Novel Document

Ranar Naka Complete Novel Document

Ranar Naka Complete Novel Document By Farida Abdullahi

Description/Story:

Ranar Naka Complete Novel Document

Written By Farida Abdullahi 

 

Description

Duk da yadda ƙofar ta kasance ta bature mai masifar tsada, irin mai taushinnan sosai da ko an buɗe ba ta ƙara, daga yadda ta murɗa hannun ƙofar da ƙarfi, ta danno a haukace kuma a fusace, sai da ƙofar tayi wata siririyar ƙara mai kama da fitar iska. Hakan yasa mazauna ɗakin waiwayowa da sauri suna kallonta da wani yanayi mai kama da maɗaukakin mamaki a fuskokinsu.

Ganin irin kallon da suke mata yasa ta ƙara harhaɗe girar sama da ƙasa tayi murtuk! Kamar an sheƙawa ƙullun kunu tafasassasshen ruwa. Kallon huɗu saura kwata ta watsa musu gaba ɗaya, sannan ta ba iska ajiyarsu ta hanyar jan tsaki ƙasa-ƙasa. Ta taka kai tsaye ba tare da tsoro ko fargaba ba zuwa gurin mamallakiyar ɗakin da take zaune kan kujerar gaban madubi, da kakkausar murya ta ce

“Abincin Innaye da aka manta da wanzuwarta a cikin gidannan na zo karɓa…”

“Ke dabbar ina ce ƴar ƙauyen-ƙayau da bata san abinda ya kamata ba? How dare you da za ki shigo min ɗaki kai tsaye da wani ƙazamin jikinki ba tare da neman izini ba ina tare da abokan aiki na?”

Ta katse yarinyar da maganganun cikin fushi. Da miƙewarta tsaye a fusace, da ɗaga hannu ta kai ma yarinyar wani mahaukacin mari baza’a ce ga wanda ya riga wani ba.

Cikin zafin nama da ƙwarewa a zamiya yarinyar tayi saurin duƙawa ƙasa marin ya bi iska. A haukace ta miƙe tsaye tana haki, domin an shammaceta, a zuciyarta take ayyana lallai da marinnan ya sauka a kumatunta ta rantse da girman Allah babu abinda zai hana ta ɗaukar wannan figaggiyar matar mai shegen girman kan tsiya da wulaƙanta ɗan Adam ta nuna ma Allah sannan ta maka ta da ƙasa. Sai dai duk abinda zai faru ya faru.

“Kan Uba… Ni kika mara?”

Ta faɗa cikin ɗaga murya.

“Me nai miki da za ki mare ni?”

Ta sake jefa mata tambayar tun kafin ta bata amsar tambayar farko. A ranta take kitsa lallai ya kamata ta nuna ma matar nan halin dabbobi da jahilan ƴan ƙauye da take yawan zaginta da su.

Bazai yiwu duk zagi da tozarcin da tayi mata a cikin kwanaki bakwai na zamansu a gidan ya tafi a banza ba, lallai ya kamata ta nuna mata shiru-shiru fa ba tsoro bane, gudun magana ne.

Kafin matar ta amsa, ko kuma ɗaya daga cikin mazauna ɗakin ta ce wani abu ta ɗaga hannu biyu da sauri ta ɗora akai, ta fasa wani gigitaccen ihu da muryarta mai bala’in ƙara, cikin ƙanƙanin lokaci muryar yayi amsa kuwwa a ko wane lungu da saƙo na cikin gidan.

Tsakanin Innaye da take zaune kan dadduma a ɗakin da aka sauke ta acan BQ tana gyangyaɗi, da Hafiz da dawowarsu kenan mai gadi ya buɗe musu ƙofar get direba yana ƙoƙarin daidaita fakin ɗin motar a tsakar gidan. Baza a ce ga wabda ya riga wani isa cikin ɗakin Bintu da ihun Zulaikha ke fitowa ba.

Tana ganin Innaye da Hafiz sun shigo ba tare da jin nauyin jikinta ba kasancewarta yarinya mai garin jiki da wani irin gudu tayi gurin Innayen ta ruƙun-ƙumeta tana ƙara ƙarfin kukanta.

Taga-taga sukai za su faɗi, domin jikin Innaye irin na fulani ne ga kuma rashin ƙarfi saboda tsufa da rashin lafiyar da take fama da shi cikin kwanaki biyun, a dabarance Zulaikha ta riƙe Innayen tare da rage nauyin da ta sakar mata.

Cikin kuka da yanayin shagwaɓa da taɓara ta fara cewa

“Innaye mari na fa tayi, wai don kawai a ladabce na ce mata Aunty Bintu ina abincin Innaye? Mai aikin da take kai mata kila yau ta manta ne bata kai mata ba, ga shi har yamma ta yi. Shi ne fa kawai ta ɗaga hannu ta gaura min mari… Wayyo Allah kumatuna, zafi, zafi, zafi kumatuna Innaye ki duba min ko ya saɓule…”

Tana zuwa nan a maganganun da take yi cikin kuka ta sake yanka ihun da yasa da sauri Hafiz ya saka yatsarshi manuniya ya toshe kunnuwansa, saboda jin wani zazzaƙar ƙara da ya karaɗe cikin kunnuwanshi mai barazanar fasa dodon kunne.

Ita kuwa Innaye da ta yarda da maganganun da Zulaikha ta faɗa ɗari bisa ɗari, wani kallon kin kyauta ta aika ma Bintu a fakaice, sannan ta ƙara janyo Zulaikha jikinta tana duba ɓangaren kumatunta na hagu da hannunta ke dafe da gurin tana risgar kuka. A lokaci guda kuma tana rarrashinta da tausasan kalamai

“Yi haƙuri Auta, ƙyale ta kin ji ko? Ta yi ma kanta. Yau in sha Allah za mu tattara ina-mu ina-mu mu koma inda muka fito.”

Tana gama faɗin haka bata jira wani ƙarin bayani ba ta ja hannun Zulaikha suka fice daga ɗakin zuwa masaukinsu.

Hankali tashe, a firgice Hafiz ya bi bayansu bayan ya aika ma da Bintu da abokan aikinta wani kakkausan kallo da ko a wasa bai taɓa shiga tsakaninsu da shi ba.

Gudu-gudu yake taka matakalar benen yana kiran sunan da suke faɗa mata cikin magiya da ban haƙuri.

“Innaye, Innaye, don Allah kiyi haƙuri… Ki saurareni don girman Allah…”

Duk yadda yake bin bayanta yana magiya da maganganun ban haƙuri bata saurare shi ba sai da suka isa masaukinsu a can Bq.

Babban waje ne, kuma masauki ne mai kyau, ɗauke da gado da saitin kujeru masu kyau na matsakaitan kuɗi. Sai dai fa Bq ɗin can bayan gida ne da yayi banbaraƙwai ace an sauki Uwar miji a gurin. Idan da sanin darajar ɗan’adam ko ƙanwar miji bata cancanta a sauketa a gurin ba ballantana uwa. Domin tun tale-tale an tsara gurin ne a matsayin masaukin ƴan aikin gidan.

Baya ga haka kuma, a can cikin muhallin da masu gidan ke zaune, akwai ɗakunan baƙi har guda uku, ko wane ɗaki da bayi a ciki, ɗauke da setin gado masu tsada. Sai dai duk bayan sati guda mai aiki ke buɗewa ta gyara a sake mayar da ƙofofin ɗakunan a kuk-kulle. Saboda masu gidan basa amfani da su, sai dai idan matar gidan tayi baƙi daga ɓangarenta masu matuƙar muhimmanci sosai take buɗe musu suyi masauki a ciki.

“Ina saurarenka! Ya aka yi Hafizu?”

Innaye ta tambaye shi da murmushi a fuskarta, murmushin da duk mai hange da lura idan ya kalle ta kai tsaye zai fahimci murmushin yaƙe ne, irin murmushinnan da ko kusa bai kai zuci ba.

Amma da yake Hafiz a firgice yake, sam bai lura da kalar murmushin da take yi ba. Ajiyar zuciya kaɗan ya sauke don ganin murmushin yasa shi ji a ransa lallai fa Innaye bata ɗauki abinda ya faru da zafi ba.

Daman tun tale-tale ita ɗin mai haƙuri ce, kuma har yanzu ita ɗin uwa ce mai matuƙar haƙuri da kawar da kai akan duk muradun ƴaƴanta, matuƙar bai saɓawa doron addininmu na musulunci ba.

A marairaice ya duƙa a gabanta ya cigaba da magiya

“Innaye, don girman Allah da darajar fiyayyen halitta SAW kiyi haƙuri da abinda ya faru.”

Yayi maganar cikin ƙanƙan da kai da taushin murya, fuskarsa a takwarkwashe kamar zai saka mata kuka.

Daƙiƙu talatin ta ɓata tana kallonshi, zuciyarta cike da tunanika mabanbanta. Daga bisani ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. A hankali ta ce

“Babu komai Hafizu. Ya wuce.”

Ta faɗa a taƙaice. Sannan ta kawar da idanunta daga kan shi ta maida kan Zulaikha.

Wacce izuwa wannan lokacin ta daina kukan da take yi, tana kwance ne akan gado ta duƙunƙune ƙafafu da hannaye cikin hijabin jikinta, ja juya fuskarta can ta basu baya, ita kaɗai take sakarwa kanta ƙayataccen murmushi, idan ta tuna diramar da ya faru yanzu-yanzu.

Abin kamar a shirin film, ko kuma a iri labaran nan na littafi.

Ta sake sakarwa kanta murmushi tana maganar zuci

‘Ko babu komai dai a yanzu an fara goge raini tsakaninta da matar can. Ta gwada mata kaɗan daga cikin halin dabbobi da jahilan ƴan ƙauye da take kiranta da su. Idan da ragowar hankali a jikinta gobe baza ta sake gwaɓa mata maganar banza makamantan waɗannan ba…’

“Auta?”

Innaye ta katse mata tunani ta hanyar kiran sunanta a tausashe.

Da saurin gaske ta ɓata yanayin fuskarta kafin ta juyo a hankali da shagwaɓaɓɓiyar murya ta ce

“Na’am Innaye.”

Cikin kulawa Innaye ta sake ce mata

“Ya kumatun na ki? Ya daina zafi?”

Ranar Naka Complete Novel Document Txt

File Name Ranar Naka… Hausa Novel Doc.
Title Ranar Naka Complete Novel Document 
Author   Fareedah Abdullahi
Group    Ai  Hausa Novels
Genre    Fiction Story
Published Date    07/11/2024
File Size    100KB
Format Size    TXT
Book Price    ₦1000
Phone No    07039080978
Download Ranar Naka Complete Novel Document By Farida Abdullahi

Click the below green button to read the novel online

READ THE NOVEL


Proceed with your download by clicking the below button

Be With Us

 

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Back to top button