Novel Document

Anya Baiwa Ce Hausa Novel Complete Document

An Ya Baiwa Ce Complete Document

Written By: Ameera Adam

Tafe take tana ɗan waige dan gudun kar wani ya ganta ko taci karo da wani a hanya, saboda abin da ta gano take san zuwa ta isar da shi ko ta samu ɗan alheri, aikuwa batayi aune ba tana shiga soron tsakiya suka yi gware da mutum a zabure ta ja da baya tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tayi tseren gudu, kallan tsaf yayi mata yana karantar yanayinta yasan tabbas akwai abinda ke ƙunshe cikin bakin ta, aɗan diriri ce ta kalle shi ta ce.

“Yautai mugun tsuntsu masha miyarka sai yayi dare”

Kallanta yayi sai da yayi murmushin gefen baki yana ƙara karantar yanayin ta sannan ya ce, ” Tauraruwa mai wutsiya…, Kura kike ga tsoro ga ban tsoro. Ina zaki kike sauri kina ta juye-juye haka? ” Sai da ta juya hagu da dama ta kuma leƙa soron ƙarshe tana mai miƙa wuya cikin ƙasa da murya ta ce, ” Gobara daga teku maganin ta sai Allah, wata ƙura ce take ƙoƙarin kunno kai a cikin gidan nan amma karka ce kaji daga baki na ” ta ƙarasa magana tana kuma duba gabanta da bayanta.

“Jakadiya Kubura kenan, ay harbi ga ɗan jaki gado ne, kuma iya ruwa fidda kai gayamun ina sauraron ki kowa ya biya allon sa ya wanke ” ya faɗa cikin son jin labarin.

Sunkuyowa tayi dabda shi sannan ta ce, ” Kasan koda girgiza kurna tafi magarya, mai tsoron a mutu shi yake maho ” Ƙara gyara tsayuwarta tayi sannan ta ce, ” Ƙaramar kyauta tafi babbar rowa ” ta ƙarasa faɗa tana miƙa masa hannu alamar ya bata wani abu.

Ya gano abinda Jakadiya ta ke nufi, dan haka ya sa hannu cikin aljihu ya ɗebo mata silallah ya zuba mata akan hannun ta yana faɗin, ” Ke dai ciki kike mai manta kyautar jiya, kuma Kura kike mai manta alherin baya”

Juya su tayi cikin jindaɗi ta kunto bakin zaninta ta ɗauresu tana faɗin, ” Domin rana ɗaya ba’a ƙin zuguri, kuturu da kuɗinsa alkaki sai na ƙasan langa, buɗe kunnen ka yanzu zaka sha labari, ashe Fulani Zaliha ciki gareta har ya girma, kasanta da shegen nunkufurci ba ta cika bada fuska a shiga sashenta ba ” zaro idanu yayi waje shima yana waigen bayansa sannan ya ce, ” Lallai tsugunne bata ƙare ba ansai da kare an sayi Mage, naji daɗin wannan albishir naki jeki anjima zan neme ki ” ya faɗa yana yin gaba abinsa.

Jakadiya Kubura ta fahimci sarai inda maganar Galadima ta dosa har yaje bakin ƙofa ta ce masa, ” Injunan ka sammako wani tafe ya kwana, kuma hargagin ɗan damisa bashi tsorata Namijin zaki, ka taka a sannu kasan Fulani Maryama ba kanwar lasa ba ce ” kamar bazai bata amsa ba sai kuma ya juyo ya ce mata, ” Tabbas inkaji mutum na tsoron dare ba’a ɗaure shi ya ƙwance bane, Ki bar ganin allura ƙarama itama ƙarfe ce, dan haka bazan ce miki komai ba mu zuba mu gani kowa tasa ta fishsheshi ” yana gama faɗa ya sanya kai ya fice daga cikin soron.

Bin bayansa tayi da mugun kallo sannan ta ce, ” Mai ƙafa huɗu ma ya faɗi bare mai biyu, ajuri zuwa rafi wata ran tulin zai fashe ” tana faɗa ta juya ta cigaba da tafiya, kai tsaye sashen Fulani Maryama ta nufa.

Karanta>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel – Aihausanovels

Tana shiga ta zube ƙasa cikin salon kirari ta fara magana, ” Barka da hutawa Uwargida na bango madafar bayi, uwar marayu uwar mara gata mai iyayenma kin gamai musu komai, Ƴar sarki jikar sarki Matar Sarki kuma gaki Uwar Sarki, Allah ya ƙara girma ya raya mana Yarima mai jiran gado, Mulki da Sarautar Masarautar Kano gaba ɗaya ta ku ce, Mai Uwa agindin murhu bazai ci miyarsa lami ba… ” murmushi Fulani Maryama tayi saboda jin daɗin kirarin da Jakadiya tayi shiyasa ma ta katse ta da faɗin, ” Jakadiya anjima zan turo da saƙon maɗi mai ke tafe da ke?? ” russunar da kai Jakadiya tayi tana mai sauya yanayin fuskarta cikin damuwa ta ce, ” Tuba nake Uwar gijiyata banzo dan isar da mugun labarin nan dan wata manufa ba sai dan ki tashi tsaye ki ɗau mataki kuma asan abin yi, Kaicona da tuntuni ban ankare ba har lamarin ya girmama, amma dukda haka ba za’a rasa abinyi ba dan ba’a rasa nono a riga, ina mai neman gafarar ki saboda labarin bamai daɗi bane ranki shi daɗe ”

Tunda Jakadiya ta fara magana Fulani Maryama gabanta ya yanke ya faɗi saboda tasan labarin bazai mata daɗi ba, shiyasa a hargitse ta wurgo mata tambaya, ” Jakadiya banasan Kewaye-kewaye tafi kanki tsaye, Me yake faruwa ne?”

Jakadiya kara sauya muryarta tayi ta ce, ” Ina neman gafararki da jin kalamai na dama Fulani Zaliha ce ke da juna biyu, kuma ayanayin dana lura har yayi ƙwari…” cikin tsananin tashin hankali Fulani Maryama ta ƙunduma wani ashar sannan ta ce, ” Aikin me kike tun tuni baki sanar dani ba tunda wuri? ”

Karanta>>> Abban Sojoji Book 2 Complete Novel

Jakadiya ta bata amsa da, ” A gafarce ni Uwargijiya ta kinsan Yarinyar da nunk…”

Katseta Fulani tayi cikin tsawa ta na faɗin, ” Ya isa haka, Lallai Fulani Zaliha ta ɗebo ruwan dafa kanta, Samun sararin kuturu gaɗa a cikin rama, wato haka ta miƙe ƙafa da yawa? Lallai abinda ya faru a shekarun baya dole ya ƙara faruwa yanzu, tabbatas dole labari ya ƙara maimaita kansa, Aikuwa kowa yaci tuwo dani miya yasha, tashi kije Jakadiya anjima zan neme ki bayan Sallar Isha’i ”

Jakadiya najin haka ta kuma rissinawa ta ce, ” ALLAH ya huci zuciyar Fulani, Ramin kura da wuyar shiga a gayawa kare yayi hankali, tabbas bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane wace ce Fulani Zaliha da zata iya haɗa sahu da Uwar ɗakina, ni mai bin Umarnin ki ce akowanne lokaci ” Jakadiya na gama faɗa ta tashi ta fice zuciyarta fess saboda tasan ba ƙaramin alheri zata samu ba.

Karanta>>> Boss Lady Romantic And Comedian Novel Complete

Tunda Jakadiya ta fito daga ɗakin, Fulani Maryama ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da komawa take, abun duniya gabaɗaya ya isheta, ita kaɗai sai saƙa da warwara ta ke tana san nemarwa kanta mafita, Jaririnta ɗan kimanin wata biyar da ke kwance ta je tasa hannu ta ɗauke shi tana juya shi cikin zuciyarta da shawarar da ta yankewa kanta.

A fili ta fara surutai kamar wata zautacciya, ” Yarima yanzu kai ake shirin yiwa kishiya a gidan nan, tabbas bazata yuwu ba tunda ban bari wata ta haifi namiji ba dole na dakatar da cikin Zaliha ”

Jakadiya tunda ta fito daga sashen Fulani Maryama kai tsaye sashen su ta wuce tana zumuɗin sauraron kiran da Fulani Maryama ta ce zata yi mata, kamar wacce a ka mintsina tashi tayi ta fito daga sashen bayi wani gida ta faɗa bakin ta ɗauke da sallama, ” Balaraba matar Ciroma dake tankaɗe ta amsa mata sallamar tana faɗin.

 

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Danna Inda Aka Saka Download

 

Back to top button