Haihuwa Da Hanji Page 40 Hausa Novel
Ya jima zaune yana kallon figure ɗinta cikin duhun ɗakin kan ya zame ya kai kwance yana sanya pillow a kirjinshi, idanunshi a lumshe sama da awannin da ba zai iya lissafawa ba har bacci ya ɗauke shi a haka ɗin, chan cikin baccin shi ya fara jin abin da yake ji muddin ya rufe idanu da sunan baccin dare ji yake kaman zai mutu, kaman an saka abu ne aka danne mishi kirji numfashinshi ya toshe juye juye yake ya haɗa zufa sharkaf sai numfarfashi yake fitarwa sama sama.Cikin baccinta ta soma jinshi a hankali ta buɗe idanu sai dai jin yadda yake yin yasa bata san ta miƙe ba taje ta kunna wuta gabanta na faɗuwa ganin kaman zai faɗo daga kan gadon ta ƙarasa wurinshi da gudu tana jijjiga shi Muryarta na shaking take ƙiran sunanshi “Ya…ya Saraki! Ya Saraki…!Ka buɗe ido.. Ka tashi ya Saraki mafarki ne… Don Allah ka bude ido…innalillahi!”Duk ta rikice ta ruɗe sai dai kaman bai san tana yi ba har lokacin idanunshi a rufe suke yana jan numfashi da kyar, kuka ta saki tana janyo wayanshi ta shiga neman Layin likitarshi jikinta na tsuma saboda tashin hankali, kiranta tayi Allah ya taimaka ya kusa yankewa ta ɗaga “Dr. Yaya Saraki ne… Ban san me zan mishi ba ya ƙi tashi sai juye juye yake kaman zai mutu ki taimakeni..!”Likitan da take sensing tashin hankali a Muryar Afeefah tausayinsu duk ya rufeta ta ce “Ki natsu Afeefah natsu! Faɗa min me yake yi?”Kaman za ta taya shi kokawa da numfashi ta shiga cewa “juye juye yake yi, ya jiƙe sharkar da zufa, he’s just gasping for air kaman baya iya isar da numfashi inda ya kamata jikinshi rawa yake..””Ki ji Afeefah Rayyan na gab da shiga cikin mummunan yanayin matsalar kwakwalwa idan baki taimakemu ba, ki taimaka ki san yadda zaki yi ki saka shi yayi kuka ya zub da hawaye in ba haka ba akwai matsala…”Wasu tips ta bata tare da yanke wayan akan dole gobe da safe su tafi asibiti he cannot continue like that.Jefar da wayan tayi a kan gadon ta tattare ƙarfinta gabaɗaya ta ɗago shi ta jijjigashi da karfin gaske tana ambatar sunanshi sai ya ja numfashi mai tsawo yana buɗe idanu amma sai idanun su tafi luuu kaman za su rufu idan ta sake ƙira sai su buɗu sun yi wani irin ja da sauri ta kafa gwiwowinta akan gadon ta zare hijabinta ta jefar tare da ma kanshi ta mishi kyakyawar masauki a kan kirjinta ta rungumeshi Tsam tana kuka sossai, yadda ta yi hugging nashi, yadda take shafa kanshi da duk hannayenta biyu zuwa wuyanshi yadda take kara matse shi, sautin fitan muryarta cikin kuka ya sa bai san sadda ya mayar da hannayenshi jikinta ba ya rungumeta ƙamƙam… Cikin sautin kuka take furta “Ya Saraki ka sassautawa zuciyarka don Allah, wannan wahalar yayi maka yawa don Allah ka daure ka zub da hawaye ko kaɗan ne… Zan zama kurma daga jin sautin Muryar fitar damuwarka! Zan zama makauniya daga kallon ruwan hawayenka! Kwakwalwana zai shiga ɗimuwa har lokacin nan ya zama tamkar mafarki ko dilusion a gareni just cry ka ji? Ka yi kuka ba zan ji muryarka ba i promise…Muna mu…na son lafiyarka we will always be there for you… Ka yi kuka just let your worries our this will be our Lil secret ka ji?”Har lokacin bata daina shafa suman kanshi ba cikin wani irin kulawa, sake ƙamƙameta yayi kaman zai ɓallata jikinshi na sake ɗaukar rawa zuciyarshi na wani irin tsitsinkewa Dukda irin yadda take ji da zafi dake ratsa ta haka ta sake hugging nashi, she hugged him until his soul melts into tears sai ji tayi yana sauke wani irin numfashi mai tafe da zafafan hawaye masu rikitarwa.Lips ɗinta ta datse tana runtse ido a sadda sautin shi ke shiga cikin kunnuwanta a hankali yana samun masauki a cikin zuciyarta, bata daina shafa shi ba shi kuma bai daina sake kankanmeta ba ya fi mintuna talatin cikin wannan yanayi kan a hankali ya fara sassauta riƙon, gefe gefe tayi ta kwanta yayinda ya bita har lokacin kanshi na kan chest ɗinta dake beating so so fast tana shafa shi da hannunta tana jin jikinshi na sauyawa daga zufa zuwa zafi dake shiga har cikin jikinta, sai da suka kai kwance ta iya jin ruwan hawayen shi na sauka a kan silk maroon rigan baccinta Yana taɓa fatarta ta runtse ido kawai. Basu san iya adadin lokutan da suka ɗauka a hakan ba har bacci ya ɗauke shi itama baccin tayi.Ƙarfe biyu da wani abu ya sake farkawa, shiru yayi yana shakar fitinannen kamshinta yana jin hannayenta a jikinshi, ɗaya a cikin tattausan gashin kansa ɗaya a bayan wuyanshi, a hankali ya zame ya miƙe zaune wutan ɗakin a kunne har lokacin amma ba tarrr ba mai ɗan duhun yana iya kallon fuskarta a haka, idanu ya zuba mata yana aikin kallo her caramel skin, dogin lashes ɗinta pointed nose ɗinta zuwa thin beautiful lips ɗinta he just felt lost a kallon nata moments ɗinsu na ɗazu na dawo mishi kaman yanzu, he can’t believe that it happened. It really happened! he cried in this little Girl’s arms, the way she caresses him, pet him like a Lil boy ya tsaya mishi sossai a rai. Sauƙa yayi daga gadon ya ja duvet ɗin ya rufeta zuwa kirji sai ta ɗan gyara kwanciya kaman dama a takure take ya shiga toilet yana jin wannan nauyin na cikin zuciyarshi ya ragu, ruwa ya kunnawa kanshi ya jima a ciki har lokacin kuma duk motsinshi kallon kanshi yake akan chest ɗinta tana bashi utmost kulawa, wanka yayi ya fita ya zo ya nemi jallabiya ya saka ya fara nafilfili har sai da ya ji zazzabi na neman fin karfinshi ya miƙe ya zare jallabiyar ya saura daga shi sai guntun wando da karamar vest da ya bayyana duk wani kakkarfar sura mai cike da zati da Allah ya mishi gadon ya hau ya ja bargon shima ya ɗan rufa tare da juyawa ya zubawa face ɗinta idanu tana baccinta peacefully har bacci ya sake sace shi a haka.Ita ta fara farkawa da asuba ta sauke idanunta akan kyakyawar fuskarshi, ta ɗan jima tana kallonshi kwakwalwarta na tuna mata abin da ya faru a daren, nauyi da kunyarshi suka lallaɓo suka rufeta amma ta kasa ɗauke idanu daga kallonshi he’s just handsome so so handsome da bata san ya zata kwatanta shi ba, yana baccin kaman ba shi bane Saraki mai zuciya a kusa, wannan masifaffen marar fara’a da son Magana murmushi ta tsinci kanta da yi Alhamdulillah atleast ta samu riba a kanshi wani abin dole ta san ya ragu mishi hakan kaɗai ya faranta mata, sauƙa tayi daga gadon tare da ɗaukan hijabinta ta saka ta shiga toilet don yin alwala tana jin ko me ta mishi bata ragu ta kowani fanni ba saboda he’s her life savior ba don shi ɗin ba da yanzu tana cikin matattu matattun ma cikin sahun masu gingimemen laifi wa ubangijinta.Tana rufe kofan bayin ya buɗe idanu sai dai bai motsa ba don zazzabi ne sossai a jikinshi har numfashin da yake fesarwa na fitar da zafin hucin zazzabin, bayan tayi alwala ta taho gadon ta taɓa goshinshi sai taji shi rau a hankali ta shiga kiran sunanshi “Ya Saraki..! Ya Saraki…!!”Ya rasa wani irin effect sunan ke dashi a zuciyarshi don wani irin tsalle zuciyar tashi tayi a sadda ta ƙira sunan cikin tsiririyar muryarta Idanu ya buɗe ya kalleta “Sannu! Na ji jikinka zafi sossai za ka iya tashi ka yi sallah? Ko in idar in kawo maka ruwan nan?”Idanunta kawai yake kallo hakan ya sa ta kawar da idanun yace a hankali “Zan iya”Daga haka ta koma baya ta tada sallah kar ya ga kaman ta cika zaƙewa, shi kuwa ya ɗan jima a haka kan ya yunkura ya miƙe zaune yana dafe kanshi, a hankali yake tafiya har ya isa bayi yayi alwala ya dawo sai ya kasa Sallar a tsaye duk kafin halinshi a zaune ya gabatar bayan ya idar ya miƙe ya koma gadon tare da lullubuwa, bayan ta idar ta miƙe ta ninke sallayar tana shirin fita wayanshi ya ɗauki ƙara sai ta koma taje ta ɗauka ganin Likitarshi yasa ta ɗaga suka gaisa take tambayarta ya ya kwana nan ta mata bayanin zazzabi ne a jikinshi sossai Dukda ya samu ya zub da hawayen.Hamdala tayi da farko kan tace za ta turo yanzu collegue ɗinta zai zo ya saka mishi drip da wasu allurai in shaa Allahu zuwa yamma zai samu lafiya don Allah ta kula dashi ta amsa tare da godiya ta sauƙe wayan, ficewa tayi zuwa kitchen ta ga abinda suka fara a lokacin gari ma ya fara haske taje ta watsa ruwa don duk yadda ta motsa kamshinshi kaman tayi wanka da turarenshi kamshin na sakata jin kaman har lokacin yana kwance ne a jikinta rungume da ita Dukda ba don soyayya ko wani romance suka yi ba taimako ne ta mishi amma hakan ya mugun tsaya mata,bayan ta fito ta shirya cikin atampharta riga da siket da ya zauna mata chass ta ɗaura dankwali sai ta nemi gyale mai girma da kauri ta yafa ta fita parlor tana shirin shiga side dinshi aka yi mata sallama.”Mery ya dai?””Wai wani likita ne ya zo duba Oga Rayyan””oaky ki ce ya shigo”Tana nan tsaye har ya shigo suka gaisa kan ta mishi jagora har ciki, har lokacin yana kwance ba bacci kuma yake ba don zafin zazzabin bai barshi ba, tana daga chan gefe har likitan ya haɗa drip ya mishi allura ciki ya saka mishi canular yayi wani a canular kan ya ɗaura ruwan sai ɓata fuska take kaman ita ake ɓula wa.”Toh madam za ki iya samun ruwa masu ɗan dumi kaɗan da towel ƙarami a shafa mishi a kan nan da Goshi zafin jikin zai ragu Dukda na mishi allurai amma hakan ma na da kyau don temperature ɗin shi is very very high””in shaa Allahu mun gode kwarai Dr””Mention not”Daga haka ya fice, bayi ta tafi ta haɗa ruwan ta samo ƙaramin towel ta dawo bakin gadon ta zauna ganganshi ta cire gyalen ta ajiye tare da matsa ruwan ta ɗora mishi a Goshi ya buɗe ido ya kalleta saboda sanyin da ya ratsa shi yana sauƙe ajiyar zuciya mai nauyi, wani iri take ji da kallon nashi amma ta dake ta cigaba da shafa mishi da kanshi ya gaji ya mayar da idanun ya rufe sai ta sauke numfashin da ta riƙe tuntuni, idan ta zo daidai kwantaccen sajenshi sai ta tsinci kanta da zame towel ta bar fatar hannunta na shafa lallausan gashin wurin a hankali.Jin abin nata na so ya fi karfinshi ya ɗaga hannu ya ture hannunta, ta ɗan tura baki ta miƙe ta nufi bayi tana mita ‘Mutum bama shi da lafiya amma hali ba zai chanza ba!’ Sarai ya ji ta a maimakon ya ji haushi Sai ɗan murmushi da yayi a cikin zuciyarshi wanda ko alama bai fito fili ba, bata ma fito ba bacci ya ɗauke shi don akwai allurar bacci ciki daga nan ta ɗauki gyalenta ta yafa ta nufi cikin gidan, ɗakin su Abeeha ta shiga inda ta samu suna zaune sun yiyyi wanka Mommy da mama da suna nan tun rasuwar basu tafi ba suma suna ɗakin da alamu sun zo duba kwanansu ne.Har ƙasa ta duƙa ta gaishe su suka amsa cikin kulawa kan ta dubi jannah ta gaisheta tare da mata sannu da jiki suka gaisa da Abeeha a karshe, wata cousin ɗinsu Aaliyah ce tace “Na ga likita yana shiga wurin ku da safen nan Allah dai ya sa ba wani abu bane?”Kanta ƙasa tace “Wlh Ya Saraki ne ya kwana da zazzabi amma Alhamdulillah an saka mishi drip yanzu haka bacci yake”Cike da jimami suke mishi Allah ya kara sauƙi ta ɗan jima anan har aka gama fito da kayan kari ta karya anan suna hira kaman dama chan ita ma she’s part of the family don basu ware ta ba sam.Sashensu ta koma ta leƙa ta samu har lokacin bacci yake ta koma parlor tana kallon time, a chan kuwa fitan ta ba jimawa sai ga su mommy sun shigo babban parlor aka dawo da gaisuwar makota dai kan shigo a yi gaisuwa da su Ƙawayen su Afeefah har ma da dangin mijin jannah ita dai Samha sai baza ido take ta ga ta inda Afeefah za ta ɓullo amma bata ganta ba.Ko da Saleem ya shigo suka gaisa Abeeha ya tambaya Rayyan fa don ya ta kiran wayanshi ba’a picking nan ta faɗa mishi ai bashi da lafiya an ma saka mishi drip kila bai tashi ba har lokacin, bai shiga ba don ya san akwai bambancin da da yanzu ba zai yiwu ya je har ɗakin ba sai fita yayi akan yana parlorn waje.Sai karfe sha ɗaya da rabi da Afeefah ta leƙa ta samu baya kan gadon alamar ya shiga wanka, gadon ta gyara tsaf kaman ba’a kwanta ba ta fice chan sai gata rike da tray mai dauke da dafaffen dankali sai wani curry chicken soup da ta mishi da kifi gasashe a gefe sanin yana so sai tea da ta haɗa mishi, ya gama shiryawa cikin riga da wando masu taushi don ba jeans bane wandon cotton ne mai ɗan faɗi Brown, shirt ɗin burnt orange ya karɓe shi sossai ya sake zama pale kana kallonshi zaka san yana ciwo.A kan table na gaban couches na ɗakin ta ajiye ta kalleshi shima ita ya kalla sai suka haɗa idanu ta ɗan rausayar da nata tace “Ina kwana Ya Saraki? Ya jikin?”Bata zaci zai wani amsa ba sai kuma taji ya ce “Alhamdulillah da sauƙi”Dukda a hankali yayi magana amma ta ji ta ɗan murmusa “ka karya sai ka sha magani”Ya nufo inda take sai da ya ɗan wuce taji ya ce “Thank you!”Zama yayi ya ja abincin ya shiga ci hakan ya faranta ranta sossai ta juya ta fice, a parlor ta zauna tana kallo kusan mintuna talatin sai gashi ya fito ya fita waje. Sai lokacin hankalinta ya kwanta ta miƙe itama ta nufi wurin su Jannah tana shiga babban parlorn da sallama suka hada idanu da Mommy…


