Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 5 Hausa Novel

Hannunta ta riƙe cike da tarin tausayinta da kuma ƙaunar da take jin tana mata fiye da ƙima ta shiga cewa”Na san ba ki kashe kowa ba Afeefah, ƙage ne kawai da Ƙazafi irin da jahilai daga cikin al’ummar mu, ƙarancin ilimi yayi yawa ta yadda mutane suke kasa yarda komai daga Allah ne, a ƙarƙarorin mu ne musamman wanda babu addini sossai za ki samu ko tuntuɓe bawa yayi sai an faɗi dalili da silar shi basu yarda cewa komai Allah ne yake yi ba.Afeefah Kowacce rayuwa akwai ƙalubale ciki ke kuma ta ki kalar ƙalubalen kenan, amma fa na faɗa na sake kar ki saka hakan a ranki saboda babu mai kashewa da raya wa sai ubangiji, duk kuma wanda kika ga ya rasa ransa tabbas lokacin shi ya riga ya ƙare ne ko da sanadi ko babu dole babu maƙawa sai ya tafi, tsakanin ki da su Adu’a ne shine zai ba su tabbacin irin ƙaunar da kike musu. Afeefah mahaifiyarki ba za ta so ta ga kina zub da hawaye ko kin ƙuntatawa kan ki saboda ƙaddarar da ba ke kika ɗorawa kan ki ba, kaman kowace uwa ni ma zan baki shawara ki saka zuciyarki gaba, ki yi Adu’a ki kuma jajirce ki zama tamkar bishiyar gamji sara ko sassaƙa ba su isa su hana ki toho ba”Jikin Aunty zee kawai ta faɗa tana shesheka da kyar ta lallasheta ta bar kukan kan ta ɗago “Na miki alƙawari in shaa Allahu Aunty za ki yi alfahari da ni nan gaba, ba za ki taɓa kuka a kaina ba””Allah ya amince hajiya ta”Dariya Afeefah ta saki jin ta kirata hajiyarta wadda babban burinta kenan ta zama shahararriyar ‘yar kasuwa don tana so tayi kuɗi saboda wani dalili nata. Ƙaurin kamawar leda da suka ji ya sa ta tashi da gudu taje ta sauke tukunyar alelenta daga kan gano tana furta”Aunty alele na so yayi mana buƙulu”Aunty zee na dariya tace “Hira ta yi daaɗi ba, duba ki ga Allah ya sa bata yi komai ba”Sun ci sa’a bata yi komai ba sai na ƙasan guda biyu da ledar ya ƙone nan ta zuba musu tare da Auntyn ta zuba na uncle a kula suka zauna suka ci tare suna hirar su gwanin sha’awa bayan sun gama ita ta yi wanke wanke, ko da ta dawo kan taburman hoton Aunty zee ta bata “Gashi na bar miki, ki ajiye a wurinki”Murmushi ta saki kan ta karɓa tana godiya.Wasa wasa cikin Aunty zee ya shiga watan haihuwa, ta ɓangaren Afeefah tana nan tana ƙoƙarin karatu ka’in da na’in don 2nd term da suka koma ita ta ɗauki na ɗaya kuma 3rd term nan suna ƙare ta tare da ita za’a zana Junior waec ta tafi ss1, a yanzu hatta turanci ya zauna a bakinta ba kaman baya ba da bata wani jin komai, duk wani sayayyar haihuwa tare suke zuwa saboda a hankali ciki ya sa Aunty zee ɗin ta shigar da Afeefah cikin business ɗin ta, wani lokacin ta kan aike ta ita kaɗai ma kasuwa wurin customers ɗinta kuma ta zo ta raba wa clients ɗinta kayan, asusu Aunty zee ta yi mata ta kan ware ladar ta na kasuwanci ta saka mata ciki duk da Afeefah ta nuna ita bata so, tufafi, karatu da kuma cima sau uku da ake bata ya wadatar da ita. Amma Aunty zee ta nuna hakan shine adalci kuma ko nan gaba zata iya anfani da kayanta idan buƙatar hakan ta taso.A yau Aunty zee take cika wata tara da kwana tara kuma a ranar ta kwana da labour mai zafi, hankali tashe da asuba suka tarkata asibiti har da kishiyarta da ta zo ta kwanan musu kasancewar tun da abin ya fara mijin ya ƙirata, ta fi kowa shiga damuwa an ƙarbe ta zuwa ɗakin haihuwa sai jiran abin da hali zai yi, duk Afeefah ta fi ruɗewa babu abin da take tunawa vividly sai irin wahalar nakudar da innarta tayi ƙarshe daga ita har babyn suka koma wannan abu ba zata taɓa mantawa ba, duk kuma ta ga mai ciki sai hantar cikinta ya kaɗa a yanzu Allah kaɗai ya san halin da take ciki na tsoro da fargaba duk adu’ar da ta zo Bakinta ita take yi. Sai Azahar Allah ya taimakesu midwifes ɗin da suka karɓi haihuwar suka fito suna musu albishir na ta samu ‘yan biyu mace da namiji faɗin kalar murnar da suka yi ɓata baki ne. Karo na barkatai kenan da Afeefah ta ke kai idanunta kan yaran hakwaranta duk waje, yaran gwanin sha’awa kaman ta Haɗiye su, sam bata san Aunty zee ta farka ba sai ji ta yi tana furta “Suna ba ki sha’awa ko Afeefah?”Da sauri ta juyo tana dariya “Sossai ma Aunty zee, sannu kin farka? Ya jikin?”Ta ɗan saki murmushi.”Masha Allah, jiki Alhamdulillah”Ta furta hawaye na gangaro mata Dukda tana sauƙa sai da ta ji ɗuminsu kan wannan wahalallen baccin ya yi awon gaba da ita amma yanzu da ta farka sai take ganin kaman mafarki, kaman ba’a gaske ba ita ce yau da shekaru arba’in da biyu a duniya kan Allah ya nufe ta da ganin ƙwanta? Har biyu kyautar Allah? Bata san wani irin godiya za ta yiwa mahallicinta ba don ko yau ta faɗi ta mutu ta san ta bar bayan da za su iya tunawa da ita su yi mata Adu’a, bata san daaɗin haihuwar ya kai har haka ba a ganinsu da take kawai ji take kaman ta rabu da baƙin ciki har abada matukar suna kusa da ita.A hankali Afeefah take kokarin ɗaukar su ta kaiwa uwar, daidai shigowan kishiyar Auntyn “A’a Afeefah me haka? Sabbin haihuwan kike ɗaga su anyhow? Wa kika tambaya da za ki ɗaga su?”Yadda take maganan zaka zata wani gagarumin abu Afeefar ta aikata don har ta tsorata, da ta kurawa matar idanu sai ta fahimci kaman akwai dalilin maganar nata amma bata wani mai da hankali ba don Aunty zee ta amsa mata “A’a hamdiyya ai Afeefah ba yarinya ba ce da zata kada yaran baki san ko yanzu ta yi aure zata iya haihuwa ba? Getting to 18yrs ba wasa ba””kin ga Aunty sabbin haihuwa ne kuma ji da abin mu muke ko kuda bama so ya taɓa su bare wasu da idonsu idon sabon jini su ke Sha’awa”Da sauri Afeefah ta mayar da idanunta kan matar, Aunty zee ma ta ɗago ta kalleta “Me kike nufi Hamdiyya?””Gaskiya nake faɗa Aunty, hanyar lafiya sai a bi ta da shekara ba za mu so farin cikinmu ya koma baƙin ciki ba”Hawaye ne ke kokarin zubowa Afeefah da jikinta yayi wani irin sanyi, bata ankara ba sai ji ta yi Aunty zee ta ɗora mata yaran duk biyu a kan kafafunta “Afeefah ga su nan ƙannenki ne, ki riƙe su yadda kike so”Juyawa ta yi ga hamdiyya “A kan Afeefah za mu iya samun matsala da ke, ba zan taɓa zuba ido ki tozarta ɗiyata a gabana ba, kin ga yau na haife su ko? Kuma na san daaɗin su ko? To wallahi zan iya zaɓar Afeefah sau dubu kan in zaɓe su sau ɗaya. Ki kiyaye kan mu yi uwar watsi da ke a kan ‘yata””Aunty ni kike yi wa gori a kan wannan mayyar?”Ko kan Aunty zee ta yi magana Uncle ya shigo, kafin ya tambayi me ya faru Hamdiyya ta fashe da kuka mai ƙarfi tana yunƙurin fita, da sauri uncle ya tare ta don shi mutum ne da baya son abin da zai kawo mishi matsala da iyalanshi, yayi kokari ƙwarai wurin haɗe kawunansu ba zai so ko ma menene ya raba su ba, ban da ma yanzu da suka soma tara zuri’a suke kuma cikin farin ciki tsantsa.”Me ya faru hamdiyya? Zainab me ya haɗa ku?”Aunty zee dai komawa ta yi ta zauna sai hamdiyya ce ta kara karfin kukanta “Ka yi haƙuri ni ce da laifi na zaci da ni da Aunty duk ɗaya mu ke kuma ‘ya’yanta za su iya zama nawa amma ashe na yi kuskure, in shaa Allah ba zan sake ba””Zainab!”Uncle ya furta sunan cikin rashin jin daaɗi “Gori kika yi mata?””Amma dai ka fi kowa sanin hali na Usman, ban yi mata gori ba kuma ba zan taɓa yi mata ba don nima babu wayo na bare dabara ta Allah ya ba ni, abin da take shirin shigowa da shi ne ba zan lamunta ba sam”Hannunshi dake cikin nata hamdiyya ta janye “jita-jita bai taɓa wanzuwa ba matukar babu kamshin gaskiya, an sha tare ni ana gargadina a kan Afeefah amma na ɗauke kai saboda ganin yadda Aunty zee ke ƙaunarta, abin da nake tsoro an ce suna kaunar sababbin jini to don na ce Afeefar ta yi haƙuri da daukar su har su yi kwari shikenan na yi laifi…? Ku yi haƙuri bari na je gida”Tana kai nan ta fice uncle bai ce komai ba don shima karo na ba adadi an tare shi an faɗa mishi abubuwa dayawa kan Afeefah amma baya bari ya shige shi, sai dai kuma bai ji daaɗin reaction na zainab ba da sai a bi abin a hankali tunda dai already akwai maganganu kan Afeefar.”Amma ba ki kyauta ba zainab, na sani kina kaunar Afeefah kasancewar ta marainiya kuma abin tausayi amma kuma sai ki duba kokarin hamdiyya wurin ganin ta bai wa jininki kariya, tun fa jiya tana tare da ke ko runtsawa bata yi ba, ko da kika sauka kika fara bacci haka ta koma gida ta dafo miki ruwan zafi ta biya ta sayo kayan tea saboda kar ki tashi da yunwa babu abunda zai taimaka miki, ai gyara kayanka baya zama sauƙe mu raba”Yana kai nan ya juya ya fice.Idanunta ta mayar kan Afeefah dake hawaye sossai, rabon da taji raɗaɗin zuciya tun ranar da uncle ya amince ta zauna da su sai yau.Yanzu ko da tana cin naman mutum wani bala’in ne da rashin tausayi haɗe da rashin imani zai sa ta ci naman waennan talikan da isowarsu duniya kenan? Me zai sa ta cutar da ‘ya’yan wacce ta rungumeta ta cicciɓota ta zaro ta daga cikin bala’i da ƙuncin rayuwa?”Afeefah…”Auntyn ta ƙira sunanta a hankali sai kuma ta kasa magana duk suka yi shiru tsawon lokaci kan nurses suka shigo, hakan ya tilastawa Afeefah barin ɗakin kai tsaye fita tayi daga asibiti ta tsare abin hawa ta faɗa mishi inda za ta, gidan Hamdiyya ta nufa don ta tabbatar a chan za ta samu Uncle usman da ma ita karan kanta hamdiyyar.Hasashenta ya tabbata don kuwa ta same shi tare da hamdiyyar yana ta kokarin bata baki tana tuburewa, maganganu take gayamishi cikin ɗaci da nuna kaman shi ne ai ya zaɓi ya ba Zainabun ciki har ta haifi ‘yan biyu tana mata gori.”Haba hamdiyya kema kin san da mutum shi ke ba kanshi haihuwa da yanzu mun tara yaran da bakya zato saboda Zainab macece mai kaunar yara, tun aurenmu na shekara duk inda taji magani muddin bai saba shari’a ba nema take amma da Allah bai turo ba ba gashi yanzu ta haihun ba? Ba’a cire rai daga rahamar ubangiji kema kuma ya san dalilin da ya jinkirta naki namu Adu’a ne kawai da neman zabin alkhairi daga rabbissamawati”.”A’a Usman ai ka fi ƙaunar Zainabun idan da Zainabun ta haihu tun farkon aurenku da baka auro ni ba, silar rashin haihuwar ne ta saka ka kara aure ba don kana so na ba kuma ta haihun ai…”sallamar ta ya katse musu maganar duk suka mayar da hankali kanta.

Back to top button