Gargadar So Chapter 121 By M Shakur
Mom tai murmushin jin dadi ganin yanda yaronta yatafi, Baba da Ammi ma sunji dadin abinda Khaleel yayi Excellency ne cikeda so yace “it’s okay Hawwa na, he will come around, je flat naku kihuta I want to talk to your parents” gyadama Excellency kai tayi tamike tsaye ahankali tana tafiya da kyar tasa hannu tabude kofa tafito, da hankali da hankali take tafiya har zuwa side nata tabude kofa tana shiga tawuce carpet na tsakiyan falon kawai ta kwanta tana kuka mai radadi da soya zuciya.Kallonsu Baba Excellency yayi yace “daga Khaleel har Hawwa duka yarane, duk mu bisu a sannu muna correcting nasu, shima Khaleel din bawai he’s innocent bane, duk matsalan shi ta haddasa wannan fadan, d’ana na shaye shaye” Excellency yafadi ahankali there no point aboye an zama daya yanzu, daga Baba har Ammi suka kalleshi dan basu dauka zai iya fadin kalan maganan ba, ahankali Excellency yace “duk laifi nane inason Khaleel da yawa da nakasa gyara kuskuren shi but namuku alkawari komi zai chanza daga yanzu zamu tsaya tsayin daka akanshi ya gyaru”Excellency yace “kuma dan Allah Malam da Hajiya kada ku kara tabamin yarinya kuka kara dokanmin diya shari’a zanyi daku sosai” dan murmushi both Ammi da Baba sukayi Ammi tace “diyar taka akwai taurin kai ne amman za’a kiyaye harda fushi” Excellency yace “ga abin doka Khaleel ba’a dakaba sai iya” Mom ta tashi kaman ba itaba anatse tace “ko ruwa ba’a baku ba” shi kanshi saida Excellency ya kalli Mom but harta wuce Excellency yakalli su Baba yace “kar maganganun da Zainab tayi yasa ku dauka Hawwa zata wahala ko zata takura mata bar Zainab da masifa amman batada mugunta, abu kadan Hawwa zata iyayi ta sace zuciyanta” Baba da Ammi sukai murmushi saiga Mommy tareda ma’aikata dasuka dauko hadaddun ubansun trays dake dauke da drinks da ruwa da kulolin abinci da su fruits duk aka ijiye a tsakar falon Excellency ya sauko yace “bismaillah Malam” Mom ta kalli Ammi ahankali tace “ni banson bakunta fa” Ammi cikeda raha tace “kikazo gidana Allah sa kada kiyi” Mom ta sauko Ammi ma ta sauko suka shiga hira da Mom har tana tambayan Ammi garinta suna hira sosai kaman ba fada yaransu suka gamayi ba sai wajajen shabiyu sukace zasu tafi har waje su Excellencu suka rakosu Ammi tace “bari taga Hawwa” tawuceHawwa na kwance akasan Ammi tabude kofan dakin ta shigo tana kirne fuska Hawwa na ganinta ta tashi zaune da sauri tana goge fuskanta Ammi tayi kaman bataga tana kuka ba, tace “abu daya nazo gayamiki kije tiktok ko IG kiyi searching M Shakur ki shiga class dinta na Kissa training da Intimacy ki koyi yanda ake abubuwa, idan zaki zage damtse kiyi zaman aure kiyi Hawwa, ga mijinki nan yayi fushi dake, tun wuri kafin dare yamiki kisan yanda zakiyi ki lallaba ki shawo kansa ku shirya, ni natafi zaria bazan kara dawowa Abuja sabida kin tapka hauka ba kome kika shirya yi kiyi, duk abinda zakiyi ki tabbatar kinyi kin shawo kan Khaleel kafin ya tsaneki da gaske” Ammi tayi kofa daidai zata fita taji Hawwa ta kama mata hannu dasauri Ammi tajuyo sai kawai Hawwa ta rungumeta tama kasa magana kuka kawai take jikin Ammi, ga jikinta yayi zafi, Ammi na so ta karaya but ta tuna this is the same thing she did jiya ta tausaya mata tahakura amman da safiyan Allah tayi shirmen dayafi na jiya so taji ajikinta, cireta kawai tayi daga jikinta tajuya abinta tafice tarufo mata kofa Hawwa ta tafi wajen window taga su Ammi sun shiga wata mota daban da yaron daya kawosu sun tafi.Komawa Hawwa tayi tasake zama sai kallon kofa take jira kawai take Khaleel yashigo ahaka wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, tana cikin bacci taji motsi dayake batai nisa a baccin ba da gudu tabude idanunta Khaleel tagani awajen kofa yana fita dawasu manyan akwatinan shi na LV guda biyu, mugun faduwa gabanta yayi da gudu ta tashi kirjinta nawani irin bugawa tayi wajen kofan tace “Khal…..” mugun kallon daya mata yasa takasa karasa kiran sunansa kawai yaja kofan ya kulle yawuce abinshi, Hawwa tayi wajen window dagudu tadaga labule taga flat dinsu yashiga da akwatinan sai kawai taji kuka yazo mata saida taji ana salla ta iya barin wajen tawuce dakinta bayi ta shiga tayi alwala, tafito tazauna kan dadduma tayi salla ta kwanta akan dadduma tana wani kalan sauke ijiyan zuciya her heart is so heavy kaman an daura mata manya manyan duwatsu, takasa cin abinci takasa bacci sai kuka har bayan sallan isha da kyar ta tashi tajawo wani first aid box taga PCM tadauka tasha ta mike ta tsaya tsaye wajen window ta tana kallo babu Khaleel a compound din, ina yaje? She’s missing him, wayanta ta dauka ta zauna bakin gado tai dialing number shi saitaji ana cemata number shi bayama kan network gabaki daya ijiye wayan tayi ta tashi tafada bayi da kyar tai wanka tafito tasaka wani sexy rigan bacci ta feffesa turare sai kawai tawuce ta tafi dakinshi tabude ahankali everything smells like him, zama tayi abakin gadon ahankali tana kallon gadon tana tuna how happy Khaleel use to be, his full smile yana kallonta, his loving eyes, his erotic talks, his sleep, yanda yake kankameta, yanda yake bacci ajikinta, yanda yake tashi da kyar, the way yake amsawa ummm idan ta tadashi, the way he acts like a baby, the way he dances for her, the way yake tsokanan ta, the way he calls her Kulu, Yar Sanda, muguwa menene menene, bata taba sanin she loves all the moments ba sai yanzu, like she will give anything just to experience those moments one more time yanzu, hawaye masu dumi taji yana bin hancinta yana diddiga ta tip na nose nata yana sauka a hannunta dasauri ta share da bayan hannu kaman mai mura cikin wani irin murya na ban tausayi da nadama da dana sani tace “I am sorry Khaleel!” Sake goge hawayen tayi tace “I really am, I’m badly sorry Khaleel, I miss you, I missed everything about you, please come back to me kayakuri” tayi maganan tana kwanciya ta kifa kanta jikin pillow dinshi Hawaye na gangarowa daga idanunta tana kallon kofan tamika hannu tadauki pillow daya ta rungume a kirjinta tana kallon kofa har 2 nadare takasa bacci ta tashi taje ta dauro alwala tadauko hijabinta tadawo dakin tai salla har four sannan bacci ya iya kwasheta akan dadduman.


