Halysaah Page 152 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 152…Ajay ya karasa har kusa da gadon ya zauna kusa da ita yana kallonta tana bacci, hannu ya kai a hankali yana gyara mata gashinta don babu hula a kanta, murya can kasa yace “Good morning Jeeddah” He was being very careful not to wake her up ganin yanda take baccin peacefully, bayan ya gama gyara mata gashin ya jingina da gadon yana ta kallonta, yafi minti goma a haka daga karshe ya mike ya nufi kofa walking slowly ya fita daga dakin. That same day da yamma Jay ya shigo bangaren Mami bayan ta kirasa a waya, da mamaki yake kallon akwatin dake gabanta tana zaune parlor yace “Mami ina kuma za ki?” Mami tace “Gombe zan je in kwana biyu wajen Karima, ina bukatar in dan huta Jawwad” Jay yayi shiru yana kallon akwatin, Mami ta mike tace “Ka kai min akwatin parking space driver yana jira, zan shiga bangaren Hajja in masu sallama” Daga haka ta fita daga parlon Jay ya bi ta da kallo, Mami na shiga Parlon Hajja ta sameta zaune tare da Hadiyah da ta dora kanta a katar Hajja, Hajja ta hade rai tana ci gaba da maganar da take ma Hadiyah, Mami ta zauna tace “Hajja zan je Gombe, shi ne nace in zo in maki sallama” a takaice Hajja tace “Allah ya tsare” Mami tace “Ameen” Mikewa tayi ta wuce dakin da Khaleesat take, zaune ta sameta kan pillow a kasa Yakumbo na oiling din mata gashinta tana combing dinsa, Mami na ta kallon dogon gashin dake ta sheki ga cika, tace “Gyaran gashi ku ke” Yakumbo ta gaida Mami da ladabi bayan ta sake gashin Khaleesat tace “Ai kam gyara muke Fulani, kwana biyu tace bata shafa ma gashin Mai ba shine nake shafa mata yanxu, barka da shigowa ranki shi dade” Mami tace “Maa sha Allah, ina Noor?” Yakumbo tace “Babu jimawan nan Yarima Junaid ya fita da ita….” Mami tace “Ohk, zan je Gombe Halysaah, ki maida hankali ki kula da kanki kinji, ki ci gaba da shiga ruwan dumi, sannan kar kiyi wasa da cin abinci, duk sanda Hajja ta bada umarnin ki koma bangarenki sai ku koma can din tare da Yakumbo ta ci gaba da kula da ke. Khaleesat dake ta kallon Mami a hankali tace “To yaushe za ki dawo Mami?” Mami ta dan yi murmushi tace “In sha Allah idan na gama abinda naje yi zan dawo Halysaah” Sosai jikin Khaleesat yayi sanyi don Mami kadai take gani a gidan nan ta samu relieve, ita kadai take sakin jiki idan ta ganta, shi Ajay yanxu haushinsa na musamman take ji yanxu don ko idonta biyu ya shigo daki yi take kamar tana bacci har sai ya fita, Hajja kuma ta kasa sakin jiki da ita har yanxu duk da kulan da take nuna mata, Mami da ta lura da yanayin da ta shiga tayi murmushi tace “Do not worry dear, I will be back soon in sha Allah, take care of ur self” Tana kai wa nan tayi ma Yakumbo sallama ta juya ta nufi kofa Yakumbo nayi mata Allah ya kiyaye hanya. Mai martaba na zaune parlonsa da daddare ya sauke kansa yana sauraron maganganun da Hajja ke yi, Hajja ta kare da cewa “Don haka nace dole ta bar gidan nan Yusuf, zamanta babu alkhairi a masarautar nan, Jawwad bai da wayon rufe ma matarsa kofa, in dai ba ita ta dorasa akan yayi hakan ba, don makirci bayan ta san abinda ta hada shine zata shirya akwati tace ta tafi Gombe, to kuwa sai dai ta dauwama a Gomben” Tana kai wa nan tayi shiru fuskarta a daure, Mai martaba ya daga kai ya kalli Ummi dake zaune parlon ita ma, bai dai ce komai ba don yana jiran isowar Jay ne, bude kofar parlon aka yi sai ga Jay ya shigo da sallama, Ummi ta hade rai don bata san Sarki ya aika kiransa ba, ita kanta Hajja bata sani ba, ya karaso har cikin parlon kansa a kasa ya zauna kan Carpet, Hajja ya fara gaidawa sannan ya gaida Ummi, Mai martaba yace “Jawwad me ya hadaka da matarka?” Jay ya girgiza kai a hankali yace “Na ce ta je gida ne sai na nemeta ranka shi dade” Mai martaba yace “Haka kawai baza kace ta tafi gida babu dalili ba ai, meye dalilin ka?” Jay ya sauke idonsa a hankali yace “Saboda bata min biyayya ranka shi dade, and they are so many things that i don’t want to talk about here, I have been enduring all this for months….” Hajja tace “Biyayya wani iri kake nufi bayan wanda take maka Jawwad? Kuma meye shi wannan abun that you don’t want to talk about idan ba sharri kake son kala mata ba?” Ummi dai sai wani hararansa take, Sarki yayi shiru yana kallon Jay, cause he could hear the pain in his voice as he speaks, Calmly yace “Kamar zuwa yaushe kenan zaka neme ta?” Hajja ta ma sarki wani kallo tace “Haba Mai martaba, wannan wani irin tambaya ne kake masa? Wato ka goyi bayan ya aika Hadiyah gida kenan kake nufi? Sannan naga ai nan din ma gidansu ne ko kai da shi kun manta ne? yanda Hadiyah take bala’in sonsa har ya isa yace ta masa wani laifin da bazai jure ba sai yace ta tafı gida? yarinyar da ko nesa bata son suna yi da juna” Mai martaba yace “Hajja baza ki yi judging base on that ba, definitely akwai abinda tayi da har yayi triggering action dinsa, kuma yace bazai fada a nan ba, we have to reason with him….” A fusace Hajja tace “Me tayi kuwa, ba abinda tayi kawai uwarsa ce ta sa yayi haka, shi ne ita ma ta hada akwatinta ta bar gidan tun ba a waiwayo ta ba….” Mai martaba ya sake kallon Jay yace “Yanxu zuwa yaushe zaka nemeta din idan ta tafi, shi nake son sani Jawwad A hankali Jay yace “Zuwa sanda na shirya zan nemeta ranka shi dade” Mai martaba ya kalli Ummi yace “Ki tafi da Hadiyah in zaki tafı, duk yanda ake ciki zan tuntube ki ta waya” Ummi ta saki baki tana kallon sarki, Hajja ma dai haka tayi tana kallonsa, can Hajja tace “To babu inda zata tafi sai dai ta zauna bangarena tunda nan ma gidansu ne, meye shi abinda bazai fada ba in ba sharri yake mata ba? Kawai uwarsa ta masa umarnin ya kora Hadiyah gida tunda naje na sameta na nuna mata bacin rai na akan abinda take ma jikata, amma in ta san wata ai bata san wata ba” Mai martaba ya kalli Jay yace “Kana ganin zaka iya gaya ma Hajja abubuwan da Hadiyah ke maka wanda baza ka fadi a nan ba?” Jay ya daga kai yace “Zan iya gaya mata ranka shi dade” Mai martaba yace “To idan ta koma sashinta sai kaje can ka sameta ku yi magana” Daga nan Parlon Sarki Hajja ta tisa keyan Jay zuwa bangarenta tana cewa “In ma kaurace ma shimfidarka take yi naga dai yarinya ce Hadiyah, iya laifin da zata yi kenan ka kasa hakuri, kuma duk yarinta ce ba wani abu ba, kazanta kuwa nasan sam bata da shi, bar ta dai da son jiki da rashin son aiki amma bata da kazanta, kuma wannan ba wani abu bane tunda ga masu aiki kaca kaca duk za su yi aikin, ta taso cikin gata ne da sarauta shi yasa baza ta so aiki ba kamar jaka….” Shi dai Jay bai ce ma Hajja komai ba har suka isa part dinta, Khaleesat na zaune parlon Hajja tare da Yakumbo dake ta bata labari, yanxu kam she is very much okay tana jin sauki sosai and she is healing very fast, Hajja ta shigo parlon Jay na biye da ita a baya, Khaleesat ta sauke kanta bayan sun hada ido da shi, ya zauna kan kujera yace “Good evening Halysaah, ya jikin?” Khaleesat ta mayar masa da gaisuwan sannan tace “Da sauki” Yace “Allah ya kara lafiya” Amsa gaisuwan Yakumbo yayi sannan ya mike ya wuce Bedroom din Hajja, ya sameta zaune tana jiransa, ya zauna kan kujera, Hajja tace “Ina jin ka….” Jay yace “I wish kaurace min take a shimfida akan tace sai an siya mata abu kaza kafin ayi mu’amala kuma ta tubure akan hakan, tun da taga matar Junaid da designers during her convocation kullum bata da aiki sai demand na designers now and then, kuma demand din nata baya tashi sai za ayi mu’amala, it’s always like this for almost 3 months now, har na hakura na zuba mata ido…….” Tun da ya fara magana Hajja ta bude baki tana kallonsa with shock, can tayi kasa da murya tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, Kar ka kuskura kaje ka fadi maganar nan a wani waje Jawwad, ko Mai martaba kada ka bari yaji wannan batu, gwara da ka gaya min ni kadai, zan kuma yi maganinta, ashe Hadiyah mutuniyar banza ce ban sani ba, Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Jay yace “That aside, few days ago naga wasu abubuwa a bedroom dinmu da ban gane kansu ba….” Hajja ta kara gwalo ido da sauri tace “Abubuwa kamar me?” Yace “I don’t even know how to put it, but suna nan na ajiye su, kamar dai abubuwan shirka or something like that” Hajja ta saki wani salatin tace “Ta shi mu je bangaren naka, tashi mu je, wannan ba maganar da kowa zai ji bane Jawwad gwara a rufa asiri ko uwarka da Sarki kar ka gaya ma wannan abu, nasan kai ba me surutu bane, Hadiyah jinin ka ce idan baka rufa mata asiri ba wa zai rufa mata, dariya za ayi mana a masarautar nan idan magana ta fita, ta shi mu je” Mikewa yayi ya nufi kofa Hajja ta bi bayansa suka fita, har Bedroom dinsu Hajja ta shiga, Jay ya dauko abubuwan da ya nannade a karamin towel har sannan kuma Hadiyah bata san ya gani ba, ya bude towel din ya ajiye kasa Hajja ta dinga kallon layun da aka nannade da jan zare, ga wani shi ma an nannade da bakin zare, sai wasu tarkace su ma duk akan towel din, har da layan da aka garkame da kwado, Hajja ta daga kai ta kallesa cikin firgici tace “A ina kaga wannan Jawwad?” Ya rungume hannunsa yace “A dakin nan na gani ina gyare gyare, don tun da muka yi aure bata taba gyaran dakin nan ba sai dai ni inyi, banda ke babu wanda na nuna ma abun nan har yanxu” Hajja ta saki salati ta nemi kujera ta zauna tana kallon abubuwan kan towel din ta rasa abun cewa, Jay yace “All this not enough, Hadiyah bata respecting Mamina, ko gaisheta bata yi a gidan nan, always saying ill about Mami in my presence” Hajja ta hade rai tace “A’a ita ma Mamin tana da nata, ka bar maganar wata Mami yanxu mu ji da wannan bala’in dake kan tawul, a ina Hadiyah ta samo abubuwan nan ni Fatsuma? Su waye kawayenta don dai uwarta bazata taba dorata kan wannan kazamin hanyar ba tunda ba haka ta taso taga ina yi ba a gidan nan nima, ba irin wahalan da ban sha ba a gidan sarauta har sai da na kusa samun tabin hankali, jifana ake ta ko wani bangare amma kwata kwata basu samu galaba a kaina ba, why because na rike Allah daya, babu ruwana da harkan tsibbu kamar yanda su suke yi, amma fa na sha wahala ainun daga karshe kuma gashi ni na ci riba, ni ce a saman su, to kuwa lallai zan je in kira Hadiyah yanxu ta gaya mana inda ta samo wannan abubuwan sabon Allahn, don ba halina bane kuma ba halin uwarta bane” Shi dai Jay kallon Hajja kawai yake, Hajja ta mike ta fita daga dakin rai bace, yana zaune parlonsa bayan kusan minti arba’in sai ga Hajja ta dawo, ta zauna kan kujera tace “To wallahi tace wata kawarta ce wai ta kawo mata su, ita kanta bata san ko na menene ba kawai ta ajiye su Jawwad, ni dama nasan sai dai in sharrin kawaye amma ina Hadiyah tasan wani bin boka ko malamai, ka dauko min su yanxu aje a zubar kawai cikin rufin asiri, kuma don Allah komai ya wuce wannan bai kai dalilin da zaka ce ta bi Maimuna Lagos ba, na kuma yi mata fada sosai, har Maimuna na taya ni, batun kwanciya ma duk nayi mata fada wallahi, in sha Allahu zata dena, yarinta ce kawai ke damunta” Jay yace “Hajja it’s better ta bi Ummi su tafi ta huta nima in huta, bazan boye maki ba on a serious note haushinta nake ji a yanzu, so ta bani space for now pls” Hajja tayi shiru tana kallonsa, can tace “Wannan dai ba kowa ya tsara maka ba sai uwarka, ita ce zata ce kace Hadiyah ta bi Maimuna, kuma babu inda Hadiyah zata tafi tana gidan nan zata zauna a bangarena tunda baka isa ka koreta a can ba….” Tana kai wa nan ta fita daga parlon. Tunda Hadiyah ta dawo part din Hajja Khaleesat taji part din ya isheta gaba daya, gashi Hadiyah ta dau karan tsana ta dora ma Noor ba gaira babu dalili, har sai da Noor ta dena zama parlor sai dai daki wajen Khaleesat, Bayan Magrib Noor na idar da sallah ta tafi kusa da Khaleesat dake shan fruit salad ta zauna, a hankali tace “Aunty ina son komawa gidan Aunty Murja” Khaleesat tayi shiru tana kallonta, can tace “Idan ya shigo anjima ki gaya masa Noor tace “Ohk” Khaleesat ta gama duk abinda zata yi kafin a idar da sallan isha’i ta kwanta don dai dai lokacin Ajay ke shigowa dubata, kuma kullum ya shigo zai ganta kamar me bacci, karfe takwas da few minutes ya bude kofar dakin ya shigo da sallama, tuni dama tayi kwanciyarta ta rufe ido kamar warce ta dade da bacci, Noor kanta tayi zaton tayi bacci, Noor ta gaishesa, ya zauna kan kujera ya amsa yace “Have u eaten?” Kai ta gyada masa, sai kuma ta sunkuyar da kai tace “Yaya ina son zan koma gidan Aunty Murja” Yace “Why?” Murmushi tayi tana wasa da hijab dinta bata ce komai ba, yace “Ohk gobe zan sa driver ya kai ki sai ku dawo tare ko?” Still dai tayi murmushi bata ce komai ba amma a ranta tasan bazata dawo ba idan ta tafi, ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin kamar yanda take yi duk sanda ya shigo, kallon saman gadon dakin yayi, ya mike ya karasa kan gadon ya zauna yana kallonta ya kai fuskarsa kusa da nata yayi kasa da murya yace “I know you are not sleeping Jeeddah, plss ki bude idonki don Allah….” Ganin ba bude idon zata yi ba, a hankali yace “Shikenan since you don’t want to see me, i am leaving for Abuja before dawn tomorrow in sha Allah, zan je wajen Ammi she lost her father this night” Yana kai wa nan yayi pecking cheek dinta a hankali ya mike ya fara tafiya yana waigota, tana jin ya tashi daga kusa da ita ta bude idonta a hankali abinda yace na mata yawo a kai, sai da taji ya bude kofar dakin ta kasa daurewa kawai ta juya kanta a hankali suka yi ido hudu da shi, tsaye yayi yana kallonta hannunsa rike da handle din kofar dakin, ta cire idonta daga nasa tana jin zuciyarta na bugawa, cire hannunsa yayi a handle din kofar walking slowly ya koma kusa da ita ya zauna yana kallonta yayi kasa da murya yace “Jeeddah” Ta daga ido ta kallesa nan da nan taji hawaye sun kawo idon nata, dai dai nan Aunty ta shigo dakin tare da cousin sister dinta Hajiya Nafisah, hakan yasa ya mike without looking at them ya gaida Hajiya Nafisah sannan ya fita daga dakin, Aunty sai kallon Khaleesat take babu ko kiftawa abinda Hajiya Nafisah tace na mata yawo a kai, ko amsa gaisuwar Khaleesat din bata yi ba ta juya ta fita daga dakin, Hajiya Nafisah ta juya ta bi bayanta, sai da suka fita daga part din Hajja gaba daya Aunty na kallon Hajiya Nafisah tayi kasa da murya tace “Ni duk kaina ya kulle fa Nafisah, anya baki yi kuskuren suna ba kuwa?” Nafisah tace “Haba sai kace wata shashasha, ba ita bace Hauwa Aliyu, ana kiranta Khaleesat” Aunty tace “Kwarai…” Aunty Nafisa tace “To ita zata haifi Yarima karami na masarautar nan, kuma ko muna raye ko a mace sai dan ta yayi mulki a masarautar nan” Aunty tace “To ni abinda ban gane ba, sake amshe title din Yariman za ayi wajen Jawwad a mayar ma Junaid kenan ko kuwa? Don maganar da nake maki yanxu dai Jawwad ne magajin sarki a Emirate din nan, sarki bai canza haka ba” Nafisa tace “Abu ya zama wasan yara ma kenan in aka sake mayar ma Junaid title, kuma ni ba ace min za a mayar masa ba, ni nafi tunanin kilan wataran Jawwad din zai nada dan Junaid din matsayin Yarima a maimakon dan sa, nan kawai tunanina ya tafi gaskiya, in kuma na kara yin wani tunani sai in ga ae su Maimuna baza su taba barin haka ya faru ba…. A fusace Aunty tayi kasa da murya tace “To ba a gaya maki menene makomar Walid ba a gidan nan? Shi bazai yi sarauta ba kenan ake nufi ko me? To wallahi sunan Jawwad matattce, ko da last kobo dina ne sai an kawar da shi, ae sai yana da ran zai yi sarauta dai ko?? Da yayi sarauta astagfirullah ba gwara Junaid yayi ba zan fi jin kamshin sarautar a kusa” Nafisa tayi kasa da murya tace “Mu je dai sashinki fulani, don maganar ba ta tsayuwa bace, Junaid kam babu zancen sarauta a tare da shi sai dai Jawwad, har nuna min shi aka yi a throne din mulki” Rai bace Aunty ta dinga bin Nafisah za su koma part dinta, saukan Nafisah gidan kenan ta dawo daga kasar Nijar duk akan aikin Aunty. Ajay na zaune parlon Mai martaba wajen karfe tara da rabi na dare, Aunty ma na zaune parlon, Mai martaba na kallonsa yace “Allah ya kai mu goben, karfe nawa zaka tafi?” Ajay yace “Before subhi in sha Allah, driving zan yi zuwa Kano sai in bi jirgin karfe takwas zuwa Abuja Mai martaba yace “Me yasa baza ka tafi Abujan direct daga nan ba?” Ajay yace “Babu jirgi time din, kuma ina son in samu sallan jana’iza ne Mai martaba yayi shiru, sai kuma yace “Tare za ku tafi da Jawwad? Ajay ya girgiza kai yace “Ban gaya masa ba tukunna, seems ya fita baya nan” Aunty tace “Ya kamata kam ku je tare da shi, tafiyar mutum biyu ma tafi dadi ai” Ajay dai ko kallonta bai yi ba, Sarki yace “To ya maganar tafiyarku zuwa Tanzania da matar ka? Fulani Aseeyah tace can zaka fara zuwa, in kun dawo sai ku tafi Ethiopia da Jawwad haka ne?” Ajay ya gyada kai yace “In sha Allah, jibi ne tafiyar dama, amma zan yi rescheduling ticket din zuwa nan da 4 days, don zan yi kwana biyu a Abuja Mai martaba yace “Alright, amma kayi ma Jawwad magana ku tafi gaisuwan tare” Aunty tace “Gaskiya kam, hakan yafi ku je tare” Ajay Yace “In sha Allah ranka shi dade” Ajay na barin parlon Sarki ya hadu da Jay ya dawo zai tafi part dinsa, kallo daya Jay yayi masa yace “Evening” Daga haka ya ci gaba da tafiyarsa bai tsaya ba, Ajay ya juya ya bi sa da kallo, yace “Za mu je Abuja gaisuwa gobe, Ammi lost her Dad” Jay ya tsaya ya juyo yace “Allah ya gafarta masa, but i am occupied gobe, sae dai jibi” Ajay yayi shiru at first don ba haka ya so ba, tamkar Grand dad dinsa yake kallon mahaifin Ammi saboda love din da ya nuna masa tun yana karami, sai kuma yace “Ohk… Allah ya kai mu Jay yace “Ameen” Daga haka ya ci gaba da tafiya zuwa part dinsa. Aunty na zaune dakin Walid wajen karfe sha biyun dare tana magana kasa kasa tace “Kuma tunda sarki yayi magana nasan dole tare za su je gaisuwan nan” Walid ya zauna da kyar saboda har Ikcn kugunsa bai dawo dai dai ba, yace “To a motar wa za ayi tafiyar?” Aunty tayi shiru, sai kuma tace “Bazai wuce motar Junaid ba mana tunda tafiyar tasa ce, kafin sallan asuba dae za su dau hanya, wallahi ko yau sai da Nafisah ta sake maimaita cewar Malamin yace in dai ba kawar da Jawwad aka yi ba to babu kai babu mulki, yau Jawwad na barin duniya kai za a nada Yarima tunda babu zancen wani Junaid” Walid yace “Shikenan, kawai ki tafi ku kwanta nasan me zan yi Momy Aunty tayi murmushi tace “I trust you my son, but be extremely careful” Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita har Ikcn tana murmushi, Walid ya dau wayarsa ya fara dialing number wani dogari dake masa aiki idan bukatar hakan ta taso a gidan, su biyu ne trusted people dinsa a masarautar, duk wani evil plan dinsa da su yake shiryawa ko ma wani iri ne, be it na cikin masarauta ko outside of the emirate, Yana fara ringing dogarin ya daga ya fara jero masa kirari.


