Hausa novels

Wace Ce Ita (Who Was She) Chapter 74 Complete Novel

WECE CE ITA⁉️(WHO IS SHE⁉️)

                 Unique Barakancy🌹

                    SEVENTY-FOUR📍

A gigice sudais yayi kanshi yana jijjigasa yana ihun kiran sunansa, fadi yake ‘saif! Saif! What’s happening? Dan Allah ka tashi brooooooo!’….
Duk wannan ihun da yake yi ko motsi deen beyi ba, hankalin sudais ne yayi balakin tashi ya fita da sauri yayi part din mami hankali tashe, yana fitowa daga part din deen ya hango umm na fitowa daga mota a parking space, dama dawowarsu kenan daga unguwa, da gudu ya karasa inda take a gigice yace;
“Umm saif baya numfashi, please come and save his life”….
Ko tsayawa tambayar abinda ke faruwa umm batayi ba tayi part din deen da sauri daidai nan mami ta fito daga motar itama da yake tare suka fita, hankali tashe ta tambayi sudais abinda yake faruwa umm tayi ciki da sauri haka, labari ya bata suna cikin waya da saif kawai yaji shiru, hankalinsa be kwanta ba yace bari yazo ya duba yaga ko lafiya, yana zuwa ya ganshi a sume, sosai hankalin mami ya tashi itama da jin wannan zance, sai ta juya tayi side din deen din da sauri sudais na biye da ita……

Karanta>>> Abban Sojoji Book 2 Complete

A razane umm ta tsaya tana kallon deen da har lokacin yake a sume, shida ko rashin lafiya yake da wuya a gane saboda karfin halinsa, wai shine yanzu a gabanta kamar wani gawa….
“innalillahi wa inna ilaihi raji’un”…..
Shine abinda kawai take maimaitawa yayinda ta dora hannunta akan hancinsa dan taji ko yana numfashi, kasa tantancewa tayi ta mike da sauri ta taro ruwa a toilet ta fara shafa masa a fuska, tana cikin haka mami da sudais suka shigo hankalinsu ya kara tashi ganin sai ruwa take zuba masa amma be farfado ba…
“Sudais tun yaushe ya suma?”….
Umm ta tambaya while tana cigaba da zuba masa ruwan a fuska….
“Yanzu fa muke waya dashi umm, muna cikin magana kawai naji karar faduwar abu shine hankalina ya kasa kwanciya na tawo”….

Download>>> Bintu Diyar Bayi Ce Book 1 Complete Document

Umm ta dade tana shafa masa ruwan kafin taji yanayin fitar numfashinsa ya danyi sama har tana iya ji, wani sassanyar ajiyar zuciya ta saki a kasan makoshinta tace ‘alhamdulillah’ sannan ta sake duban sudais tace;
“ya fada maka bashi da lafiya ne?”….
“A’a be fadamin ba, amma a yanayin maganarsa na fuskanci bayajin dadi”…..
Bata kara cewa komai ba ta mike ta isa ga wardrobe dinsa, janyo drawer wardrobe din tayi ta dauko cuff ta dawo inda yake, har zata daura masa a hannu taga ya bude ido, hamdala tayi tana kara godewa Allah…..
“sudais zo ka taimaka masa ya koma kan gado”…
Da hanzari sudais ya tawo zeyi kamar yanda umm tace deen yayi saurin daga masa hannu sannan ya mike a hankula ya hau gadon ya kwanta….
Bin shi umm tayi ta fara kokarin daura masa cuff din dan ta duba bp dinsa, da sauri ya janye cikin muryar marasa lafiya yace;
“I’m fine umm, you don’t need to check my blood pressure”….
“Just stay still, bansan musu dan Allah”….
Dole ya barta ta daura masa yayinda hankalinsa yayi wani guri daban yana tinanin daya saba…..
“Ya hayyu ya qayyum tinanin me kakeyi saif? Kashe kanka zakayi ne? Ta yaya bazaka suma ba, kaga blood pressure dinka kuwa?, lahaula wala kuwwata illa billah saif hawan jini fa da kananan shekarunka”…
Maganar data dawo dashi daga tinanin daya nitsa kenan, ko kadan beyi mamaki ba saboda yanda jikinsa ke daukan zafi kadai yasan hakan ze iya faru, amma ya kasa controlling kansa, duk yanda yayi kokarin kauda damuwarsa sai yaji kamar kara yawa takeyi……
“Hawan jini fa jam? Saifuddeen din?”…
Cewar mami tana dafe kirji dan Allah ya sani she wasn’t expecting it shiyasa ta zama very surprised….
“Wallahi yaya, I don’t even know what to think of right now, wannan wani kalan masifa ne, da kananun shekarunsa me yake tinani haka, kar kiso kiji what his bp is reading”…..
Sake komawa inda ta dauko bp cuff tayi ta fara bincika abubuwan dake wajan, dakyar taga allurar da take nema ta zuba a syringe sannan ta sake nufar gadon, allura ta fara masa sannan ta sake daura masa cuff din a hannu, girgiza kai tayi a raunace tace;
“saif breath in and out”….
Yi yayi kamar yadda tace ta sake cewa;
“exhale continuously”….
Hakan yayi, after some minutes ta sake kada kai tace;
“your blood pressure keep on rising, stop thinking please, ko kana san wani abu? Anything that will calm your bp down, just name it I’ll get it now”……
Sosai ta bashi tausayi yanda duk ta damu sai yayi murmushi yace;
“kwantar da hankalinki umm, I’ll be fine”…..
“hankalina baze iya kwanciya ba saif, in kuma kanaso hankalina ya kwanta ka fadamin damuwarka dan Allah”….
“Bani da wata damuwa umm, ciwo ne kawai daga Allah”…
Da sallama suka shigo parlourn, hussy na gaba tana biye da ita a bata, sai yaba haduwar parlourn take dukda a hargitse yake, dakin deen hussy ta nufa da ita, suka shiga da sallama, mami ce ta fara ganinsu, ta kalli hussy tana jiran karin bayani dan bata gane wacce take bayanta ba….
“A landline aka ce yaya saif yayi bakuwa wai tana ta kiranshi baya shiga kuma yasan da zuwanta shine na tafi na shigo da ita”…

Karanta>>> Idan Ba Ke Complete Novel Document

Cewar hussy tana nuna suhaima dake gefenta….
Gyada kai mami tayi tace
“okay you can go”…
Sannan ta dubi suhaima datayi idon tausayi tace;
“sannu da zuwa baiwar Allah”….
Duk a tinaninta ko tasan bashi da lafiya ne tazo dubashi……
Kallonta suhaima tayi tana tinanin anya itace mahaifiyarsa kuwa because she look way younger, amma dai taga yana kama da su biyun, tasan kuma dole yan uwansu ne, so babu lefi in sunji abinda tazo dashi…
Memakon ta amsa sannun da mami take mata sai ta fashe da kuka harda shessheka, da mamaki mami tace;
“subhanallah, ya da kuka baiwar Allah?”….
Ta karashe tana binta da kallon tausayawa, duk a tinaninta ramar da taga deen yayi ne yasata kuka…..
Sake rushewa tayi da kuka cikin ban tausayi da nuna yanda abun yake mata ciwo ta nuna saif tana fadin;
“Ka cuceni ka yaudareni, sai da ka gama lalata min rayuwa sannan zaka auri wata bani ba? Irin sakayyar son da nake maka da zaka min kenan? Wa kake so ya aureni bayan na gama watsewa dakai a titi”….
Banbarakwai haka mami da umm sukaji zancen, sam hankalinsu be dau ka ba, saidai yanda take maganar ya nuna yanayin yanda takejin zafin abun matuka, ga kukan da takeyi gwanin ban tausayi , babu yanda za’ayi mutum yace karyane sannan duniyar nan an daina shedan mutum dan ze iya baka kunya, so tari yanda kake tinanin sai kaga ba haka yake ba…..
Tabbas zancen ya dakesa saboda shi sharri bashida dadi ko kankani ne, ko magana akace ka fada kuma baka fada ba da ciwo ballanta kazafi irin wannan na zina dayafi komai muni, amma hankalinsa a kwance yake saboda yasan yana da gaskiya, ko ba yanzu ba kuma yasan gaskiya zata bayyana…..
Sudais ma jin zancen kawai yayi dan yasan wanene deen, yasan abinda ze iya yi dan wanda baze iya ba, saboda haka wannan zance ya jisa kawai yasasa a kwandon shara ne, wani mugun kallo ya watsa mata yace;
“Karya kikeyi! Wannan kirkirarran zance ne! Kuma baze taba aurenki ba!”…
Marairaicewa tayi idonta na zubar da hawaye kamar gaske tace;
“Wallahi ba karya na masa ba, ko last week yace in samesa a hotel, inada message din ma”….
Ta karashe tana zaro wayarta a cikin jaka, mami ta mikawa wayar shi kuma sudais ya karasa kan bedside drawer din deen dayake hango wayar dayake amfani da ita inba personal call ba ba wanda sukayi waya dazu ba, papers yaji ya taka saura kadan ya zame, matsawa yayi ya sunkuya yana kallon papers din mamaki sosai, baby ce gabadaya a jikin papers din ga dukkan alamu kuma deen ne ya zana, da dabara ya turasu karkashin gado sannan ya dauko wayar ya tawo, messages din deen ya shiga dan yaga ko zega message din datace inma dagaske ne ya gogeshi, saidai ko fara scrolling beyi ba umm da bata saka musu baki ba tun dazu tace;
“Mikomin wayar!”….
Mika mata yayi, mami ma ta mika mata na suhaima dake hannunta bayan ta karanta message din, na suhaima umm ta fara dubawa taga tabbas dashi sukayi exchanging messages, dialing number sa a wayar suhaima tayi sai taga baayi saving ba, sai kawai tashiga message takan number a wayar deen, a take taga exact message dayake kan wayar suhaima, wani dadi suhaima taji ganin be goge message din ba, tasan kuma dole su yarda da abinda tace yanzu…..
Sai da umm ta gama duba komai tsap sannan a nitse ta juyo ta kalli suhaima tace;
“Young lady, I’m barrister Jamila S. Shuwa, as a barrister this messages aren’t enough for me to justify your words, zatayiwu kun hadu a hotel dinne for business because hotel ba iya batanci akeyi ba, I personally use to have alot of business meetings in the hotel as an entrepreneur, saboda haka inaso ki bani other valid reasons da zan yarda da’na ya yaudareki kamar yanda kika fada!”….
Wani mugun bugawa kirjin suhaima yayi, bata taba tinanin yanda suka nuna alhini a fuskarsu zasu mata irin wannan tambayar ba, infact bata taba tinanin itace mamansa ba, dabara ce ta fadomata aranta tace in kinsan wata ai bakisan wata ba, cikin kukan makircin data sake kakalowa tace;
“Ina da cikinsa na wata biyu, wallahi ba karya nake ba”…..

Also Download Ɗaudar Gora Page 8 By Billyn Abdul

Murmushi me ma’ana umm tayi dan ko a yanda tayi jimm kafin ta bata amsa batasan ta kama kanta ba, daure fuska tayi tace;
“Young lady I’m also a Doctor, not just an ordinary Doctor but an attending physician, gidannan is full of materials na komai, you’re going to take a pregnancy test, if it’s positive then we proceed in miki scanning muga na wata nawa ne, remember all this will be done in this house ba sai munje ko ina ba, now urine test kikeso ko blood test?”….
Sosai suhaima tasha jinin jikinta tsoro ya bayyana akan fuskarta, ta dade bataga wanda ya rikita mata lissafi irin haka ba, kasa cewa komai tayi tanaji kamar ta fita a guje….
Murmushin mugunta sudais yayi dan kallo daya zaka mata kasan bata da gaskiya, tinda ta fara zubo zance yake tausaya mata dama dan da tasan su waye a gidan bazatayi gigin yin wannan haukar ba, iya umm kenan ma ina ga justice ta tsareta da tambayoyi itama….
“Ke nake sauraro wanne kikeso?”…..
Umm ta sake tambaya tana kara daure fuska….
A sanyaye tace;
“Kowanne”…..
“Sudais jeka cema baby tee ta dauko pregnancy test strip a locket din bedroom dina ta kawo, naga saif bashi dashi anan”….
Juyawa sudais yayi harda dan gudunsa yanayi yana sheka dariya dan yasan kwanan suhaima ya kare yau, koshi baze kyale zancen nan ba….
Yayinda suhaima ta nemi hawaye ta rasa sai neman mafita kuma, mamaki ta farayi ko shima saif din likita ne taji ance bashida test strip anan, itako meya aiketa jamming da wannan professional family din?…..
Hassy sudais ya sama a parlour ya fadamata sakon umm ya kuma ce ta fadawa baby tee tayi sauri dan Allah sannan ya juya ya tafi, sai da yayi making call a hanya kafin ya shiga part din deen….
Ba’a kara minti goma ba sai ga baby tee tashigo da sallama hannunta dauke da test strip din, akan suhaima idonta ya fara sauka tayi kicin kicin da fuska tace;
“Umm itace yaya saif ya bawa numbersa a Hypermarket dinchan”…..
A zabure saif daya lula duniyar tinaninta ya dago jin zazzakar muryarta ta daki kunnensa, ko sallamarta beji ba saboda tinanin daya tafi, shi kwata kwata ma bata case din da suke yake ba ta abinda ke damun rai da ruhinsa yake, amma kuma abinda ya basa mamaki shine baby tee ta bawa umm labarin kenan?……
“It’s not even up to three weeks ko?”….
Umm ta tambayi baby tee….
“Yes”…
Suhaima na jin haka ta saddakar kashinta ya bushe, dama bata tinanin zata iya tsayawa ayi test din, karfin hali ne kawai yasata amsawa, durkusawa tayi har kasa ta fashe da kukan gaske tace;
“Dan Allah dan annabi kuyi hakuri, wallahi karya nake babu abinda ya shiga tsakanina dashi, kawai so nake ya aureni amma ba dan in masa sharri nayi ba”…
Ko direwa sudais be bari tayi ba yace;
“You’re under arrest!”….
Ko seconds biyu ba’a kara ba jiniyar motar sojoji ya cika unguwar, kafin kace me har sun shigo sun sawa suhaima handcuff tana kuka tana komai sudais yace su tafi da ita a tabbatar an gana mata azabar da bazata kara yiwa wani irin haka ba, wani in aka masa irin wannan mugun sharrin har duniya ta nade ba lallai ya iya fidda kansa ba, tare da su umm suka fita kamar yanda sudais ya bukata saboda su tattauna lamarin suka bar baby tee kadai a dakin…
Har suka fita deen be sani ba saboda yanda hankalinshi yayi kan baby tee, sudais kadai ne ya lura da irin kallon daya ke mata shiyasa yayiwa su umm wayo suka fita tare, su kuma basu kawo komai a ransu ba….
Sai da yaji shiru sannan ya gane basa nan, kamar ze hadiyeta saboda kallo yace;
“Come over here baby girl”….
A hankali ta karasa bakin gadon ta tsaya akansa, sai a lokacin ta samu ganinsa da kyau dama tun dazu ya tsaya mata arai, gani tayi ya chanza mata gabadaya kamar bashi ba, he’s just looking very rough ga wani uban rama dayayi, kasa shiru tayi kamar zatayi kuka tace;
“Yaya baka da lafiya ne?”..,,,,
Memakon ya bata amsar tambayarta sai ya janyota ta fado kansa, chusata yayi a cikin kirjinsa ya kankameta, kokarin tashi tayi saboda yanda zafin jikinsa ke gasata amma yaki bata dama sai ma kara turata cikin jikinsa yake yana dada matseta kamar ze maidata cikinsa…..
Yasan dole zataji zafin rukon daya mata amma shi kadai yasan irin relief din da hakan yake basa, babu yanda ta iya dole haka ta tsaya zafin jikinsa na ratsata sai sauke ajiyar zuciya yake a jejjere….
Sundade a haka kafin ya dan sassauta mata rukon daya mata at the same time zafin jikinsa na raguwa, dan janyota sama yayi ya saita bakinsa daidai kunnenta murya chan kasa in a whisper yace;
“I miss you so much that I can’t even sleep baby girl!”…..
Sosai maganar ta aika mata da wasu sakwanni a cikin jikinta ta lumshe ido tana sauraron bugun zuciyarsa……
“Me su mami suka baki haka kikayi kiba?”…..
“Fruits”…
Ta bashi amsa da iyakar gaskiyarta….
“And what?”….
“That’s all”…
“Nima ki kawomin nasha nayi kyau kamarki, bakiga na rame ba?”…..
Cikin tausayawa tace;
“Nagani, idan aka bani anjima zan kawo musha tare”….
“That’s my baby girl! Ina jira”….
A hankali kamar me rada tace;
“To meyasa ka rame?”….
Cikin irin muryar data masa magana yace;
“Saboda tinanin wata yarinya, kinasan sanin WACECE ITA?”….

Also Download Abban Sojoji Book 1 Complete Novel Document

“A’a”….
Tabashi amsa tana bata rai….
Dariyar daya dade beyi ba yayi yana mamakin wautarta, mutum ya gama ce maka ya kasa bacci saboda kai amma ka kasa gane tinaninka yake….
Sai da suka kara wasu yan mintuna a haka kafin a nutse yace;
“Inaji a jikina na kusa mutuwa!”…
Zaro ido tayi daga kwancen tace;
“Mutuwa fa kace yaya, saboda me zaka mutu?”…..
“Saboda zakiyi aure!”….
“Toh bakaso nayi aure?”…..
“Eh, ko kinaso na mutu?”…..
“Nooooo”….
Ta bashi amsa a sanyaye…..
“Toh zaki hakura da yin auren?”……
Turo baki tayi tace;
“Ai nima banaso nayi yanzu, kuma saida na fadawa umm tace bappa baze yarda ba”….
“Kawai ta fada miki haka ne amma kina kiran bappa da kanki kikace masa bakyaso ina tabbatar miki za’a fasa”….
Bata fuska tayi tace;
“Kaima ba ance aure zakayi ba, idan na fasa zaka fasa ne?”….
“Da gudu ma kuwa, ai in kika fasa nima za’a fasa nawa”….
“Toh shikenan, yanzu in kira bappa?”…
“Eh ina wayarki?”….
“Tana daki”…
Sakinta yayi yace;
“Tashi kije ki dauko wayar ki boye achan cikin garden ki kirasa yanda babu wanda zeji, idan yace miki meyasa kikeso a fasa kice masa saboda kinada wanda kikeso ne”…..
Tashi tsaye tayi tace;
“Idan yace wa nakeso ince wa?”…..
“Kice masa zaki kawo masa shi har gida”..
“Okay bari inje in kirasa”….
Ta fada tana barin dakin…..
Baby tee na fita umm tashigo, bata ce komai ba ta sake gwada blood pressure dinsa, miraculously taga ya koma normal, cike da mamaki tace;
“Ikon Allah saif bp dinka ya koma normal, how comes?”……
Murmushi yayi yace;
“Ikon Allah”…
Baby tee na fita part din mami ta tafi ta dauko wayarta sannan ta sake fitowa ta tafi chan karshen garden kamar yanda deen yace tayi, harga Allah ta yarda mutuwan zeyi kamar yanda ya fada sannan har cikin zuciyarta takejin bataso ya mutu kuma zata iya hakura da auren akan ya mutu, dukda bata kin khaleel amma tafi damuwa da rayuwar deen akan yin auren, without second thought tayi dialing number bappa…..

Back to top button