Karfe A Wuta Chapter 72 By Ayshercool
*Ina ma’abota bibiyar litattafan bright pens, ƙarƙashin mikiya writers association, marubutan da suka kawo muku CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI, A first batch ga second batch, ƘARFE A WUTA, MUTALLAB ya fara zuwar muku da na sa saloz sai kuma ZAYTOON DA HADARIN GABAS NA NAN TAFE SUMA A CIKIN WANNAN WATAN, KAR KU BARI A BAKU LABARI.Waro ido suka yi waje, jin abun da Nabila ta yi wa Viper, liti ya doko tsalle yana faɗin “Ke! Saken da ki ka samu har ya kai haka, mai zamanin ki ke yi wa tsawa?””Nayi ɗin, kai kuma a suwa?” Tayi maganar cike da son huce takaicinta a kan liti.Walid ya yinƙuro ya fito, amma Viper tuni ya danƙi ƙeyar Nabila, Walid ya yinƙuro, amma Viper ya ɗaga masa hannu, ya yi waje da Nabila.Sai da ya yi nisa da ita, sannan ya saki ƙeyarta, ta ja da baya, tana ƙifta idanu.Ya taka a hankali ya ƙarasa gabanta, ya tsaya ya kalleta ya ce “Ni ki ke wa tsawa a gaban jama’a ko?”Ta sunkuyar da kai, tana yamutsa fuska tare da tura baki.”Karki yi ƙoƙarin tsallake iyaka, ki kaini bango, idan na yi magana bana son jayayya, ki ƙyale wannan maganar, ki tafi da id card ɗinki zan tura miki adress ɗin da zaki je, a asibiti ne kiga shaidan da nake da shi, wato madaki.Ta ɗago ta kalleshi ta ce “Kai ba zaka je ba?”Ya girgiza kai ya ce “Tsoro nake ji, na samu labarin yayanki ya ƙara tsananta nemana kar ya kamani”Nabila ta ce “Hotonka yake nema, ya ce a samo masa hotunanka, ina tunanin hotunanka za ayi sharing ace ana nemanka”Ya ce “Duk neman da yake yi mini ma bai sanni ba, a confused blind man” yayi maganar tare da yin murmushi. Sai da ta kuma kallonsa, ganin yana murmushi, murmushin ma a nutse yake yi.Kallonta da ya yi, ya sanya ta daina kallonsa, ya ce “Amm kwanaki, kamar akwai maganar da ki ke son ki yi mini, something like wani abu yana damunki””Baka tambaye ni a lokacin ba sai yanzu, ka manta ba wani abu bane, ya wuce” tayi maganar cikin tsiwa, tana kawar da kanta gefe.Kallonta yayi, bai ce uffan ba, ya zira hannu a aljihunsa, ya ciro wayarsa, ya danna ya saka a kunnensa, ya ce “Kawo mini abun nan, na ƙasan katifata, ina wajen bishiyar kalgon nan”Shiru ya wanzu a tsakaninsu, sai ga ɗan mama ya ƙaraso, ya miƙawa Viper envelope, ya saka hannu ya karɓa ya ce “Zaka iya tafiya”Ya kalli Nabila ya ce “Gashi, wani abu ne daga aikinki ne na fara biyanki wani abu, idan komai ya kammala, in sha Allah zan yi miki kyakykyawan biya”Ta karɓi envelope ɗin ta jujjuyata, ta saƙala masa a hannunsa ta ce “Da dan kuɗi zan yi maka aikin nan, da ba zan yi shi ba, bana buƙatar kuɗinka, a wurin Allah nake neman ladan abun da zan yi maka, ba wai dan halinka ba”Shi ma ya jujjuya envelope ɗin, ya ce “Rashin sani, ya fi dare duhu, abun da yake ciki yafi kuɗi muhimmanci a wurinki, zaki dawo ki nema da kanki, shikenan a sauka lafiya”Ta shagwaɓe fuska tana kallonsa, shi ma ita yake kallo, ji yake kamar ya tambayeta me yake damunta, ta rame, amma ya kasa.”Kayi haƙuri””Da me?””Kayi haƙuri ka bani”Ya zira aljihunsa ya ce “Ai kuma kin yi wa kanki, maganin mara kunya, wuce ki tafi gida, kan a fara nemanki”Ta sake marairaicewa ta ce “Dan Allah”Viper ya ce “Kar ki ɓata mini rai, wuce ki tafi””Korata ka ke yi ko? Dan Allah meyasa ka tsane ni ne? Me nayi maka?, Kalli duk rashin lafiyar nan da nayi, ko sannu fa Viper, sannu kawai baka iya yi mini ba, abun yayi mini zafi fa””Really?”Ta haɗiye wani abu mai ɗaci, ta gyaɗa kai ta ce “Shikenan, bari na tafi, in sha Allah zan yi duk abun da ya dace” ta juya zata tafi ya ce “Amm meye ma sunan naki? Abla ko?” Ta waiwayo ta kalleshi, ta fara tunanin a ina ma aka taɓa kiranta da wannan sunan?.Ta girgiza kai ta ce “A’a Nabila””Ohh, sunan yayi mini tsayi, just accept it Abla”Kamar ba yanzu ya gama yi mata wulaƙanci ba, ta ce “Nice one, na gode sosai” tayi maganar tana ɗaga masa hannu.***”Hello, Salim kana ina ne?””Bokan turai, ya aka yi ne?””Dan Allah gida nake son ka samo mini”Salim ya ce “Gida kuma?””Eh salim, amma ba na son kowa ya sani, a wajen gari kuma, saboda na san daddy zai saka a fara bibiyata, sun dage lallai sai sun gano in da rahama take”.”To kai yanzu hakan da ka ke yi kana ganin shi ne dai-dai?”Abdul ya ce “Shi ne, dole zan danƙata a wurin iyayenta, na kai ta makaranta kafin su san in da take””Abdul, ina tsoron abun da zai biyo bayan abun da kake yi ne?””Salim, rayuwar rahama nake ƙoƙarin karewa da ingantanwa, dan Allah ka taimaka mini, kar a kuma cutar da yarinyar nan a wannan karon””Shikenan, babu damuwa za a duba in sha Allah””And sirri ne Please, ko saif ba na son ya sani””Haba mutumina, ba sai ka jaddada mini ba, you are safe””Thank you”***Kankarofi yana zaune a kan gadonsa, yana daddana wayarsa, ya ci karo da lambar Hafsat. Ya yi shiru yana kallon lambar ta ta, ya shafi saman lambar yana tuno ta, yarinyar ta nuna masa so, kuma shi kansa ya san ba dan yana son ta ya aureta ba, amma beside his wealth, ta so shi, ta yi iya ƙoƙarin ta a kansa, amma ya kasa sakewa da ita, yayi mata adalci, har auren ya mutu.Amma ita jidda bai ji haka a kanta ba, hasali ma sosai suke gogawa ita da Safiyya, duk da dama Jidda tsohuwar budurwarsa ce, lokacin tun suna jam’iyya ɗaya da Indabo, kuma za su yi sa’anni da Safiyya, ita kuwa hafsa yarinya ce dama. Ya ji ciwon rashin samun auren jauhar da bai yi ba, amma duk da haka yana yi wa Allah godiya, da ba jauhar ya aura ta wahala suka rabu ba.Shiyasa ko zai ƙarar da duk abun da ya mallaka, sai ya tabattar da indabo ya girbi abun da ya shuka, ba ƙanwarsa yake aure ba, ko babarsa yake aure, bai ji zai iya ɗaga masa ƙafa ba, kisan mummuƙe zai yi masa, kamar yadda shima indabon yake yi.Jidda ta ce ta shigo ɗakin, sanye cikin doguwar riga, ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi, ya ce “Ya dai?”Ta yi guntun tsaki ta ce “Nifa gaskiya na gaji””Da me?””Haryanzu ana yi mini sintiri a kan rashin mutuncin da Abdul yayi, yau wannan ya zo, gobe wancan ya zo, duk security ɗin nan, gaskiya ni kawai ka canza mini gida, mu bar estate ɗin nan, na gaji wallahi””Mu bar estate ɗin nan, amma ɗaya gidan kin san na sister ɗinki ne, a nan suke zama idan sun zo hutu””So find another one mana, am tired hell of all this, abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, tun da abun ya faru ban sake ganin Abdul ba, ga babarsa ta kira ni tana nema ta gaggaya mini magana, wallahi rashin ramma a gidan nan, gaba ɗaya bana samun komai yadda nake so, khalifa da ansar haryanzu suna tambayata, yaushe yarinyar nan zata dawo, sun saba da ita, Abdul yayi mini hauka wallahi ” har ta gama surutanta, murmushi kawai Alhaji mu’azzam yake yi, bai ce mata uffan ba.***”Hello Ambassador Tahir Arabi””Distinguish, ya aiki ya Nigeria?””Alhamdilillah””Masha Allah, dama maganar yaron nan ne”Indabo ya ce “Na wurina? Jafar?”Amb Tahir ya ce “Eh shi, wallahi distinguish sai haƙuri, sun bawa America shi, kuma yana daf da fara fuskantar shari’a, kuma na lura babu wani abu da embassy ɗin mu zasu iya yi a kai, duk da dai haryanzu muna cigaba da ƙoƙari”Indabo ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, Ambassador ba wani abu da za a iya fa ka ce?””Wallahi kuwa, ka san kisan kai yayi a amurka ya gudu Mexico ya cigaba da harkar ƙwayoyi da hodar iblis tsakanin Nigeria da mexico, yadda aka shirya kama shi, akwai ƙwarewa sosai da sosai, bisa ga wata yarjejeniya da haryanzu bamu san ta mecece ba tsakanin Amurka da mexico suka basu shi, wataƙila musayar fursunoni suka yi”Jiki a sanyaye Indabo ya ce “Na gode sosai da sosai”Ya katse wayar ya dafe goshinsa ya rasa abun da yake yi masa daɗi.*****Da daddare Nabila na kwance, tana ta tattara bayanai a kan shari’ar Viper, sai ƙarfe ɗaya na dare, sannan ta samu sukunin kwanciya.Ta janyo wayarta, tana duddubawa, ta ga lambar Viper, kawai ta danna kira.Bisa ga mamakinta kawai ta ji ya ɗaga.Ta ce “Viper””Mmm””Ba ka yi bacci ba?””Mmm”Tayi murmushi ta ce “Me ka ke yi ba ka yi bacci ba?”Muryarsa ƙasa-ƙasa kamar mai jin baccin ya ce “Abun da ya hanaki bacci ne hana ni”Ta ce “Wai ni? Ai ni soyayya ce ta hana bacci” tayi maganar tana murmushi.Viper ya ce “Nima haka, tunani da kewar matata ne ya hana ni bacci””Ai addu’a zaka yi mata””Ina yi mata, zafi ya dame ni, ina missing fankata” yayi maganar very serious yana lumshe idanunsa.Nabila ta ce “Fanka? Wace irin fanka kuma?Ya ce “Fankar solar ce, iskarta daidai ba mai cutarwa ba”Nabila ta ce “To ko sayo fankar za ayi, ban zaci ana zafi a wurin nan ba ai””A’a nikaɗai nake jin zafin ai”Tayi dariya ta ce “Ko ƙiba ka yi ne? Zan sayo maka fanka in sha Allah”Viper ya ce “Ki ƙyale maganar fankar nan, ba ki da kuɗin sayenta, ba irin wadda nake buƙata zaki saya ba” yayi maganar yana juyi tare da gyara kwanciyar sa.”Ka gaya mini, zan sai maka in sha Allah, wace iri ka ke so i promise”Ya ce “Ba zaki iya sayenta ba””Ka gaya mini, zan nemota in sha Allah”Viper ya ce “Ita fankar?””Eh mana”Kawai ta ji yana dariya, har da gyaran murya.”Kai, dama kana dariya?” Tayi maganar tana tashi zaune.Yayi shiru bai ce komai ba.”Viper””Mmm””Dan Allah me ka bani a envelope ka ce zan dawo ina nema da kaina?””Ki manta, ya wuce kawai, zan baki address ɗin nan, ki je ki samu mutumin nan”Tayi ajiyar zuciya ta ce “To, kayi bacci mai daɗi””Zafi ya dame ni, ba zan iya bacci ba”Ta ce “Ka tashi liti yayi maka fifita””Na gaya miki fanka nake so ai, sai da safe””Ai ka ƙi gaya mini wace iri ce, dan dai fanka sai na saya maka, shikenan yau na ci pass an yi mini dariya””Hmm” kawai ya ce.Ta sake cewa “Viper””Kar sunan ya ƙare”Tayi murmushi ta ce “Sunan daɗin faɗa, Viper, in shot kuma V.Snake” ta faɗa tana murmushi.Ta sake cewa “Wai a ina aka yi maka rigar nan, nima ina so””Wacce?””Wadda aka rubuta sunanka a jiki””Nawa zaki saya?” Gyara zama tayi, jin yana kulata yau.”Ayi mata kuɗi, zan saya ko nawa ce, ka san wani abu, idan Allah ya sa muka yi wining a court, rigar nan zan saka in yi ta yawo ina murna””To, Allah ya bamu sa’a””Amin V snake”Wasu lokutan simple da shi, wasu lokutan kuwa, sai ka rasa gane kansa gaba ɗaya.Ta ce “Sai da safe””Hmm” kawai ya ce, ta katse kiran.***Sanarwa ko ta ina, a kan tsananta neman Al’amin Viper, tare da alƙawarin kyauta mai tsoka ga duk wanda ya nuna ko ya bayar da information a kan in da za a same shi.Nabila ta damu sosai, ga Sumayya ta daina ɗaga wayarta, dan haka ta shirya tsaf, ta tafi wurin aikin sumayya.Sumayya na ganinta ta haɗe rai, Nabila ba ta yi fushi ba ta ƙarasa in da take ta ce “Sumayya ba kya ɗaga wayata meyasa?””Ban sani ba, na gaji da wahalar da ki ke saka mu ne, babu dalili Nabila, daga wannan sai wancan? Gaba ɗaya kin hanamu nutsuwa da sukuni, ki jijjigo mana wannan masifa muna zaune, wane irin kallo ki ke so ayi miki, idan aka ga kin koma bawa ɗan ta’adda kariya, hukumar yan sanda na nemansa ruwa a jallo, ke kina tare da shi””Sumayya, baki yi mamakin yadda na sauya lokaci guda ba? Har kin manta huci da haƙilon da nake yi a kan a kama shi, kwatsam ki ji na koma na ce zan tsaya masa na bashi kariya, ayar tambaya yakamata ki fara saka mini, meyafaru?”Sumayya ta ce “Ba wani in tambayi meyafaru, kawai ki cire kanki daga wannan sabgar”Nabila ta ce “Wallahi ba zan ajiye ba, ko me za ayi mini” kawai ta saki baki tana kallon Nabila.”Ko dai ki tayani a wannan karon ma, ko kuma ki ƙyale ni ki zuba mini ido, yanzu ya maganar program”Sumayya ta ce “Mhmm yana nan, Nabila ni yanzu kin daina bani mamaki tsoro ki ke bani, yanzu duk bala’in nan, kin san in da Viper yake””Ƙwarai ki gaya wa uban kowa da ki ke so masoyiyya””To, Allah ya taimaka””Amin, gama mu tafi ki rakani wani wuri”Sumayya ta ce “A’a ba zaki kai ni in da za a kashe ni ba”Nabila ta ce “Wane irin kashe ki kuma, mu je dan Allah””To ki tsaya na kammala abun da nake yi, sai mu tafi”Ta kammala abun da take yi, suka fita, tare da sumayya.Tiryan-tiryan suna tafe, har ƙofar ɗakin da Viper ya rubuto mata, wasu masu sanye da kaki, suka tarar a ƙofar ɗakin a tsaye, Nabila suka gaisa, ta ciro id card ta nuna musu.Suka ce ta shiga, amma ban da sumayya, Nabila ta ce “Ita ma ma’aikaciya ce, yar jarida ce”Suka ce “A’a kekaɗai aka ce mu bari ki shiga”.Sumayya ta ce “Ba damuwa, zan jira ki a nan”Nabila ta shiga, ta yi sallama ta tarar da mutum a zaune a kan gado, hannunsa ɗaya an saka masa sarƙa, ƙafarsa kuma ɗaya an yanke ta.Ta ƙarasa gaban gadon, ta ja kujera ta zauna, ta kalleshi ta ce “Sannu malam”Ya ce “Yauwwa”Ta ciro id card ta nuna masa ta ce “Sunana barrister Nabila, na zo ne a kan case ɗinka da Al’amin mai zamani.Ya ɗago ya kalli Nabila amma bai yi magana ba.”Ka yi magana, dan ka sauƙaƙa wa shari’a, me ka sani game da kisan da aka yi wa matar mai zamani?”ya yi shiru ya ƙi magana.Tayi tayi, amma yaƙi cewa komai, ƙarshe haka ta fito bai yi magana ba.Sumayya suna ta hira da security ɗin wurin, Nabila ta fito, tana ganin Nabila ta tashi ta ce “Kin gama?”Nabila ta ce “Eh mu tafi”Suna tafe ta kira Viper a waya, ta ce “Hello V snake””Barrister””Naje wurin gayen nan, amma yaƙi magana, nayi nayi, yaƙi magana”Viper ya ce “Rabu da shi, zai yi ta ƙarfin tsiya, ki tafi kawai””Ok, na ma taho, amma yakamata yayi magana gaskiya, bari na ƙarasa gida sai anjima” ta kashe wayar.Sumayya ta ce “Nabila wai wurin wa ki ka zo ne?””Zan yi miki bayani, amma ba yanzu ba”Ta ce “Ok shikenan”***”Rahama kina ji na?””Ina jinka””Zamu sake barin gidan nan” “Zuwa ka mayar da ni gida?””Wai na mayar da ke gida ki yi me? Ai kin san iya wuya muna tare, nan zamu bari temporarily, daga can kuma zan kai ki gida, sai kuma makaranta, a abuja zaki koma da karatu ai””Yar ƙauye a Abuja, to ai ban iya turanci ba, ni gaskiya na fi son makarantar garinmu”Abdul ya yi dariya ya ce “Ai Shiyasa zaki je Abujan, zaki iya turanci, kan ki gama ki ƙara gogewa ki zama her excellency rahama””Taɓ abun ma ba tsari””Kamar ya babu tsari?””Wata zaka aura ai, kuma ni a lokacin mutane zasu ji daɗin nuna ni suna aibata ni”Abdul ya girgiza kai ya ce “Muna tare, babu wanda zai aibata mini ke”Ramma ta yi murmushi ta ce “Ba zaka iya canza komai ba, ɗabi’ace ta al’ummar hausawa”Ya ce “Shikenan, mu bar maganar”Ta ce “Ya dai fi”Wayarsa ya ɗaga, ya ɗan gyara zamansa ya ce “Na’am Mummy””Wato Abdul kafi son ka yi ta sakani a tashin hankali da damuwa ko?””Mummy me nayi kuma?””Ban sani ba, ka saka babanka yana yi mini kallon ni nake goya maka baya ka ke yi masa rashin ɗa’a, ka fito da yarinyar nan ka huta su huta ka ƙi, rashin mutuncinka har ya kai ka ajiye mace kana lalata da ita, bayan na keta mata haddi,, ga ɗan uwanka can an mayar da shi america, sai abun da Allah ya yi, shiyasa ake ta fafutukar ka zama gwamnan nan ko a samu ya fito, amma ka ƙi, ya ka ke so na yi Abdul, in bar muku duniyar ka huta ko?”Cikin damuwa ya ce “Mummy ki yi haƙuri dan Allah, ki fahimce ni, ya za ayi na so ki mutu, ba haka bane ba. Wallahi Mumm tsoro nake ji na fito da yarinyar nan, ayi mata wani abu na daban, dan Allah ki yi haƙuri, zan zo gida nayi miki bayani, na san zaki fahimce ni in sha Allah. Kuma yaya jafar zai fito in sha Allah, ki yi haƙuri dan Allah””Ai shikenan, ka yi abun da ka ke so””A’a ba za ayi haka ba, zan zo har gida nayi miki bayani” ta katse wayar, yayi ajiyar zuciya yana lumshe idanunsa ya buɗe yana kallon ramma, da ta yi kamar ba ta jin me yake faɗa a wayar.”Rahama””Na’am””An sakoni a gaba a kanki””An san ka sace ni kenan?”Abdul ya ce “Ke fa ba a abun arziki da ke, ke da ban sace kin ba, da yanzu wani zancen ake ba wannan ba””Ai ba da kyakywar manufa ka sace ni ba, kashe ni ka ce zaka yi””Amma ai ban kashe kin ba ko?” Tayi masa shiru ta cigaba da aikin ta.****Nabila ta fito daga banɗaki, kawai ta tarar da Nasir a tsaye a ɗakinta, ta kalleshi ta ce “Lafiya?”Ya ɗago mata file ɗin Viper da yake hannunsa, ta bar shi a kan gadonta tana aiki, ya faɗo mata ɗaki.”Menene wannan?” Ta ƙarasa gabansa ta saka hannu zata karɓa, ya janye yana sake tambayarta “Menene wannan Nabila?””Babu ruwanka da ko menene, ka bani file ɗina kuma ka daina shigo mini ɗaki ba tare da iznina ba”Cikin tsawa ya ce “Ki yi mini bayani kin tsaya kina wasu kame-kame da wasu maganganun banza da na wofi”Cikin dakewa ta ce “DSP aikina nake yi, ka fita daga harkata ka bani file ɗina””Nabila, ta tabatta goyon bayan ɗan ta’adda ki ke yi?””Ni bayan gaskiya nake bi, kawai, ka bani file ɗina””Nabila kina haɗuwa da mutumin nan, kin san in da yake””Ni ban san in da yake ba, ka bani file ɗina tun ina ganin mutuncinka”Shammatarsa tayi, ta kafa masa haƙora a hannunsa, ba shiri ya sakar mata file ɗin, ta kwashe abun ta tayi waje, ya bi ta da kallo, ya kalli hannunsa yadda yake tsatstsafar da jini saboda iya ƙarfinta ta cije shi.Cikin yarfe hannu, ya bi bayanta, sai dai ko sama ko ƙasa ya nemeta ya rasa a cikin gidan nan.Zuciyar sa ta daɗe tana mamakin abun da ya gani, amma haryanzu ya kasa gazgata cewar Nabila tana haɗuwa da Viper, ta san in da yake, amma me zai haɗata da ƙasurgumin ɗan ta’adda haka tana ya mace, idan kuwa haka ne, duk hukuncin da doka tayi a kanta shi ba zai ce komai ba, amma ya yanke ya sake tuntuɓar Abba, ya kirata ya ja mata kunne, a lallaɓata a cikin gida idan da abun da ta sani, a sasanta abun, kar asiri ya tonu, dan shi kansa abun kunya ne a gare shi, ace yana can yana haƙilon neman ɗan daba, Nabila na zagewa ta haɗu da shi a ɓoye.Da daddare Nabila na zaune a falon Abba, ga Nasir a gefe, sai kuma shi kansa Abban, tayi shiru ta sunkuyar da kai fuskarta babu annuri.”Arfa” Abba ya kira sunanta a kausashe.”Na’am Abba””Gaske ne abun da ɗan uwanki ya gaya mini?””Abba ai ban san me ya gaya makan ba”Abba ya gyara zama ya ce “Gaske ne, kin san in da wanda yake ta haƙilon nema yake? Nabila meye haɗinki da ɗan daba ne? Kina ‘ya mace?”Ta girgiza kai ta ce “Abba ya za ayi na haɗu da wanda yan sanda ma suka kasa kamawa, file ɗin shari’arsa kawai ya gani a ɗakina, kuma ba nawa bane ba, na barrister Habib ne, nima karɓa nayi na duba, ina dudduba yadda aka gudanar da shari’ar sa a wancan lokacin ne, an ce yayi shekara biyar a prison ba ayi masa shari’a, kwatsam kuma aka ce an sake shi, aka dawo ana nemansa sai nake jin kamar akwai wani ɓoyayyen lamari, shi ne nake ta bibiya, ka san muna program da sumayya, so ina binciken cases makamantan nasa shi ne kawai, amma sai zargina yake yi, ni ban san meyasa ba”Abba ya yi ajiyar zuciya ya ce “To kai ka ji abun da ta ce, me zaka ce?”Sam Nasir bai ji ya yarda da abun da Nabilan ta faɗa ba, amma ya ce “Shikenan Abba, tun da haka ta ce””Dan Allah ku daina wannan rigingimun, da ba haka kuke ba, naga tare kuke sharing working experience ɗinku, amma yanzu kuna nema ku lalata tsakaninku, ni ban ji dama arfa zata iya bin wani ɗan daba ba, tana ƙyamar irin wannan laifukan, dan haka dan Allah duk ku yi haƙuri Allah ya yi muku jagora, ya rufa muku asiri”Nabila ce ta fara miƙewa ta amsa da Amin, ta fice tana hararar Nasir, shi kuma ya bi bayanta da kallo, sam bai yarda da ita ba.Washegari aka dawo da motar Nabila, an gyarota fes har fenti an canza mata, ta ji daɗin dawowar motar nan, dama yawan zirga-zirgar nan ya isheta.Ɓangaren sumayya ma, nata program ɗin da take gabatarwa a kan shirin siyasa, na an yi walƙiyya, yana ta jan dubban masu sauraro, sakamakon yadda take baje wa mutane komai, game da irin kuɗaɗen da gwamantin tarayya take bayarwa domin ayyukan raya ƙasa, ta kan ɗauki ƙananan hukumomin shiyya ɗaya, ta kawo kuɗin da suka samu na wata, na tarayya, na jiha da na ƙanan hukumomin, da iya ayyukan da aka yi musu.Sai dai tun da ta zo kan na Indabo, a ƙalla tafi sati uku, program ɗin a kansa yake, dan sai da ta faro tun daga farkon tenure sa, yadda take hawa da sauka a kansa, zai tabattar maka akwai wata a ƙasa tsakaninta da shi. Yan siyasa da dama, sun kawo wa program ɗin hari, da neman a dakatar da shi, amma hukumar gudanarwa ta tashar suka tabattar da cewa an riga an biya su ɗaukar nauyin program ɗin, dan haka ba zasu dakatar ba, wanda bai gamsu ba, ko ya ji an yi masa sharri ko cin zarafin sa, to ya kai kotu.Da safe Nabila ta fito da motarta, sai ƙyalli take yi, ta batta a kunne, ta shiga gida ta haɗo kayan breakfast ɗin ta, ta koma cikin mota, Viper ya kirata a waya.Ta ɗaga ta ce “Hello V snake”Cikin dakakkiyar muryarsa ya ce “Kin fita aiki ne?””Ina ƙofar gida ne, yanzu zan tafi ka tayani da addu’a, yau zan kai kokenmi kotu”Ya ɗan ja numfashi ya ce “Ki bi ta farkon layinku, wurin incomplete building ɗin nan, ina nan ina jiran ki””Ok sir, gani nan”Ta ja motar ta ƙarasa in da ya ce mata, a wurin ta tarar da shi, ya tako a hankali, cikin nutsuwa. Ta zura masa ido tana murmushi ba tare da ta san tana yi ba.Ya shigo ya rufe ƙofar, ta kalleshi ta ce “Good morning””Morning” ya amsa ba tare da ya kalleta ba, ya ajiye mata baƙar leda.Ta ɗauka ta ciro abun ciki, baƙar riga ce, da sunansa a jiki Viper, da hoton maciji.”Wow masha Allah, har an yi mini? Na gode sosai, wai waye yake yi maka rigunan nan?” Yayi shiru bai amsa mata ba.Sai kuma ta ce “Sanyin Ac yayi maka normal ko na rage?” Kawai ya jingina da seat ɗin motar ya zuba mata ido.Sai ta ɗan rikice ta ce “Menene? Ko wani abun ne?” Still bai yi magana ba.Ji tayi tsigar jikinta na tashi, ta ce “Dan Allah ka gaya mini menene?””Ina jin ƙwarin gwiwa a kan shari’ar nan, wanda ke ki ka bani shi, and at the same time scared, idan rayuwarki ta salwanta saboda ni, ba zan yafe wa kaina ba, dan rayuwar ki kika saka a haɗari saboda ni, na zo ne in ce miki good luck”Duk da ta takura da kallon da yake yi mata, tamkar ta nutse, ga wata fargaba da bata san ta mecece ba, amma ta dake ta ce “Allah yana tare da mu, in sha Allah zamu yi nasara””Allah ya sa, ko mun yi nasara ko bamu yi ba, ina da kyakykyawan tukuici gareki””Ni zuciyarka kawai nake so, shi ne tukuicin da nake so” haɗe rai yayi ya ce “You are not serious, ba zaki daina wannan shirmen ba ko? Wahala zaki yi ta sha kuwa, ba na kallon kowace mace mace idan ba jauhar ba, ki je ki samu wani ku daidaita” yayi maganar ba tare da ya kalleta ba, yana ƙoƙarin buɗe ƙofa ya fita, jikinta har yayi sanyi, idonta ya cika da hawaye” yayi saurin ficewa, ba tare da ya sake kallonta ba. A guje ta fizgi motar, ta bar wurin, wanda hakan sai da ya bashi dariya, dan ya san fushi ta yi.Nabila tana tafe hawaye na zuba daga idanunta, duk ta ɓata kwalliyar ta, sai taga kamar zata yi nasara, kawai sai ya buntsure, gashi ita kullum ƙara son sa take yi so mai zafin gaske.Da haka ta ƙarasa court, ta tsaya ta ƙara gyara fuskarta, sannan ta fita ta shiga cikin court ɗin.Nabila ta nemi kotu, ta hana hukumar ‘yan sanda kama Muhammad Al’amin Ibrahim, da aka fi sani da Viper, har sai an yi cikakken bincike a kan kisan kan da aka yi wa matarsa shekaru biyar da suka gabata, hakazalika yana neman hakkinsa, na tsare shi shekaru biyar ba tare da yi masa shari’a ba, a kan laifin da ba shi ya aikata ba. Ta gabatarwa kotu kwafin shari’ar da aka yi masa a baya.Duk da ba ma a fara shari’ar ba, amma haka nan ta din ga jin tamkar ta kama hanyar sauke gingimemen nauyin da yake kanta.Abun da Nabila bata sani ba shi ne, tuni aka kira Nasir, aka sanar masa da an ganta da wani, a wurin sabbin gine-gine da ake yi a unguwar, kamar yadda ya saka CID ta ko ina a kanta.Ya shiga kitchen ɗaukar lemo a fridge ya tarar da wayar Nabila a kitchen tana ringing, ita kuma bata kitchen ɗin, ya ƙarasa in da wayar take, kiran ya yanke. Ya kalli wallpaper ɗin ta Hoton sunan Viper ne, da maciji a kan wallpaper da wani heart.Ya saka hannu ya ɗauki wayar, wani kiran ya kuma shigowa.Kawai ya ɗaga kiran ya saka a kunnensa ya ce “Waye?””Viper ne, mai zamani
Ayshercool 08081012143




