Description/Story:
Dijah Qaya! Complete Hausa Novel Document Written By Asma’u Galadima
Description
๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ
*DIJAH QAYA*
๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ
*BY ASMA’U GALADIMA* ๐ฆ๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ๐ฟ๐ฆ๐ฟ
๐ฆ ๐ฆ
๐ฆ ๐ฆ ๐ฆ ๐ฆ
*OH* *ALLAH* *HELP* *MY* *COUNTRY* ๐ณ๐ฌ
*AND* *MY* *RELIGION*๐
*PAGE*โฏ1โฃ
*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINQAI*
Likita! Likita!! Likita!!!
Wani dattijon Bafulatani ke fadi, sanye yake da Riga da wando “yar Shara light green irin wanda mazan fulani ke sawa da hulansa malfa wanda akasaka da kaba bakin takalmine kwafta na roba akafanshi yana rataye da Goran ruwansa a wuyansa da sandansa ahanunsa farine shi kal har yana Kore Kore kyakykyawa dashi, kallo daya zaka masa ka fahimci tsananin damuwan da yake ciki
gudu gudu yakaraso jerin dakunan ganin likita yana kokarin kutsa kansa sai dai cincirindon mutanen da ke zaman bin Layin ganin likitan ne yasa shi yin turus awajen yana kalle kalle
Daga dan gefe ya hango wani daki guda daya bai da layin mutane sosai ahanzarce ya nufi dakin baiyi wata wataba ya murda handle din ya shiga, wani matashi ne zaune akan kujera yana sanye da jeans blue da shirt light pink da lapcoat asamanta da fari kal din glass manne a idonsa matashin dan kimanin shekaru 27 fari ne shi amma ba kalba yana da kyau sosai, Rubutu yakeyi, gefenshi wata nurse ce tana shirya files
agabansa,
yakaraso gabanshi yana fadin
Likita likita “yata zata mutu don ALLAH kataimaka min kazo ka dubata,
Dasauri likitan yadago kai yana kallonshi ganin yanda jikin sa yake barine yasashi yatashi ahanzarce yana kokarin fita daga cikin kujeran zamanshi yace ” ina take? Da yatsa ya nuna masa hanyan waje tana can jikin mota Doctor, Don Allah ka taimakeni kar in rasa ta bata ko iya tsayuwa,
Doctorn ya dubi nurse din da take shirya folder yace ” sister jeki shigo da ita, cikin girmamawa tace ” Ranka ya Dade ba nan ya kamata yakawo taba G O P D zai kaita in suka duba suka ga case din yafi karfinsu sai suturosu nan, “no problem sister shigo da ita kawai ya fada yana kokarin zama,
ta karasa ta dauki well chair tafita gudu gudu dattijon yake binta har suka isa inda yarinyan take kwance agalaibaice take batasan inda take ba,
Shi yadagata yasata aciki nurse din ta turo har office din,
nan ya umurcesu dasu kwantar da ita akan gadon da yake office din,
Ya jawo kwalin hand glovs yazari guda biyu yasa ahanunsa sannan ya karaso gadon yafara dubata kusan minti biyar yana dubata sannan yaja jininta yazuba a “yar kwalba ya mika ma nurse din yace” sister akai aje amana test yanzu mukeson answer tadan rusuna ta karba tafice, ya dauko srinji yaja ruwan Allura yamata yazare glovs din yazuba a dosbin sannan yakarasa wajen fanfo ya wanke hanunsa yagoge sannan yadawo yazauna sai lokacin yadubi dattijon
yace” bismillah Baba zauna anan yanunamasa wurin zama, yazauna yana ajiyan zuciya, sabon file yadauko ya bude yayi dan Rubuta sannan ya kalleshi,
Baba meye sunan Mara lafiyan? Yace sunanta Dija Bukar, Doctor yayi dan murmushi
yace Baba Dija ba suna bane, kafadamin asalin sunanta,
haka muke kiranta yaro, Doctor yakara dan murmusawa Yace Baba na Asalin sunan ai KHADIJA ne, ko?
Eh hakane asalin sunanta khadija Abubakar, “yauwa Baba adinga cikamata sunanta yafi, “hakane dannan amma tafi gane Dijan yayi murmushi yace” Meyasa metane Baba? Wlh ciwon cikine yake damunta sannan wani lokaci da daddare sai jikinta yayi zafi kamar wuta kuma tana yawan kukan ciwon kai ga amai komi taci sai tayi amai, yadanyi rubutu sannan yadago ya kalleshi yace “tun yaushe ta fara Baba?,
“kusan wata kenan tana fama, “wata? Likitan ya fada yana zaro ido “haba Baba wata guda tana ciwo anma ba kukaita asibitiba? ” mun kaita wani asibiti can gaba da ruganmu sati d’aya suka sallamemu muka koma gida ba sauki shine muka sake komamusu shine suka turo munan,
Sai da yagama Rubuce Rubucensa, sannan ya kalleshi duk ya diririce sai zufa yakeyi tun kafin yaye magana Baban ya rigashi, araunane yace” Likita me ke damunta? Zata tashi kuwa? Doctor ya gyara zama yace “ka kwantar da hankalinka insha ALLAH zata tashi bansan damuwanba tukun sai ankawo saka makon gwajin sai asan abin yi, daidai lokacin nurse din tashigo ta mika masa result din
Bayan yagama dubawa ya jawo takarda yayi rubuce rubucensa ajiki ya mika masa, yace “Baba wannan magungunan za’asayo, yakarba yana Dubawa ” a’ina ake sayarwa? Doctor yayi jim “Baba kaikadai kazone bakazo da wani wanda zai sauna da itaba? Ni kadaine Likita ba damuwa zan kula da ita Doctor Yadago ya kalli nurse yace” sister hadashi da cleaner ya nuna masa phermercy Baba kazo da kudi? “Eh nazo da kudi sosai ko nawane zan iya saye. Insha ALLAH, “ok to kabi wannan zata hada ka da wanda zai nuna maka wajen da ake saida maganin, tana kaishi ga dawo, tadan rusuna tace “ranka yadade kana da petaint guda biyar da suke da appointment naganinka yau, yadan lumshe ridonsa yabude, yace ” bazan samu daman ganinsu ayauba amma kidauki files dinsu ki kaima Doctor Habib yadubasu, tadan juya idonta Doctor bakwai guda daya da yake da bukatan ganinka bazaiyuwu yaga waniba sai kai, ok bani filedinsa naga meye Case dinsa? Saida ya duba shi sannan ya tashi yace” , inaso amai da yarinyannan world yanzunnan yafada yana fita, kai tsaye word din Ya nufa yana duba wasu da yakwantar bayan yadan dubasu yadawo jikin gadon da da’aka kwantar da ita, har yanzu bata cikin hayyacinta, dai dai lokacin baban yashigo da magungunan
Drip ya daura mata sannan ya samata magungunan, yajuyo yana cire gloves din hanunsa yana kallon Baba da ya dogare sandansa ya harde kafafunsa ya kurama diyar tashi ido, saida ya wanke hannayensa sannan yafita can sashin Cosmo ya nufa,
Tunda mama jummai ta hangoshi ta tasi da saurinta tana washe baki don tasan abun nima yasamu, duk lokacin da taga Doctor KB yazo wajen da Duke tasan kakanta ta yanke saka don ba karamin kudi yake bataba ta kula da peteint
Sannu Doctor tafada dai dai lokacin da ta iso wajensa yadan murmusa cikin girmamawa yace “mama karki gaji Dani don ALLAH wani datijjone yazo da “yarshi, anbata gado kuma shi kadai yazo baizo da kowaba,
Da saurinta ta katseshi Lah bakomi likita za’a kula dasu yanda yadace ALLAH dai yasakama da khairan irin wannan taimako da kakeyi,
Baice komiba yajuya ta rufa masa baya
Zaune suka sami Baban yarafka tagumi ya tsura mata ido ,
Doctor KB yace” sannu Baba yadora da zaka iya tafiya yanzu, kaje kayi sallah kahuta ga mama zata cigaba da kula da ita in akwai abun da kake bukata kuma kasanar dani, Baba yadago yana dubanshi yace” bana bukatan komi likita nagode sosai da karramawan da kamin Allah ya maka Albarka, mama jummai ta amsa da Ameen, Doctor KB yajuyo da kallonsa ga nurse ita ma shi take kallo tana mamakin Doctor KB aduk lokacin da wasu daga Kauye sukazo da Mara lfy muddin case din ahanunsa yake sai ya dauki dawainiyansu wasu kamma kacokam din maganin shi zai ke saya yana musu amfani dashi
Sister hadashi da baba Garba yanuna mishi dakin da zai zauna aciki yajuya ba tare da yaji daga garetaba,
Kai tsaye office dinshi yanufa bayan yakammala abunda zaiyi yafito ya nufi word anan ya samu Doctorn da zai karbeshi,
Yafara mishi handing over har suka iso kan Dija da zuwa yanxu ta farfado bacci takeyi Doctor na’im yace ” wanna yaushe aka Admitting dinta? KB yazura hannayenshi a aljihu yana kallonta
yace” Da safe aka kawota kuma case dinta serious ne typhoid ne yamata chronicHar yana shirin taba heart dinta ga malaria shima yayi mata munmunan kamu kasan mutanen namu San basa son zuwa asibiti saida ciwo yagama mata illa aka kawota,
yafada yana shafa sajensa ransa a dagule amatsayinsa na cusaltant Sam baiji dadin ganin result din yarinyanba,
Doctor na’im yagirgiza Kansas cike da takaici yace “ba FULANI bane sam bansan yaushe zasu daina irin wannan haliba, yanzu me yakamata amata? Yajuya yana fita yace” yanzu saidai gobe in Allah yakaimu,
Yana bude motansa ya hango Baba zaune duk hankalinsa yatashi katuwar darduma yadauko abayan motansa yakaraso inda Baban yake agefe ya shinfida masa “yace Baba ga gurin zama nizan tafi gida insha ALLAH zanzo da dare, “likita yaza muyi inkatafi? Yadan murmusa “Baba kanaji da wannan”yar taka gaskiya
” Ayyah Likita mamatace fa awajen,
Murmushi likatan yayi yace “karkadamu na damqata ahanun wani likita zai kula da ita, yajuya yatafi sai godiya yake masa,
Tun kafin yayi horn masu Gadi suka wangame gate ya shigo idonsa akan Mami sai sintiri take atsakar gidan dama yayi tunanin za’ayi haka murmushi yayi ya bude Motan da sauri ya nufo wajenta atsakiya suka hadu tayi saurin riko hanunsa cikin damuwa saida takaishi har cikin falo sannan takalleshi da damuwa “Haba Kabir meyasa ? Meyasa ka koro body gaurd dinka? Ka zauna kai kadanka tsawon wannan lokacin awaje? Kasan damuwan da kasani kuwa? Nakasa samun nitsuwa gashi ka kashe wayoyinka Kabir kamanta abun da yafaru abayane?
Yakamo hanunta yana murmushi” bakomi Mami kafin infita sai da nayi Addu’an Safiya da maraice sannan nayi Addu’an hawa abun hawa nakumayi na barin gida ba abinda zai sameni ina da bodyguard din gaske ajkina Mami pls banison kidinga daga hankalinki innafita ni kadai ta sauke ajiyan zuciya “nasanka da sakacine kabir don ALLAH kadinga tayani kulawa dakai, tafada tana shafan Kansa Insha ALLAH My luvly mami
Yamiqe zai fita Mami tace ”
ga Abinci fa yana jiranka eh zanyi wanka ne Mami aifa ko kwado haka yaganka yabarka Indai wanka ne sauran daganan kuma inji shiru nayi magana kacemin aidaga fitowankane bacci ya kwasheka Baka saniba, yajuya yana dariya har zai fita yadawo yace” Mami akwai wanda za’a kaiwa Abinci Asibiti
“to yau kuma wa kasamo ko mutanenkane?
“no wa incan an sallanesu wani dattijone Mami shi da “yarsa bafulatanine wlh
yadanyi karanin tsaki yana shafa Kansa Mami tace ” meyafaru kuma?
“tausayi mutumin yabani yana matikar son “yartashi gashi kuma zata mutu tabarshi
arazane Mami tazaro ido “kamar yaya zata mutu ta barshi kabir?
Yadan furzar da numfashi Mami sunriga da sunbarta agida ciwon ya mata illa zaiyi wuya ta tashi,
cikin damuwa Mami tace “wannan na ALLAH ne kabir karkasake fadin haka aqidankune kawai na likitoci amma tsananin ciwo bai kawo mutuwa,
yadaga kafadanshi alamun shikenan yana tafiya yana fadin Mami da ALLAH ashirya akai musu yanzu mama jummai tana wurin “ok yanzu za’akai,
yashiga part dinsa yana balle maballan rigansa akayi knocking yabada izini aka shigo sai da yazanme rigan sannan yajuyo suna hada ido da sani yaballamasa harara, yana dariya ya karaso har gabanshi yace” haba KB me kuma nayi?
Cikin dakewa yace” Haka mukayi da kai? Bance karkabari Mami tagane kunbarni a can kundawoba? Shine har da cemata na koroku ko?
“No bahakabane KB akwai matsalafa sosai cikin barinka kai kadan, yadora hanunsa kan bakinsa “shiittt Sani kudaina wannan tunanin abunda yafaru ya wuce kuma ma wancan lokacin da akasa bom amotana ai ba a asbiti bane kamanta can wajan meting din campani ne? ” To inbanda KB kasan daga ina aka biyoka? Ai ko ba komi xamu kula da motanka yanda baza’a samu daman samaka wani abunba pls kaba Mami hadin kai wajen kiwon lfynka
, “mmnhh naji jeka zanyi wanka ne kai dama ba aikin soja kazaba da low kayi dan kafi dacewa dashi parrot kawai, yafada yana shiga bed room Sani kuma yajuya ya fita yana dariya,
kusan minti talatin yafito sanye cikin fara kal din lallausan jallabiya mai gotun hannu, Fallon Mami yashiga tun kan ya iso kamshin sa ya iso,
Ahankali tadago tana kallonshi ta lumshe ido ta bude aranta tana gulmata kyau da Gayu irin na KB matsalansa. Daya dan banzan jin kai da izza,
Tana matikan son KB tun ba yauba shiyasa fir taki zaman London wajen Abbanta kusan kowani qarshen watanni uku sai tazo Nigeria, wani alokacin har sai Abbanta yayi ta waya yananumata bacin ransa kafin ta koma NAFISA kenan ” yar kanin Mahaifin KB
Sam bai lura da ita ba har saida yazo tsakiyan Fallon tayi dan gyaran murya Yadago suna hada ido ya sakar mata harara ya wuce dakin Mami murmushi kawai tayi tabishi da ido ya murda handle din qofan ya leqa da kanshi yace “Mami na “tadanyi gyaran murya abayan gida maida qofan Yayi ya rufe ya dawo fallo ya nufi dining yazauna, ya dago wayansa yana danne danne,
Nafisa ta taso tazo tajawo kujera daf dashi ta zauna tana. Kallonshi barka da dawowa mijina, yadanyi murmushi gefen baki “kinimi mijinki tun dare bai mikiba Kaine mijina insha ALLAH hade rai yayi batare da ya kuma tankawaba, tadan ya mutsa fuska “yinwa fa nakeji KB “toni meye nawa aciki dakike gayamin? Dai dai lokacin Mami ta iso ” sai yanzu kagadaman fitowa? Ka wani shanya mutane suna jiranka “I’m sory my Mami ” Nafisa samishi Abinci yadan yatsine fuska yace “Mami kina arhantar dani da yawa nidinfa mai tsadane, yaza’ayi ace wannan abarce zata samin Abinci Nafisa ta kaylkyale da dariya Mami “tace ina wani tsada ga gouron da bai da mata? “to ai Mami ke kika ki auraddani, gashi sa’annina daga mai da daya sai mai biyu ya fada cike da zolaya don kalman da mamin take yawan gaya masa kenan,
Ta balla masa harara ” tace af kar kadamu kwanannan zan auradda kai inaga ma. Kafin hutun nafisa ya kare za amuku aure Inyaso saita karashe karatun da aurenta Mami tafada cike da tsokana tana gimtse dariyanta don tasan tagama kunnashi
Nafisa ji tayi kamar ta Goya Mami tsaban farin ciki dariya take qasa qasa tana kallonshi yayi kicinkicin da fuska yana danna wayansa har tagama zuba wa ta tura masa gabansa ta zauna Mami tajawo nata tafara ci tana dan murmushi, nafisa ta sunkuyo dai dai kunnensa tace” my luv ko inbaka abakine? Dan gajeren tsaki yayi yajawo abincin yafara ci “Mami ankai Abincin Asibitin ne? Eh dazu nafisa sunkai ita da driver, tabe baki baki yayi yace mhmm ALLAH yasa dai ba’amusu raahin kunyanba,
Nafisa ta yamutsa fuska wa za’ayima rashin kunya? “Yan qauyan? Mami tace “CI Abincin ki nafisa baki sabo da halin kabir,
Dadauri sauri yake shiri yana duba agogo yasan yanzu haka Mami tana tasintiri tana jiran shigowanshi, tsaf yagama shirinshi cikin wando cinos brown da shirt millk colour sai takalminsa sau ciki brouwn da farar safa aciki ya manna farar glass a idonsa ya dauki brief case dinsa brown yarataya akafadansa yana daura agogon hanunsa mai Cain din silve wayassa tahau ruri dan murmushi yayi yadauka yakara akunnensa “Hello Mami gani nan zuwa nagama, aqofan sashinsa ya taradda securitynsa suna jiransa hanu yamika musu daya bayan daya sukayi musabaha, yawuce sashin Mami tana tsaye jikin dining kamar yadda yazata nafisa kuma tana kan kujeran dining din, hannayensa biyu yahada waje daya yadaga yana kallonta da dan murmushi afuskansa yana juya kanshi “I’m sorry my Mami ta matsoshi tariqo hannayen ta zaunar dashi kan kujera tana fadin kar kadamu kabir nasan maganinka kwanannan zanyayeka in huta kaikenan kullum latti zan samarmaka mai hanaka wannan baccin, tana magana tana zuba mishi a falate shikuma sai murmushi yake yana kallonta, ta turomasa dumamen tuwon shinkafa miyar danyen kubiya don tasan shine fevourite dinsa ta zuba masa kunun gyada ta turomasa tana kallonshi shima din ita yake kallo Mami waye zai hanani baccin? Inna aurad dakai dakafara “ya”ya ai shikenan bakai ba baccin safe yadan murmusa yadauki spoon yafara cin abincin, Nafisa ta lumshe idonta ta bude tana kallonshi ko Rabin baibciba yature yana shirin tashi Mami tace ” yanzu ko kununma bazaka shanyeba? Yadan shafi cikinsa “wlh Mami na qoshi ta tabe bakinta kawai tabishi da kallo,
Bayangidan Fallon yashiga ya kurkure bakinsa yafito briefcase dinsa yahango rataye akafadan nafisa baikobi takantaba yafara sallaman Mami, Addu’o’in datasaba mishi tashiga mishi har sai da tagama yace” ameen mamina nafisa tamiko masa briefcase dinsa, yaharde hanunshi aqirjisa yana kallonta “da ahanuna kika samu? tadanyi farr da idonta “dannabaka ahanunka ai balaifi nayiba yajuyo da kallonshi ga Mami “yace Mami yarinyannan ta rainani kiga ko gaisheni batayiba, tazo yanzu zatamin rashin kunya Mami tace”ni na isa shiga tsakaninku? ” Mami wlh in nagaisheshi kin amsawa yakeyi “shikenan Mami kinbani dama intattakata kenan? Mami tazaro ido waje ni inbaka daman kataka matarka!? Afusace yafinciki briefcase dinsa yafita yabarsu agun,
Sam bayason Mami take hadashi da nafisa amaganan aure yafison suyi mu’amala da ita matsayin yaya da qanwa don duk familyn Su bawanda yafi shiri da ita irin nafisan
Tunda yafito daga cikin mota yake gaisawa da mutane har yashiga office, sister Amina yatarar tana shirya folder yaja kujera yazauna tadan rusuna tana makale murya tagaisheshi ko kallonta baiyiba ya amasa aggagauce yana duba wani file, kimanin Awanni hudu yadauka a office din ya shiga word a bakin qofa sukayi kicibus da Baba, “sannu likita da murmushi ya amsa da “sannu Baba ya maijikin dai? a wlh jiki Alhadulillah “ta tashi ne? “Eh ta tashi likita har tana dan cin Abinci, nagode likita wlh har bansan mezance makaba sai dawainiya akeyi damu tunjiya ake takawo mana Abinci Niki Niki ALLAH ya maka Albarka kaida iyalanka, “Ameen Baba ALLAH yaqara mata lfy munje inganta,
Yana gaba Baban nabiye dashi har jiki gadonta, bacci take amma yaga alamun sauqi sosai afuskanta, yajima yana kallonta yana nazartan yanayin fitan numfashinta yanadan rubuce rubuce, kafin yakai dubanshi ga mama jummai yace “jiya da yaushe tafarka? “Kusan magriba taci Abinci alokacin? “a’a maltina kawai tasha amma yau da safe tadan ci, ya gyada kansa “baccifa tayi da daddare? “Eh tayi sosai ma, sai da yagama “yace idan ta farka za’azo akaita can wajen masu xray, yazaro kodi mai yawa yamiqa wa mama jummai takarba sai zabga godiya take yajuya ya fita zuwa yanzu kam Baba yafara tsananin mamakin likitan dama anasamun irin wa’innan mutanen abirni? ๐ค yatambayi kansa
Sai can bayan la’asar tafarka da sauri mama jummai ta tariketa tana tambayanta zaki zagane? ta girgiza kai gyaramata Zama tayi dai dai lokacin Baba Garba yashigo da katan din maltina da kayan tea wai gashi inji Doctor KB Dija kam gyara zama tayi tana kallonsu suna magana tana tambayan kanta to ko sudin suwaye? Tunda tafarka taga mama jummai tana ta hidima da ita datayi motsi zata matso ta tambayeta me takeso?
File Name | ย Dijah Qayaโฆ Hausa Novel Doc. |
Title | ย Dijah Qaya Complete |
Author | ย ย Asma’u Galadimaย |
Group | ย ย Aiย Hausa Novels |
Genre | ย ย Fictionย Story |
Published Date | ย ย 17/07/2024 |
File Size | ย ย 845 KB |
Format Size | ย ย TXT |
Book Price | ย ย Free |
Phone No |
Download Dijah Qaya Complete Novel Document By Asma’u Galadimaย
Click the below green button to read the novel online
Proceed with your download by clicking the below button
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page :ย Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page :ย @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel:ย Ai Hausa Novels
DOWNLOADย More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.