Hausa novels

Halysaah Page 214 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 214…Safiyyah ta tafi har dakin da Khaleesat ta shiga ta zauna kan kujera tana kallonta tace “To yanxu ina Ajay din?” Khaleesat ta hade rai tace “Ni kar ki sake kiran sunansa a kunne na” Safiyyah na murmushi tace “To amma dai wannan mata er iska ce, likita ce ko nurse a asibitin?” Khaleesat tace “Yanda kika san fa wata prostitute haka take, sai rawan jiki take da ta gansa, shi kuma ya kyaleta tana ta shafa masa kai yana jin dadi” Safiyyah bata san sanda tayi dariya ba tace “Ji min jaraba, shi yace maki yana jin dadi?” Wani kallo Khaleesat ta jefa mata, Safiyyah tace “Allah sa dai ba a asibitin kika baro sa ba don nasan halin ki” Khaleesat tace “In zauna in yi masa me a asibitin?” Safiyyah tace “To wai ma me ku ka je yi a asibitin, ko ciki gare ki? Dama naga kin wani yi fresh kin cicciko” Mikewa Khaleesat tayi ta fice daga dakin ta koma parlor ta zauna, Safiyyah tayi murmushi ta tashi ta bi bayanta. Har kusan karfe hudu da rabi na yamma Khaleesat na tare da Safiyyah a parlor tana mata one complain or another about Ajay, ita dai Safiyyah sauraronta kawai take don duk a complain dinta bata ga reasonable one ba, har abinda ya hadasu a Benue sai da ta gaya ma Safiyyah da yanda ta dawo Kano har aka yi admitting dinta a hospital bayan ta suma a compound, Safiyyah ta sauke ajiyar zuciya after listening to all her complain tace “Amma dai naga Khaleesat ba shi ya jawo yarinyar nan ya rungume ba fa a kauyen nan….” Khaleesat da ke mata wani kallo tace “Sai kar yayi retaliating hug din just to respect my present mana, amma wallahi rungumeta yayi shi ma, irin rungumar da ke nuna you missed someone, ai ko waye aka ma haka bazai ji dadi ba, a gabana fa? kuma da bai rungumeta in return ba ma bazan wani ji haushi sosai ba, in gaya maki gaba daya yanxu ya canza daga yanda kika san sa, ya koyi wasu mugayen halayya, can you believe har yanxu bai bude baki yace min ya jiki ba for almost a week now, sai kace ni ce nayi ma kaina cikin? Kwata kwata ya canza daga yanda kika san sa” Safiyyah tace “Ko dai kin canza sa Khaleesat, kin san ki akwai abun haushi, akwai kular da mutum, ji yanda nayi ta fama da ke a Maryland sanda mu ke schl fa, wallahi kilan he is fed up with ur attitude ne let be Sincere to our selves” Khaleesat tace “Sophie da ma kin dena wasu zagaye zagaye kin fito kin gaya min ni fitinanniya ce mara son zaman lafiya, tun daxu na lura ba goyan bayana kike ba goyan bayansa kike, shi ne me gaskiya ni ce mara gaskiya, har wani attitude gare ni da baza a iya tolerating ba dama? shikenan sakayyar da zai min kenan after everything, after all what i went through because of him….” Tana magana tana goge hawayen da ya fara zuba idonta, Safiyyah tace “Ni ba haka nake nufi ba kawata, shi fa rayuwar aure daban yake da yanda kike daukansa Khaleesat, balle idan aka yi settling fully, dole za a fuskanci kalubale, rayuwar aure fa rayuwa ce ta har abada ake fata, babu ta yanda kuma aure zai zama hundred percent perfect it is never possible, dole akwai up and down a rayuwar aure da unforseen circumstances, You know who Ajay is, kin san halinsa, kuma har muka gama rayuwar Maryland baki taɓa ganinsa da mace a sunan suna hira ba ko suna soyayya, sai dai ko abokiyar karatu kuma basa wuce turawa don baya ma harka da bakaken fata, so why are you being in secured now? Baki yarda da mijin ki ba kike nufi kenan? Ko kin kama sa da wani act ne mara kyau da ya sa kika zama not secured with him? Bai kamata kina ɗaga masa hankali ba after all the challenges he faced in life, baki tunanin wannan matsalar da ku ke samu now and then zai iya ja masa shiga wata damuwar daban? Ba fa yayi recovering fully bane daga abinda ya samesa Khaleesat, duka duka watanni nawa kenan da dawowarsa har za ki fara saka shi cikin damuwa? Ni wallahi na zata in the next 2 years to come za kiyi ta lallaba mijin ki ne ko bata maki rai yayi zaki shanye considering all what he went through for 2 years, meye don kawai warce ba musulma ba ta rungumesa, su ai a wajensu ba komai bane hakan da tayi, she was just happy to see him, shi kuma kinga ai bazai gwaleta ba duba da hidimar da suka yi da shi, kuma mutanen nan dai ya kamata su zama second family din ku, don da ba don su ba da wani zance muke yanxu ba wannan ba, Ajay is alive today as a result of their help Khaleesat, kika san gwagwarmayar da suka sha wajen nema masa traditional medicine da har ya farfado? Kika san effort dinsu akan Ajay? Duk wanda zai maka haka ai ba abun wasa bane a gare ka Khaleesat, don ya basu kulawa kuma ya ba yarinyarsu attention ba abu bane da ya kamata ki mayar issue, plsss ni ban san ki da mummunan kishi irin wannan ba gaskiya, don Allah kar ki ari halin da ba naki ba ki yafa kawata, ki zama mace ta gari me kwantar ma mijinta hankali ba wai me ɗaga masa hankali ba akan abinda bai kai ya kawo ba, da wani abu ya samu cikin jikinki kin zata bazai shiga damuwa ba, wallahi a yanxu dai kulawa da soyayya kadai Ajay ke bukata not all this things you are doing” Bude kofar parlon aka yi, Khaleesat ta jawo hijab dinta ta saka, Yaya Mustapha ya shigo parlon da sallama, Khaleesat ta amsa tana yi masa sannu da zuwa, da fara’a ya amsa yana kallonta yace “Hajiya Khaleesat ce a gidan namu yau?” Tana ɗan murmushi tace “Ina yini Ya Mustapha?” Yace “Lafiya lau, ya kike ya kwana biyu?” Tace “Alhamdulillah” Yace “Ya mai gidan fa?” Tace “Yana lafiya” Yace “To maa sha Allah, sannu da zuwa” Bedroom dinsa ya wuce, Safiyyah ta mike ta bi bayansa, Khaleesat ta bi ta da kallon mamaki kamar idanuwanta za su fito… Har bayan magrib Khaleesat bata ga keyar Safiyyah ba, har ta gaji da zaman parlorn ta tafi dakin baƙi, Safiyyah ta kasheta da mamaki sosai ba kadan ba, saboda mijinta ya dawo shi ne zata bar ta a gantale a parlor bayan tasan dalilin zuwan ta gidan, don ma bata da kudi a hannunta ne da tafiyarta zata yi kawai, wajen karfe bakwai da rabi yunwa ya ishi Khaleesat gashi ko kadan bata da juriyar yunwa yanxu, tashi tayi ta fita daga dakin bayan ta bude kofa a hankali, ta tafi kitchen ta debi abinci ta dau ruwa ta koma dakin, bayan ta gama cin abincin tayi sallah ta shiga bandaki ta wanke bakinta da mouth wash da ta gani sannan ta fito ta kwanta. Washegari wajen karfe bakwai na safe Safiyyah ta shigo dakin ta tarar da Khaleesat na cin bread da ta dauko a kitchen don da yunwa ta tashi, wani kallo tayi ma Safiyyah, Safiyyah taki yarda su hada ido tace “Ke yanxu da wuri kike bacci ashe? Jiya na shigo kawo maki abinci da fruits naga kin yi bacci, na tashe ki kika ki tashi” Khaleesat tace “Za ma ki gama kame kamen ki, wato ni zaki walakanta ki tafi ki makale wajen mijinki ki bar ni kamar gantalalliya a parlor ko” Dariya Safiyyah tayi tace “Ni fa waya naje ina yi da momy, duk yunwa ne yasa kike cin bread gaya, bari in maki breakfast yanxu” Bata jira cewar Khaleesat ba tayi saurin ficewa daga dakin tun kan Khaleesat tace komai, Khaleesat ta kyabe baki, wai sai ga Safiyyah da makalewa a dakin ya Musty duk cika bakin da ta dinga yi, murmushi kawai Khaleesat tayi tana ci gaba da cin bread din hannunta. Wajen karfe sha biyu na rana Khaleesat ta shirya zata tafi gida, Safiyyah na kallonta tace “To yanxu in kin koma sai ki ce ma su Umma ina kika kwana?” Khaleesat tace “Babu wanda zai ce min komai tunda an san da wanda na fita ai” Safiyyah tace “What if yaje can gidan yana neman ki bakya nan?” Khaleesat ta hade rai tace “Bazai ma je ba, bayan yasan abinda ya aikata ai bazai ce zai je gidanmu ba” Safiyyah tace “Zai ma yi tunanin gida kika tafi direct” Tabe baki Khaleesat tayi ta gama yafa veil dinta sannan tace “Wai Maman Aslam fa?” Hade rai Safiyyah tayi kamar an kira enemy dinta tace “Oho” Khaleesat tayi murmushi tace “Amma dai ba gida daya za ku zauna in kun koma Baltimore ba?” Safiyyah tace “Waye zai zauna gida daya da ita, ai ya ma dawo nan da aiki yanxu” Khaleesat ta bude ido sosai tace “Kai don Allah?” Safiyyah tace “Wallahi” Khaleesat tace “Allah sarki….” Wayar Safiyyah ya fara ringing tana dubawa taga Ya Mustapha ke kiranta ta mike zata fita daga dakin Khaleesat ta fixgota tace “To wallahi ba ni zaki shanya ba ke me miji, dadin abun nima dai ina da mijin nan” Dariya sosai Safiyyah tayi tace “Mijin da kika gantalar, ni dai ki sakeni, yanxu zan dawo wallahi” Khaleesat tace “Ikon Allah, to amma inji dai ba gado daya ku ke kwana da ya Mustapha ba dai ko?” Safiyyah taki kallonta tana dariya tace “Don Allah ki sakeni, i will back soon” Khaleesat tace “Ai kuwa sai dai Ya Musty yayi hakuri, mu je ki ma driver magana ya maida ni gida tukunna sai ki dawo ku shige daki” Khaleesat bata bar Safiyyah ta je wajen Ya Mustapha ba har sai da tayi mata rakiya zuwa compound, sannan Safiyyah tayi ma Driver magana yayi dropping dinta a gida…. Bayan driver yayi parking a kofar gidan su Khaleesat ta bude motar ta sauka tayi masa godiya, sauka yayi daga motar yace “Madam ta bada sako za a baki Hajiya” Zagawa yayi ya bude trunk din motar ya ciro wata babban leda ya mika ma Khaleesat, Khaleesat ta dinga kallon ledan sannan ta amsa tana duba ciki, lokaci daya ta fahimci menene a ledan ta mayar masa tace “Don Allah ka mayar mata gida kawai” Drivern yace “Wallahi tace kar in dawo da su Hajiya kiyi hakuri” Bude driver seat yayi ya shiga sannan yayi ma Khaleesat sallama, ita dai kasa cewa komai tayi har ya bar kofar gidan, ta juya ta shiga gida, sai da ta shiga daki sannan ta bude kayan cikin ledan taga atamfofi ne guda biyu sai Abaya biyu masu tsada, da sauran tarkacen cikin kayan lefe, Khaleesat tayi murmushi kawai ta ajiye kayan. Jay na zaune parlor yana operating laptop aka bude kofar parlon, daga kai yayi ya dinga kallon Ajay da mamaki, ya matsar da laptop din kusa da shi yace “Dawowa ku ka yi?” Ajay ya karasa ya zauna kan kujera yace “Ni da wa?” Jay yace “Ina Halysaar?” Ajay ya jinginar da kansa da kujera kamar bazai ce komai ba, sai kuma yace “Ba tace sai ta haihu ba, duk bayan sati zan dinga zuwa dubata kawai” Jay dai kallonsa kawai yake, can ya mike ya karasa kusa da shi ya kai hannunsa jikinsa, zaunawa yayi gefensa yace “You are sick Ajay” Ajay ya ɗaga kai ya kallesa, after some seconds a hankali yace “Yanda nake ji few months back haka nake ji yanxu, i couldn’t breath well yesterday night” Jay yayi shiru yana kallonsa, can ya sauke idonsa, kana kallonsa zaka fahimci jikinsa yayi sanyi ya kuma shiga damuwa, a hankali ya tashi ya dau makullin motarsa yace “Tashi mu tafi asibiti” Ajay yace “A’a, just prescribe me medicine, I will be fine idan na sha” Yana fadin haka ya kwanta kan 3 sitter din parlon, Jay yace “No Junaid, ka tashi mu je asibiti, this is not something we should take likely….”

Back to top button