” C.i.d Research ya jinjina kai ya ce

“Duk binciken da aka yi shine a ruwa, gwajin hannu, yatsun hannu da sahun tafin ƙafa da CCTV camera na kan titin unguwar da aka kai amaryar tasa duk bincika shine”

Shiru sukai suna tunanin gabaɗaya kansu ya ɗauki zafi. Yana da can inda yake ya ja idanunsa ya lumshe yana fesar da iska daga cikin hancin wacce hucinta ya sauka har saman fuskarsa “BESTIE” haka ya ji saukar muryarta a kunnensa kamar yanzu ne suke tare da ita. Ya sake lumshe idanunsa yana jin saukar dariyarta sosai ya tuna lokacin yana zaune shi kaɗai a cikin class ranar aka dawo hutun makaranta shi kaɗai ne zaune ciki yana sanye da farar riga sai wando blue black ya ɗora ƙafarsa ɗaya saman benci tare da yin baya.

A hankali ta shigo cikin class ɗin hannunta riƙe da lunchbox da textbook sai school bag data goya, hijab ɗinta daidai da ƙirjinta ita ce ta fara shigowa da mamaki take kallonsa zuciyarta na bugawa ta je ga zauna inda yake ta zuba masa idanu sai kuma ta ce “Ka yi holiday assignment?”

Ya buɗe manyan idanunsa bai ce komai ba ta sake ƙasa da murya ta ce “Na san bama ka yi ba ka daina haɗe mini fuska, ka naso a yi ta faɗa da kai da teachers” nan ma bai kula ta ba a hankali taci sautin da cikinsa yake yi sai ta jawo lunchbox ɗinta ta buɗe tare da tura masa gabansa ta ce “Your breakfast, ka ci kafin a shigo na san baka karya ba” sai a lokacin ya buɗe idanu ya juya gabaɗaya yana kallonta sosai ta yi ƙasa da murya kamar zai yi faɗa sai kuma a hankali ya ce

“Kuma ga mayunwaci ko?” Ta yi murmushi ta ce “Da ƙyar na jure ban biyoka gida ba, na yi kewar ka sosai bestie” ya yi mata shiru sai kuma ya haɗe fuska sosai yana janyo abincin yaga dankali ne aka soya da ƙwai ya yi ɗan tsaki ya ajjiye spoon ɗin ya damƙa ya kai bakinsa ta yi saurin kama hannunsa ta ce

“Kai baka iya komai bane? Sai a yi maka dariya cin abinci da hannu” ya ware idanu sai kuma ya murtuke fuska ya ture hannunta a hankali duk da muryarsa a kumbure take ya ce “Ki daina kusanta kan ki dani, ni fa ba ɗan iska bane”

“Laaa Allah Ya baka haƙuri kai duk abin soyayya baka iya ba” a taƙaice ya ce “Ke kika santa” ta ja baya tana ɗaga hannu ta ce “Lalala to shikenan ni dai ƙaddararka ce, na faɗa a gida a yi mini aure, ka san me na ce?” Ya girgiza mata kai kawai yana sake damƙo dankalin yana dannawa cikin bakinsa saboda yunwa ko gani baya yi sosai ta buɗe gorar ruwa ta miƙa masa a hankali ta ce

“Na ce su yi mini aure wallahi bana son karatun nan, na ji aure nake so kuma na faɗa musu kai nake so, amma wai ban isa ba karatu ya zama dole kuma shekaruna sun yi kaɗan amma ai ma girma shekararmu 15 years fa, ko kai baka isa aure bane?” Ya yi mata shiru sai ta fashe da kuka sosai ta ce “I love you so much Bestie, don Allah ka aure ni zan zauna dakai a duk yadda kake ka taimakawa rayuwata” ya zame hannunsa tas ta miƙa masa tissue ya goge ya ja baya yana lumshe idanunsa har yanzu students basu fara shigowa ba, ta ɗan yi gaba kamar za ta shige masa ya cikin tsawa ya ce “Zan kwaɗe ki kuwa”

“But what if i told you i love bestie? You mean the world to me, wallahi aure nake so ba karatu ba” ta faɗa tana shassheƙar kuka sai a lokacin ya kalleta fuska babu walwala ya dubi yadda take kukan sosai ya ce

“Ke, babanki ne ya mutu? Ko uwarki ce?” Ta girgiza masa kai ya sake haɗe fuska yana rarraba idanu a cikin ajin kamar mai neman wani abu can ya ce “To kece za ki mutu kenan?” Ta girgiza kai sai kuma ta ce “A’a”

“Kukan fa?”

“Na soyayyarka ne bestie taɓa ƙirjina ka ji wallahi ni ce ƙaddararka ba zaka gane hakan a yanzu ba, da ina da ikon cire abin da nake ji a ƙirjina da na yi hakan ina jin dama na mutu na huta kuma idan ban aure ka ba zuciyata zata iya bugawa”

“To gwara ta buga na huta da na ci, shekaruna 15 za ki lalata ni da batun aure, ke tashi ki ware daga nan ɗauki kwananki kar ki ƙara kawo mini abinci” ta miƙe jiki a sanyaye zata bar wajan ya nuna mata lunchbox ɗin daya cinye komai “Ko daɗi bai yi ba abincin”

Sai a lokacin ta kyalkyale da dariya kamar ba ita ta yi kukan ba, dimples ɗinta na lomawa ta ajjiye masa 500 ta yi waje tana cewa “You’re my darling jarumina, i love you Mai dawa da jeji” ta faɗa tana sake yin dariya tare da yin waje…….

Ya yi saurin dafe kansa jikinsa na rawa yana jin dariyar nata na yi masa amasa kuwwa a kunne kamar yanzu ne take yi jikinsa ya ɗauki rawa sosai daidai lokacin aka tura shi cikin motar shiga babu biya, aka nufi kuto. Tun kafin a shigar da shi suka ci karo da wani saƙo daya basu mamaki ainun suka tsaya suna kallon juna sosai cike da tsoro da shakku musamman Sp Gali ya juya ya kalli wanda ake zargin a karo na farko yaga ya yi wani irin murmushin kefen baki wanda ya bada sauti kamat na tsaki yana murza kai gefe.

Cikin sauri Sp Gali ya ce “Amma wane ya yi hakan? Bayan ba a gama bincike an tabbatar da hakan ba, mene matsayin ran yarinyar daya kashe ina matsayin iyayenta” “Sp Ghali ka yi abin da aka ce, kuto ta wanke shi daga zargin da ake yi masa ku sake shi ya tafi gida baku da ikon riƙe shi”

Sp Gali ya girgiza kai cike da damuwa ya ce “Sir kana nufin bashi ya kashe ta ba” cikin tsawa ya ce “Ko shine ya zaka yi? Ka yi abin da ya dace a matsayinka na jami’i Sp Ghali karka matsa” jiki a matuƙar sanyaye Sp Ghali ya kunce shi tas ya ce “Congratulations. Ka sani shari’a saɓanin hankali ce” shi dai bai ce komai ba ya ciri biron gaban rigar Sp Gali ya fara yi masa rubutu a tafin hannunsa dam zuciyar Sp ta buga ganin ya rubuta kalmar SCORPIO kafin ya yi magana tuni ya juya ya fara tafiya cikin sauri duk da rashin kuzarin da yake dashi yana jin inda iskar ƴanci ke ratsa jikinsa yana shaƙa tare da kaiwa hunhunsa.

Kano/Birget
Dambe suke yi a tsakiyar tsakar gidan mata wajan uku ne kowacce da ɗaurin ƙirji ga tukunyar abincin dake saman murhu. Banda sautin hayaniyarsu babu abin da ake ji hatta Malam dake waje da Almajirai yana jin yadda suke aibata juna da zagin juna hakan ya saka ya miƙe riƙe da bulala yana ajjiye allon hannunsu da yake rubutu ya yi cikin gidan.

“Ke har kin isa ki ce za ki hana Mufeederh abinci a gidan nan? Wace ke?” Cikin ɗagawa Inna Binta ta ce “Ni Binta matar malam ki faɗa mini nawa Mufee ta bayar aka haɗa wajan yin abincin nan? Ke uban yaran nan bai bada kuɗin abinci ba, ba zai yiwuwa yara su haɗa kuɗi kuɗi a siyo dusar awara a yi dambun nan ki ce wai na zubawa Mufee ba ƴar banzar yarinyar da bata da kunya, kina kallo sauran ƴan’uwanta suka fita nemo kuɗi ita ta yi kwanciyarta tunda ƴar mai ce ai yanzu sai ta ci hantar ubanta Malam gashi can yana zaman banza ba fuss”

 

Mutallab Complete Novel Document

File Name   Mutallab… Hausa Novel Doc.
Title Mutallab Complete Novel Document 
Author Na’ima Sulaiman (Nimcy)
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Romantic Story
Published Date    17/11/2024
File Size    300KB
Format Size    TXT
Book Price    ₦500
Phone No   08119237616
Download Mutallab Complete Novel Document By Nimcy Sarauta

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button