Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 25 Complete Novel

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                           TWENTY-FIVE📍

       A nitse suke tafiya motar Deen a gaba sai tasu Mami dake biye dashi a baya, musamman mami tace ya shiga gaba dan suna ganinsa kar suce ya biyosu a baya yayi wata hanyar yanda ya nuna musu bayasan komawa dama….. 

Minti minti Deen yake juyowa ya kalleta gabadaya zuciyarsa a dagule, shi bawai bayasan komawa prison din bane a’a so yake ta farfado ta fadamasa WACECE ITA? sannan ya kaita gidansu ya musu kashedi akan rashin kula da ita gashi ana so a cutar da ita….

 Haka ya cigaba da sake sake har suka karaso prison, parking yayi yaki fitowa daga motar saima juyawa da yayi yana kallonta, nan wani tinani yashiga ransa kan meyasa koda yaushe take kunshe cikin hijabi? Kodai akwai wani abun da take boyewa ne? Shifa yanzu baze iya yarda da yarinyar nan ba, sai ya fara dana sani da be cire hijab din gabadaya ba ranar da ya mata allura, sai kuma yaga ai yana cikin tashin hankalin haukar data dingayi ranar, shi ko kallonta beyiba daya dage hijab dinta, amma zeyi maganinta dan sai ya gano me take boyewa, hardasu hand gloves da socks tsabar munafurci?… 

Umm ce ta katsesa da fadin

     “Ya kayi zamanka a ciki kuma, fito mana”….

Fitowa yayi yana addu’ar Allah ya dorasa akan Umm ta tayasa bawa mami hakuri a barsa ko zuwa gobe ne.. Cikin fuskar tausayi da damuwa yace;

     “Umm na yanzu dawo dani kukayi da gaske?”…

Ba yabo ba fallasa tace;

    “Ga zahiri ka gani”…

“Dan Allah ku barni zuwa gobe idan na mayar da ita gidansu”….. 

   “Karka damu zamu mayar da ita”…

 “Bazaku iya da ita ba, kinga fa yanda takeyi Umm”…

 “Aljanu ne suke damunta ba kariga ka cire su ba? Insha Allah lafiya lau zata farka”….

   “Ai basu fita ba, zasu dawo”…

Ya fada cikin rashin sanin abinda zece su yarda ya zauna”……. 

Harara mami tashiga aika masa batareda tace komai ba, Umm ce ta zaro ido itace;

     “Ikon Allah wato fata kake mata su dawo kenan? Anya saif wannan taimakon na tsakani da Allah ne?”…

  “Wallahi tsakani da Allah ne, ni nasan basu gama tafiya bane, ina ganewa idan aljanu na jikin mutum”.

     “Yaushe ka zama sheikh bamu sani ba? Kafa ji tsoron Allah saif!”…..

    “Ke kika tsaya kina kulasa ma yanata zuba miki shashanci, mu zaka maida wanda basu san abinda sukeyi ba, yaushe ka fara harka da aljanu bamu da labari?”…..

Sai a lokacin mami tayi magana….

Shiru yayi yana shafa gemu kamar wani ustaz, ya rasa meyasa yake sakin layi akan yarinyar, idan yayi kokarin billewa wani gurin sai yaga ashe kama kansa da kansa yayi, in banda haka shi meya hadashi da gane masu aljanu? Bema taba yiwa wata karatu ba sai a kanta…..

Gyaran murya mami tayi tace;

      “Ka bude kunnuwanka da kyau ka saurareni sannan ka gayamin iya gaskiyarka, hakan ze iyasa na maka sassauci, sannan inaso ka sani maganar nan daga gurinnan ba zaa kara tadota ba, ya rage naka ka fadi gaskiya”…..

      “Ina ji”….

  “Are you in love with her? Dan wannan rawar kafar da kakeyi akanta ba kalau ba, so tell me kana sonta ne?”….. 

        “Mami wani kalan tambaya ne wannan?”…

    “Bansan dogon surutu, just tell me yes or no?”….

        “NO!”….

    “Good, Umm ki zama witness even though kema kin masa same question, we’re not coming back to this, that no will be forever!! Wallahi wallahi baza a sake tada maganarnan ba!!”……

Gyada kai Umm tayi tace;

    “I’m a living witness, Insha Allah maganarnan an barta har abada!!”…..

     “Ina mask din daka fita dashi?”….

       “In the car”…

Deen ya fada murya a sanyaye…..

     “Shiga ka saka, ta inda aka hau tanan zaa sakko”…..

         “Ok, amma mami ya zakuyi da ita, naga bata tashi ba haryanzu”….

    “Karka damu!”…

  “Zaku tafi da ita ne?”.

    “Yes”…

Wani sanyi yaji aransa datace zasu tafi da ita gida, ko banza yasan inda ze sameta”…

     “Toh insa muku ita a motar ku?”…

    “Who’s car is this, nasan dai ba taka bace”….

      “Ta sameer ce”…

     “Ina yake sameer din”…

Dan jimm yayi yana tinanin abinda ya dace ya fadamata dan harga Allah bayaso yayi exposing dinsa……

     “He left the country today”…

   “It’s a lie, yaushe kazama makaryaci Saifuddeen ?”……

Mami ta fada dan a iya saninta dashi komin dacin abu fadarsa yake ba ruwansa shiyasa ta tambayesa ko yana san yarinyar dan tasan in yana so kai tsaye ze fada…..

    “I’m not lying, munyi dashi yau zebar kasarnan and probably ya tafi by now”…

    “Oh kai ka bashi shawara ya gudu kenan? Yayi kyau, go get the mask”….

Bece komai ba ya shiga yasa face mask din ko kallon fatima zainab beyiba dan bayasan ya karawa kansa damuwa…..

Fitowa yayi suka bisa da kallo da jinjina wayo irin nashi na kawo idea din mask, ta ina zaka kallesa kace Deen ne when the mask looks so perfect kamar face din real mutum? har colour din skin dinsa yayi rhyming da mask din…

Dauke ido yayi be damu da kallon da suke masa ba ya sake komawa motar ya daukota ya sata a back seat din motarsu sannan ya sake dawowa cikin motar ya bude dashboard ya dauki wani abu a kulle a leda ya zira a aljihunsa sannan ya kashe motar ya zare key din ya boye a aljihunsa yana addu’ar Allah yasa kar mami tace ya kawo…

     “Wayace ka daukota ka sata a motarmu?”…. 

Cewar mami bayan ya dawo inda suke….

     “Naga kince tafiya zakuyi da ita”…

    “Sai kuma akace ka dauketa? Naga you have legalized taba yarinyarnan kamar wata muharramarka, wani kalan sakalci ne wannan?”….

    “Wallahi mami bada wani abu nakeyi ba, naga ku bazaku iya daukanta bane”….

    “Haka muka fadamaka?”…

      “No, I’m sorry”…

     “This should be the last time da zaka taba yarinyarnan, am I clear?”…

    “Insha Allah”…

     “Good, muje ciki”….

Saida suka gaisa da securities din gurin da har lokacin basu gane komai ba sannan suka shiga ciki…

Tinda suka tafi ya kasa zaune ya kasa tsaye, ganin yake kamar zaa zo a kashesa anytime kamar yanda Umm tace what if a aiko a kashe Deen a kashesi a madadin Deen?… Ko dan kara yaji saiya rikice ya fara kalmar shahada, gashi sunce yanzu zasu dawo amma shiru basu dawo ba, hakadai ya cigaba da zagaye dakin….. 

Yana cikin wannan hali yaji sallamar mutane, saida gabansa ya fadi dan bashi da tabbacin ko sune suka dawo…. 

Wani ajiyar zuciya ya sauke da suka shigo, ya tsuguna har kasa ya shiga gaishe su……

Deen be bi takansu ba ya dauki kaya daga cikin kayansa dake gurin ya shiga toilet ya chanja ya fito, cire mask din yayi ya mikawa guy din…. 

Bayan sun gaisa suka cemasa shima ya shiga yayi changing ya fito su tafi…. Kamar jira yake ya tashi da sauri ya shiga ya shirya….. 

      

     “Yanzu ya zamuyi dashi?”…

Cewar Umm bayan sun iso parking space….

     “Inaso muje gidansu badan haka ba danasa driver yazo ya mayar dashi gida, zaki zauna da yarinyar ko ni in zauna da ita sai ya shiga front sit?”….

       “That’s not an issue bari na zauna da ita,let’s go”….

Front sit mami ta bude masa tace ya shiga, cikin dari dari ya shiga sannan ta shiga driver seat…..

Umm kuma ta shiga back seat inda fatima zainab take, zama tayi ta daura kanta a cinyarta ta shiga shafa fuskarta, haka kawai takejin son yarinyar a ranta, ita kadai tasan yanda taji da Saif yace bayason yarinyar, taga rashin hankalinsa na rejecting kyakkyawar yarinya haka though abun baa nan yake ba, watsar da zancen Deen tayi ta hau yimata addu’ar Allah ya bata miji nagari da ze sota ya kula da ita sosai…..…..

 Tada motar mami tayi tana tambayarsa sunansa…

        “Aliyu”….

Ya fada yana sunkuyar da kai

       A nitse mami take driving bayan sun bar gidansu aliyu, babu wanda yake cewa wani abu a cikinsu dan har lokacin jikinsu a sanyayye yake, ashe akwai wa’yanda suke cikin talauci irin haka? Ba karamin tausaya musu sukayi ba suka kuma tabbatar da abinda yasa aliyu ya karbi offer din, 200k Umm ta bawa aliyu ya dan siyo musu abu dake tanada sauran cash din data cira lokacin data shigo Nigeria, mami kuma tace aliyu ya kawo takaddunsa zata bashi aiki suka kuma musu alkawarin zasu dawo gobe Insha Allah……..

 After a short silent Umm ta dubi mami tace;

       “Dama ana irin wannan talaucin a Nigeria? This is serious!”…….

Dariya sosai mami tayi tace;

    “Ta ina  zaki sani kin tafi UK kinyi zamanki for a decade, atleast da kina karban cases a nan you would know”……..

     “Seriously I thought everyone is living normal, not all wealthy but not this poor!”..

    “Tabb wani normal, you’re thinking that way because bakisan talauci ba tinda aka haifeki upto date, dama da kinyi aiki da first degree dinki na law anan Nigeria shine zakisha cases that will clear your eyes kika gudu kika tafi medicine”…..

      “Toh befi min ba? So kike duk mutaru a court, I still handle some court issues ai, you know I own a chamber in UK”…..

 Umm ta fada tana dariya…..

        “To ai ba irin cases din Nigeria kukeyi ba”….

    “Yeah hakane da wannan kuma”….

Haka sukata hirarsu har suka karasa gida…..

    

      “Ya zamuyi da ita yanzu?, yaro yana taimaka mana kin koreshi”…..

Cewar Umm tana dan dariya bayan mami tayi parking sun fito daga motar…..

Bata rai mami tayi tana fadin;

     “Au haka ma zakice? Kinfiso yayita taba yar mutane haka kawai, dama ke kike daure masa gindi yake abinda yaga dama”…..

Dariya tayi sosai tace;

     “A’a a’a maida wukar ni wasa nakeyi, akan me zanso yana tabata ba muharramarsa ba, bari kiga in dubata ma”…..

 Karasawa tayi ta bude back sit inda fatima zainab take kwance, nan ta hangota a zaune ta kifa kanta akan cinyarta…. Ganin kamar ta farka ne ya sata fadin;

       “Hey baby!”…

Dagowa tayi da sauri ta kalleta…

Murmushi ta mata tana mika mata hannu tace;

     “Ashe kin tashi? Toh tawo”…..

Hakanan ta samu kanta da mika mata hannu ko musu babu, ta taimaka mata ta fito daga motar….

Rike hannunta ta cigaba dayi har suka shiga ciki….. 

Suna shiga main parlour idonta ya sauka akan katon picture din Deen dake yiwa mutane welcome, hankalinta taji ya tashi sosai, lokaci daya taji batasan shiga gidan kuma, tirjewa tayi tana kokarin kwace hannunta daga na Umm… 

Ganin tana kwace hannunta yasa Umm juyowa da sauri tace;

     “What happened?”….

    “Ni bazan shiga ba”…

Fatima zainab ta fada cikin muryarta me sanyi…

      “Why?”….

Nuna hoton Deen tayi tace;

    “Meyasa zaki kawoni gidansa, mugu ne fah”…

      “Ba gidansa bane, this is my house, he’s my son”..

Bude lumsassun idanunta tayi sosai ta kalleta irin dama danta ne take cewa zata kasheshi a gabanta? Ta kuma dinga zaginsa ashe mamansa ce? Amma shine taketa mata mutunci…. For the second time ta karajin ba dadi akan abinda tayiwa wani taji kuma tanasan bata hakuri amma bata san ta ina zata fara ba dan bata saba ba, cikin san faranta mata tace;

      “When I said zan kasheshi I don’t mean it!”…

Dariya Umm tayi ganin yarinya zata tsarata tadai basar tace;

      “Oh don’t worry dear, I know you don’t mean, badai bakyasan ganinsa ba? I’m assuring you that you’ll not meet him har ki bar gidannan, now let’s get in”……

Ba musu tabi Umm suka shiga….. 

Mami ce ta ruko hannunta bayan sun shiga parlourn ta kaita wani bedroom da yake da komai a ciki, ta mata providing duk wani necessary abubuwa sannan tace ta shiga tayi wanka tayi sallah……

Idar da sallanta keda wuya taji ana knocking, tashi tayi ta ninke sallayar sannan ta karasa bakin kofar, tana budewa taga Umm a tsaye tana murmushinnan nata as usual..

     “Umm”…

Ta samu kanta da fadin hakan…

       “Yes dear, would you like your food serve here ko zakizo dining”….

      “I’m not hungry”…..

     “You must be joking tun safe har dare kice you’re not hungry?”…

    “I hardly eat!”….

    “Bangane you hardly eat ba, who does that? Come on let’s go to the dining”…..

Batace komai ba ta fita ta bita, haka kawai mutanen suke mata kwarjini, sam bata iya musu musu…..

      “Sit!”….

Umm ta fada tana ja mata kujera a dining….

Ga abinci kala kala a gabanta amma ta kasa tabawa dan dagaske take she hardly eat….. 

      “Are you a vegetarian?”….

Cewar Umm da taga ta kasa taba komai…. 

Girgiza kai tayi alamun no….

     “Are you on diet?”….

Nan ma kada kai ta sakeyi….

     “Toh what would you like to have”…..

Cewar Mami da taga kamar da gaske bata san taci abincin….. 

      “Fruits”… 

Ta fada kamar bata san magana….

 Landline din dake kusa da dining din mami ta kira ta musu bayanin abinda zasu kawo…….

After 10mins aka shigo da katon tray dauke da varieties na fruits ko wanne a ciki bowl, a kalla fruit din ciki zasu kai kala goma…..

Gabanta mami ta nuna musu su ajye, matsar da abubuwan dake kai sukayi kasancewar dining din extra large yana daukan abubuwa dayawa, sannan suka saka mata tray din a gabanta…..

       “Oya eat”….

Mami ta fada tana mata murmushi…. 

Batace komai ba ta shiga tsakuran fruit din tanaci, kadan taci tace ta koshi….

 Girgiza kai mami tayi tace;

     “Haba dear, ki kara mana”…

     “Na koshi”….

Karban fork din dake hannunta Umm tayi ta dauko slice din pineapple tace;

     “Haaa!”…

   “Dagaske na koshi”

Ta fada cikin fuskar tausayi…..

    “Allah in baki bude baki ba zamu bata, bazan kara kulaki ba and I mean it”….

Da sauri ta bude baki dan haka kawai taji bataso matar ta dena kulata, Umm dama akwai shiga rai….

Nan tashiga bata sai bata fuska take tana turo baki, Umm ko a ranta cewa take kyayi ki gama….. 

Saida ta tabbatar ta cika mata ciki da fruit sosai sannan ta kyaleta, cikin tsokana;

    “Ko ke fah? Bakiga har kin kara kyau ba?”…

Bata rai tayi batace komai ba….

      “Au bazaki kulani ba dan na miki dure? Shikenan nima ba ruwana dake”……

Ciki ciki tace;

     “Ni bance haka ba”….

     “Naji, tell me about yourself”…,

    “Zan fadamiki gobe, I’m feeling sleepy now”….

Ta waske da wannan dan bata jin zata iya bude baki ta basu labarin kanta….

    “Ok no prob, jeki kwanta”…….

Mikewa tayi batace komai ba….

      “Goodnight dear”…

Umm da mami suka hada baki gurin fadin haka….

Hannu kawai ta daga musu ta wuce ciki….

   

    “She is indifferent!”….

Mami ta fada tana bin bayanta da kallo….

    “She really is! Kiga fa magana kamar ana forcing dinta, koya suke coping da ita a gida?”….

    “Maybe bata da surutu ne kawai, ni kuma tashiga raina wallahi, yanda kika san ince tayi zamanta a gidannan”…..

     “Ta shiga ranki ko tashiga rai na? Ji nake kamar na tafi da ita UK, jinta nake kamar baby tee wallahi”.

    “Same wallahi, baby tee kam ai talkative ce”……

    “Gaskiya kam, ai kwata kwata yanayinsu ba daya ba”……

     “That’s true!”……

Tinda suka tafi yake zaune going so deep in thoughts, bini bini ya dago ya kalli time yana tinanin abinda sukeyi yanzu, ya sukayi da ita? Ta farka? Taci abinci? Yasan zasu tambayeta wacece ita kuma kila ta fada musu yanda yaga tana hira dasu, ga Umm da mugun siyasa sai ka saki baki kana bata labari baka sani ba, kota musu fashe fashe data farka? Lots of things dai, haka ya cigaba da tinani tinani har aka kira sallar magrib yayi alwala yayi sallah……

Yana idar da sallah ya dora daga inda ya tsaya, wani abune ya shiga fadomasa ya danji tsoro ya kamasa dan yasan tsap zata aikata, kar taje ta gudu daga gidan a sake kai mata hari dan yasan sameer baze bar kasar ba idan ya koma beganta a gidan ba..

Ji yayi inaaa baze iya zama ba dole sai yaje ya ganta koya samu nitsuwa, besha wahala wahala wajan gano hanyar dazebi ya fita ba, dama ya dauko abun a mota, wani powder ne dayake sumar da mutane instantly kamar dai wanda ya sakawa wa’yenda sukayi kidnapping dinsa, shine kuma wanda sameer ya shakawa fatima zainab…….

Saida ya bari dare ya karayi yanda yasan su Mami sunyi bacci dan suna bacci da wuri, yanda ze samu yaje ya ganta batareda sun sani ba tinda sunfara tinanin sonta yake shida bata ishesa kallo ba kawai tausayinta yake ganin mutane dayawa na harinta, bacin wannan he has nothing to do with her…..

Fitowa yayi ya labe ya musu barin powder kamar yanda ya tsara, a take suka sume duka kuma…

 Fita yayi da sauri ya nufi inda yabar motar sameer dama key din na jikinsa, shiga yayi me gadi da besan wainar da ake toyawa ba ya bude masa gate batareda yasan waye a ciki ba…..

      

       Har karfe tara juyi takeyi a gado ta kasa bacci dukda tafi awa daya da cemusu zatayi bacci, sai yanzu take dana sani da bata cemusu zata tafi ba su kuma basu nuna mata komai akan hakan ba, yanzu gashi dare yayi babu abunda yake sata bacci a kusa, gabadaya sai taji kanta na mugun mata ciwo, lokaci daya idonta ya rikide yayi ja jijiyoyin kanta suka tashi, mikewa tayi da sauri tana tinanin mafita dan dole sai tasha abinnan inba hakaba babu kwanciyar hankali komai kuma ze iya biyowa baya, yanke shawarar ta gudu daga gidan tayi deep down tanajin batasan rabuwa dasu amma ina gwara ta tafi ta nemi mafita da tazo tana dana sani daga baya……

Cikin sanda ta fita parlour taga ko ina tsit alamun duk yan gidan sun kwanta, dadi taji tana mamakin yanda suke bacci da wuri kamar ita bada wurin take bacci ba…….

Me gadi ne ya taso da sauri yace;

    “Hajiya wani abun zaa siyo miki ne, ga isa shi ake aika”….

      “No, sako zan karba yanzu zan dawo”…

    “Toh shikenan hajiya a dawo lafiya”…

Batace komai ba ya bude mata gate ta fita….

Tafiya ta hau yi batareda tasan inda ta nufa ba har tazo wani pharmacy dake few walks away from the house ta shiga, ta masa bayanin abinda takeso ya bata, daukowa yayi ya mika mata,ta karba tace;

     “Zan kawo maka kudin gobe”…..

Baya bada bashi amma sai yaji ta masa kwarjini sosai da har ya kasa mata musu yace;

     “Ba matsala hajiya”……

A 360 yake driving saida ya karaso street din su mami sannan yayi slowing down kasancewarsa highly secured area, yanzu sai a taresa ana interrogating dinsa…..

Kamar ance juya yaga kamar ita yake hangowa a cikin pharmacy din dake dan nesa da gidan mami, parking yayi a daidai gaban pharmacy din though bashida tabbacin itace, fitowa yayi ya jingina da motar yana jiran ta fito yagani inba ita bace ya karasa gidan Mami…….

Tinda ta fito daga pharmacy din ya gane itace hakan yasa ya gyara tsayuwarsa tambayoyi fal ransa kan  abinda ya fito da ita a darennan…..

Itama tun kafin ta karaso ta hangosa, saida taji gabanta ya fadi batasan dalili ba, kodai ganin ya hadarai ne oho, ta kuma samu kanta da boye abinda ke hannunta a cikin hijabi, itama ta hade rai tana jin dama akwai wata hanyar da zata bi ta gudu…..

        “Mallam bani hanya in wuce”…

Ta fada tana sake kaucewa daga inda ya tare mata, shi kuma ya kara tare inda ta koma…..

      “Dalla mallam ka bani hanya in wuce, ina ruwanka dani ne?”…….

Be kulata ba saima jewo mata tambaya dayayi;

     “Me kika fitoyi a darennan duk securities din dake gidan mami?”…

     “It’s none of your business”….

Ta fada tana kara boye abinda yake hannunta….

      “Karki sake kimin rashin kunya yarinya, now tell me abinda ya fito dake”…..

       “Ka bani hanya in wuce mallam!!!”….

      “Anki a baki hanyar, in kinga kin bar gurinnan toh kin fadamin abinda kikazo yi ne”….

Dage kafada tayi tace;

     “Toh sai me? Ashe ko zamu kwana anan, dama ba yau na saba kwanan waje ba!”…….

     “Ai nasani sarai, shiyasa ko wani hotel sai an ganki”…..

     “Good you know!!!”….

     “Kehh me kike boyewa ne naga kinata wani kunshe hannu a hijabi, kiyitasa hijabi kamar wata ta Allah”……..

     “Kayi kadan in boye maka abinda yake hannuna wallahi, idan ka gani meka isa kayi toh?”…..

    “Kodai shaye shaye kike dan daga gani babu abinda bazaki aikata ba!”….

Lumshe idanunta dataji suna mata zafi tayi cikin sanyin muryarta dake kasa bayyana masifarta tace;

    “Wallahi kamar ka sani, cocaine ne, ko zaka sha?”..

Zaro ido yayi sosai yace;

    “Kikace meh?”….

   “You heard me right! Babu kalan kwayar da bana sha”……:

     “Dallah rufe mana baki stupid girl kawai! Shiyasa kullum idonki kamar na yan shaye shaye, Ko kunya bakyaji wai babu kwayar da banasha?”…

     “Kunya? Who cares? Karka kuskura ka kara zagina kuma dan wallahi zan maka abinda harka mutu bazaka manta ba”….

    “Ai dama nadade da sanin ke fitsararriya ce, sai kizo kina yiwa mutane sexy voice da seductive eyes duk dan mutum yayi falling into trap dinki ko, irin abinda kike yiwa wayen chan mahaukatan da suke hauka akanki”……

Wata muguwar dariya tayi tace;

     “Ko kai naso yiwa irin abinda nake musu yanzu zakayi falling, try me!”….

    “Oh wow! Bismillah toh!”…

    “Mallam bani hanya in wuce bani da lokacinka!”…

  “Au harkin karaya, where do you think you’re going? Ki rufawa kanki asiri kishiga mota mu tafi kawai!”.,

     “Kawai sai in shiga mota in fara binka bansan ka ba, how is that even possible?”……

     “Ko kishiga da kanki ko in daukeki in saki da kaina wallahi!”…

Ya fada seriously….

Harara ta zuba masa tace;

    “Kai ka isa ka daukeni? You can’t dare do that!”….

Wani mugun dariya ne ya taso masa ya dai maze dan bayaso ta dauka wasa yake, yace;

      “Daukanki na nawa kuma? Ke har abinda yafi dauka na miki yarinya!!”…..

      “In your weirdest dream ba!!!”….

    “Yanzu ze faru in real ki tabbatar in baki shiga motarnan ba”…

Wani killer smile tayi da tagama lissafin yanda zatayi fooling dinsa yanzu yanzun nan, ta kalleshi tace;

     “Naji amma sai dai inyi driving”

    “Hauka nake zan barki kiyi driving? Haka kika kusa kashemu fah?”……

    “Trust me wannan tsautsayi ne but I’m a good driver and I promise to drive gently”…..

    “Hmmm ashe rashin manners din naki iskanci ne, so you can be this sweet?”……

Murmushi tayi batace komai ba….

Bude mata driver seat yayi yace;

    “Toh shiga”….

Shiga tayi ya rufe mata kofar sannan ya tafi ya zagaya seat din me zaman banza ya zauna….

Ya dora hannunsa akan handle din kofar kenan yaga ta figi motar a guje ta bar gurin….. 

Dafe kansa yayi unbelievably yace;

    “She really fooled me, wai ni smart zaayi playing smart?”… 

Sai kuma ya fashe da dariya yace;

      “kingudu baki tsira ba yarinya there’s a tracker in the car!!!!”

Domin karanta cikakken littattafin sai ku danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇👇

https://www.aihausanovels.com.ng/2022/12/wace-ce-ita-chapter-17-complete-novel.html

👆👆👆👆

Back to top button