Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 87 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

Waro ido waje tayi tana kallonshi,la66anta har rawa sukeyi wurin furta”bab..babban..yaya,” tsananin tsoro ne ya bayyana akan fuskarta,babban abunda ya tayar mata da hankali shine batasan tun yaushe yake tsaye abakin ƙopar ɗakin ba!in kuwa har ya jima a tsaye to tabbas yaji duk abunda tace,

Yana tsaye a bakin ƙopar,ya goya hannayenshi asaman faffaɗan ƙirjinshi,farar shirt ce ajikinsa mai dogon hannu tare da wandon suits ɗinsa fari,hannun nan nashi na sanye da agogon diamond ɗinsa,Ya ɗaure sumar kansa ta baya,fuskar nan babu annuri ko misƙala zarratin,ya ɗaureta tamau,a hankali ya furta”On My bed!”
Jiki na rawa Sehrish ta sauko ƙasa daga saman gadon,cikin in ena tace”am..umm..dama gyara gadon nake yi,shine na hau sama don in samu in tattaro zanin gadon da bar….’
bata ƙarasa maganar ba,ya dakatar da ita”Shut up!banason jin komai”ya ƙarasa maganar tare da shigewa cikin ɗakin,kama hanyar fita daga ɗakin tayi,muryarshi ce ta kuma katseta da cewa”are u done”?
“A’a bangama ba,”ta bashi amsa,
“Okey,”ya ambaci hakan a yayin da yake zame agogon dake hannunshi,
Komawa ciki tayi,sannan taci gaba da gyaran gadon,tana jin lokacin daya shige cikin toilet,da alama wanka zaiyi,ajiyar zuciya ta sauke aranta tace”Allah yaso ni baiji abunda nace ba,dana shiga uku yau,nasan cewa dole ya sanyani tsallan kwaɗi,”shaf shaf ta kammala gyara tamfatsetsen gadon,ta canza mashi bedsheet,ta kuma canza mashi bargon da zai lullu6a dashi,in ya tashi kwanciya,bayan ta kammala gyara bedroom ɗin,ta dawo falo,nan ma ta shiga gyara mashi falon,Cikin ƙankanin lokaci ta kammala gyaran,ko’ina ya koma tamkar sabo,sae ƙamshi ke tashi,

Fitowa tayi daga part ɗin nashi,ta wuce kitchen don ta shirya mashi dinner ɗinsa,a kitchen ta samu Azmee ita da Saude,sun kammala dinner suna gyara kitchen ɗin,gaishe dasu ta fara yi,fuskokinsu a sake suka amsa mata,
“Aunty azmee a shirya mun dinner ɗin babban yaya,inaso zan kai mashi ne,”
Murmushi Azmee tasaki tare da cewa”Masha Allah,ki ce Anyi welcome back kenan,”
Dariya sehrish tayi har fararen hakoranta suka bayyana,bayan ta tsagaita da yin dariyar tace”ae daddy,Ya amince na cigaba da zuwa part ɗinsa,inayi mashi aiki,”
“Amma naji daɗin jin hakan sosai,yanzu bari na shirya maki dinner ɗin,”
Amsa mata tayi da toh,sannan ta tsaya tana jiranta,
Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta kammala shirya mata a warmers da sauran food stuffs asaman tray,ta miƙa mata,kar6a sehrish tayi tare da kama hanyar fita daga kitchen ɗin tana faɗin”nagode Aunty azmee,”

Babu kowa a main palour ɗin,yawanci duk basu kaiga dawowa cikin gidan ba,wasu kuma suna acikin ɗakunansu,tana cikin tafiya hannunta ɗauke da tray,taji maganar mutun abayanta,
“Ƴar shila,”a ɗan firgice ta juya don taga kowanene,gabanta ne ya faɗi Rassss!cike da mamaki take bin shi da kallo yaushe rabon da ta sanyashi acikin idanunta harta manta,ita duk a tunaninta ma an tura shi aikine,ashe yana nan cikin gidan,
Fuskar nan tashi ɗauke da wannan shu’umin Murmushin nashi,ya ƙarasa tare da cin burki ya tsaya tagabanta,Face to face suka fuskanci juna,
Jikinshi na sanye da rigar ankara har guiwarsa,sae wandon jeans,sumar kan nan nashi yayi mata ɗan iskan gyaran gashin nan daya saba yi,an saisaye gefe da gefe na kan,tsakiyar kuma anbar sumar a tsaye ba ladabi,
“Nayi kewarki sosai,abubuwa da yawa sun faru,bansamu isasshen lokacin da zamuyi magana ba,naso nazo na taya ki Murna na kasancewarki ƴar wurin Uncle ɗinmu Abusufyan,abun ya ƙayartar dani,”
Sakin baki sehrish tayi tana kallonshi,abun ya ɗaure mata kai,Yadda yake tsara kalami kamar ba wannan mashayin giyar ba,wata irin natsuwa wadda bata saba ganinshi da ita ba,har wani kyau ya ƙara,yayi haske abunshi,duk da ramar da ya ɗanyi,
“Naji kinyi shiru baki ce komai ba”
Jin muryarshi yasa ta dawo daga zurfin tunanin da tashiga,muryarta a ɗan ruɗe tace”amma kaine dagaske?ko an yi musayarka ne,”
Wani ƙayataccen murmushi ya saki na gefen fuska,kafin yace”Ni ne mana HAROON ɗin da kika sani,koda yake na canza a yanzu,nayi ma kaina karatun ta natsu,saboda inaso in zama mutumin kirki,kamar kowa,inaso na shiryu,don na samu mace ta gari,a kwanakin baya kin ta6a yi mun nasiha akan cewa kinaso nazama tamkar ƴan uwana,naji daɗin maganar nan da kikayi mun,kuma nayi amfani da hakan gashi yanzu ni kaina inajin daɗin sauyawar da nayi,”

Zuba mashi ido sehrish tayi tana ƙare mashi kallo har yakai ƙarshen maganar tashi,tayi matuƙar mamakin jin abunda haroon ke faɗa mata,kokwanto ta shiga yi anya haroon ba wani plan yake shirya mata ba?
Ganin ta tsaya tana kallonshi yasa shi gane cewar kokwanto takeyi akanshi,Cikin sauri yace”nasan zaiyi wuya ki yadda dani,saboda sanin da kikayi mun ada,amma na canza ayanzu fiye da tunaninki,”
“Amma na daina ganinka acikin gidan nan”?
“Masallaci nake kwana,shiya sanya baki cika ganina ba,yanzu bana jin daɗin zama ko ina,in ba masallaci ba,acan nake rayuwata,in kinga na fita daga cikin masallaci to wani abu mai muhimmanci ne ya fidda ni,kinsan na tara zunubi sosai shiyasa nake kusanta kaina da ubangiji sosae,saboda in samu yafiyarshi….”

Yanayin yadda haroon yayi mata maganar ba ƙaramin tausayi ya bata ba,domin kuwa har hawaye sun taru acikin idanunshi,wata siririyar ƙwalla ce ta gangaro cikin idonshi,da sauri ya sanya hannu ya shareta,
“Yaya haroon,ka daina zubar da kwallarka,tunda dai har ka shiryu ka koma ga Allah,zai kar6i tubanka ne,fata na shine Allah yasa ka daina duk wani abu mara kyau da kake aikatawa,”
Tana kai ƙarshen maganarta,yace”In sha Allah nadaina,bazan ƙara ba,Ni dai yanzu babban burin da nake dashi arayuwata shine in samu mace tagari inyi aure,zan fi samun kwanciyar hankali,”
“Kada ka damu,in sha Allah zaka samu,”
Tana kai karshen maganar ta kama hanya da sauri ta nufi upstairs,
Bin bayanta da kallo haroon yayi har sai da ta 6ace ma ganinshi,fashewa yayi da dariya,a fili yace”Mata kenan!zuciyarku da rauni take,wannan alƙawari ne na ɗaukar ma kaina,Sai na cimma burina ko da ace shikaɗae ne abunda zan aikata kafin in bar duniya,”yana faɗin hakan ya wuce bedroom ɗinshi,

Sehrish kuwa,tun bayan da tabar wurin,zuciyarta ke cike tab da tausayin Haroon,bakomai take tunawa ba fa ce fuskarshi,yadda yayi mata magana yau ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba,sanya ƙafarta tayi acikin falon Sgr,sannan ta shiga da sallama abakinta,ganin bai fito falon ba,yasa ta wuce bedroom ɗin nashi,sanin cewa ya shiga wanka,yasa ta shiga cikin bedroom ɗin kaitsaye batare da yin sallama ba,
Gabanta ne ya fadi rass!!ganinshi tsaye gaban mirror daga shi sai short ajikinshi,hannunshi ruƙe da comb yana taje doguwar sumar kanshi,
Juyawa tayi da sauri zata koma falon,ta cikin mirror ya hangota,gyaran Muryar da yayi ne yasa ta ɗan dakata daga ƙoƙarin da takeyi na fita daga bedroom ɗin nashi,

Also Download Wace ce ita (Who was she) Hausa Novel Complete Document

“Where are u going?”
Muryarta na kerma tace”Falo,dama dinner ne na kawo maka,”
“Okey,idan kin kai abincin falo,kizo inason ganinki”
Da sauri ta amsa mashi da toh,fita daga cikin bedroom ɗin tayi,a saman table ta ajiye mashi tray din kayan abincin,sai da ta bada kusan minti 10 sannan ta koma bedroom ɗin nashi,A lokacin har ya kammala zura sleeping dress ɗinshi,Red colour sun fito da natural beauty dinshi,gefen gadonshi ya zauna,tare da aza ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya,yana karkaɗa ƙafarshi ta hannun dama wadda ya aza asaman ta hagun,yayin da hannunshi ke ruƙe da wayarshi yana daddanawa
Da yatsan hannunshi yayi mata nuni da tazo gabanshi,cike da fargaba ta ƙarasa tare da tsayawa a tsaye tana faman zare ido,
“Haka ya dace ki tsaya gabana?C’mon Kneel down”!
Hankali atashe ta zube saman guiwowinta,jikinta nata faman kerma,
Tun kafin ya kuma cewa wani abu,tayi saurin cewa”Am sorry babban yaya,daddy yace na baka haƙuri game da abunda ya faru jiya,dan Allah kayi haƙuri,”
Banza yayi da ita tamkar baiji abunda tace ba,gaba ɗaya hankalinsa na akan wayar hannunshi,sae da ya mula yasha iska sannan yace”Wanene SA”?
Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu,hannu ta aza akai tana fadin”Innalillahi!nashiga uku,”ƙasa ƙasa tayi maganar tuni ido ya raina fata,
“Idan har kika bari na maimaita tambayar da nayi maki,jikinki ne zai gaya maki”,
Wani irin wahalallan yawu ta haɗiya,muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”Wlh babban yaya ba dakai nake ba,su6ul da baka ne nayi bansan nace ba,kuma Allah bakai nace ma sa ba,Ni kawai nasan dai nace kullum fuska a ɗaure kamar sa,Kuma fa waƙa ce nake rairawa…”
Bata ƙarasa maganar ba,ya katseta da cewa”Just one answer nakeso!ki faɗamun menene ma’anar kalmar SA da kika faɗi,if not u will be in serious trouble,”tashin hankali!
Nan fa sehrish tashiga mazurai,shin tayaya zatayi mashi bayanin cewa shanu take nufi da sa!tabɗijancan,hauka ma takeyi da zata sanar dashi ainihin mai kalmar SA ke nufi,ta fahimci cewa baisan menene SA ɗin ke nufi ba,shiyasa har ya tambayeta don yaji ma’anarta,yadda zaiji daɗin hukunta ta,
Shirun da tayi mashi ne ya 6ata mashi rai,tsawa ya daka mata wadda ta firgitar da ita,a ruɗe tace”SIR na Yalla6ai nake nufi,wani malamin mu ne na makaranta,muke kiranshi da SA,kuna kama dashi sosai,kyakkyawa ne shima,shiyasa nace fuskarka irin tashi,”
Guntun tsoki SGR yaja,kafin yace”Tashi kiban wuri,”da sauri ta miƙe,ta fito daga bedroom ɗin nashi,gaba daya ma tabar masa part ɗin,don ta lura yau kamar asama yake,

Bedroom ɗinsu ta koma hannu tasa tare da tura ƙopar ta shiga ciki,Jahad ta samu a zaune saman gadon nasu hannunta ruƙe da wayarta,ta ƙurama screen ɗin wayar ido da alama wani abu take karantawa wanda yaja hankalinta har bata ji shigowar Sehrish ɗin ba,hosana kuwa tuni bacci yayi awon gaba da ita,tana kwance naɗe cikin bargo,

Kamar daga sama taji an fisge wayar,a ɗan firgice ta juya don taga wanene ganin sehrish yasa ta sauke a jiyar zuciya tare da cewa”Ashe ke ce,wlh har kin bani tsoro,ƙoƙarin hawa gadon sehrish tayi tana cewa”Halan karatun Novel ɗinne?tayi maganar ayayin da ta aza idonta kan screen ɗin wayar,Ganin rubutun ƙur’ani yasata cewa”Oh ashe karatun qur’ani kikeyi hakan yayi kyau sosai,’
“Ina kika je ne?tun ɗazu ina jiranki,kizo muyi fira don bana jin bacci yanzu,”
Shiru sehrish ta ɗan yi da alamun damuwa a fuskarta,hakan yasa jahad ta kuma cewa”faɗamun meya faru ne?na tambayeki kinyi shiru baki bani amsa ba,ko akwai wani abu ne dake damunki”?
Shaking head sehrish ta ɗan yi kafin tace”bakomai jahad,naje part din babban yaya ne,nayi masa gyaran ɗaki dana falo,shiyasa na jima ban dawo ba,’
Jinjina kai jahad tayi tare da cewa”amma duk da haka akwai sauran wani abu da ki ke ƙoƙarin 6oye mun,ko kin manta cewa ni ƴar uwarki ce,rabin ranki,koma nace ranki gaba ɗaya”
Dariya sehrish tayi jin abunda jahad tace,
“Jahad,akwai abunda ke damuna amma na barshi acikin zuciyata ne kawai,saboda baida amfani kona furta shi,kawai ki tayani addu’a ”
Ruƙo hannunta jahad tayi acikin nata,sannan tace”in sha Allah,rishi zan tayaki da addu’a,dama kuma kullum cikin yi maku addu’a nake yi gaba ɗayanku,”ta ƙarasa maganar,jikinta asanyaye saboda tunawa da mahaifiyarsu,a hankali taci gaba da magana”Ko wani hali Oumman mu take ciki a yanzu?nadamu sosai akan rashin mahaifiyarmu a kusa damu,baiwar Allah bazan ta6a mantawa da wasu kalami nata ba,tana yawan cewa ina sonku sosai ƴan ukuna,a duk lokacin dana kalleku,sai inji wani sanyi ya ratsa zuciyata,ku kaɗae ne dangin da nake dasu a duniyar nan,ina addu’a akan Allah ya raya mun ku…….”kasa ƙarasa maganar jahad tayi saboda hawayen da suka shiga gangarowa daga cikin idanunta,ita sehrish nan take taji hawaye sun shiga wanke mata fuskarta,
Sehrish ce ta ɗaura da cewar”babu tabbacin cewa zanyi tsawancin kwana,baƙin cikin wannan mutumin ma kaɗai ya isa ya halakar dani,zanyi kuka sosai,naci buri akan naga girmanku amma zaiyi matuƙar wuya hakan ya faru……….”duk wannan zancen da suke yi gaba daya kaf kalaman da mahaifiyarsu ke yawan faɗi masu ne,tun suna yara,dama kuma yaro akwai shi da ruƙo,in ya ruƙe abu aranshi da wuya ya manta shi har girmanshi,kuka sosai suka shiga yi babu mai lallashin wani,cikin shessheƙar kuka jahad tace”Oumman mu ta ta6a sanar dani cewa mu ba ƴan uku bane,Ƴan shida ne ɗaya ta mutu,biyu kuma Ya sayyadi ya kwashe su ya siyar ma ƙungiyarsu don ya samu kuɗi ……..”hannu tasa tana share hawayenta a yayin da takai ƙarshen maganarta,,

Girgiza kai sehrish ta shiga yi yayin da hawayen idanunta ke cigaba da zuba,
“Jahad,wannan maganar ba gaskiya bace,nacewa mu ba ƴan uku bane!daga baya Oumma ta tabbatar mun da cewa mu ƴan ukune ta haifa,Ya sayyadine yayi mata ƙaryar cewar mu ƴan shida ne ta haifa,ɗaya ta mutu biyu kuma ya kwashe su ya siyar ma ƙungiyarsu,da farko ta yadda da kalamanshi saboda ta sanar dani cewa a lokacin da ta haife mu ba’a hayyacinta take ba saboda matsanancin ciwon nakuda daya taso mata gashi ita kadai ce a gidan,sae dai kawai ta farka a gadon asibiti,taga jarirai guda uku a gefenta,a yayin da shi kuma yake tsaye akanta,batasan meya faru ba,wannan dalilin ne yasa ta yarda da maganarshi daya faɗa mata,Ashe yayi hakanne kawai don ya ƙona mata rai,dama kuma rabi da kwata na kalaman ya sayyadi ƙaryane,zaiyi wuya ya faɗi gaskiya a bakinshi,mugun maƙaryaci ne,hakanan ma yana iya tsara ƙarya,ya mayar da ita tamkar gaskiya,don haka ki cire wannan aranki!”

Also Download Nurul Kalb Hausa Novel Complete Document

Wata nauyayyiyar ajiyar Zuciya jahad ta sauke,muryarta ɗauke da tsantsar farin ciki tace”Har hankalina ya kwanta wlh,bakiji yadda naji ba,ashe ƙaryane ba gaskiya ba,Amma gaskiya mutumin nan baya tsoran Allah,ni fa duk a tunani na dagaske mu ba ƴan uku bane,akwai wasu suna nan a raye,kullum zullumin da nakeyi shine Suna ina?A wane hali suke ciki su ma?kamannin fuskarsu irin namu ne sak ko kuwa?Ashe duk ƙanzan kurege ne,Ya sayyadi dai ya shiga uku,in ya mutu yana aikata waɗannan mugayen halayan nashi,’
Sehrish ta ɗaura da cewa”ae wannan mutumin bazai kai labari ba,irinsu tun a gidan duniya suke fara gir6ar abunda suka shuka,ƙaddara ce kawai tasa Oumman mu ta aureshi,Ashe shima da wani mugun nufin ya aureta,In sha Allah asirinshi sae ya tonu,kuma Ammi tayi mana al’ƙawarin cewa in aka kamoshi sae mun wanke mata mummunar fuskarshi da mari,Ranar kawai nake jira,in da rai da lafiya,nasan rayuwarmu a hannun Allah take,amma zan roƙi Allah akan ya nuna mun wannan lokacin,koda ace shikaɗae ne burina na ƙarshe da zan cika kafin in bar duniya!!”
Jahad tace”Ni dai koda ace bana raye aka kamo ya sayyadi,alhakin marina na akan ki,Ki haɗa da nawa duka ki kifa mashi su a fuskarshi,”
“Allah shikaɗae yasan wanene gawar fari acikinmu jahad,nima idan bana raye,Alhakin Marina na akanki Jahad,ki haɗa da nawa da naki ki kifa mashi su a fuskarsa,”ta ƙarasa maganar tana nuna ma jahad yadda zata kifa ma ya sayyadi mari a fuskarshi,
“Allah ya kiyaye in ta6a fatar fuskarshi da hannuna!wannan ƙazamin mutumin,sai dai in sanya glove a hannuna,”jahad ce tayi maganar,tare da 6ata fuskarta,
Sun jima suna fira atsakaninsu,kafin daga bisani,jahad ta kwanta,Sehrish kuma ta wuce toilet,bayan ta fito tayi alwala tayi sallah,komawa saman gadon tayi tare da ja musu bargo ta lullu6esu hadi da tofa masu addu’oi.

*Aunty Babba*

A 6angarensu Aunty babba kuwa,sam bacci ya ƙaurace ma idanunta,tsabar baƙin ciki ne ƙumshe acikin zuciyarta,tagaza samun natsuwa,tun bayan da Major ya ajiyesu a hotel ɗin,suka shiga ɗakin da aka kama masu,bata samu ta zauna ba,sae faman safa da marwa takeyi acikin ɗakin,Hayaam kuwa tuni bacci yayi awon gaba da ita asaman gadon,

Allah kaɗae yasan mugun abunda take ƙullawa acikin ranta,don kuwa taci alwashin cewa,a gobe goben nan zasu wuce dajin nan na enugu inda wannan ƙasurgumin fasiƙin bokan yake,Wato Baba Ibliss,kuɗi ne matsalarsu,amma ta yanke shawarar cewa zata siyar da sarƙar gold ɗinta da kuma awarwaron sarƙar,hadda Earrings duka zata siyar don su samu tunkarar Bokan,

*Allah yaba mai rabo sa’a*

*Boss Bature*

❤🤍❤

*A washe garin Juma’a,

Cikin bacci Sehrish ta dinga jin sautin waƙa ƙasa kasa”Takusa Aure ƙara faɗa breaker!ta kusa aure ƙara faɗa breaker,”sae faman mutsu mutsu takeyi acikin bargo,ga baccin bai isheta ba,gashi kuma an takura mata,Ranta yayi mugun 6aci,shiru kawai tayi acikin bargon tayi lamo tana tunanin wani shaiɗani ne tunda sanyin safe yake raira masu waƙa acikin ɗaki,ta kasa gane muryar wacece kamar hosana kamar kuma Muryar jahad,a ƙarshe ta tsayar da tunaninta akan cewa Hosana ce,saboda itace gwanar iya raira waƙa,da wuya kaji waƙa a bakin jahad sae dai karatun ƙur’ani,bata ƙarasa zancen zucin nata ba,taji an ƙara Volume hada ma kiɗa gangan gangan acikin kunnanta”Takusa aure ƙara faɗa breaker!takusa aure ƙara faɗa breaker,”
a fusace sehrish ta yaye bargon da ta lullu6a dashi,karaf idanunta suka sauka akan hosana,dake zaune saman front chair ɗin dressing mirror ɗinsu,ta dage da iya ƙarfinta na ƙarshe,sae faman kiɗa takeyi da hannayenta,
“OMG!!!” pillow ta raruma ta daddage ta jefa ma Hosana,cikin sa’a ya samu tsakiyar kanta,amma ko ajikinta da alama bata ji pillown ba,lalubo wani pillow ɗin sehrish tayi da ƙarfi ta wurga mata shi,Ya daki kanta,a firgice hosana ta juya don taga menene,pillows ta gani guda biyu a ƙasa,a hankali ta ɗago da idanunta kan wanda ya jefo mata da filon,

Download>>> Miji Nagari Burin Ya Mace Complete Document

Daƙuwa Sehrish tayi mata da hannunta”Ungo nan don ubanki!Dama sai da raina ya bani cewa kece,Saboda baki da hankali,Mahaukaciya ce ke,Tunda sanyin safiya kin addabi mutane kin takurawa rayuwarsu,saboda tsabar rashin hankali waqa kike rairawa hada kiɗa,maimakon ki kama azkhar ɗin safe kinayi abakinki,…..”.
Muryar jahad ce ta katse mata hanzarinta da cewa”Wai dama hosana ce ke raira mana waƙa da kiɗa!Nifa nayi tunanin cewa ko ringing ɗin wayarki ne,Amma dae hosana baki da hankali bakisan ciwon kanki ba!shiyasa har yanzu haukan naki ƙara gaba yakeyi,babu abunda zai hana in yiwa Daddy magana akai ki asibitin mahaukata,don abincika notikan kwakwalwarki da suka kwance a ɗauɗaure maki su,”tana magana tana kwatanta yadda za’a ɗaure mata notikan kan nata da hannunta,
Tashin ta kenan itama daga bacci,Kiɗan hosana ne ya farkar da ita,
Tunda suka fara maganar hosana ta zuba masu ido tana kallonsu tsabar bakin ciki ya hanata tanka masu,zuciyarta sae faman tafarfasa takeyi,arayuwarta ta tsani ace mata zararra ko mahaukaciya,fuskarta tacika fam ta kumbura kamar alkubus,a ƙule tace”Ni ce Zararra ko?kuma mahaukaciya”?
Har suna haɗa baki wurin cewa”Eh ance zararra kuma mahaukaciya kiyi abunda zakiyi,”hakan da sukayi ba ƙaramin tunzurata sukayi ba,miƙewa tayi daga saman kujerar,ta shiga nannaɗe hannun rigarta,hakan ya tabbatar masu da cewar dambe zasuyi,
Tana kammala naɗe hannun rigar,ta danƙara da gudu,ta daka uban tsalle ta haye saman gadon,kafin suyi wani yunƙuri,gaba ɗaya ta haɗe kawunansu ta bugasu jikin na juna,ƙara suka saki saboda zafin da sukaji,Ransu yayi mugun 6aci,Aikuwa gaba ɗaya suka tarar ma hosana suka shiga bugunta,ita ma kuma ta shiga kai masu naushi bana wasa ba,dama tafisu ƙarfi,don bala’e suna kuka suna faɗa su duka ukun,gashi babu mai rabasu,
hafsat ce ta nufo bedroom ɗin nasu tun kafin ta ƙaraso ƙopar ɗakin,taji sautin kukansu da kuma sautin buge bugen da sukeyi,
Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,bugun ƙopar tashiga yi amma arufe take,sun datse ƙopar tun jiya da daddare da zasu kwanta

Next page na nan tafe,amma fa in mutun najin bacci ya kwanta,don zai iya kai 10,😟
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋Boss Bature💋*

 

Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1

 

قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*

 

 

 

Hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,bugun ƙopar tashiga yi amma arufe take,sun datse ƙopar tun jiya da daddare da zasu kwanta,tana cikin bugun ƙopar ɗakin nasu sai ga Azmee ta shigo corridor ɗin ɗakin nasu,da alama daga kitchen take,ganin hafsat a ƙopar ɗakinsu sehrish tana ta faman yi masu magiya akan su buɗe mata ƙopar,yasa azmee yin hanzarin ƙarasawa kusa da ita tana tambayar ko lafiya,tun kafin ma hafsat ta bata amsa ta jiyo sautin kukansu Jahad acikin ɗakin,kuka fa bana wasa ba,hankali atashe azmee tace”Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un!Meke faruwa ne!meyasa su ke kuka”?
Fuskar hafsat ɗauke da damuwa tace”Wlh bansani ba,zuwana kenan najiyo sautin kukansu hada ma buge buge da alama faɗa suke atsakaninsu,Ni tsorona ma kada su lahanta junansu,’
A ruɗe Azmee ta shiga bugun ƙopar tana kwala masu

Download>>> Anya Baiwa Complete Document

kira”Jahad!Sehrish!hosana!wai bazaku daina ba!Me kukeyi haka!kuzo ku buɗe ƙopar nan tun kafin ranku ya 6aci,” duk wannan kwakwazon da azmee keyi a banza domin kuwa babu mai sauraronta,hasalima basu son tana yi ba saboda basu a hayyacinsu,
“Hafsat!kije ki sanar da Daddynsu ko wani daga cikin yayyensu game da abunda ke faruwa,su taimaka suzo ko ƙopar ce a 6alle,tun kafin yaran nan su halaka kansu,”acewar Azmee wadda hankalinta ya gama tashi,
Da gudun gaske hafsat ta fita daga corridor ɗin ɗakin,A main palour ta samu Mommynsu junaid tare da Abbansu da kuma Hajiya Azeema suna tattaunawa,wurinsu ta tunkara tana faman yarfa hannu idonta cike tab da kwalla,
Tun kafin tayi magana suna ganinta suka miƙe tsaye suna tambayar ko lafiya,
Muryarta na kerma tace”Su jahad ne,suke faɗa acikin ɗakinsu,gashi can suna ƙoƙarin halaka kansu,munyi munyi su buɗe ƙopar sunƙi buɗewa sae dai sautin kukansu kawai da muke ji,”
Tun kafin ma ta karasa maganar,Jiki na rawa suka nufi ɗakin nasu,hajiya azeema hada tuntu6e saboda tsabar sauri,a ƙopar dakin nasu suka tsaya,bubbuga ƙopar ɗakin Abbansu ya shiga yi a tsawace yake ambaton sunayensu,amma shiru babu wadda ta amsa masa,sae dai sautin kukan nan da suke ji na tashin hankali,
“Ina ganin bari na kira mahaifinsu wata’ƙil idan yayi masu magana sun ji maganar shi,’Abba ne yayi maganar tare da zura hannu cikin aljihun wandonshi ya ɗauko wayarshi,yatsun hannunshi har kerma sukeyi wurin lalubo number Abusufyan,ya danna mashi kira ta soma ringing,
Hajiya Azeema da Alexandra duk sun bi sun ruɗe,
“Ni babban tashin hankalina ma kada yaran nan su illata kansu,Wlh abun ya tsoratar dani sosai ya tayar mun da hankalina,”Hajiya azeema ce tayi maganar,fuskarta tamkar zata fashe da kuka,
Hafsat kuwa tana acikin main palour ɗin,Sae faman kuka takeyi,kwatsamm taji takun takalmi,da sauri takai idanunta wurin MARSHAL OMAR ne ke saukowa daga upstairs da gudun gaske ta tunkare shi tana fadin”Ya Omar,gasu jahad can suna faɗa acikin ɗakinsu,kuma sun kulle ƙopa,anyi anyi su buɗe sun ƙi su buɗe…..”
Jin wannan maganar yasa hankalin Omar mugun tashi,da sauri ya nufi bedroom ɗin nasu,lokaci guda kowa na gidan labarin abunda ke faruwa yaje musu,hatta su Junaid dake ɗakunansu suna bacci sae da suka tashi,su fawan twins,dasu Irfan,hada Dr hariis da gwaggon katsina,da Ammi,dukkansu kowa fa amma banda Sgr dake a bedroom ɗinshi,
A ƙopar ɗakin nasu sukayi cirko cirko,Abusufyan yafi kowa shiga damuwa bawan Allah,kamar ya zauce haka yake bugun ƙopar ɗakin nasu yana roƙonsu akan su daina kokoyin da sukeyi suzo su buɗe mashi ƙopa amma shiru babu wanda ya tanka mashi,Haka Marshal Omar ma,Tamkar zai 6alle ƙopar haka ya dinga bugun ƙopar ɗakin nasu,amma duk abanza,Junaid kuwa tuni ya fashe da kuka,yadda kasan wani ƙaramin yaro,
Cikin shessheƙar kuka Gwaggon katsina tace”nashiga uku..Wayyo Allah na,wlh nasan duk sharrin Ya sayyadine bazai barsu hakanan ba,yanzu haka shine ya shiga tsakaninsu,Ya Allah kayi mana maganin wannan baƙin shaiɗanin….’kuka takeyi hada majina,
Lokaci guda sukaji shiru tsit cikin bedroom ɗin nasu babu wani gunjin kuka,hakan ya tabbatar masu da cewar wani mummunan abunne ya faru dasu,nan fa kowa ya shiga kallon kallo,yayin da zuciyoyinsu keta bugawa da karfi,
Jiki asanyaye Abusufyan ya zame ƙasa,tare da aza hannayenshi saman kanshi,yayin da bakinsa ke furta kalmar”Innalillahi wa’Inna ilaihirraji’un,’
“Abba,ina ganin kawai a 6alle ƙopar,” acewar kanal yousouf,
Omar yace”Nima abunda nake tunani kenan,amma ƙopar fa ta cije sosai,na buga na buga amman ko motsi batayi,duk irin ƙarfin da nake dashi,”
Cikin shesshekar kuka junaid yace”Bari naje na ɗauko zarto sai a datse kubar,”
Ya ambaci hakan tare da watsawa da gudu ya nufi weapons Room ɗinsu (ɗakin ajiye makamansu,”A rufe ya samu ɗakin,sam ya manta cewar key ɗin yana a wurin babban yayansu,sae da yayi arba da ƙopar a rufe sannan yasha kwana ya dawo da gudu ya haye upstairs ɗin,
Faɗawa part ɗin SGR yayi,a rikice ya shiga bedroom ɗinshi,a lokacin Sgr na kwance saman shimfiɗeɗen gadonshi yana bacci,
Junaid baibi takanshi ba saboda a ruɗe yake,side drawer ɗinsa ya tunkara,ya shiga bubbuɗeta yana neman key ɗin,duk inda ya duba babu key ɗin,saman gadon ya hau,yana kiran sunanshi”Babban yaya!Babban yaya!pls wake up!babban yaya ka tashi dan Allah,’
Cikin bacci rafayet yaji muryar junaid dake ta faman kiran sunanshi,a hankali ya buɗe idanunshi kai tsaye suka sauka kan fuskar junaid,ganin hawaye jaga jaga a fuskar junaid yasa Sgr yin hanzarin miƙewa daga zaune,hankalinshi aɗan tashe yake kallon junaid,da wata irin kasalalliyar murya ya ambaci sunanshi”Junaid!what are u crying for?meya faru ne?.
“Babban yaya,key nake nema na weapon’s room,inaso in ɗauko saw ne,za’a 6alle ƙopar ɗakinsu Sehrish”
Cike da mamaki Sgr yace”For what reason?wani abu ya samu door ɗin da za’a 6alleta”?
Ganin bai fahimci inda zancen nashi ya dosa ba,yasa shi yi mashi bayanin abunda ke faruwa,
Saukowa Sgr yayi daga saman gadon nashi,junaid na biye da bayanshi suka fito daga part ɗin nasa,da sauri da sauri suke saukowa down stairs,
Lokacin da suka shigo Corridor(doguwar hanyar) da ɗakunnansu sehrish suke a jere,Hankalin Sgr ya ɗan tashi musamman daya ga dandazon matasan gidan,ga kuma su Abbansu kowa atsaye cirko cirko,fuskokinsu sun nuna alamun damuwa atattare dasu,’
Abbansu na ganinshi yayi saurin ruƙe hannunshi yana fadin”Yawwa rafayet,nasan zaku iya kai da Omar,dan Allah ku haɗu ku 6alle ƙopar nan,ko mun samu muga meke faruwa aciki,’
A hanzarce kowa ya dare ya basu wuri,da iya ƙarfinsu Na ƙarshe suka daddage suka kaima ƙopar wani irin kwakkwaran bugu ji kake daraamm!nan take Sakatar ciki ta zame da kanta,ƙopar ta buɗe,gaba daya suka afka ciki,
Ba ƙaramin girgiza sukayi ba,gaba dayansu musamman Abusufyan,abunda suka gani yayi matuƙar tayar masu da hankali,Innalillahi’wa’inna ilaihirraji’un!!!wannan shine abunda suke ambato a bakunansu,
Sun tarwatsa komai na bedroom ɗin nasu,ɗigon jini jinin da suka gani shi yafi komai tayar masu da hankali,
Jahad ce kwance ƙasan gadon saman tiles,damtsen hannunta duk sawun cizo ne,wurin duk ya farfashe,hatta saman kumatunta cizon ne,daga can saman gadon kuwa hosana ce,baje hannunta dafe da kanta ta toshe kunnuwanta sae faman mutsu mutsu takeyi da ƙafafuwanta,alamar idonta biyu,Sehrish kuwa basu san ina ta lula ba,
Zubewa Abusufyan yayi agaban Jahad dake kwance,hannu yasa yana jijjigata yana ambaton sunanta saboda ya gane itace,hawaye sae faman sintiri sukeyi akan fuskarshi,

Download>>> Sexxy Boss Lady Romantic And Comedian Novel Complete Document

Jikin kowa yayi sanyi,zukunnawa Abbansu yayi agaban Abusufyan din yana kallon jahad dake kwance,Sawun haƙoran dake asaman fatar jahad ya tabbatar mashi da cewar faɗa ne ya 6arke a tsakaninsu har sukayi kokoyin nan,
“Ina tunanin suma tayi ne,wani ya ɗauko mun ruwa dan Allah,”Abbansu ne yayi maganar,da sauri fawan ya fuce daga dakin,ya nufi babban falo don ya ɗauko masu ruwan da za’a yayyafa mata,
….a hankali Sgr yake bin ɗakin nasu da kallo,sunyi mashi kaca kaca,damben daga saman gadon nasu ya fara,Hatta bargon lullu6arsu duk sun jefo shi ƙasa,zagayawa yayi ta dayan gefen gadon,6angaren hannun hagu,tunkan ya ƙarasa ya hango ƙafafun mutun,hakan ya tabbatar mashi da cewar cikon ta ukunsu ce,ta wuntsila ta baya,lokacin daya ƙarasa wurin a kwance ya samu Sehrish,gefen bakinta ya ɗan fashe,ga kuma sawun haƙora asaman ƙirjinta,da kuma damtsen hannunta,zuƙunnawa yayi agabanta yana ƙare mata kallo,
“Rafayet!wacece anan?ko cikon ƴar ukun tasu ce”?Ishaq ne yayi maganar ganin rafayet ɗin zuƙunne a wurin,
“Itace,” ya bashi amsa atakaice,da sauri Abusufyan ya miƙe tare da sauran suka nufo wurin don suga a wani hali take ciki,
Tun kafin su ƙaraso Sgr yayi saurin kai hannunshi gaban rigarta yaja rigar ya lullu6e mata ƙirjinta daya fito sosai,
Fashewa da kuka gwaggon katsina tayi tana fadin”Wayyo Allah ƴa’ƴan Abusufyan ɗina!ni nasan cewa ba yin kanku bane,Wlh sai Allah ya saka maku,Bayin Allah sunji jiki,kowanene yayi masu wannan ɗanyen aikin,jibi yadda aka ciccije masu fata,Yanzu haka ya sayyadine yazo masu da suffar kura yayi masu wannan aika… aikan,’ Harris ne ya katseta da cewa”pls gwaggo kibarmu muji da abunda ke damunmu idan ma kina magana ƙara masu zafin ciwon kikeyi,
Jin haka yasa tayi saurin rufe bakinta,tana cigaba da matsar kwalla a idonta,
“Abun ya ɗaure mun kai!garin yaya haka ya faru?gaba daya kowannansu sawun cizo ne a fatar jikinsu”,Abbansu junaid ne yayi maganar,a yayin da suke tsaye gaban sehrish,Sgr kuma na a zuƙunne,
Hafsat ce ta basu amsa da cewa”lokacin da nazo ƙopar dakinsu,naji sautin Kukansu acikin ɗakin da kuma sautin bugu kamar suna dambe a tsakaninsu,ina tunanin cewa faɗa sukeyi a tsakaninsu,’
Jinjina kai marshal Omar yayi tare da cewa”Tabbas sunyi sa insa a tsakaninsu ne har abun yakai ga fada,Kuma wannan cizon dake asaman fatar jikinsu,ba kowa bace tayi masu shi ba fa ce HOSANA!saboda nima ta ta6a cizo na a kwanakin baya,da ranta ya 6aci a asibiti,ta cije ni kuma ba ƙaramin zafi naji ba a lokacin,”
Abba yace”No wonder!in kuka lura babu sawun cizo a fatar jikinta,indai itace kwance asaman gadonsu,ku kalli jikinta dakyau,kuma bata jigata ba,kamar yarda ƴan uwan nata suka jigata,”
Suna cikin maganar nan,Fawan ya shigo hannunshi ɗauke da robar ruwan daya dauko masu a fridge,da sauri kanal yousouf ya kar6i bottle water din,ya 6alle murfin,tare da tarbo ruwan a tafin hannunsa na dama,ya watsa shi a fuskar jahad,Nan take taja dogon numfashi tana ambaton sunan Allah abakinta,ajiyar zuciya suka shiga saukewa,da sauri Abusufyan ya dawo wurinta,tare da zukunnawa agabanta,ya ɗago da ita ajikinshi yana ambaton sunanta”Jahad!Jahad!”koda jahad ta buɗe idanunta tayi tozali da fuskar Daddynsu saita fashe da matsanancin kuka tana cewa”daddy kaga abunda hosana tayi mana?kawai daga magana ta hau bugunmu ni da Sehrish,duk tabi ta gartsa mana ciwo a fatar jikinmu….’tana magana hawaye na zuba a idanunta,
Runtse ido Abusufyan yayi tare da buɗesu a hankali,abun ba ƙaramin ta6a mashi zuciya yayi ba,
Hannu Omar yasa tare da kar6ar Robar ruwan dake hannun Kanal yousouf ya taka izuwa inda Sgr ke a zuƙunne ya miƙa mashi ita,Kar6a Sgr yayi tare da kur6ar ruwan abakinshi,ya fesar dashi akan fuskar Sehrish,a firgice ta farka gami da mikewa zaune tana faman zazzare idanunta,one by one tabi su da kallo,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba,ganin Sgr,ga kuma su hajiya azeema tsaye duk akanta,tafin hannuwanta tasa tare da rufe fuskarta,tana kuka,

Download>>> Boddiya Complete Hausa Novel Document

“Wani ya ɗauko min FA box a medical room”Sgr ne ya ambaci hakan,da sauri irfan ya fuce daga ɗakin don zuwa ɗauko akwatin,ruƙo hannun Sehrish Hajiya azeema tayi tare da zaunar da ita gefen gadon,”sannu kinji,yi shiru ki daina kuka,”cikin lallashi takeyi mata maganar,
Hawa saman gadon nasu Hafsat tayi,tare da kai hannunta ta ɗago da hosana ajikinta,sae faman kerma jikinta yakeyi,ciwonta ya motsa,da alama an rabu da shan magani,duk a tunanin su abun yayi sauƙi,ashe da sauranta,tabbas hosana tana buƙatar ganin likitan mahaukata,
A faɗace Omar ya daka masu tsawa gaba dayansu yace”wai duk menene yajawo hakan!ba zaku buɗe baki kuyi ma mutane bayani ba!”
Cikin shessheƙar kuka Sehrish tace”Hosana ce,tunda sanyin safiya tafarka,tana raira mana waƙar takusa aure ƙara faɗa breaker,kuma hada kiɗa take raira waƙar duk ta takura kunnuwanmu,har muka farka daga bacci,Don munyi mata faɗa shine ta naɗe hannun rigarta ta hau mu da bugu da cizo kamar ta samu jakuna….’
Cike da mamaki kowa ke kallon sehrish dake kora masu bayani,Ishaq yace”Wai yanzu duk don saboda wannan ku ka kusa illata junanku?gaskiya akwai gagarumar matsala babba ma kuwa,’
Abbas yace”dama da wuya kaga ƴan biyu ko ƴan uku suna zaman lafiya a tsakaninsu,zakaga suna tsananin son junansu,amma ta wani 6angaren basu jituwa,don akwai labarin dana ta6a ji shigen irin wannan daga kokowa suka kashe kawunansu,”
Jin wannan maganar ta Abbas ya ƙara daga masu hankali,Abba yace”in sha Allah,ba zamu bari hakan ta faru ba!tunda abun har yakai ga faɗa da jima juna ciwo,dole a raba masu wurin kwana,shine kawai mafita,”
“Abunda nake ƙokarin cewa kenan”acewar hajiya azeema,
Ammi dai abun yafi ƙarfinta daga ita har Alexandra da hajiya Saratu suna atsaye sun zuba ma sarautar Allah ido,Lamarin yaran yayi matukar daure masu kai,
Dawowa cikin ɗakin nasu Irfan yayi hannunshi ɗauke da First aid box ɗin,ya ƙaraso tare da miƙa ma Sgr akwatin,hannu yasa ya kar6e shi tare da ajiye shi a ƙasa,
Sannan ya zauna,daga gefen gadon,suna fuskantar juna shi da sehrish,wadda ke ta faman shessheƙar kuka,wani irin kallo daya jefa mata,tuni ta nemi kukan da takeyi ta rasa,
“Close ur eyes,”da sauri ta rufe idanunta kamar yarda ya umarta,tana ji yasa mata audiga a wurin ciwon yana goge mata jinin,a sannu ya shiga yi mata dressing din ciwon da taji,bayan ya kammala da ita,Abusufyan ya ruƙo hannun jahad,ya dawo da ita gefen Sgr ya zaunar da ita,cikin lokaci ƙankani Sgr ya kammala yi mata dressing ɗin itama,
“Ita kuma hosana ya zamuyi da ita?kodai asibiti zamu kai ta?Acewar Abusufyan,
Omar yace”Rafayet zai iya duba mana ita anan gida ma”
“Omar am not a psychiatric doctor,though i’ve experience about their work,zan iya duba ta,Amma a ƙa’ida,psychiatric doctor ya kamata yayi checking ɗinta,bazan shiga aikin da banawa ba,”kaji turawa,ƴan bin ƙa’ida,
Jinjina kai Omar yayi fuskarshi ɗauke da murmushi,ya juya tare da kallon Dr harris dake tsaye ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi yace”Bismillah,”yayi maganar yayin da yake yi mashi nuni da hosana wadda ke kwance ajikin hafsat,idanunta sun birkice sae farar kwayar idon kawai,yatsunta kuwa sae faman kerma sukeyi,hada na kafafunta,
Kallonta kawai Dr harris yayi batare daya ta6a jikinta ba,ya faɗi sunan allurar da take buƙata ayi mata,
Da sauri Omar ya ciro wayarshi tare daddana wasu numbobi,ya kira Dr Emran na asibitin Sgr,kiran na shiga emran ya ɗauka,don haka Omar ya miƙa ma Dr harris wayar don suyi magana,
Bayan sun kammala wayar,ya dago tare da kallon Marshal yace”Ya sanar dani cewa within 15 mins zaizo tare da allurar da kuma medicine ɗinta,”
Omar yace”Okey,Allah ya kawo shi lafiya,

“Ku kwanta saman gadon,itama mara lafiyar a kwantar da ita before doctor din yazo,Azmee ki shirya masu breakfast dinsu,yanzu haka ma Yunwa ce ke Cinsu,shiyasa su kayi wannan damban,” sae yanzu ammi ta tanka masu,saboda tsabar gatanci maimakon asamu wanda xaiyi masu faɗa da tsumagiya a Zane su, amma kowa ya rufe ido,sae lalla6a su akeyi,diyanso kenan,shalelen abusufyan,

miƙewa sgr yayi daga zaunen da yake,sannan yayi masu nuni da su kwanta,a hankali kowaccensu ta kwanta yadda kasan waɗanda suka yi wata suna Jinya don sunji jiki,a hankali Hafsat ta janye Hosana daga  jikinta ta kwantar da ita,har lokacin bata dawo hayyacinta ba,sae faman fari takeyi da idanuwanta,yatsun hannunta dana ƙafafunta sae kerma suke yi,

Haɗa baki su fawan su kayi wurin yi masu ya jiki,kafin daga bisani matasan  suka fita daga ɗakin nasu tare da Ammi da hajiya saratu,Ya rage daga Sgr sae Marshal Omar,Hajiya azeema da kuma abusufyan da kuma gwaggwon katsina sae hafsat,Azmee ta wuce kitchen don ta shirya masu breakfast ɗinsu,within 15 mins,Dr Emran ya ƙaraso gidan,a cikin motarshi yazo,tun a waje ya haďu da dr Harris tare da kanal Yusuf a tsaye,dama shi suke jira,fitowa yayi daga cikin Motar hannunshi dauke da Ledar maganin Hosana da kuma injection din da xa’ayi mata,gaisawa suka fara yi  fuskar kowannansu dauke da murmushi,canal Yusuf ne ya kar6i Ledar da Emran din yaxo da ita,sun so ya shigo daga ciki suyi breakfast atare dashi,Amma ya sanar dasu uzurinshi,hakan yasa suka ƙyale shi,sallama sukayi da juna sannan suka koma ciki da sauri,

Cikin bedroom din nasu,Dr Harris ya shigo ganinshi yasa Omar da Sgr suka bashi wuri donya ƙarasa gaban gadon,batare da 6ata lokaci ba,ya ɗura ruwan allurar acikin syringe,aikuwa kamar akan idon Hosana yana kai hannu zai ruƙota ta zabura,tashiga yan buge²,ganin haka yasa sgr da Omar matsawa kusa dashi,sae da suka rurruketa dakyar aka samu yayi mata allurar,yana  kammala yi mata allurar,nan take zufa ta Shiga tsastsafowa daga jikinta,Kafin wani lokaci tuni bacci yayi awon gaba da ita,hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yayi ba,
Juyawa dr Harris yayi tare da kallonsu Omar yace”in sha Allah,Zata ji sauƙin jikin nata,sannan idan ta farka,ga medicines ɗinta nan,bayan taci abinci,akwai direction ajikin kowani magani sae a duba,idan za’a bata,”
Amsa mashi sukayi da toh,Omar yace”aikin ka na kyau dr,”sannan ya mayar da idanunshi kan hajiya azeema tunkafin yayi mata magana tace”Zan kula dasu,idan tafarka zan bata maganin da yardar Allah,”murmushi ya saki tare da juyawa ya kalli sgr,”Muje ko?time karya ƙure mana,naga yanzu har 12 ta kusa,nan da wani lokaci xa’a shafa fati…..’bai ƙarasa maganar ba ganin irin kallon da rafayet ya jefa mashi,Dariya Omar yayi yana faɗin”Sorry bro,kada ranka ya 6aci mana,Yau fa ranar farin ciki ce agaremu,murmushi yakamata a gani akan fuskokinmu,ɗanyi murmushi mana,cike da zolaya Omar keyi mashi magana,shi kuwa Namijin sae faman tamke fuska yake yi,daga bisani suka fita daga ɗakin atare da dr harris,

Download>>> Yar Harka Romantic Hausa Novel

Komawa hajiya azeema tayi tare da samun wuri gefen gadon ta zauna tana kallonsu,duk sun rufe idanunsu kamar masu yin bacci,
“Bismillah gwaggo ku zauna mana,”azeema ce tayi maganar tare da yi mata nuni da saman bedside drawer dinsu,jiki asanyaye gwaggon katsina ta karasa ta zauna saman drawer din,ita dae har  yanzu bata yarda Cewar Hosana ce ta ciccijesu ba,
“Azeeme yanzu kema kin yarda cewa yarinyar nan itace da kanta ta gartsa ma ƴan uwanta cizo har haka?Ni nafi tunanin cewa Ya Sayyadine yazo da suffar kura yayi masu wannan aika aikar,mutumin nan fa ba ƙaramin Taƙadari  bane,banbancinshi da shaiďan kaho ne kawai da babu,”wannan maganar da gwaggon katsina tayi ba karamin dariya tabasu ba,
Girgiza kai hajiya azeema tayi fuskarta ɗauke da dariya tace”gwaggon shagali,ae in ma shine to ta Allah ba tashi ba,ki kwantar da hankalinki,Sayyadi yake kowa,ba abunda ya isa yayi masu bi’iznillahi,”
Washe Baki gwaggo tayi da alama taji dadin abunda Azeema tace mata,
“Allah yayi mana maganin la’ananne,”
Azeema ta amsa mata da ameen,
Sae wuraren karfe sha biyu da rabi Hosana ta farka jikinta da sauki sosai,kuma tana bude ido ta fashe da kuka tana ambaton  sunansu sehrish da jahad,sae da aka nuna mata su sannan hankalinta ya kwanta,

Tuni azmee ta kawo masu breakfast ɗinsu acikin dakin,da taimakon Hafsat da kuma hajiya azeema suka ci abincin,bayan sun kammala cin abincin,Hajiya azeema da gwaggo suka bar dakin,ya rage saura hafsat ita kaɗai,gyara masu bedroom din nasu ta Shiga yi,komai yadawo normal Ba kamar daba da suka hargitsa dakin,bayan ta kammala gyaran ɗakin,wuri tasamu saman side drawer dinsu ta zauna tana kallonsu,
“Hosana ki ji tsoran Allah,jibi yadda kika raunata mu sae kace ba yan uwanki ba,”jahad ce tayi maganar ranta a6ace,
A kule hosana tace”ae laifin ku ne,saboda me zakuyi mun rashin kunya?ni ba yayarku bace?oumma tace ni ce babba acikin ku,saboda majnun ya faɗa mata cewa ni ce na fara zuwa duniya,sae da na shaƙi iskar duniya da minti biyar sannan ke kika zo daga ke kuma sae waccen uwar tsiwar” “dakyar take magana,saboda har yanxu jikin nata da sauranshi,
Guntun tsoki sehrish taja”karki kara ce mun uwar tsiwa,in ba haka ba zan nuna maki kalar nawa haukan,mara mutunci kawai,kuranya mai cin naman ýan uwanta…”
Tunkan ta ƙarasa maganar,da Sauri jahad ta toshe mata bakinta,”Dan Allah ya isa haka,da alama baki ji jiki ba,shiyasa kike ƙoƙarin tsokanota,salon Kija mana jinyar  ta koma a gadon asibiti,”

KARANTA>>> Mafarkin Ruwan Sama 

Hafsat dake zaune tana sauraronsu,sae faman kunshe Dariya takeyi,

*Boss Bature*

❤🤍❤

Gaba ďaya matasan gidan,kowa ya Shiga yin wankan juma’a,Kafin wani lokaci duk sun shirya halarta Sallar Juma’a tsaf,kowa ya ɗauki wanka na mutunci wankan shadda,abun sai wanda ya gani,bakowa ne yasan da zancen ɗaurin auren babban yayan nasu ba ko acikin matasan  gidan,manyan su ne kawai suka son da ɗaurin auren,sauran kuwa koda zasu san da auren sai dai suji  a masallaci a yayin da ake sanarwa.

Zuba mashi ido Alexandra tayi ganin yadda  yake ta rawar jiki,yaci uban ado cikin farar shadda,ya zura malunmalun,ya sanya sabuwar hula akanshi,ga agogo sabuwa ya Sanya a hannunshi,ga haɗaɗɗun takalma masu tsadar gaske ya zura a kafafunshi,sae faman sakin Fara’a ya keyi kamar wani sabon ango,yana tsaye agaban mirror hannunshi dauke da kwalbar Turare sae bin jikinshi yakeyi ko ina yana feshe shi saƙo da lungu na jikinshi tamkar  zai ƙarar da turaren dukansa,
Abun ya ɗaure mata kai cike da mamaki tace”Darling,irin wannan daukar wanka haka?kaji tsoran Allah kodai kishiya Zaka ƙaromin ne”? dariya abbansu yayi tare da ďan juyawa ya kalli wurin da take zaune gafen gadonsu,ta kura  mashi ido ko kyaftawa batayi,
“Ni da nake da Alexandra,Me zanyi da wata ya’ mace?Ni na isa ma nayi maki kishiya?kefa ta dabance ko acikin mata,shiyasa lokacin da kika tafi kika barni nagaza samun natsuwa,kuma naqi kula kowa,saboda son da nake yi maki,”
ƴar hararar wasa ta jefa mashi tare da cewa”daɗin baki zakayi mun ko?
“No,ba haka bane,am serious fa,taya zanyi aure baki sani ba?kamar dai wani munafuki,wannan fa wankar sallar juma’a ne,ko kin manta cewa Yau juma’a ne”?
Shiru ta ɗanyi tana kallonshi,kafin ta ɗan ta6e bakinta tare da cewa”Okey,natuna,nidae duk da haka ban yarda dakai ba Allah,ji nake kamar na bika masallacin nan,”
Dariya sosai abba yayi,bayan ya tsagaita da yin dariyar yace”Ashe kina kishi ne?shine kuma kika tafi kika barni,ba kiyi tunanin cewa zan iya ƙara aure ba,a bayan idonki ba”?
“Ae nasan cewa ba zaka iya ƙara aure ba,that’s why ban damu akan haka ba,nasan wanene mijina,kuma na yarda da irin son da yake yi mun,bazai haɗa ni da wata ba,” acikin zuciyarta kuwa cewa takeyi”Mutun ma ya kuskura yayi mun kishi,da kuwa na tashi gidan nan da bomb,kowa ya rasa,”
Suna cikin magana,sae ga junaid ya faɗo cikin ɗakin,jikinshi na sanye da farar shadda,sae ƙamshi ke tashi ajikinshi,hannunshi na ruke da hularshi,mommynsu na ganinshi ta miƙe jiki na rawa,ta rungumoshi tana shafa sumar kanshi,
“My baby boy,U look so beautiful,Har ma kaso kafi daddynku kyau,”ta ƙarasa maganar a yayin da take raba jikinta daga nashi,
Ashagwa6e yace”Mommy,yanzu kina nufin Abba ya fi ni kyau?kallar ni fa dakyau ki gani tun daga ƙasa har sama,son kowa ƙin wanda ya rasa,”
Dariya sukayi gaba ɗayansu,Abbansu yace”To fa!junaid kishi kake dani”?
Turo baki yayi yana faman ƙunƙuni,irin na shagwa6a66un nan,
Alexandra tace”wasa nake nima,kafi shi kyau nesa ba kusa ba,”
Ƙayataccen murmushi ya saki jin abunda tace,
Mayar da hankalinshi yayi kan abban nasu tare da cewa”Abba mu tafi,kada lokaci ya ƙure mana,”
“Toh,Uban sauri,mu tafi,” yayi maganar tare da ruƙo hannunshi,
“Madam mu zamu wuce”
Murmushi tasaki tare da ɗaga masu hannu tace”Adawo lafiya,in anje anyi mana addu’a,”
Junaid yace”kada ki damu mommy zanyi maki addu’a akan Allah yasa daddy ya ƙara maki kishiya,”
ɗan zaro ido waje tayi tana kallonshi,da sauri yaja hannun abbansu suka fuce suna dariya,

A main palour Matasan gidan suka hallara ga6a dayansu,sae ƙamshi ke tashi,kowannansu fuskarshi na ɗauke da murmushi,musamman abusufyan,shigowa abba yayi cikin falon hannunshi cikin na junaid,tunkan ya ƙaraso ya lura cewa babu Rafayet acikinsu,
Kowa sai tambayar ina babban yaya yake,saboda sun saba tafiya masallacin juma’a atare,gaba ɗayansu suke hallara a babban falon nasu duk juma’a before su wuce masallaci,shiru babu rafayet,sae Faman duba agogon hannuwansu sukeyi suna kallon lokaci,har sai da Marshal Omar yace”bari naje bedroom ɗinshi yanzu haka bai kammala shiryawa bane,”da sauri ya tunkari upstairs ɗin yana ƙoƙarin hawa saman benen,Suka jiyo sautin takalmansa,
Gaba ɗayansu suka ɗaga idanunsu sama suna kallonshi,Cike da tsananin mamaki,tunda suke arayuwarsu basu ta6a ganin sgr ya sanya shadda ajikinshi ba,this is the first time daya fara sanya shadda ajikinshi,tabarakallahu ahsanul khaliƙin,Getzner ce sky blue mai ɗaukar ido,wadda sehrish ta ta6a ɗauko mashi a kwanakin baya,donya sanya amma yaƙi sanyawa,To yau dai itace ya sanya ajikinshi,Babu hula akanshi amma ba ƙaramin kyau sumar kanshi tayi ba,yayi mata gyara na musamman,hannunshi kuwa na sanye da Wannan diamond watch ɗin tashi,yayin da ƙafarshi ke sanye da penny loafers,tunkan ya ƙaraso down stairs din ƙamshin turarenshi ya gauraye ko’ina,yadda kasan tauraro acikin taurari haka ya bayyana,tafiya yakeyi gently tamkar baisan taka ƙasa,fuskar nan tashi aɗaure babu fara’a ko miskala zarratin,sae kace ba yau zai angwance ba,

A hankali yake tattaka stairs ɗin, yayin da yake manna links ɗin hannun rigarshi,koda ya ƙaraso cikin falon,batare daya kalli kowannansu ba,ya nufi hanyar fita daga main falo ɗin,Murmushi abbansu ya saki aranshi yace”Rafayet kenan”
batare da 6ata lokaci ba,Suka fito waje gaba dayansu,dama already motocinsu na nan a jere,Nan kowa ya buɗe motarshi ya shiga,A jere motocin suka fuce daga cikin gidan ɗauke da jiniya,

*💃💃💃ALHAMDULILLAH, A YAU JUMA’A DUBBAN JAMA’A SUN SHAIDA ƊAURIN AUREN RAFAYET SALAHUDDEEN HOSSEIN,TARE DA AMARYARSA SEHRISH SALAHUDDEEEN ABUSUFYAN💃💃💃*,

bayan kammala sallar juma’a aka ɗaura auren nasu,Sae dai muce Allah ya basu zaman Lafiya atsakaninsu❤

*Finally Rafayet weds sehrish*🥳🥳🥳😘

Back to top button