Uncategorized

Matar Makaho Part 8 Hausa Novel

 

MATAR MAKAHO

Chapter 8

“Ni Kaya na saya” ta basa amsa

Wani irin Kaya kenan?

sannan Ina Kayana?

“Nina yarda kayayyakin ka duka sabo na sai maka Naga nakan sun kode,Amma kayi hakuri bazan sake ba” tace tana Kama hannunsa dake kokarin zare jallabiyan jikinsa

Sumayya akan me Zaki sayamin Kaya bazaki fad’a mini ba saboda bani da ido saiki zo ki musanya mini,kamar wani yaro.

“Kayi hakuri kaga yanda jallabiyar nan ta karbe ka kuwa yayan khadija” tace ta ja maza zip in gaban jallabiyar,hade da d’aukar Turare ta fisa Masa,vayan ya shafa Mai 

Nagode Allah ya miki albarka ya hanani Miki butulci a rayuwa Sumayya

“Ameen” tace tana jera abincin karyawan, Bismillah ta Masa suka fara ci cikin kwanciyar hankali

Bayan sun  Gama cin abinci  tattara Kwanukan yayi yakai waje,bayan ya ajeye, d’akin yadawo 

“Toh yayan khadija wacece kamila”Sumayya ta tambaye sa 

Nifa nayi Miki Alkawari ,ai basai kin Kara tambaya taba nida kaina Zan fad’a Miki kome Daya shafe kamila.

“Uhmm ba Dole na tambaya ba tunda sai jamin Rai kake yaufa da wure na Gama aiki Amma sai wani sham kamshi kake”

Nasha kamshin, kema saiki Rama.

“Wallahih ka Gama iyya jarabanka bazan biye maka ba sai naji lbrn nan ehen”

Toh zoki zauna a kusa Dani samun lbrn yafi Dadi,yace Yana zama akan kujera

Saboda tsabar sonjin lbr yasa Sumayya mikewa da sauri tazo Kan kujeran ta xauna kusa dashi

Hannu yasa ya matsota jikinsa a hankali ya rungume ta a jikinsa cikin sanyin hallintarsa murya a sanyaye yace Sumayya!

“Na’am yayan khadija”

Yau Zan baki labarin kamila Amma saikin ji labarina Nima kafun ki gane lbrn kamila dakyau.

“Yauwa Aiko Ina sonjin lbrn ka da dangan takarka da gidan ADARA duk da Ina tunanin dangin mahaifinkane Amma halayenku sun banbanta,hakan matsayinka da khadija a gidan nan na fahimci a kaskance kuke ba Kamar sauran Yan gidan ba”

Duk xakiji insha Allah Koh Nima Zan samu amsar dalilin auren mu Wanda har yau bansan dalili ba.

“Wai kana nufin ba Kaine kace kana Sona ba,aka aura maka ni “?ta tambaye sa cikin zare ido. 

Nima ban sani ba Sumayya bansan dalilin auren muba Amma koma menene inaji a jikina insha Allah haduwar mu dake alkhari ce

 

“Insha Allah insha Allah yayan khadija” tace tana share  hawaye Daya gangaro mata

Gyara zama Al’ameen Yayi a hankali ya fara magana…………….

 *Shikaru Talatin da biyar da suka wuce baya* 🕢

Malam Yusuf sumul, shine cikekken sunansa da aka Sansa dashi matashine Dan shikara 35,Yusuf mutum ne Mai Hakuri addini ga kawaici baid’auki duniya da zafi ba,Yana da tsananin zurfin ciki duk yanda zaka zauna dashi bazaka taba fahimtar wani abu a tattare dashi ba shiyasa ba Wanda yasan shid’an inane Koh daga Ina yake, duk da kowa ya gansa Kuma yaji yanayin hausar sa da maganar sa Dole yasan cewa ba D’an kasa bane .

Alhaji Rabi’u ubangari. Wanda akafi sani da ubangari,maikacin gonnati ne Kuma Mai rufin asiri sosai,Yana da Mata biyu.

shine Mai gidan Yusuf, saboda tsananin hankali da nitsuwar yusuf yasa ya d’aukesa Kamar D’an gida ya basa d’aki a cikin gidansa,Yusuf na Masa aikace aikace kamar zuwa kasuwa wanki da gugan kayan yaransa da NASA na kansa Yana Kai kananun yaransa makaranta ya dawo dasu,

Yaran ubangari guda biyar ne sai yaran Yan uwansa maza biyu Mata hudu,kenan yara goma Sha D’aya ne a gidan ubangari

Zainab Fatima Auwalu lukman Nasir,sune yaran ubangari na cikinsa

Haidar Umar khairat munira safara’u murja sune yaran Yan uwansa Dayake rikewa

Yusuf da ubangari akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu duk da baisan Yusuf ba Amma da zuciya d’aya yake zaune dashi ganin tsawon shikaru Bai taba nuna wani mugun halinsa Wanda mutane zasuye Allah wadai dashi ba.

Yaran gidan na basa girmansa kasancewar duk yaran gidan ya fisu a shikaru,yanajin dadin zaman gidan sosai don tun kafun Alhaji yayi aure suke tare har Allah yasa yayi aure 

Yaran suna ganin girman Yusuf saboda yanda mahaifin su ke tare tashi hakan yasa suke kiransa da bappa yusufa

Zaman Yusuf a gidan ya fara gunduran sane bayan girman Yar Alhaji Rabi’u ubangari zainab,wance Allah ya diga Mata son yusuf Mai tsanani duk da a lokacin tana da shikaru 14 yayin da Yusuf keda shikara 35    

Tun tana boyewa har abin ya gagara ta tinkare Yusuf da maganar.

Sosai Yusuf ya ja Mata kunne akan zancen kuma ya tabbatar Mata shi bazai aureta ba donshi a matsayin diyarsa,ya d’auketa duk yanda tayi kokarin ganin tashawo Kan Yusuf abin ya gagara,taso fad’awa  mahaifyarta zancen tanason Yusuf Amma khairat Yar bappanta ta hanata saboda tasan mundin maman zainab tasan zancen daker zainab ta aure Yusuf.

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 1 HAUSA NOVEL”


 ADARA FAMILY HOUSE haifafun jalingo ne tun iyaye da kakanni anan gidan Adara suka tashi don duk fad’in sintali ba gida Mai dumbin tarihi da shikarun mazauna ciki irin family ADARA tun husul sai chanje chanjen gini da ake in zamani ya shude,

Tun husul ma haka suke mutane ne masu masifan tsiya ga fad’a kamar ahlin dambe shiyasa aka musu lakabi da ADARA  

Aishan ADARA  d’aya ce daga cikin yaran gidan adara ,macece Mai matsifa na bugawa a jarida duk yanda kaga mala’in yaran gidan ADARA Aisha ta damasu ta shanye saboda tsananin masifarta yasa Koh saurayi Bata dashi don a lokacin abin kunyane mace takai shikara 20 batayi aure ba Amma Aisha shikarunta 20 Koh saurayi Bata dashi saboda tsananin tsoronta da maza keye 

Gidan ADARA tun asali haka yake har wa yanzun.

Aishan ADARA na Saida Dan wake a bakin kasuwan main market na jalingo

Sun hadu da Yusuf ne lokacin da yaje kasuwa sayayyan kayan Miyan gidan ubangidansa,ya saye danwaken ta by mistake robanta ya fashe a hannunsa,

Ba karamin bala’i Aishan ADARA ta sauke Masa ma kwando kwando da Kuma uzzurawa saiya biyata robanta 

Yusuf Kam ba karamin mamaki yasha ba ganin irin bala’in da Mai danwake ke Masa akan robanda Bai wuce sule biyar ba sai bala’i take Masa Kamar ya Mata Satan jari

Sosai Yusuf yaji haushi kala baice Mata ba ya Kama hanya Yana tafiya itakam sai binsa take sayya Biya robanta

Yusuf kam yasha Alwashin bazai biya ba ganin jarabanda take Masa haka tayita binsa harya Gama cefenen ya Kama hanyar gida bayan ya tare machine.

Duk jaraban Aishan ADARA yau taga iyyakarta don ba zagi ba duka da Mannin hauka Yusuf ya rabu da ita

Bayan dawowar Yusuf gida Sam ya rasa sukuni,tunanin Mai danwake Kam ya hanasa sukuni Sam

Ta bangaren Aishan ADARA ma hakane Sam bayan tafiyar kyakkyawar mutumin da Bata Sansa ba  gabaki daya ya hanata sakat a tsawon shikarun ta Bata taba bi takan soyayya ba Amma wannan Karo tayi tuntuben so a bakin titi Wanda Bata San inda zata sake ganinsa ba

Bayan sati biyu Sam Yusuf ya kasa sukuni ya kasa hakuri sosai Y’an kwanakin nan ya gane meke d’awainiya dashi,sai a lokacin yaji tausayin zainab Ashe haka takeji yake wulakanta ta,

Farga bansa d’ayane kar yaje gareta da soyayya ta tsigalesa don Tabbas daga ganinta Yar bala’i ce sosai Abu na biyu Kuma asalinsa kar rashin sanin danginsa yasa a hanasa auren ta.

A hankali Yusuf ya fara zuwa gun Aishan ADARA cin danwake Wasa Wasa harya kasance ba ranan da baya zuwa ci haka ba ranan da basa fad’a a tsakaninsu kafun su rabu ,har shakuwa yazo ya shiga tsakaninsu Mai tsanani Wanda a zahiri kowa son junane ke d’awainiya dashi,Amma ya kasa sanar da D’an uwansa

A hankali Yusuf ya fahimci masifar Aisha a tarbiyan gidansu  yake a Hankali ya Soma nutsar da ita sosai yake nuna Mata abin Bai dace ma Abu kamar Wasa Aishan ADARA ta nutsu sosai sai dai fa har lokacin in ka tabota zaka Sha bala’i sai dai in abinda ba ruwantane Bata Shiga haka zalika ta daina dambe da kowa,abin harya fara bawa jama’a mamaki sauyawan ta

Lokaci da Yusuf ya bayyana ma Aisha soyayyarsa gareta Babu wani jinkiri ta amsa sosai  suke zuba love

Yusuf ya samu Alhaji akan maganar Aisha ba karamin murna alhajin yayi ba dayaji Yusuf ya samu wance yake so don burinsa kenan,ya tambaye Yusuf danginsa don maganar aure Dole ana bukatan dangi na jini

Hankalin Yusuf ya Tashi matuka don har kwanciya yayi a gadon asibiti Akan zancen danginsa da Alhaji ya matsa Masa akai

Karshe dai fa ubangari yaga abin fa nayine yasa sa hakura da tambayar Yusuf shi yashiga maganar auren Yusuf

Da yake ubangari ya jima tare da Yusuf kowa gani yake kamar Yan uwane hakan yasa ba dogon zance aka basa auren Aisha don Suma sun Matsu tayi aure ganin ta girma a gida

Ta bangaren zainab Yar ubangari Kam in hankalin ta yayi dubu ya Tashi tayi kuka tayi kuka Kamar zatayi hauka Amma khairat ta taka Mata birki tare da Mata alkawarin sai Yusuf ya aureta amma tabare ayi auren taga matakin da zata d’aukar Mata

Bayan auren Yusuf sumul da Aishan ADARA, Alhaji yaki yarda Yusuf ya Kama gidan haya a gidansa sukaci gaba da zama, soyayya suke shimfid’a wa Mai tsafta sosai Aisha ta nutsu suna zaune da yaran ubangari da matansa  lfy Sam bata nuna musu Yar Hali  sai daifa basa shiri da zainab ganin kallon banza da take mata

Sai Bayan shikara uku da auren Aishan ADARA da Yusuf kafun Allah ya baiwa Aisha ciki sosai sukayi farinciki da wannan cikin da Allah ya azurtasu,sukaci gaba da rainon cikin cikin farin ciki

Bayan Aisha ta haihuwa sun samu d’a namiji Mai matukar Kama da mahaifinsa Kamar an tsaga Kara,  mahaifinsa yasa Masa suna muhammad.

Mahaifiyarsa na kiransa Al’ameen.

Da sauri Sumayya ta d’aga ido tana kallon Al’ameen dake Bata lbr”kana nufin kace mini gidan n……..”

Bai bare ta karasa ba ya girgiza Mata Kai Yana Kara kwantar ta ita a jikinsa,ki aje tambayoyin ki Inna Gama saiki tambaya

Kai kawai ta gyad’a Masa 

Ya cigaba…..har lokacin zainab Bata saduda da soyayyar Yusuf ba don a lokacin ta kammala secondary school nata,Amma Taki aure Dole yasa babanta nema Mata wani makarantan gaba da secondary taci gaba 

Bayan haihuwa Al’ameen da shikara uku Aisha ta Kara haihuwar wani da namiji yaci sunan Salim, tun daga lokacin Aisha Bata sake samun ciki ba,sukaci gaba da kula da yaransu don a lokacin Alhaji ya budewa Yusuf shago yabar aikace aikacen gida basuda wata matsala sai na d’ansu Salim Wanda ke fama da mummunan ciwon zuciya,duk bayan wata D’aya sai sunga likita Kuma sai anci kudi.

A hakan rayuwa tayita tafiya yau Dadi gobe akasinsa Al’ameen da Salim suna matukar samun kula daga iyayen su suna Isa shiga makaranta aka sakasu yarane da suka shagu da junansu matika Kamar wasu tagwaye Dayake Salim nada gaban girma tuni ya tsara da yayansa har lokacin Aisha Bata San cewa Yusuf ba Dan uwan Alhaji bane duk da tana yawan tambayan sa labarin Yan uwansa Amma Yusuf daga tayi tambar saiya hau hada Mata fuska

Bayan wasu shikaru lokacin Al’ameen nada shikara 11 Salim nada shikara 8 a duniya. Aisha na d’auke da karamin ciki.

wata ranan juma’a da zuriyan yusuf bazasu taba mantawa da ranan b a tsawon rayuwansu ba har Abada ciwon bazaibar  zukatan su ba

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 2 HAUSA NOVEL”


Da misalin karfe bakwai na dare yusuf ya dawo gida,Yana kokarin shiga shashen su sai ga khairat taresa tayi cikin kuka Wai zainab ba lfy  tana dakinta Alhaji yace yaje su kaita asibiti

Da gudu yusuf ya bi bayan kairan zuwa shashen Yan matan gidan,shiya fara Shiga d’akin Yana shiga khairat taja kofar ta rufe kofar ta waje da makulli.

Yusuf na shiga d’akin ya ware ido ganin zainab ba Kaya daga ita sai d’aurin kirji a zaune akan gado

Tambayar ta yusuf ya farayi, zainab menene haka Kuma ki nemi riga ki saka yace Yana Mai kokarin bude kofar

Dariya zainab ta sake hade da furta wallahih kaji na rantse maka Yusuf tunda ka hofantar da soyayya ta kasa kafa ka shureta Nima saina jazamaka bala’i inda zaisa ka aureni Dole wannan itace kad’ai abinda zanyi na mallakeka,ka ‘dauka Koh shurun da nayi na hakurane?

Ah ah wallahih ban hakura ba tanadi nake maka.

Subhanallah shine abinda yusuf ya furta cikin gigita, zainab Ashe bakida hankali wani irin shirmene haka

Hauka zakace ba shirme ba tabasa amsa tana matsowa garesa hade da fizgo kwalar rigansa ta yaga sosai tana ihu

Sosai yusuf ya razana ya Shiga kokarin k’wace kansa

Khairat Kam tana rufe d’akin ta tsaya kamar minutes biyu kafun ta fara rafka salati a tsakar gidan wayyo jama’a wani zaima zainab fyade a d’akinta yanzun nazo shiga kawai naji kofa a rufe zainab nata kuka ku kawo d’auki

Da gudu Yan gidan harda Aisha  da makwanta Dayake darene ga madalisa a kofar gidan  suka ruga da gudu zuwa d’akin zainab da suke Jin kukanta na tashi har lokacin

Jin kofar a rufe yasa matasan samarin unguwan suka dauko katon itace suka bugawa kofar take kofar ta balle,cikin mamaki tsoro Al’ajabi suka zubawa d’akin ido ganin abinda ke faruwa kamar a mafarki y.

Yusuf ne kwance akan zainab suna dambe

Salati dumbin Alumman dake wajen suka sake,zainab Kam da sauri ta sake Yusuf ta matsa gefe tana kuka da rawan jiki 

Yusuf Kam ya kasa magana sunkuyar da Kai kawai yayi don bazai iyya hada ido da ubangari ba 

Yusuf Ashe Kai Maci Amana ne Yusuf Ashe Kai mugune Yusuf shiyasa tsawon shikarun nan kake zaune Dani da fuska biyu azzalumi maha’inci   kawai wallahih nayi Dana sanin zama dakai, Allah ya isan mini tunda ka rasa Wanda zakabi sai Yar cikinka,yace hawaye na taruwan Masa a ido,matasan samarin nan basuye wata wata ba suka rufe Yusuf da duka duk yanda yaso musu bayani Basu basa dama ba

Aisha Kam ba karamin shock ta Shiga ba Daman Yusuf ba D’an uwan ubangari bane? shiyasa inta tambaye sa Ahlinsa sai yahau fushi Ashe baida gaskiya ne kwata kwata, Aisha Kam kuka take tana dana sanin Yusuf, ya zubar Mata da mutunci ya ha’ince  ta

Matar ubangari waya ta d’auka ta Kira police lokacin Amma Yusuf jina jina Koh tsayuwa baya iyyayi,ga matan sa da yaransa duk suna kuka, A lokacin yaran basusan me uban yayi ba Amma tabbas sunsan ba lfy

Police na zuwa daker suka k’wace Yusuf ganin ana kokarin kisan kai, lokacin da police suka Kama Yusuf za’a fita dashi cikin tsananin azaba yake rokonsu su barshi yaga MATARSA zai Mata magana.

Ba musu domin tabbas su kansu police a lokacin sunji tausayin sa sosai da sosai,wani ne a cikinsu ya taimaka Masa suka nufi wajen da Aisha ke duke tana kuka

Yusuf na Isa dukawa yayi yasa gwuwarshi a kasa cikin galabaita ya fara magana, Aisha Koh kowa zai yarda akan abinda yafaru don Allah Aisha ke kad’ai  ki yarda Dani, yardan ki kawai nafiso akaf fad’in duniyan nan bayan yardan Allah,don kece abokiyar rayuwa ta in kowa zai juyamin baya ke Kika rungumeni bani da kaito Aisha Ina neman Wannan alfarman. ya karasa maganar hawaye nabin fuskar sa 

Aishan ADARA Kam yau Hali ya motsa jikinta har bare yake cikin kakkauran murya ta mike ,Yusuf Yusuf wallahih nayi Dana sanin haihuwa da Kai Yusuf, nayi Dana sanin auren ka Yusuf ka cuce kanka ka cuceni Yusuf bana bukatar ka a rayuwa ta ni daga yau mijina ya mutu.

Sosai Yusuf ya fashe da kuka maicin Rai Wai waye zai fahimce sane kowa bazai yarda dashi ba kawai don an gansa a d’akin yarinya Babu bincike sai kawai ad’au mataki, me yasa tunani bazaizo musu ba duba da cewa ya rasa inda zai nemi zainab sai a cikin gidansu?

Yunkurin magana yafara ais……,da saure Aisha ta d’aga Masa hannu Yusuf Koh Babu Kai zamu rayu da yarana Koh bakai Zan iyya rayuwa Koh ba Kai rayuwar zata Mana Dadi,Amma zaman ka acikin mu shine kuncinta ka tafi bana bukatarka a yanzun,tace tana Mai kokarin baren wajen.

Da sauri yusuf ya Kama hannun Aisha,bataye wata wata ba ta tsinka Masa Mari.

Da sauri Yusuf ya sake Mata hannu

Da sauri Al’ameen Yayi wajen babansa cikin kuka ya rungume sa,abbajo menene Kaye musu suke dukanka abbajo ga fuskarka duk jini,abbajo muje asibiti a maka treatment kaji abbajon mu ka bawa police hakuri karsu tafi dakai,kuka Yusuf ya sake hade da rungumar d’ansa Dayake Jinsa Kamar bugun numfashin sa, cikin su biyun yafi kaunar Muhammad sosai.

Karka damu muhammad Zan dawo kaji laifin da ba nawa bane aka d’aura mini Wanda duniya kaf ni ake gani da laifin ,Yusuf yace ma d’ansa Yana Mai  d’aukar sarkan dake wuyansa fari Mai azabebben kyau da walkiya ya d’aurawa Al’ameen a wuya, Muhammad ka kula da mamanku da kaninka kaji in mamanku ta haifi mace kace asa Mata khadija Inna mijine asa masa Shitu,Yana fad’a Masa hakan police sukazo suka Tisa keyarsa zuwa cikin mota 

Bayan an tafi da Yusuf, Alhaji ubangari da danginsa Koran Kare sukama Aisha da yaranta,sosai Aisha tayita kuka tana tattara kayanta zubawa tayi a ak’watin karfe ta d’aurawa Al’ameen da salim,suka Kama hanyar sintali.

Gari gabaki d’aya ya d’auka zancen Yusuf yayi kokarin mawa Yar ubangidansa fyade,bayan isar Aisha gidan ADARA zuwa lokacin labari yazo kunnensu Dayake unguwan da suke da sintali ba nisa

Bayan isar Aisha gida ta sake haduwa da wani tashin hankali shine mahaifinta yace sai ta mayarda yaran Yusuf gun danginsa kafun ta zauna musu a gida Dayake mahaifiyar ta tarasu tun kafun auren ta,yasa ba Wanda yayi yunkurin baiwa baban ta hakuri 

Aishan ADARA ta shiga tashin hankali ba kad’an ba na rashin sanin asalin Yusuf abin yayi mugun daga Mata hankali,ta rasa Ina zatasa kanta taji Dadi,don da ta koma gidan ubangari tunda shine waliyin Yusuf ya fad’a Mata inda dangin Yusuf suke Amma rashin mutunci da aka Mata a gidan Koh kyaun gani Babu,karshe dai  wani abokin Yusuf ne Wanda sukaye mutunci sosai ya taimaki Aisha bayan Jin labarin abinda ya faru tabbas shima ya shiga tashin hankali Amma Sam Bai yarda Yusuf ne zai aikata wannan abinba, d’auko Aisha yayi ya Basu d’aki a gidansa duk da MATARSA ta tsani zaman su Aisha Amma ba yanda zata iyya Aisha ta koma gidan abokin Yusuf da zama.

Wannan zaman gidan abokin Yusuf shine mafarin haduwar

 Al’ameen da kamila 

An Kai Yusuf kotu,Amma  bashi da hujjan Kare kansa haka yanaji Yana gani,laifinda ba nasaba aka yanke Masa hukunci.

Bayan Shari’a abubuwa sun ma Aisha yawa na rashin mijinta don abinda zataci  ma gagaransu yake Dole karatun su Al’ameen a private ya gagara ta ciresu ta maidasu Government school, sukaci gaba da zuwa,itakam wankau take Koh daka take sama musu abinda zasuci sosai Aisha take fama da rayuwa ga bakin cikin_ abinda Yusuf ya aikata,ba karamin bakin jini ya shafawa yaransa ba 

Hankalin Aisha Bai Kara tashi ba Saida lokacin komawar Salim asibiti Amma Bata da Koh sisi haka ta d’aukesa sukaje asibitin Amma abin mamaki duk yanda suka Saba da zuwa ganin likita Amma yau kawai da basu da kudin magani haka suka dawo gida kayan sakawarta Aisha ta tattara da kayan dakinta take sayarwa a hakan ta ringa ma Salim jinya da kayyakinta don abokin Yusuf d’aki kawai ya Basu Amma abinci Kam sai dai ta nema musu,

Ta bangaren zainab Kam tayi Dana sani Dana saninda har abada bazata daina yinsu ba sai yanzun take ganin wautarta na biyewa khairat harta aikata wannan mumunan kazafi wa Yusuf gashi abin Bai tsaya iyya Yusuf ba ta raba ma’aurata ta raba uba da yaransa ganin Yusuf da take taji Dadi yanzun Babu shi gashi  Koh samarinta ma yanzun duk sun gujeta a dalilin labarin da suka samu

Zainab rayuwa ta Mata zafi Koh baccin kirki Bata iyya wa taso sanar da iyayenta gaskiya Amma kairat ta kwabeta don hakan zai iyya zubar Mata da mutunci fiye Dana yanzun da take ciki.

Al’ameen da kamila yaran makwanta ne gidansu kamila.na kusa da gidan bala abokin Yusuf,

Kamila dalibar makaranta i private school ne Wanda ke kusa da goverments day da Yusuf ke ciki

Farkon haduwar kamila da Yusuf a hanyar makaranta zai tafi itama zata fita.

Tunda kamila.taga Al’ameen take yawan shige Masa har gidansu take zuwa tun Al’ameen baya kulata hardai ya fara kulata Aisha Karan kanta da farko bataso mu’amalar Al’ameen da kamila ba ganin Al’ameen lokacin shikara biyar ya bawa kamila Amma haka ta barsu ganin karatu Yusuf ke koya Mata kullum insun hadu

Bayan wata uku lokacin cikin Aisha ya Shiga wata bakwai,zuwa lokacin Aisha Bata da kome a dakinta sai taburma sai sarkan wuyan muhammad sai tsummo karansu saboda duk kudin sun Kare akan kudin maganin Salim ga rayuwa dai anata gargarawa

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 3 HAUSA NOVEL”


Yau ranan juma’a Al’ameen da Salim sun dawo makaranta bayan sun kara kamila gida don yanzun shakuwane Mai tsanani a tsakanin su wanda in kamila bataga Al’ameen ba zatazo gidansu haka shima, suna zaune dumamen safe da ya rage shine Aisha ta Basu itakam haka ta hakura saboda yau sun tashi bako sisi,zainab ce ta shigo gidan da sallama a bakinta

Aisha ta amsa Mata Dan Sam bata Jin haushin family ubangari don Koh itane abinda Yusuf ya aikata saita Masa fiye da haka

Kallon zainab take Wanda duk tabi ta rame kallo d’aya zaka Mata kasan Bata cikin hayyacinta,bayan  sun gaisa zainab ta d’aga ido tana kallon Aisha Bata San ta Ina zata fara ba yau tayi Alkawarin zata Fad’i gaskiya Koh zata samu sassauci a rayuwan ta 

Hawaye ne ya cika idanun zainab ta bude baki a Hankali tace,maman Muhammad akwai wani magana da zanfada Miki bansan ya Zaki d’auki maganar ba Amma na g’wammaci na karbi Koh wani hukunci akan Wanda nake ciki

Cikin mamaki Aisha kam ke kallon zainab a iyya zamansu da zainab Bata taba ganin ta Mata magana a mutunce ba Kamar yau,toh zainab Allah yasa naji alkhari

Gaskiyan abinda ya faru maman Al’ameen babu ruwan Yusuf aciki,tace tana kallon Aisha

Kamar ya bangane ba zainab?

Eh tabbas Kamar yanda nace , Yusuf Babu ruwansa a ciki nice da khairat Muka had’a kome a tunanin mu Koh in aka Kama Yusuf xai mini fyade babana zai tilastashi ya aure ni Amma ban taba tunanin abinda na aikata ba daidai bane Saida Naga yanda na wargaza muku farin cikin na dasa muku bakin ciki, wallahih maman Al’ameen nayi nadama,Dana biyewa khairat ban tashi nadama ba Saida naji jiya tana Hira da kawarta a waya suna mini dariya, na tsokancin danayi harna yarda da abinda ta gayamin Ashe itama son Yusuf take,ta karasa maganar hawaye ya zuba akan fuskarta

Aishan ADARA Kam daskarewa tayi a zaune itakam wace irin mace ce Mai mantuwa me yasa ta kasa yarda da Yusuf, namijin daya yarda zai rayu da ita Bai damu da tarbiyan gidansu ba Koh halinta ba ya aureta Koda Yusuf Zina yayi hukuncin da ta yanke Masa yayi tsauri,wani irin murdawa mararta yayi na tashin hankali atake jini ya balle Mata durkusawa Aisha tayi tana Kiran sunan Allah.

Da gudu matar Bala dake tsaye tun d’azun tanajin bayanin da zainab keye tazo da gudu,tana kwalawa mijinta Kira da gudu ya fitoh su uku suka ciccibi Aisha zuwa asibiti

Al’ameen Kam Kama hannun Salim yayi suka Kama hanyar gidan ADARA,suna Isa kakansu suka samu a kofar gida suka fad’a Masa mamarsu ba lfy an kaita asibiti, hankali baban Aisha ya Tashi matuka don shi Karan kamshi korinda Yama Aisha na haushin yaran Yusuf ne, Amma Yana son yarsa tura su Salim yayi gidan Amina (Goggo) shi Kuma ya wuce gidan Bala agun ya samu wa’inda ke zaune aka fita da Aisha, aka Masa kwatancen asibitin da aka Kai Aisha

Bayan zuwansa ne yaji labarin abinda ya haddasa ma Aisha nakudar Dole abakin Matar Bala,shima sosai ransa ya baci duk da Bai gamu da zainab a asibitin ba Amma ransa ya matukar baci gida ya koma ya sanar da yaransa da yaran Yan uwansa akan suje su fara d’aukar mataki akan zainab kafun hukuma ta shiga

Ayarin gidan ADARA daga Yan Mata har  zaurawa da  samari sukaye Ayari guda suka fasa unguwa  da kafa suka taka har  gidan ubangari.

Zainab Kam gabaki d’aya ta rasa nutsuwarta Koh zama takasa waje Daya, tunda ta gudo daga hospital karshe dai Saida mamarta ta tambaye ta Koh meke damunta haka? tunda abinnan ya faru ta fahimci walwalar zainab ya d’auke, zainab Kam kin fad’a Mata gaskiya tayi

Suna zaune dukansu a gida dayake yau Friday ne ubangari ya dawo aiki da wure haka Yan makaranta,ji kawai sukaye an bankado get in gidan an shigo ciki kafun ma su gama tantance suwaye ne har kanwar Aisha ta nufi d’akin zainab jawota sukaye har kofar gidan da gudu su ubangari suka Mara musu baya.

 Rufeta da duka ADARA sukaye, saiga khairat tafitob  gida makwantan su, Aiko kamota sukayi suka Had’asu suna jibga duk yanda Yan unguwa da ubangari suke kokarin k’wace zainab da khairat abin ya gagara ganin zasuye kisan kai don zainab ta Suma Amma haka Ayarin gidan Adara Basu daina jibgarta  ba Saida ta farfado da duka

Police aka Kira lokacin unguwan ya cika makil day’an kallo, abinka da Friday kowa na gida,

bayan zuwan police kafun aka samu aka k’wace su zainab anso Kama Yan ADARA Amma Ina abin ya gagara don fad’ane ya kusa zama na police da Yan gidan Adara,ganin jaraba irin na Yan gidan yasa polisawan tambayar musabbabin fad’an don dai sunyi sunyi su bisu station aye kome agun Amma sunki, D’aya daga cikin samarin gidan ne ya nuna zainab,ke don uwarki fada musu meya faru tsakaninki da yusuf mijin Aisha?

Hakika zainab tayi mugun tsorata hakan yasa Bata boye kome ba ta fad’a duk abinda ya faru,atake Alumman suka fara Allah wadai da zainab da khairat ubangari Kam yanke jiki yayi ya Fadi hawan jininsa ya tashi, police ma tafiyarsu sukaye Basu d’auki kowa ba.

Ta bangaren Aisha Kam  ganin tana kokarin rasa Ranta yasa likitoti Mata operation aka cire baby girl bakwaini aka saka a kwalba,Aisha na farfadowa sunan mijinta ta fara Ambata tana sambatu,tunda ta farfado batada magana sai a kaita wajen Yusuf ta nemi gafaransa Amma ba’a barta ta fita a asibitin ba saboda yanayin jikinta Dana baby.

Ta bangaren ubangari ma hakan take jinya ya kwanta har kusan sati baisan inda kansa yake ba abubuwa sun taru sun Masa yawa,Yana Jin sauki kad’an ya Tashi da kafarsa ya koma wajen Alkalin da yayi musu Shari’a,

  An nemi ganin Yusuf don a wankesa a kotu Amma abin tashin hankali shine, Yusuf a Randa aka kaisa prison Bai kwanaba ya fita tare da sa hannun kotsosin kasa

Wannan magana ita tafi ko wace magana tashin hankali agun Aisha don anye iyya bincike an had’a hannu da masu kudin da Yusuf yayi mu’amalan kasuwanci dasu don binciko inda Yusuf yake Koh suwa suka fiddasa 

Duk Wanda aka tuhuma Mai hannun a cire Yusuf magana D’aya yake fad’a baisan Yusuf ba kawai umurni aka basa daga sama

Wannan magana tayi mugun dagawa Aisha hankali atake ta sake kwantawa ciwo Wanda an rasa kansa kullum gaba gaba yake duk abinda babanta ke dashi ya kare a jinyar Aisha da Salim don shima zuwa lokacin zuciyarsa ta fara tashi.

Tsawon wata biyar ana binciken case in Yusuf Amma shuru ba wani cigaba,yau dai jikin Aisha da sauki,bayan Salim da Yusuf sunzo duba mamar tasu ,don yanzun suna zaune a gidan Adara ne 

A hankali ta Kama hannun Al’ameen ta rike cikin nata ta fara magana hawaye nabin Gefen idanunta,Al’ameen ga kaninka nan da Yar uwarka khadija Muhammad ka kula dasu ka zama uba a garesu Koda kowa zai gaji dasu Kai ka zaman musu gata, jagora,Garkuwa,inaji a jikina wata Rana zaka Hadu da mahaifinka,kace Masa ni Aisha Ina neman afuwarsa ya yafe mini Koh Zan samu salama,ka zamo Mai hakuri kamar mahaifinka duk abinda zakaye a rayuwa ka ringa bincike karka yanke hukunci a cikin fushi don karshin sa Dana sanine.

Al’ameen duk da yarone Amma hankalinsa in yayi dubu toh ya tashe in Bai manta ba haka abbajonsa yayi Masa, shikenan ya gudu ya barsu don shi har yanzun baisan takammamen abinda yake faruwa ba,

Mami kema gudu zakiye kamar abbajo ki barmu?yace Yana kuka shida Salim dake kusa dashi

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 4 HAUSA NOVEL”


Ah ah Yusuf ba gudu zanye na barku ba inda zanje kowa ma zaije in lokacin sa yayi sanan abbajonka Bai gudu ba wata Rana zai dawo kaji,ga kaninka na kuka ka rarrashesa karka barsa ya zubda hawaye kasan ciwonsa bayason damuwa Koh?ta tambaye sa muryanta na shakewa

Kai muhammad ya gyad’a Mata hade da Kama hannun Salim Yana rarrashensa,

Ji kawai yayi mamin su na wani irin shakuwa hade da Kiran sunan Allah,da sauri ya fita a d’akin yaje Kiran Doctor

Suna shigowa dakin da sauri Muhammad ya matso gareta cikin matukar razana ganin maminsu Bata m.

              

Aishan ADARA ne kwance Bata motse, cikin sauri Al’ameen ya Isa gareta yana kuka,don zuwa yanzun sun fara sanin ciwon kansu daga shi har Salim in,rungumar mahaifiyar sa yayi Yana kuka,don Allah Mami karki tafi ki barmu mami karki tafi ki barmu wayyo mamin mu yace Yana fashewa da kuka Salim Kam tsabar tashin hankali ciwon sa ne ya tashi,da sauri likitoti suka Kira baban Aisha dake waje a zaune yazo ya fitar da Al’ameen shi Kuma Salim Nurse suka d’aukesa zuwa wani gadon.

Sumayya dake kwance a kirjin Al’ameen kukane ya k’wace Mata hannu tasa ta Kara rungumar sa tana kuka,shikam gabaki d’aya jijiyoyin kansa sun mike sosai, kallo D’aya mutum zai Masa yasan ran maza ya tsogalu.

Kafun ya Kara bude baki, ji kawai sukaye kuka na tashi a bakin kofar d’akin su da sauri Sumayya ta mike hade da kamo hannun Al’ameen suka fitoh wajen tare

Khadija ce duke tana kuka fuskarta harta kumbura Alamu dai ta Dade tanayinsa kasa kasa sune dai basuji ba.

Yaya Daman gidan ADARA ba dangin mahaifin mu bane? Shiyasa suka nuna Mana launin fata,khadija ke tambayar yayan ta

Ah ah khadija ba saboda haka bane suke wulakanta mu dama can haka kaddarar Rayuwar mu take, kishare hawayen ki maza ki tafi gida 

Ni wallahih Yaya inason Jin karashin labarin mu don Allah Yaya kaga ba Wanda ya taba ban Tarihin iyayen mu kullum na tambaye ka Koh Goggo sai kuce mu Marayu ne.

Al’ameen nada niyar magana Sumayya ta regasa”gaskiya ne khadija tayi girman da zata San abubuwanda suka shafeta especially irin wa’innan Tarihin”

Shikenan naji ana Kiran azahar bara nayi sallah Kuma kuyi Inna dawo saimu d’aura daga inda na tsaya,yace Yana Mai laluben buta 

Da sauri Sumayya ta nufi butar dake zaune a Gefen baranda ta Mika Masa.

Alwala sukayi Sumayya kudi ta baiwa Al’ameen 1k in zai shigo gida yasai musu doya soyayye a bakin titi na 500

Ba musu ya karba ya fita

Bayan an idar da sallah Al’ameen doya yasai musu suka ci su ukun, duka a plate d’aya bayan Sumayya ta matsa musu don har lokacin khadija kuka take Kamar yau Abubuwan da suka shige ya faru.

Khadija inkin San kuka  zakiyi toh Zaki bar gidan nan Banga amfanin kina kuka Kuma kice na cigaba da baki labarin ba kije ki samu wani damuwanne Koh me? Al’ameen ya fad’a ransa a bace,don shima dauriyane kawai

“Don Allah yayan khadija kayi Hakuri mutuwar iyaye Koh shikara d’arine zafine da shi”

Kayi hakuri Yaya,khadija tace tana share hawayen ta 

Dukansu Basuci wani abin kirki ba Al’ameen Kam doya yanka biyu kawai yace khadija Kam ma tanaci Amai tayi saboda yanda take ajiyar zuciya

Bayan sun wanke hannunsu Al’ameen ya cigaba……..

Bayan mutuwar Aisha Alhaji ubangari yaso d’aukar su Al’ameen ya rike, Amma baban Aisha ya murza ido yace ba dashi ba Koh kudi ubangari ya baiwa su Al’ameen sai an mayar Masa da kayansa sosai abubuwa suka ma ubangari yawa don yanzun Koh fita zainab Bata iyyawa,tana fita ana nunata .

Khadija Kam, kanwar Aisha aka bawa wance ta h Bata jima da haihuwa  ba ta shayar da khadija, Amma khadija Taki karban nono Sam sai madara,ganin Amina Bata taba haihuwa ba yasa baba karban khadija ya Baiwa Amina Amana.

Al’ameen sunyi matukar kewar iyayensu Wanda Salim yafi saka abin a ransa shiyasa kullum cikin ciwo yake don yanzun dai Al’ameen wani abokin babane ya ajesa a shagonsa Yana sayar Masa da kayan marmari duk Rana Yana biyansa,da wannan yake Tarawa su had’a da baba akai Salim asibiti 

Duk da wannan d’awainiyar Salim Bai hanasu karatu ba a hakan Alameda yake zuwa makarantan gwannati Dayake lokacin duniya sanyi kalau ba kamar yanzun ba da ake kashiwa makarantan gwannati kudi.

Relationship insu da kamila ba abinda ya ragu kullum saiya rakata gida kafun ya nufi unguwan su sosai Abu kamar Wasa shakuwarsu ta Kara karfin sosai saidai kamila Bata taba zuwa unguwan dasu Al’ameen suka  koma ba shine dai Mai zuwa gunta,

Ubangari Kam zaman jalingo ya gagaresa don lafiyarsa Dana zainab sai a hankali don yanzun saita kwana ta wuni Bata cewa kome makarantar ma yanzun Bata zuwa sosai rayuwa ta musu kunci,ganin Halinda suke ciki, yasa matar ubangari Kiran Yan uwansa ta sanar dasu abinda ke faruwa,

Aiko a yanda suka tarar da ubangari da zainab don har an dakatar dashi agun aiki ganin Halinda yake ciki yasa Yan uwansa Saida gidan da suke ciki suka tatttarasu dashi da yaran NASA suka koma garinsu,Daman aikine ya kawo ubangari jalingo, Wannan kenan.

Khadija taci gaba da samun kulawa Awajen Amina Alhamdulillah yarinya ta fara girma ga wayo sai daifa Sam Bata da jiki Yar firet da ita kyakkyawa sosai don Kamar ta da Yusuf ne sak shiyasa ita da Al’ameen Koh baka sansuba ka gansu kaga jini d’aya Daman Salim ne baki a cikin su don da  Aisha yake  Kama.

Zaman su a gidan Adara Bai sauya musu hali ba, da yake abin a jininsu yake sanyi Hali da hakuri Amma fa Salim akwai zuciya mundin aka Bata Masa Rai in fa baisamu ya Rama ba saiya kwanta ciwo.

Bayan wasu shekaru mahaifin Aisha dai ya kwanta ciwon kafa Wanda Koh kofar gida baya iyya fita Sai an Taimaka masa,

don haka Abubuwa sun ma Al’ameen yawa ga kudin maganin Salim ga D’an abinda yake D’an kaima Yar kanwarsa khadija ga zaman shago ga zuwa makaranta ga soyayyar kamila wanda yake jinta har ransa.

Haka baban Aisha yayita fama da ciwo har Allah ya d’auke ransa Wanda kafun ya mutu Saida ya jaddada wa yaransa Koh bayan ransa Bai yarda Yusuf da Salim Subar gidan nan Adalilinsu ba d’akinsa da yake ya bar musu halak malak, baya cikin gado, Wannan shine kalmarsa ta karshe Kuma itace sukecin Albarkacinta har yanzun suna cikin gidan ADARA.

Bayan mutuwar baban Aisha rayuwa fa ta zamo ma su Al’ameen wani iri Sam a gidan Adara Babu Mai taimaka musu Koda ta abinda zasuci ne,Dole tasa Salim shima ya fad’a Tashar marmari Yana ma wasu jiran Kaya suna biyansa,saisu had’a da kudin Al’ameen su fidda na asibiti su fidda na abinci su fidda Wanda zasu baiwa Amina ta rage d’awainiyar khadija,hakan yasa Al’ameen aje karatunsa don ko yaje makarantan baya fahimtar kome tsabar damuwa,

Ganin ya aje karatunsa Salim ma yaki zuwa makaranta ba yanda baiyi dashi ba Amma yake ganin Al’ameen ya matsa Masa yasa sa  cewa Al’ameen,Yaya moha Koh naje makaranta asaran kudi zakayi tayi Kaine yafi cancanta Kayi karatu Koh don kanwarmu ta samu rayuwa Mai inganci

Jin Amsar da Salim ya basa Saida Hankali Al’ameen ya tashe cikin damuwa yace Masa,salim ban gane ba kana nufin Kai Babu Amfanin karatun nakane, ka sani Koh Kaine Mai rabon Tallafawa Khadijan?

Ah ah Yaya Kaine ya dace Kaye karatu don Allah badon niba Yaya ka koma makaranta nikam bazanje ba karatun ya isheni haka ya karasa maganar da kuka

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 5 HAUSA NOVEL”


Rungumar sa Al’ameen yaye shima sai yaji hawaye nabin fuskarsa don yanzun sosai sukayi wayo girma ya fara zuwa musu Kuma labarin abinda ya faru ya riskesu,sosai suka kullace zainab a ransu Kuma har abada bazasu manta da fuskarta ba.

Haka ba yanda Al’ameen ya iyya ya koma makaranta don lokacin ma ya Shiga SSS class yayinda khadija ta Kai shiga primary school da Taimakon Goggo Amina aka sakata

Soyayya Kam tsakanin kamila da Al’ameen tayi girma don har abin yakai ga iyayensu sunsan kome,don kamila Kam Amfara zama Yan Mata kowa yazo da sunan soyayya haka zata koresa itakam fa sai Al’ameen,sosai mahaifyarta ta tsani wannan mu’amalar Al’ameen da kamila ganin ba’a San Asalin ubansa ba haka zuriyan maman sa Yan Ta’adane,gashi baida wani kakkauran sana’a Koh inda zaisaka kamila,Amma haka kamila ta nace sai shi,

 duk yanda zata zugata Koh fad’a Mata abinda ya dace kamila bataji Bata gani itafa sai Al’ameen.

Hakan yasa baban kamila Kiran Al’ameen don ya yaba da Tarbiyan sa ga nutsuwa, yace Masa zai basa kamila Amma ya dage yayi karatu in waec nashi yayi kyau,ya d’auki d’awainiyar karasunsa harya kammala shi Kuma ya Masa Alkawarin xai basa kamila.

Jin hakan sosai muhammad ya Kara dagewa da neman na kansa da Kuma karatunsa don sosai yanzun yake son kamila

Shekaru sunja lokaci ya tafi rayuwa nata juyawa yau Dadi gobe Akatsen sa,hakan take  a wajen su Al’ameen

Ranar 3/8/2009 ranar da Al’ameen bazai taba mantawa dashi ba,yau ne suka kammala waec nasu gabaki d’aya makaranta kowa ka gani farin ciki ne d’auke a fuskarsa wasu Kam har kukan rabuwa da juna suke, don irin Wannan ranane Inka rabu da wani har abada bazaka Kara ganinsa ba

Haka take a wajen Al’ameen  ranar farin cikinsa ne ya kammala karatunsa na secondary sai Kuma jiran result,farin cikinsa harda hawaye ganin yau ya Gama jarabawa Amma bayada Wanda zai zauna ya nuna Masa farin ciki Kamar yanda sauran daliban iyayensu ke Basu kyaututuka da walima na murnar Ranar  

A hankali yake tafiya jikinsa sanye da uniform na makaranta Yana tafiya Yana tunane tunane rayuwa don a lokacin sun girma shi yanada shekara 18 Salim 15 Khadija 6

Ji kawai yayi wata mota Tasha gabansa kafun ya Ankara ma har sun Wasa Masa wani abu Bai Kara tuna Koh sanin inda yake ba sai bayan sati D’aya

 D’aya bude ido ya jisa a asibiti Amma baya ganin kome sai duhu,Wanda yake zaune dashi shine Wanda ya tsintosa a bayan gari wajen kauyensu ya fitoh gona kenan yaga wasu sunzo sun yarda  Al’ameen  a cikin ciyaye,shine ya daukosa ya kawosa hospital da vajin jikin uniform NASA aka gane makarantarsu har labari yaje gidan Adara Amma Amina ne kawai da Salim suka zo asibitin Kuma suke kokarin jinyansa da taimakon mutumin da ya tsintosa,

Al’ameen sosai ya Shiga damuwa Daya waye gari baya gani gashi Doctor’s sunyi iyya binciken su Amma basuga ciwo ba shi Karan kansa Al’ameen bayajin kome a cikin idon nasa 

Haka tun Yana kuka harya sadakar ya karbe kaddararsa,bayan makantarsa abin mamaki Koh da kamila ta samu labari batazo Koh duba Al’ameen ba sai abokansa na makaranta dana unguwan sune sukazozzo don ganewa idanunsu shin da gaske ne labarin da sukaji Al’ameen ya makance

 shine da kansa Yakama Salim ya Masa jagora zuwa gidansu kamila Amma Koh ganinta basu samuyi ba duk abokansa yanzun basa son Koh zama waje d’aya tare dashi kowa gudunsa yake

Bayan waec ya fitoh Salim ne ya karbo Masa result,ya samu 9credit sosai Al’ameen ya rungume result nasa a kirji Yana hawaye,yaci buri akan result nan yayi karatu har bacci bayayi,Ashe ba rabon zaiga abinda ya samu ma da idanunsa sai an duba an fad’a Masa.

Rayuwa fa Tama su Al’ameen zafi don abinda zasuci ma ya zamo musu aiki sai salim ya fita ya nema kafun su samu gashi yanzun an sallame Al’ameen a shagon da yake zama don ganin baida ido duk yanda yaso su taimake sa zai iyya ciniki koda ba idone abin ya gagara 

Bayan wata D’aya da makantar Al’ameen yaje gidansu kamila yafi kafa goma Amma kullum sai ace Masa Batanan,Wasa Wasa jikin Salim ya Tashi don ba’a je ganin likita ba har wata ya wuce,ganin ciwo yaci karfin Salim ga bamai taimakonsu, yasa Al’ameen neman taimakon yaran unguwa suka kaisa asibiti

Likita yace Masa wannan karon aiki za’a ma Salim gashe kudi masu yawane,sosai hankalinsa ya Tashi ga rashin ido gashi basuda abinda zasu Kama su sayar  sai sarkanda mahaifinsa ya bar Masa Wanda shi kad’aine abinda yake gani a matsayen Abu Mai girma da muhimmaci a Rayuwansa Wanda zai buga kirji yace Awajen iyayensa ya gada,Amma baikai Dan uwansa ba muhimmaci ba.

Haka ya d’auki sarkan yakai kasuwa don a Saya Amma masu sarka sukace bazasu Saya ba gudun karsu sayi abin sata bare sarka Mai shaki Kamar Wannan Basu taba ganin sarka Mai zubinsa ba

Duk inda Al’ameen yasan zai samu a taimaka Masa yaje Amma babu Wanda yayi yunkurin taimakon sa har gidansu kamila yaje Amma Koh sauraron sa mahaifinta baiyi ba

Karshe dai Koran su akayi a asibiti ganin Basu da Koh sisi kullum Kuma kudin gado karuwa yake,dawowar Salim gida ciwo ya Kara Tashi gadan gadan,haka Al’ameen yanaji Yana gani jikin Salim na tsanani Amma Babu yanda zaiyi haka yake fama ga rashin ido

Yauma Kamar kullum suna kwance a d’akinsu Wanda kakansu ya mutu ya barmusu tun 1:00 na dare jikin Salim ya tashi ko rimtsawa Basu samu sunyi ba dukansu biyu Al’ameen na zaune Salim ya kwantar da kansa akan cinyar D’an uwansa sosai yake Aman jini Al’ameen Kam sai kuka yake Yana Kara tallafar Kan D’an uwansa Jin Aman da Salim keyi Yana karnin jini yasaka yatsansa ya lakuto Aman tsuntsunawa yayi tabbas jinine ba Wai ba,

 ai da gudu ya fita tsakar gidan Yana kuka Yana bubuga musu kofa Amma ba Wanda ya taimaka Masa Asalima zaginsa suke,insun bude kofar,da gudu yayi waje.

 gidan makwancinsu ya shiga Yana kuka ya ringa buga masu kofa,mutumin na budewa yaga Al’ameen ne,hakika yau yaji tausayin yaran da gudu ya Kama Al’ameen sukaye cikin gidan Jin Al’ameen nace Masa Salim na Aman jini 

Suna isowa zuwa lokacin salim kam jiki yayi tsamare sosai  haka mutumin ya cicibesa Al’ameen na binsa a baya sai tuntube yake Yana buga kafarsa saboda rashin sandar jagora Koh D’an jagora

A haka suka fitoh kofar gidan, aje Salim mutumin yayi yace bara ya d’auko machine su kaisa hospital

Mutumin na shiga gidansa Salim ya ringa Kiran sunan Al’ameen Yana tari jini nabin Gefen bakinsa,Yaya Muhammad !!Yaya muhammad zuciya na, zuciya na na ciwo Yaya kamin fifita zafi nakeji a jikina Yaya bana ganinka Yaya zansha ruwa kishi nakeji

gabaki d’aya Al’ameen ya rude iyya rudewa da gudu ya ruga yayi randar masallaci saboda rashin jagora, ya hadu da pol ji kake Gauu ya buga goshinsa jini ya balle Masa duk irin azabar da yaji hakan baisa ya kasa tashi ba haka ya mike a daddafe yayi randar masallaci dumbulo ruwa yayi Yana kuka Yana sauri ya karaso kusa da Salim tsungunawa yayi ya d’ago kansa jikinsa na rawa Jin Salim ya daina kakarin Amai gashi kansa yayi nauyi daker ya d’agasa ya d’aura akan cinyarsa lalubar bakin salim yayi ya kafa Masa mod’an Amma Ina ruwa baya tafiya sai bin Gefen bakin yake Yana zuba,dagajin haka Al’ameen ya k’wala Kara

 Yayi daidai da  lokacin mutumin ya fitoh da machine da sauri ya karaso gunsu Jin ihun Al’ameen

Yana zuwa cikin hanzari ya haska su idonsa ya sauka akan Salim  kwance ido ya kafe a sama jiki a sake Wanda Koh ba’a fad’a ba yasan lokacin Salim ne yayi Innalilahih wainnailaihir rajuun kalmarda ta fitoh a bakinsa kenan

Aiko Wannan kalmar ita ta Kara tabbatar wa Al’ameen lallai ya rasa kaninsa, a karo na uku Yana rasa mutanen da sukafi soyowa a ransa, farin cikinsa,duka a gabansa suka Amsa Kiran mahalincin su(Allah Kasa mu cika da imani,muyi kyakkyawan karshe)

Ji kawai mutumin yayi Al’ameen ya Fad’i timmmmmm….

Al’ameen ne ya yanke jiki ya Fad’i,sosai mutumin ya rikice yahau salati cikin kidema 

Hayaniyar sa shiya matashe samarin dake kwana a d’akunan kofar gida,Suma dai sosai mutuwar Salim ta shigesu ruwa aka watsawa Al’ameen Amma Ina Koh farfadowa baiyi ba Dole tasa wasu daga cikin matasan d’aukar sa zuwa asibiti

Usman makwancinsu shiya d’auki gawar Salim zuwa gidansa  

Washe gari agidan malam Usman aka shirya salim.

Al’ameen dake asibiti kam Yana farfadowa da asuba ya tashi hankalin kowa sai ya dawo ankai Salim tare dashi

Haka aka kamasa g’wanin tausayi zuwa gidan malam usman,Yana shiga gida aka Kaisa Kan gawar D’an uwansa a hankali ya zauna Kan cafet in hannu yasa Yana lalube ya bude gawan jikinsa na bare yasa hannu ya shafa fuskar Dan uwansa murya na rawa hawaye nabin kuncinsa yake ma D’an uwansa Addu’a

Salim sosai ya samu jama’a kamar me don duk wanda yasansa, kuma yaji mutuwarsa  yazo,tare da Al’ameen aka kai D’an uwansa kabari. 

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 6 HAUSA NOVEL”


Bayan mutuwar Salim sosai kewa da kad’aici ke damun Al’ameen Koh bacci baya iyya wa saboda kewan D’an uwansa shikenan yanzun baida abokin Hira baida Wanda zai fad’awa damuwar sa baida Wanda zai kwana tare dashi sai Yar kanwarsa khadija ita Kuma mace ce          

Mai gidan Salim shiya bawa Al’ameen kudi Ya sari mangoro Koh a bakin kofar gidane ya fara saidawa don Bai dace Yana tsallake titi kullum zuwa kasuwa zaman shago ba

Ba musu Al’ameen ya karbi kudin yad’an fara business dashi,Kuma Allah yasama abin Albarka Yana samun na abinci da biyawa Khadija D’an hidindimun makaranta

Zancen kamila Kam baiyi fushi ba duk da Bata Masa ta’aziyar D’an uwansa ba haka ya sake Kama Khadija don lokacin ta d’anye wayo sukaje gidansu kamila.

Kamila ce tsaye da kawayen ta a waje tare da wasu samari uku A bakin mota

Al’ameen suna Isa kofar gidansu kamila,yaji hayaniyar maganar mutane Kamar harda ta kamila hakan yasa cikin murna yau dai zasu gana,  tunda ya jima Yana zuwa baya samun ganin ta

Da saurinsa yace wa Khadija suye wajen da Yake jin muryan mutane

Ba musu Khadija na rike da sandar sa suka nufi wajen, Assalamu alaikum

Waalaikumu salam D’aya daga cikin samarin  ya Amsa Masa

Ina wunin ku, Al’ameen ya gaidasu

Lafiya samarin suka amsa d’ayan ya zare kudi a Aljuhunsa Yana mikawa Khadija,ungo Yan mata

Khadija Kam kin karba tayi don bata Saba bara ba koma yayanta ya hanata roko Koh karban abin hannun Wanda Bata sani ba

Karba Mana yarinya D’aya daga cikin kawayen kamila ta fad’a don Bata San Al’ameen ba

Yayana ya hanani karban kudin Wanda ban sani ba, Khadija ta fad’a musu tana noke kafad’a

Da mamaki samarin ke kallon su Al’ameen mutum ya fitoh bara abasa yace bazai karba ba,toh lfy meya kawo ku gun mu inba bara ba

Am don Allah Ina da tambaya ne? Al’ameen yace

Allah yasa mun sani

Yauwa Kamar muryan kamila nakeji d’azun a cikin ku?

Eh ganinan lfy?kamila ta basa Amsa

Lafiya kamila in ba damuwa inason magana dake ne

Ina jinka,tace tana Masa kallon banza

Don Allah mu koma gefe

Kai MAKAHO akan me zaku kebe da matar da Zan aura Kai asuwa d’aya  daga cikin samarin yace

Wani abune ya cake zuciyar Al’ameen shikenan kamilar ma ya rasata shikam yaushe zai samu farin ciki ne duk mai kokarin faranta Masa wata Rana gudu yake ya barsa 

Kamila aure zakiyi?yace Yana kokarin faduwa tsaban shock

Eh aure zanyi Koh kana da matsala da hakan ne

Kamila Ina Alkawarin mu?

Alkawari kana nufin na aure ka kana MAKAHO Kuma talaka da wanne zanji da ciyar dakai Koh da ciyar da yaranka Koh da maka jakora Koh d’awainiya?Zan dai iyya auren ka a Talaka Amma banda kana MAKAHO kam.

Sosai zuciyar Al’ameen ta tsinke 

Dariya matasan da Y’an Matan suka sake na shekeyanci,Kai kamila bakida mutunci wallahi 😒 soyayya ce fa saikuje kusha love da lalube D’aya daga cin Yan matan ta fad’a tana dariya

Budurwar da ke gefe sanye da hijab itace kad’ai Bata ma Al’ameen tozarci ba

Kama hannun Khadija taye hade tacewa Al’ameen su tafe 

A hankali Al’ameen ke tafiya Kamar k’wai ya fashe Masa a ciki Bai d’auka Koh nakasa zaisa kamila gudunsa ba Koda kowa zai gujesa 

Suna sharan kwanan nayin,  kawar kamila ta dube Al’ameen,kaga bawan Allah don Allah Ina Mai rokon alfarma a gareka shine ka rabu da kamila Koda itace autar Mata ka barta duniyace ai Koda zata rabu dakai bada tuzarci Koh kushen halitta ba Amma ita Bata dube hakan ba y

Ta wulakanta ka kaima ka barta bari na har Abada,Kaye hakuri Allah Yana tare da musu hakure.

Insha Allah baiwar Allah na rabu da kamila Nima na hakura da ita Allah ya had’a kowa da rabonsa,

Ameen ta basa amsa tana Mai komawa layinsu tabarsa tsaye da Khadija

Wannan shine Ranar da Al’ameen  ya fita a Rayuwan kamila.

Bayan wasu shekaru karatu ya fara zama sai da kudi, a hakan yake ta faman ganin Khadija tayi karatu Koh ba kome zata tallah fawa kanta,  Amma Ina kudi ya gagara don yanzun mangoron ma sai a hankali Bai wuce a Rana yayi cinikin 200 Koh kasa da hakan. Gashi a ciki Kuma yake ciwa cikinsa hakan yasa karatun Khadija tsayawa iyya Junior.

 *An dawo labari* ………..

Khadija Kam kuka take kaman me,haka ma Sumayya Allah sarki Ashe haka rayuwar wa’innan bayin Allah yake, tasu kaddarar kenan,a cikin Yan watanni nan da mahaifinta ya juya mata baya taji kamar tafi kowa matsala,ashe itakam ma in an had’a kaddarar ta dana Muhammad nata ba kome bane tunda har tayi karatu ta tashi cikin kudi da lfyr ta Amma shifa ga maraici ga kuncin rayuwa da Talauci.

D’aga ido tayi tana kallon Al’ameen dake zaune a kujera fuska tayi ja”yayan khadija baka bani lbrn auren mu ba”?ta tambaye sa

Khadija tashi ki tafi kinji kukan ya isa haka, Al’ameen yace batare da ya amsawa Sumayya tambayar taba 

Mikewa Khadija tayi zata fita a d’akin cikin kuka abin  g’wanin tausaye”Khadija”Sumayya ta Kira sunan ta

Na’am Aunty

“Khadija kiyi hakuri kome na rayuwan duniya Mai karewane Sannan Yana da iyyaka  kinji”?

Toh Aunty tace tana share hawayenta

“Ki d’auki doyan nan ki tafi dashi gobe da safe  sauki kawo mini ducuments naki kinji Khadija”

Toh Aunty kawai tace tana d’auki laidan doyan ta fita

“Yayan khadija na tambaye ka shine kaci no   face”

Sumayya nagaji wallahih ki barni nad’an huta Mana waima me zakiye da ducuments in Khadija ne?

“Oho ba’a sani ba Ina maka magana kana tambaya ta Nima naki fad’an”

Shuru  ya Mata tare da lumshe idanunsa 

Itakam ganin ya Mata shuru tasan dai akwai abinda bayason fad’a matane,tashi taye a hankali ta Isa garesa faduwa tayi a kansa  da gangan

Washhhh yace yana gyara Mata kwanciya

“Don Allah ka fad’amin Mana”

Kinga Sumayya nifa banason na fad’a Miki abinda zaizo Yana d’aga Miki hankali.

“Allah bazan d’aga hankalina ba kawai ka fad’a mini”

Ok toh shikenan Amma sai da dare Zan fad’a Miki

“Gaskiya Nina gaji da abinda kake minin nan wani irin sai dare Kuma Wannan ai Jan Raine”

Banace Zan fad’a ba ki barni Mana zuwa Daren in ban fad’a Miki ba saiki Tuhume ni

“Uhmm toh yanzun me zakayi”?

Bacci,ya  Amsa mata

“Bacci a hakan”?

Eh…..

Tashi Sumayya tayi taje ta d’aura abincin dare ta barsa a d’akin

Bayan fitarta sosai yake tunani akan ya fad’a matane Koh karya fad’a Mata karshe dai ya yanke shawaran ya fad’a matan kawai 

Bayan isha’i Sumayya ce da Al’ameen kwance akan gado Sumayya taye matashe da cinyar Al’ameen sunfi minutes 20 a haka,tunda sukaci abincin dare sukayi sallah, suke a haka Amma Al’ameen baice mata kome akan labarin  ba abin sosai ya dame ta Amma ta danne tunda yace zai fad’a zata barsa ya fad’an da kansa.

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 7 HAUSA NOVEL”


Sumayya!!ya Kira sunanta Yana Mai shafa gashin kanta mai tsawo da kamshi

“Na’am”ta amsa Masa

Sumayya banso fad’a Miki dalilin auren mu ga ganin cewa kece kikafi kowa sanin hakikanin gaskiya don bana tunanin har yanzun ana cikin zamanin da za’a ma mace aure batare da tasan miji Koh miji ya santa ba.

“Me kake nufi”? Sumayya ta tambaye sa fuskar ta a hade Jin abinda yake fad’a Mata

Yanzun masifa Zaki mini Koh Jin lbr zakiyi? 

“Aiba labarin kake bani ba sukata kake”Sumayya tace,tana kokarin sauka a gadon

Sorry toh, yace Yana kamota

“Nikam ka sake ni “

Kin saketan yayi yana rungume da abarsa, naki sakin kin in kajimin mata fa

“Allah ni ka sakeni nace maka”tace tana kokarin xame kanta a jikinsa

Fushi kikayi ne Gimbiya?

” waye Gimbiyar”?

Sumayya mana.

“Gimbiyar wa”?

Al’ameen…

Uhmmm kawai tace bata kara magana ba

Kinga na miki Alkawari, zan fad’a miki gaskiyan abinda na sani akan auren mu?

“Nima nafasa ji yau sai gobe”ta fad’a tana mai sa  hannu ta d’auko wayarta dake gefen filo,  airp  inda ke makale a jikin wayar ta manna a kanne

Sai magana yake baiji ta amsa  masa ba hannu yasa yana tattaba ta, Gimbiya ina magana kin mini shuru

Duk da sumayya taji Al’ameen ya taba ta Amma taki koh sauraransa 

Shikam gane fushi take yasa sa dagota sama  daga jikinsa ya jefata gefen gadon

Ihu sumayya ta sake bawai zafi taji ba don laushin katifar dana blanket bazai bari taji zafi ba tsorata kawai tayi don bata tsammaci hakan ba” wayyo wuyana ya karye”  

Nashiga uku sumayya inga wuyan da gaske kinji zafi dan Allah kiyi hakuri ban dauka zakiji zafi ba, yace yana matsowa kusa da ita

Sumayya kam langobewa tayi wai wuya ya bugu”wayyo wuyata shikenan ya kasheni jama’i

Don Allah kiyi shuru muga wuyan wallahi bada niya nayi ba 

Sumayya kam kara lafewa tayi jin ya cicibeta ya daura  a cinya kamar wata baby

Sannu sumayya koh muje asibiti ne?

“Nidai goyona nakeso kayi”ta karasa maganar da make murya

Jikinsa na rawa yace, toh… toh… hau,  yana dukawa a kan gadon 

“Nika d’agani bazan iyya tashi zaune ba”

Cicibar sumayya yayi ya goya haka ya ringa lalube yana zaga d’aki zuwa baranda da ita sai kusan 10:00 sumayya taji gyangyadi kafun tace masa, ” ka kwantar da ni bacci nake ji”

Ai da sauri bawan Allah yayi d’aki da ita da lalube ya shimfid’ata a gadon duk ya gama gajiya ba kad’an ba shiyasa daya samu taye bacci ba karamin dadi yaji ba gudun fitina ma koh  tabata bayyi ba a gefe ya kwanta yanata tunanin wuyan sumayya don harga Allah ya d’auka da gaske ne

Da asuba ma hakan take sashi tayi ya d’auketa har waje tayi alwala ya dawo da ita d’aki kafun ya tafi masallaci.

Misalin karfe 9:12 na safe Al’ameen ne ke bacci  a d’aki bayan dawowar sa sallan asuba

Sumayya data gama aikinta a nitse tayi girki duka don bata tashesa ba saida ta gama harda wanka tayi kafun a Hankali tashigo d’akin  wayanta ta d’auka ta danna play in waka ta kara volume,  ta saka Eirps   kunnen Al’ameen ta mannawa

Ai kam yana cikin baccinsa yaji abu tibbbtibb ga waka kamar a kwakwalwarsa, da sauri ya mike zaune hade da furta, innalilahi sumayya wuyank……..sai kuma yayi shuru jin dariyan sumayy a kusa dashi

Hannu yasa sosai ya damkota kwantar da ita yayi a gefensa yahau kanta sosai yayi lamo yana daidaita bugun zuciyarsa har lokacin abin na kunnensa

“Wayyo menene haka”?

Shikam koh jinta bayayi, sai dad’a lumshe idonsa yake jin wakar da ke tashi a kunnensa sosai yatafi dashi 

Da sauri sumayya ta zare eirps in jin sai magana take baya kulata

Da sauri ya bude ido, tare da kamo hannunta data cire masa abin kunnensa, mena cirewa? wakarfa bai kareba

“Inata magana kamin banxa badole na cire ba”

Toh mekike son na miki kenan guda daya? tunda jiya ma ai magana nake miki kika saka abinnan a kunnenki kika manna mini nima,  duk wai akan maganar jiyanne kiketa fushi koh?

Shuru sumayya tayi

Dalilin auren mu…….

nidai bazance Miki nasan kome akan auren mu ba illah dai bazan manta ba wata Rana wani mutum yazo ya sameni agun sana’a ta yasai Mangoro ya tafi bayan kwana biyu Kuma sai gashi ya dawo Amma baifita a motarsa ba aika yaro yayi ya kirani nakai masa mangoro bayan naje ne yace na Shiga motarsa,  Yana da magana Dani,ni kuma naji tsoro gudun kar Amaimaita na baya(Randa aka makantar dashi) shiyasa naki Shiga motar duk yanda yayi Dani ki nayi,karshe dai agun mukayi magana,Kamar haka

Ni sunana mamman Ina da yarinya Naga hankalinka da nutsuwarka shine nayi maka kwad’ayin Koh zaka Amince in baka auren ta?

Sosai naji mamaki nida bana gani ad’auki yar Mai mota sukutum a bani gani Talaka haka kawai sainaji Raina Bai Kama zancen ba, shiyasa nace Masa bana bukata batare da Kuma sauraransa ba nayi tafiya ta

Bayan sati D’aya kawai bappa sulaiman yakirani Wai za’a mini aure,sosai abin yaban mamaki za’a mini aure kuma kamar mace,bappa aure Kuma Kamar Yaya?na tambaye sa

KARANTA: “MATAR MAKAHO PART 8 HAUSA NOVEL”


Kamar yanda kaji bappa sulaiman ya bani Amsa

Duk Azana Yar gidan nan za’a bani Amma bappa yace Wai Yar shugaba family ne tunda naji haka kawai nasan lallai wannan aure mai dalili ne ba auren Angani anaso ba,da farko naso nunawa bappa illan auren nan Amma ya murza ido yace sai anyi daga karshe ma cemin Yaya Wai yarinyar tanada Wanda zata aura matsala aka samu bayan anyi test shine aka samu tana d’auke da c…………….

Back to top button