Hausa novels

Matar Hariji Page 14 Romantic Hausa Novel

_______Ya dauki kamar 30 minutes sannan jirginsu ya sauka mutane suka fara fitowa yana tsaye yana kallon masu saukowar can ya hango yayan nashi riqe da hannun wata balarabiyar yarinya yayi tawassali ga ubangijin daya halicci wannan kyakkyawar baiwa tasa, karkatar dakai yayi ya zuba musu ido shima Lameer din tunda ya hangishi ya lura da inda hankalin qanin nasa yafi karkata.Nan danan wani mugun kishi ya taso masa ya janyota jikinsa hakan da yayi ya tabbatarwa da Muneef cewa Hauwah ce.Numfashi yaja ya sauke ya zuba musu ido sunyi wani fresh dasu ba qaramin dacewa sukayi da juna ba kamar dama domin junansu aka haliccesu ga wani qara narkewa da takeyi a jikinsa tana shigewa shikuma sai biye Mata yakeyi.Nandanan Muneef yaji wani shauqi ya shigeshi na ace shine take yiwa haka ba wannan rabin mutum din mijin nata ba, har suka iso baisani ba saida Lameer din ya mareshi yace “ubanme kake kallo ne?” Firgigit yayi ya dawo nutsuwarsa yace “oh sorry bansan kun iso ashe da gdan kake tafe gabadaya” Murmushi yayi ya kalleta yace “kin ganeshi?” Yatsina fuska tayi kamar taga kashi haka kawai takejin haushinsa da tsanarsa tun ranar da sukaje neman aurenta taga ya kafawa nononta ido, girgiza kai tayi tace da cewa “Notthing”🤣Sakin baki Muneef yayi shikuwa gogan ko a jikinsa yayi kissing dan qaramin bakinta yace “ok muje gida nayi miki wanka ki huta sai nayi miki bayaninsa Amma ai kin gane Zaliha ko?”Murmushi tayi wani isasshe ta sake kwanciya a jikinsa daidai lkcn da suke zama a mota tace masa “tamace idan muka dawo zatayimin gyaran amare zata tsumani wai meye tsumi babe ni bangane hausarba?” Kallonta yayi da sauri yace “aa kada ki sake kisha tsumin nan zai iya zame mana matsala kinji?” Turo baki gaba tayi tace “aa wlh nikam sai nasha tsumi ai magani ne nasan bai wucce maganin rana da basir ba” ya lura wauta a jinin Hauwah take shiyasa yayi mata Shiru ya qyaleta daga kan da zaiyi yaga Muneef ya saita mirrow yana qare musu kallo ya kuwa daka masa tsawa yace.“Ka juya mirrow din nan bansan sa ido” da sauri ya juyashi yaci gaba da tuqinsa zuciyarsa na karanta masa wasiqar jaki har suka isa gidan yayi parking ya fito ya bude musu qofar suka fito ta kalleshi sheqeqe ta kawar dakai ya cije lebe yana tuno sanda yaganta a rugarsu kamar wata mahaukaciya amma yanzu yayansa ya wayar da ita iskancinta da wulaqancinta takansa ya biyo lallai kuwa sai yayi maganinta daga ita har mijin nata da yake daure mata gindi.Kafin ya gama wannan tunanin sun bude qofar parlourn ya juyo yace dashi “ka debo kayan nan ka shigo dasu ka hauro dasu bangaren babe” bai iya cewa komai ba saboda baqin ciki suka shiga parlourn Mubaraka dake zaune tana jiran dawowarsa ta miqe da saurinta zata nufeshi wani mulmulelen abu yazo ya tokare mata qahon zuciya lkcn da tayi arba da Hauwah dake ta zuba mata murmushi tayi saurin daukar Fadwah data nufosu da gudu tana kiran “Dad yoyoyo” ta fara juyawa da ita tana dariya itama yarinyar tanayi suna hajijiya.Tsayawa zatayi jiri ya debesu suka kuwayi baya luuuuuu zasu fadi yayi saurin taresu suka fada jikinsa ta rungumeshi sosai da hannunta daya dayan kuma tana rungume da Fadwah tace “pls help me Babe jiri nakeji kaini dakina” ai kafin ta rufe bakinta ya hadasu ita da yarinyar ya dagasu cak yayi sama dasu sunata dariya ita da Fadwah shima yana tayasu saboda sabon abune a gurinsa ganin yartasa cikin farin ciki haka shi zai iya cewa tunda yake Bai taba ganin Fadwah tana dariya irinta yau ba.Daga Mubaraka har Muneef da yake shigowa sakin baki sukayi suka zubawa sarautar Allah ido shikam kusan akwatin hannunsa subucewa ya kusayi saboda mamakin yayan nasa “wai dama haka Yaya Lameer yasan darajar soyayya?” Ya tambayi kansa tare da kallon Mubaraka data zube a qasa ta dora hannu aka zata rusa ihu, saukowar Lameer dince tasa Muneef saita nutsuwarshi ya kalleshi yace “ka kaimata kayanta sama” Kamar Mai jiran umarni ya nufi saman ya bude qofar ya shiga suna baje a tsakiyar parlourn ta fuzge dankwalin da tayi rolling dashi ta ajiye a gefe suna after momy ita da Fadwah.Ajiye akwatin yayi ya kwantar da kansa jiki molu din qofar parlourn ya zuba mata ido, jin kamar ana kallonta ne yasata dagowa itama Fadwah ta dago aikuwa sai yarinyar ta rushe da kuka tana shigewa jikinta ta miqe da sauri cikin masifa tace “dallah malam ubanme ka tsaya kana kallo anan ka wani kafemu da ido saikace maye harka tsoratamin yarinya aikin banza aikin wofi to wlh yau yata bazata kwana gurin waccen matarba a gurina zata kwana kuma ko ciwon kai naga tayi kaima ka kuka da kanka stupid kawai”🤔_Hmmmm Jiddoh masifa Jiddoh bala’i Muneef dai jininku yasha bambam da Jiddoh_😆Lameer dake shigowa ya tsaya ya zuba musu ido tace “yawwa babe wlh kajawa wannan wawan qanin naka kunne ya fita daga harkata banason gulma da munafurci yazo ya wani kafeni da ido dubi yanda ya tsoratamin yarinya nifa banason shisshigi wlh rashin mutum babu ruwana ni”Figar Fadwah tayi taja uban tsaki tayi shigewarta dakinta ta ajiyeta a saman gado tace “aikin banza mutum sai shegen sa ido” wasansu sukaci gaba dayi.Duban Muneef Lameer yayi yace “meye ya hadoku da itane?” Wani takaici ya hadiye yace “nima ban sani ba wlh”Murmushi yayi yace “kayi hqr kasan yarinya ce” wani nunkin takaici muneef yaji ya taso masa wai wannan yar mitsitsiyar yarinyar data waye a gabansa itace take caccaba masa mgn saboda tasamu daurin gindi gurin mijinta bai Isa yace komai ba hakanan ya juya ya nufi upstairs din.Koda ya sauka bai tsaya ya saurari Mubaraka da ta hade kai da gwiwa taketa sharbar kuka ba yayi ficewarsa daga gdan saboda tafasar da zuciyarsa takeyi, tanaganin ya fito ta sake rushewa da tana dafe inda Lameer ya mareta saboda kawai tace saidai yabar gidan da Hauwah bazata iya ganin wannan iskancin nataba.Ta jima a zaune a gurin komai ya rikice mata daqyar ta tashi ta shiga dakinta ta cire kayanta ta kwanta tanata rera kukanta, kiran wayarta yasata tashi zaune daqyar ta daga tana ganin sunan Muneef ta kara a kunnenta yace “yarinyar nan taci uwar rashin mutunci waini tacewa wawa a gaban yaya amma bai iya cewa komai ba harma tana cemin zatayimin rashin mutunci wai nine maye kuma Yaya yana kallo qarshe ma dariya yayi yacemin nayi hqr yarinyace” Haɗiye kukanta tayi tace “nifa dukana yayi abinda Bai taba yiminba mari har uku saboda na zageta nace Mata qazama kucaka baqauyiya” hawaye ta share tace “wlh bantaba tunanin Lameer yanada zafi haka ba har cemin yayi indai bazan zauna da matarsa ba saidai ni nabar masa gdansa wai baitaba farin ciki da aurena ba kullum baqin ciki nake qunsa masa”

Back to top button