Uncategorized

Wani Kare Ya Mutu Saboda Ya Sinsini Dan Kamfan Wata Mata

 

Wani lamari da ya auku da wani kare a bainar jama’a a wurin shakatawa ya matuƙar bada mamaki da kuma daure kan al’umma sosai.

Tun farko dai karen ya kasance yana bin bayan masu shi a yayin da su ke zagaya wani beach(bakin ruwa) domin bude ido, shi kuma karen nasu yana ta binsu tare da dabiar nan ta karnuka ta shunshune-shunshune, a yayin da karen ya yi arba da wata budurwa mai cikar diri da kyan halitta sai ya juya ya bi bayan ta da nufin zai shinshina jakar da ke hannunta.

A bisa rashin sa’a sai kuma ita daidai lokacin ta duka da nufin gyara takalmin ta turo duwawu baya wadanda babu komai da ya rufe su sai wani dan kampai wanda bai rufe ko kashi 20 cikin dari nasu ba.

Related Articles

Hakan ne ya sanya nan take hancin karen ya shinshini wannan dan kampai ɗin bisa kuskure, sai kuma nan take aka ga karen ya fadi kasa a yayin da ita wadda aka shinshini wandon nata bata ma sani ba.

Yayin da masu karen su ka lura da abinda ke faruwa, nan take su ka rugo domin ganin abinda ke faruwa, sai dai kafin su karaso tuni karen nasu ya ce ga garinku nan.

Mutane da dama da su ka shaida yadda lamarin ya faru sun zargi wadda ta zama sanadiyyar mutuwar karen da maita, sai dai kuma daga karshe hukumomi sun shiga lamarin domin hana afkuwar rikici inda aka mikawa likitoci gawar karen domin gudanar da bincike domin gano takamaiman abinda ya faru.

Binciken likitoci kuwa ya tabbatar da bugawar zuciya mai karfi a matsayin sanadiyyar mutuwar karen.

Back to top button