Novel Document

Gargadar So Complete Novel Document

Description/Story:

Gargadar So Complete Novel Document Written By Maman Shakur 

 

Description

💫 GARGADAN SO 💫

 

✍🏻M SHAKUR

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINKAI

 

ANCE MONEY IS POWER! Shin kun yarda? Ance kudi kan iya maganin komi har cuta da bakin ciki kun yarda? Ance kudi na kankaro mutunci sannan kudi kan iya siyan kowa shin kun yarda? KU BIYONI A WANNAN SABON LABARIN MAI SUNA GARGADAN SO DAN WARWARE MUKU ZAREN🥳

 

 

EPISODE 1️⃣

Dankareren kerarren falo ne dazaka dauka acikin presidential villa kake sabida kyawunshi, wani Babban attajiri ne adakin yana sanye da manyan kaya da akalla zaikai 68-69yrs hakan nan yana sanye da manyan kaya dake walkiya kaman da duwatsun diamond aka kera shaddan, sai gani attajiri a gefensa shima yana sanye da manyan kaya ya kafa hula aka, sai kuma wasu mataye guda biyu suma da zasukai kaman 49 ko 50yrs haka duk zazzaune cikin shiga ta alfarma shigan da kudi ke ihu suna screaming, duk wanda ka kalla cikin falon kana iya ganin tsananin tashin hankali dasuke ciki, kap mutanen nan babu mai magana, sai zancen zuci da kowa keyi, agogon dake daure a wrist din attajirin ne yayi kara hakan yasa yadago kanshi yakalli sauran mutanen dake dakin da duk sun dagokai suna kallonshi sabida karan da agogon hannunsa yayi yabude zaiyi magana amman ba murya dan gyaran murya yayi. “Uhmm uh’umm” sannan yace “this is 72hours daidai kenan tun bayan munkai kudin dasuka bukace mu damukai amman shiru, basu saki yarinya ba, basu kiranmu ba” saikuma ya zauna da sauri kan kujera yana kallon attajiran matan da ke kuka dudda bata bari hawaye ya taba fuskanta dan tarike tissue tana mammannawa dayan matan dake kusada ita dake nuna kaman kawarta ce sabida yanda take bubbuga bayanta yace “Noor is just 4yrs, yau kwananta 5 in captivity” sai kawai yatashi kaman wanda aka tsikara da saurin gaske yayi wajen kofa dayan Alhajin yabishi da dan gudu yasa hannu yabude kofa yafice wasu manya manyan security dake sanye da kayan sojoji ne kusan su 10 gaban dakin sunyi layi biyar na kallon biyar.

Babban Riganshi ya shiga tattarewa yana sauri dayan na binshi da sauri shima yace “ina zaka Your Excellency?” Cikeda tashin hankali yana tafiya still batare daya tsayaba yace “I’m going to see Khaleelu” daidai wasu securities na budemai wani babban kofa ya shiga cikin wani lafiyayyen falo dayay mahaukacin haduwa ga duhu ya cikashi, hannu yasa ya kunna wutan dakin yayi haske dau, yawuce wajen lift dake falon ya shiga yakaisa sama babu komi dake aiki adakin banda AC, wani kofa yabude dakin shima duhu dasauri ya kunna wuta, ya Allah! Kyan dakin is worth rubutawa a littafin world record, wani matashi ne kadai zaune adakin akasa kan wani lallausan fur carpet dagashi sai joggers na aritza ash color da rigansa farin t-shirt, yabama kofan baya hakan yasa bayansa kadai zaka iya gani that’s huge and full da gashin kansa dakeda dan yawa and it’s kind of coily kaman na dan fulani baki kirin.

Dasauri attajirin yayi wajen da yaron yake ya zaga ta gabanshi yaduka cikeda damuwa yace “Khaleely, Khaleel, Son!”

Ko motsi yaron da ake kira baiyiba dayan Alhajin dai ya tsaya wajen kofa yana kallonsu, dasauri attajirin yakai hannayenshi biyu yakai wajen habansa yadago kan matashin cikin tattausan murya yace “Khaleel” ahankali matashin yabude idanunshi dakenan manya manya sannan dara dara kaman idanun yar budurwa wanda suke cike da dogayen black eyelash hakama giranshi yanada gashi sosai and giranshi is very thick gakuma fadi zaikai ahada giran wani guda biyu waje daya shine fadin nasa gashi kuma gashi ya cikasu tam, gashin kansa ma yafi na wata, bawai yatara gashi chanchan bane kawai dai akwai gashin and sunyi coils, lips dinshi are pinkinsh but ba chanchan ba, but yanada plumpy lips that’s so masculine in nature and sexy, ga dogon hanci kaman jijiyan tattasai, yanda ya zubama mutumin da kana ganinshi kasan mahaifinshi ne idanu yasa mutumin yayi kaman zaiyi kuka yakai hannunshi kan wuyanshi yace “jibi yanda yarona ya rame eh, look at you Khaleelu you don’t eat anything saidai ruwa yau day 6 babu proper meal in this ur tummy, da wanne zanji eh”? Saikuma yakai hannunshi yakama kafadanshi yace “i come to tell you I will not sit still naki komi sabida this takadiran kidnappers dinnan sunce kada muyi involving police then sainai folding hannu inbar wani abu yasameka and jikata”sai alokacin ya iya bude baki shima kana gani kasan karfin haline kawai ahankali yace “Pops if anything should happen to Noor I don’t know wat will become of me”

Dasauri Baban yace “I know Khaleel, nima idan abu yasameka I don’t know what will become of me da mahaifiyarka, tsaya kaji Khaleely” ture hannunshi Khaleel yayi daga kafadanshi yace “Pops banso naji, don’t involve police!

I don’t care idanma wani kudin sukeso they should keep calling zanta basu koda duka abinda na mallaka zai karene i just want my daughter back Dad” baki baban yabude zaiyi magana Khaleel yatashi azafafe ya tsaya tareda pointing door wai yanada tsawo and cikakken huge man ne, kai tsaye yace “leave my room Pops I wanna be alone!”

Baban zai sake magana ya kara nunamai kofa cikeda karfin hali yace “nace kafita, leave Pops i want to be alone idan sun sake kira” kallonshi babban yayi irin kallon tsantsan soyayya dakuma kauna da tausayi da damuwa duka dinnan sannan yatashi yana gyara babban rigan yace “muje Musbahu”

Wucewa sukayi suka fice, suna fitowa Abba yace “get me DIG awaya kahadani dashi” dasauri Musbahu ya tsaya yana kallonshi cikin damuwa yace “I know abinda nakeyi I will never put my granddaughter in danger but this nonesense have to end, muje office dina” office nashi suka wuce nan ma bude musu kofa akayi suka shiga ciki Babban office ne dakana gani zaka gane kaman na yan siyasa ne dan ga hotonshi an rubuta Senate President Alhassan Mangal, zama yayi kan kujera yana kallon Musbahu dake waya sai chan yamikomai wayan karban wayan yayi yasa a speaker kai tsaye cikeda isa irin yanda manyan mutane ke magana yace “abinda nakeso nafada maka yanzu is something da banso yabi gari hartakai media dan it has to do with jikata that is just 4yrs old” yayi shiru chan yace “On 21st of this month kwana biyar dasuka wuce kenan ranan asabar ankai Noor park, it’s her usual thing weekend ana kaita park, she has 2 International nannies da kuma 1 Nigerian, dakuma 2 securities nata wanda 1 happens to be driver, 5 people accompanied her to the park but right under their nose aka saceta Noor tabace bata ba alamunta kidnappers sun kira sunyi demanding for 100M munkai exact location 2days ago sun karba but shiru basu saketa ba” yadanyi shiru yace “I thought we can handle everything on our own tunda kudi ne but mun bayar but still shiru Noor is a baby, sunyi warning namu not to involve police ko bazamu sake ganinta ba forever, my son is looking miserable I need your help DIG, I need your best team that can save jikata without a scratch and wayanda zasu iya aikin discretely konawa kuke bukata I will pay”.

Gargadar So Complete Novel Document txt

File Name   Gargadar So… Hausa Novel Doc.
Title   Gargadar So Complete
Author    Maman Shakur 
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Romantic Story
Published Date    01/10/2024
File Size    300KB
Format Size    TXT
Book Price    500
Phone No   07012181461
Download Gargadar So Complete Novel Document By Maman Shakur

Click the below green button to read the novel online

 READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

 

 

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button