*ASM Bk2027*
_Destiny may be delayed but cannot be changed…._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
………..Saida Motar ta bar layin sannan duk suka juya Hajiya ta kalli Gwaggo ganin hawaye a fuskarta ta shiga bata baki kafin suka wuce gida ita dasu Saude Amadu kuwa tsaye yay duk jin jikin shi yake ba dad’i yana ganin gwaggo ta koma ciki shima ya shige gidan ya nufi d’akin shi ya kwanta, akai akai yake kai hannu yana share kwallan dake gangaro ma shi, gwaggo na shiga d’aki ta haye gado tasa kuka mai cin rae taci guri in Allah ya nuna mata auren Fatuu sai gashi komae ya juye zata yi aure ba tare da tana farin ciki da hakan ba, sosae ta sha kuka daga baya ta lallashi kanta ta yi shiru. Tun da suka hau hanya take ta kuka Baffanta da Abokin nashi nata bata Hak’uri har dae ta yi shiru sai dae kwalla basu daina zubo mata ba tana kai gefen gyalen ta tana gogewa daga baya bacci ya kwashe ta, sosae Baffanta yaji dad’in hakan don ba k’aramin ta6a mashi zuciya kukan da take ke yi ba, sai da suka tsaya Kano sannan ta farka suka siya abunda zasu ci aka mik’a mata nata kamar bazata ci ba baffanta yace tayi hak’uri ta ci idanunta duk suyi luhu luhu ba yadda ta iya dole taci don tana jin yunwa Bayan sun d’an huta suka sake d’aukar hanya duk garin da suka tsaya sai Baffanta ya siya mata abu wani ta ci wani ta k’i ci, Alhamdulillah sai Bayan la’asar wuraren karfe biyar na yamma suka isa tunda suka iso jumeta Fatuu ke jin tamkar za’a kaita kurkuku sai ma da suka isa rugar kukan zuci kawae take, Motar na tsayawa gaban gidan Kamalu da su Mino dake ta dakon isowar su suka nufo Motar cike da farinciki Baffan Fatun ya zagaya ya bud’e mata kopar ta fito sai murnar ganinta ake ita kam ta kasa yin ko murmushi ganin yanayinta yasa Kamalu da Mino suma d’an shiga damuwa baffanta yace su shiga daga ciki Mino ta kama hannunta shi kuma kamalun yace ya tsaya su sauke kaya, bin Mutane da ido kawae ta rink’a yi ana mata sannu da zuwa kan kace mi labarin zuwanta ya isa ko ina a cikin gidan harda uban kayan da aka zo dasu yan gidan duk aka fito wasu suka lek’o ta Katanga ganin kwakwaf ita dae kallon su kawae take tamkar yau ta fara ganin su, kafin su isa sashen su sai ga yadikko ta fito cike da farinciki ta zo ta rungume Fatun tana mata sannu da zuwa lokacin da ta d’agota suka had’a ido kawae sai ganin kwalla tay ta zubo mata da sauri ta Sunna kai k’asa sosae jikin yadikko yay sanyi ta kama hannunta suka nufi ciki, an gyara sashen na su sosae har da su fenti haka d’akin yadikkon an maida shi ciki da falo har da bathroom a cikin uwar d’akan, zaunar da ita yadikko tay kan kujera ta zauna gefenta haka su Mino ma duk suka zazzauna suna kallon ta ta sadda kai k’asa, kan kace mi d’akin ya cika da yara harda wasu daga cikin Matan gidan suka shigo yi mata sannu da zuwa suna ce ma yadikko ashe Amarya ta iso ita kuma tana bin su da eh kawae don tasan yawanci duk gulma ce ta kawo su, sai Bayan wani lokaci mutanen suka lafa yadikko tace ma sauran yara suje su k’yaleta ta huta bayan duk sun fita ya rage saura yan’uwan Fatun kawae cike da nuna damuwa yadikkon tace “Fatuu ki yi hakuri kin ji, kowa yasan ba’a kyauta maki ba wllh duk bamu ji dad’in wannan abun ba ba yadda zamu yi ne da muka nuna bamu so baki ga halin da muka shiga ba akai ta mana wulak’anci da Maganganu duk aka tsangwame mu Baffan ki har ciwo yayi….” Dakatawa tay tana goge kwallan da suka taru haka ma su Mino duk kwalla suke zubar wa a hankali Fatun ta d’ago ta kalli yadikko cikin rawar murya tace “ba komae ki daina kuka ai gani na zo sai suyi man Auren” kamata tay ta rungume tana mata godiyar taimakon su da tayi ta amince da wuri wanda duk basu yi tunanin hakan ba ta tambayeta har yanzu gwaggo fushi take don baffanta ya sanar da ita ta d’au ki zafi sosae Fatun tace mata a’a ta hak’ura tana nan zuwa sosae yadikko taji dad’in hakan, d’agota tay tace bari ta zubo mata Abinci ta barta da yunwa ga gajiyar hanya Fatun ta mik’e tace band’aki zata shiga da sauri Mino ta mik’e tana nuna Mata cikin d’aki tace an yi sabo a ciki suka nufi cikin tare, harda Alwala tayo Bayan ta fito ta kabbara salla a cikin uwar d’akin lokacin Baffanta da Kamalu suka shigo d’akin a Falo suka tsaya baffan ya tambayi Mino inna wuron ta kwanta ne tace mashi tana salla ne ya nemi wuri ya zauna Kamalu ma ya zauna lokacin yadikko ta shigo ta jere ma Fatun kayan Abinci kafin ta zauna a gefe tana ma Baffan ya gajiyar hanya Kamalu ya shiga basu labarin uban kayan da Fatuu tazo da su yace yawanci ma shi duk bai san mi ake dasu ba wasu dae ya san su a cikin film harda wanda ake gasa kaji duk su kae yar dariya kafin kuma shiru ta biyo baya can kuma Baffan yace ma yadikkon kayan na a d’akin shi aka kai su da d’akin Kamalu za’a sa to kuma kar a lalata wani abun tunda bashi kadae bane a ciki tace hakan yayi suna haka Fatuu ta fito duk suka d’aga ido suna kallonta ta k’araso da d’an murmushi zata zauna a k’asa kan leda Baffan yace tazo ta zauna kusa dashi yadikko tace ai Abinci zata ci yace to, saida ta tambaye ta abunda zata ci tace duk wanda ta zuba mata tasa mata burabusko tace in ta cinye sai a k’ara mata wani Abincin ita dae shiru kawae tay, Sam ta kasa sakin jiki ta ci Abincin sai dae tai ta juya cokali baffanta ne da ya kula da hakan yace ta daure ta samu ta ci tace to ta d’an k’ara tsakura kafin ta ture tace ta k’oshi, yadikko tace ai bata ci komae ba tace bata jin dad’in bakinta ne, fura ta zuba mata tace ta daure ta sha zata ji k’arfin jikin tace to, ba laifi ta sha da d’an yawa suna son suyi fira da ita saidae kowa bai cikin yanayi mai dad’i ba kamar ganin yanayin Fatun duk sunyi jigum jigum sai jefi jefi suke Magana daga baya Baffanta da Kamalu suka tafi yin salla suma suka Mik’e don su yi, Bayan sun gama sallar ne su Aysha suka matsa ma yadikko kan tazo ta ga kayan da aka zo dasu har saida ta mik’e ta bisu, koda taga kayan kitchen d’in tsananin mamaki ne ya kamata don ta san ba kananun kud’i aka kashe ba don kuwa ta ta6a yin aikatau a gidan wasu yan gayu a Abuja duk ta san amfanin kayayyakin yan gidan ma duk suna ta zuwa suna gani tuni labarin irin kayan da aka zo da su ya kai ma su Yaya, Bayan yadikkon ta koma d’aki ne ta zauna a gefen gado da d’an murmushi tace ma Fatuu dake zaune kan sallaya “ko zaki je ki gaisa da su Yaya nasan sun san da kun iso tuni” tura baki Fatuu tay ta juyar da kanta wani irin haushin Yayar take ji don ta san harda ita aka had’a komae, ganin bata ce komae ba yasa yadikkon k’ara mata Magana a hankali ta juyo tace mata ta gaji ba yanzu ba sai ta huta, d’aga mata kai kawae tayi itama gudun Magana ne yasa tace taje su gaisan don tasan sai anyi tsegumin rashin zuwan nata ta gaishe dasu, shiru suka d’an yi kafin yadikkon tace “naga uban kayan kicin gaskia gwaggo ta kashe kud’i ba kad’an ba, ni baffan ki ce man yay dubu d’ari ya tura har ina cewa sun yi kad’an don jere ake ma kicin sosae a birni kuma kayan suna da kud’i to sai yace man bai gama biyan kud’in kayan gado da kujeru ba don shi kad’ai aka bari da hidimar Ard’o ne kawae ya bashi shanu guda d’aya ya siyar yayi maki kayan d’aki sai kuma kud’in sadakin ki dubu 100, shi kuma so yake yayi maki kaya irin na yan birni shiyasa duk ya tattara kud’in shi ya biya don kayan fin rabin miliyan ne za’a maki” shiru Fatun tay yayin da tausayin mahaifin nata ya k’ara kamata,
“Wai nikam Fatuu ina Ya Handsome d’in ki??” Har saida kirjin Fatuu ya d’an buga damm jin tambayar da yadikkon tayi mata, shiru ta d’an yi sai kuma a hankali ta kalleta ganin tana kallon ta alamar jiran amsa yasa tace “Ya yi aure” dan bud’a ido yadikko tay kafin tace “Allah sarki yaushe?” tace “kusan wata ukku yanzu” rausayar da kai yadikko tay kafin ta sake cewa “a nan Katsina?”
“A’a basu nan k’asar suna America” da k’yar ta bata amsar ta d’ukar da kanta k’asa jin kwalla na niyyar zubo mata girgiza kai yadikko tay tace “Allah bai k’addara mijin ki bane don ni da nayi tunanin son ki yake wllh koda kika ce man ba haka bane wancan lokacin kawae na jiki ne na zata yana son ki ne ya bari sai kin k’ara girma don hidimar da yake tayi yawa yawanci zaki ga irin hakan ba hakanan mutum ke yi ba da dalili ashe shi don Allah yake yi” a sanyaye Fatun ta d’ago tace “shine ma ai ya turo kud’i aka siya wancan kayan” hannu yadikko tasa ta ruk’e ha6a tace kai don Allah Fatun ta d’aga mata kai alamar eh,
“Kai amman dae wannan mutumin d’an Arziki ne wllh ni bamma ta6a jin mutum mai Alkhairi irin nashi ba, ace daga makwabta ka ya dinga hidima haka ni fa wllh nayi mamakin kayan can don ko banza sai sun yi miliyan ko ma fi” dakatawa tay tana maida numfashi kafin da d’an murmushi ta dafa kafad’ar Fatun tace “amman da gaske bai son ki kuwa?” D’agowa Fatuu tay ta kalleta idanunta sun k’ara sauyawa a hankali tay shaking kanta tace “bai ta6a so na ba, dama yana tare da wadda ya auran yar uwarshi ce” cike da zolaya yadikko tace “to amman ke nasan ai kina son shi ko?” bin ta da ido Fatuu tay ta kasa ce mata komae kawae sai ganin kwalla yadikko tayi tana zubo mata zaro ido tay Fatun ta kifa kanta a jikin kafafun yadikkon ta sa kuka, wani irin sanyi jikin yadikkon yay ta kai hannu ta d’ago ta ta zaunar da ita gefenta ta rungumo ta ta gefe cikin kuka Fatun ke fad’in “ina son shi sosae yadikko nayi tunanin shima yana sona ne ashe ba haka bane bai ta6a so na ba ina ji ina gani yayi auren shi ya tafi ya barni” har idanun yadikko sun ciko da k’walla ita dama tayi mamakin saurin amincewa da Fatun tay ai mata auren ashe ashe ciwo ne da ita a zuciya sosae ta bata tausayi ta shiga rarrashinta tana bubbuga bayanta tace “kiyi hakuri Fatuu na fahimci yadda kike ji ki bar ma Allah komae in har shi rabon ki ne Allah ya k’addaro zaku rayu matsayin mata da miji ko ba dad’e ko ba jima hakan sai ta faru don in dae abu rabon ka ne kana zaune zai iske ka har inda kake har kai ta mamakin yadda hakan ya kasance wannan kad’an daga ikon Allah ne don ni kaina shaida ce na so Mahaifin ki kamar mi muna cikin soyayya aka ce an bayar dani ga wani abokin mahaifina ina ji ina gani aka man Auren dole kaman zan yi hauka naje gidan shi sam ba kwanciyar hankali ga wulak’anci dama shi bai d’auki mace a bakin komae ba tamkar riga haka yake canja mata shima Baffana harda kwad’ayi yasa ya bashi aure na k’arshe ya yi man sakin wulakanci lokacin yunwa duk ta k’arar dani abun bak’in cikin lokacin Mahaifin ku har yayi auren shi koda na tuntu6e shi Bayan na gama idda sai ya bani hak’uri ya nuna man bai da ra’ayin mata biyu, ya dae fad’a man haka ne kawae amman nasan kawae ya daina so na ne dama na samu labarin irin son da yake ma matarshi wato mahaifiyar ki gata yar birni mai ilimin boko a lokacin ne na samu aka man hanya na tafi aikatau Abuja nayi nisa da garin to ashe Allah bai kaddaro zasu rayu tare tsawon lokaci ba wllh lokacin na girgiza da jin labarin mutuwarta don lokacin ni nama fidda ran auren nashi na nemi number d’in shi ta hanyar wani Yayana na kira don yi mashi gaisuwa to anan muka samu lambar juna mu ka d’an rink’a gaisawa ina d’an kwantar mashi da hankali ana haka Bayan wani lokaci watarana sai kawae yayi man Maganar Aure yace in ba damuwa lokacin na k’ara gasgata girman ubangiji don kuwa in nace ban son shi to fa nayi k’arya Saboda son gaskiya nike mashi wanda bai k’arewa, ba 6ata lokaci na nuna mashi na amince sanin yana cikin hali ga marayun yara kuma duk da ina jin dad’i a in da nike aikatau haka na baro Abuja na dawo mu kai Aure” lamo Fatuu tay yayin da cikin ranta ta ke kokonton anya Ya Haisam zai zama mijinta ita tama fidda ran hakan, to yaushe ma ita da zata auri wani shima kuma yana can yana auren wata, Yadikko taci gaba da cewa “ina so ki sani Al’amarin mumini dukkan sa Alheri ne, in samu yay Alheri ne in ya rasa ma Alheri ne, acikin wani hadisi aka fad’i mana hakan lokacin ina zuwa islamiyya a Abuja don haka ki sa a ranki duk abunda ya faru dake mai kyau ne ki daina damuwa don duk abunda zai faru da bawa an riga da an rubuta ki ci gaba da Addu’a muma kuma muna yi maki” kai Fatun ta d’aga mata ta d’ago da fuskarta tana share mata hawayen da d’an murmushi akan fuskarta bayan ta gama goge mata tace ta tashi tayi sallar Isha sai ta ci Abinci ta amsa da to, bayan ta ci Abincin wanka tayo ta saka kayan bacci ta haye gado ta fara tunanin gwaggo tana son kiranta amman kuma tana zullumi don tasan in da Lafiya lau bata fushi ba yadda za’ai ace har yanzu bata kira taji ya suka iso ba tana cikin hakan wayarta ta fara ringing ta d’auka ta duba Kawu Amadu ne mik’ewa tay zaune ta kara wayar a kunne bayan ta d’auka, gaisawa sukae yay mata anje lafiya ta amsa kafin ta tambaye shi gwaggo yace tana d’aki shiru tay bata ce ya kaima ta ba shima bai ce zai kai Matan ba, yar hira suka yi yawanci dae lallashin ta ya k’ara yi kafin daga baya sukae sallama ta cire wayar, zaune tay bata koma ta kwanta ba gaba d’aya ta rasa ma tunanin da zata yi komae bai mata dad’i tana cikin hakan wayarta ta sake yin ringing ta kai idonta kan screen d’in sunan Ya Haisam ta gani lokaci guda ta saki murmushin da ita kanta bazata tuna when last da tayi irin shi ba don taji dad’in kiran nashi ko ba komae ta fahimci ya damu sosae da halin da take ciki, picking tay ta kara kunne kafin a hankali tay mashi sallama ya amsa mata a sake ya tambayeta ya suka isa tace mashi lpy Lou, shiru suka d’an yi sai kuma taji yace “kin daina kukan ko?” tana murmushi tace eh yace “dat’s gud ki yi hakuri haka rayuwan yake we plan but God plans d best for us and all tests from Allah are Alkhair” jinjina kai tay ta d’an had’e lips d’inta sosae take jin dad’in yadda yake mata Magana bayan d’an shiru cike da zolaya yace “kin had’u da groom d’in naki ko?” Tura baki tay kaman yana ganinta, yace “ba tura man baki zaki ba ki ban amsa” waro ido tay jin ya gane abunda tay a hankali tace “a’a ni har yanzu ban san shi ba” d’an murmushi yay sai kuma yace “Ok in kun had’u sai mu gaisa in bashi amanar ki” d’an murmushi tay bata ce komae ba yace “ko baki so?” Da sauri tace “ina so” shiru suka d’an yi can tace mashi ya Aunty Fanan yace yana wurin aiki itama tana wurin aiki tace to, “baku da Network mai kyau da na maida vedio call in ga sore eyes d’in ki” zaro ido tay da yar dariya kawae yace “ko idanun basu kumbura ba?” Tura baki tay tace “sun kumbura” lallashinta ya shiga k’ara yi suna haka yadikko ta shigo dama tana falo ita da yaran ta hana su shigo don kar su takura mata har saida tay mamakin ganin Fatun zaune tana waya kuma harda murmushi akan fuskarta ganin kallon mamakin da take mata ne yasa tace ma Ya Haisam d’in ga yadikko zasu gaisa yace Ok ta cire wayar ta mik’a mata ta fad’i mata ko wanene da sauri ta amsa ta zauna a bakin gado tana ta washe baki suka gaisa kafin ta hau yi mashi godiyar abun Arziki yace ba wani abu sosae tay mashi Addu’oi kafin ta mik’a ma Fatuu wayar tana amsa yace bari ya kyaleta ta huta sukae sallama, bayan sun gama firar Haisam d’in ta shiga yi ma Yadikko ita kuwa ganin sakewar da tay yasa ta biye mata, Washe gari tana cikin yin karin kumallo don bata tashi da wuri ba Baffanta ya shigo duk suka gaishe dashi da fara’a yabi Fatun ya samu wuri kan kujera ya zauna yana amsa gaisuwarta yadikko ma ta gaishe dashi ganin ya shirya tace har zai fita ne yace “Eh ina son zan je can jumeta ne wurin masu kayan gadon” yadikko tace “za’a d’aukko ne?” Shiru ya d’an yi kafin yace “tukunna dae kinsan har yanzu akwae sauran kud’i da zan cikashe masu dubu 200, da nayi tunanin zan samu wasu kud’i ne to amman tunda lokaci k’urewa yake zan k’ara kai shanuwa guda kasuwa sai a basu kawae” da yar damuwa yadikko tace “amman shanayen ba biyu ne suka rage ba kuma kace zaka sayar da d’aya Saboda hidimar bikin yanzu in ka saida wannan shikenan fa sun k’are” yar dariya yay yace “to ai biyan buk’ata yafi dogon buri sai a gode ma Allah da ya sa akwae” shiru kawae tay acan k’asan ranta kuwa haushi ne ya turnuke ta na Ard’o duk shi ya tattago hidimar ba tare da an shirya ba, shi yakamata ace ai yay kusan duk hidimar amman ya k’ame hannu duk tulin Arzik’in da ke gare shi, shiru Fatuu tay tana bin su da ido can kuma sai ta mik’e ta nufi cikin uwar d’akin bada jimawa ba ta dawo ta nufi gefen baffanta ta zauna da d’an murmushi ta mik’a mashi abunda ta d’aukko, bin yan kunnan dake a tafin hannunta yay da kallo kafin ya maida idanun nashi kanta cikin alamun rashin fahimta tace “Baffa wannan zinari ne kuma 200k aka siye shi in kasan in da ake sayarwa sai ka saida kayi amfani da kud’in” ba shi ba har Yadikko waro ido sukae cike da Al’ajabi baffan ya tambayeta ina ta same su ta fad’i mashi da Ya Haisam makwabcin su zai yi aure ne ya bata kud’in shine Gwaggo ta siya mata yan kunnan, jinjina kai duk sukayi a tare suka shiga yabon Haisam d’in baffan yace “to inna wuro abu mai daraja haka ai bai kamata a sayar dashi ba” yar dariya tay tace ai don ajiyar kudin aka siya tunda yanzu ana buk’ata ba sai a sayar ba, duk yadda tayi K’in Amincewa baffan yayi da a saida yan kunnan yace ta bar abunta zai mata amfani ba abunda zai gagara in sha Allah, bata ji dad’i ba ta yamutsa fuska cike da wasa yace ko tayi kuka ba zai amsa ba gwara ta adana hawayenta, can ta tuna da kud’in da ya tura mata ta siya kayan kitchen ta mik’e da sauri tace to tana zuwa, bayan ta dawo ta d’aura mashi kud’in kan cinyarshi tace “to ga wad’annan su dae dama kai ka tura man kud’in kayan kitchen to kuma an siya komae sai kai amfani dasu sannan ga Atm d’ina akwae dubu 70 a accnt d’in sai ka cire su ka had’a” baki bud’e suke kallonta ganin haka yasa tay mashi bayanin inda ta samu kud’in cikin account d’in nata 50k da Abbas ya tura mata sai dama akwae 20k cikin sauran kud’in Graduation da Haisam ya tura mata,
“Amman inna wuro ke ba amfanin da zaki da kud’in ki ne da kin bar su dama na ta6a sadakin ki” da sauri tace “a’a ba abunda zanyi da su Baffa kayi amfani dasu kawai” yace zai cire dubu 50 ta bar 20k d’in ta mata wani amfanin, sosae suka shiga yi mata godiya shida yadikko harda yar k’wallar shi yace in sha Allahu yadda ta za6i farin cikin shi fiye da nata ita ma Allah zai faranta mata haka ya shiga jera mata Addu’oi tana amsawa da Murmushi daga baya ya mik’e yay masu sallama ya tafi.
JUMETA
babban Parlor ne mai d’auke da set d’in dankara dankaran Sofas da kayan kallo irin dae falon da daka kalla zaka shaida na masu hannu da shuni ne, a kowanne 6angare na bangon d’akin akwae hotuna wanda yawanci duk na yan siyasa ne kama daga d’an majalisa, governor harda na shugaban k’asa, zaune a saman 3 seater Alhaji lawal ne yana sanye da farar jallabiya idanunshi sanye cikin glasses yana kallon labarun yamma a kai akai yake juyawa gefenshi ya kalli Matar shi Hajiya Rabi’atu dake gefenshi tana mashi hira, babbar mace ce saidae bata manyanta ba sosae kana kallonta zaka fahimci hutu ya zauna mata sosae, tana da kyau ba laifi gata jajir da ita sannan tana da k’iba ba irin mai muni ba jikinta sanye da had’addan lace ta kashe d’auri kana kallon ta kaga wayayyar bafullatana, da yar sallama ya shigo cikin parlon duk suka d’aga kai suka kalleshi, matashi ne wanda a k’alla zai iya yin shekaru 35, dogo ne sosae sai dai sam bai da jiki kuma ja ne irin kalar fatar Mahaifiyar shi har kama suke ga sumar kan shi da ta k’ara bayyana shi a matsayin bafullatani don a nad’e take amman bata da yawa, jikin shi na sanye da bak’in silk wando da blue riga mai dogon hannu da ma6allai ya yi zanzaro hakan ya bayyanar da had’addan bak’in belt d’in dake d’aure a k’ugunshi haka hannun shi na sanye da wrist watch silver, saman kujerar dake opposite da su ya zauna fuskar shi sam ba annuri ya gaishe da su duk suka amsa Alhaji lawal yace “Khalid ka dawo?” Amsa mashi yay da “Yes Dad”
“To ya aikin?” yace “Alhamdulillah” ita dae Hajiya Rabi’atun kallonsu take tana murmushi,
“Dama dalilin da ya sa na kira ka don in sanar da kai Amaryar taka ta iso tun jiya don haka sai ka samu kaje ku gana da juna, sannan duk abunda ya kamata kayi in kaje sai ka tabbatar kayi ma’ana ka sallame ta da abunda zata yi hidimarta don kasan 2 weeks ya rage so we need not to waste time” wani irin k’ara d’aure fuska Khalid d’in yay har saida Dad d’in yace bai ji bane sannan kaman an masa dole ya ce “Ok” kallon Hajiya Rabi’atu yay yace “Ke wurin ki ina fata kin kammala komae” tana murmushi tace “Eh an kammala had’a lefen dama abunda ya rage akwae kayan da za’a d’inka mata already na fitar dasu suna ma wurin d’inkin to amman ba’a d’inka ba Saboda rashin measurement nata tunda ba saninta mu kae ba amman tunda ta zo yanzu ko zuwa gobe sai Sadeeya taje da driver su taho tare aje a d’auki measurement d’in nasan ba 6ata lokaci zai d’inka” jinjina kai yay alamar gaisuwa sai kuma ya maida kallon kan Khalid yace “kai yaushe zaka je d’in?” shiru ya d’an yi sai kuma ya watsa hannu yace “ko Next tomorrow tunda naji zasu wurin d’inki goben” shiru Alhaji lawal d’in ya d’anyi yana d’an tunani can yace “kai yakamata kaje goben ku ga juna zuwa wurin d’inkin sai a bari sai Next tomorrow d’in” d’an yamutsa fuska yay yace Ok daga haka ya fara kokarin tashi ya tambayi shikenan Alhaji lawal d’in yace eh zai iya tafiya yay masu sallama ya nufi hanyar fita…………….
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.