Description/Story:
A Sanadin Makwantaka Book 2 Complete Hausa Novel Document Written By Zee Laluh
Description
Wani mugun bugu kirjin Fatuu ya fara yi tamkar ana mata luguden ta6are ganin abunda ke faruwa ta cikin glass d’in hannuwanta har wani kerma suke saboda tsabar rud’ewa da razana don abune wanda bata ta6a ganin Haisam d’in yayi ma wata Mace ba tunda take dashi, lokaci guda ta tambayi kanta wacece wannan? Kasa jurewa tayi ta bud’e Motar ta fita ta tsaya a jikin kopar tana k’are mata kallo can ta furta “AUNTY FANAN…..!” yadda ta furta da matukar razana, Ji tayi sam kafafunta suna niyyar kasa daukarta saboda kermar da suke yi ga wani irin bugu da kirjinta keyi mata saboda tsabar razana, tambayar dake ta faman kai kawo acikin zuciyarta itace, mike tsakanin Ya Handsome da Fanan da har yake mata hakan? Ko k’annanshi da suke uwa d’aya uba d’aya bata ga yana masu hakan ba sai ita da take Cousin d’inshi, to ko dae dama soyayya suke da ita ne? Damm! k’irjinta yay mata wani Mugun bugu yin wannan tunanin lokaci guda kuma taji fitsari ya d’aure mata mara yana niyyar zubo mata da sauri ta nufi gida ko kopar motar bata rufe ba ga wani duhu da take gani da kyar ta shiga gidan don har wani jiri jiri take gani tsabar rud’ewa da kuma fargaba, toilet ta shiga tayo fitsarin tana fitowa ta nufi d’akinta ko ta kan ta duba gwaggo bata bi ba tana shiga ta fad’a saman gadonta ta duk’unk’une wuri guda sai faman zare ido take……..
Nufar gaban Motar sukae hannunsu cikin na juna Fanan ta kalli wadda ke a mazaunin driver itama da gani hutu ya zauna mata duk da ba fara bace irin fatar jikinta za’a iya kiranta da chocolate fuskarta lumi tana da kyau ba laifi, da Murmushi Fanan tace “Khairat meet mah Babe” itama Murmushin take ta mik’o mashi hannu tace “Hi Haisam it’s nice meeting u” aikuwa da sauri Fanan ta ka6e hannun tace “he don’t do dat” dariya sosae khairat d’in tayi dama tsokanace kawae ba wani abu ba don tasan irin Mugun son da take ma Haisam dole ne tai kishinshi sosae, gaisawa sukai da haisam tace “so ga heartbeat d’inka na kawo maka sai a bani tukuici” fuskarshi da Murmushi yace ta fad’i abunda take so tace “bawani abu babba nike so ba just babynka zaka kawo man ta kwana gidanmu don nayi ta kwanan man but she refused” kallon Fanan d’in yay ta d’an yamutsa baki ta girgiza mashi kai alamar bazata je ba ta kwantar da kanta a shoulder d’inshi, khairat tace “so now da babe d’inki ke gefenki shine zaki gujeni ko, it’s owk zamu koma india inda zan rama ne” k’ayataccen murmushinta mai k’ara mata kyau sosae ta saki tace “kar ki damu Babe zai kawo ni in spending day” yar harara ta wurga mata tace bata so tana kokarin tashin Motar Fanan na d’aga mata hannu tace sai sunyi Magana daga haka taja ta tafi, wani kallo mai wuyar fassarawa yayi mata ta nok’e kai tana dariya har jerarrun hakoranta farare tass suka bayyana yace “Why baki sanar dani about your coming today?” cikin muryarta ta yan gayu tace “am so eager to see u babe shiyasa na baka huge suprise” ta k’arasa Maganar tana kashe mashi ido, hannu ya kai yaja dogon hancinta tayi yar k’ara yace su shiga ciki har zasu juya tace mashi Zarah fa Hajiya ta gaya mata sun fita outing tare sai lokacin ma ya tuna da Fatun na acikin Motar har ya juya ya hango kopar a bud’e ba tare daya kawo komae ba yace yana tunanin ta shiga gida ma, still hannunsu na cikin na juna suka nufi Motar tace ya zagaya d’ayan side d’in ita ta shiga side d’in driver tajasu suka idasa gidan bayan Officer CD ya bud’e masu gate, bayan sun shige ya rufe gate d’in ya dawo kan bencin daya tashi ya kalli d’ayan Officer yace “ita wanccan d’in wacece wai, ba itace naga dazun an kawo a jeep d’in nan ba?” yace mashi “eh itama jikar Hajiyarce baka ganin kalanta na zuwa”
“Itama ta wurin Hajiya Maryam d’ince kenan?” kai ya d’aga mashi alamar eh yace “Ma sha Allah amman duk tafi yan uwanta kyau gaskiya ni ban ta6a ganinta ba sai yau” Officer ya amsa mashi da eh ai bata cika zuwa ba kuma yanzu tana karatu a kasar waje ne,
tana ruke da hannun Haisam suka shiga falon Hajiya lokacin tana zaune kan kujera tana kallon tv, Fanan ce tayi sallama hajiya ta maido idonta kansu tana kallonsu da Murmushi suka nufi 2 seater suka zauna Hajiya tace “ina ta nemo ka” yana Murmushi yace “mun dawo ne”
“Ai ce man tayi in ta raka k’awarta bazata shigo ba har sai ta nemo ka wai,nace to Allah ya bada sa’a da yake ma akwae gidajen radio isassu maji cigiyarta in an tsinceta” d’an kallon fanan d’in yay still murmushi take kanta a saman kafad’arshi Hajiya taci gaba “sai kawae ganinta nayi kaman daga sama fa ni abun mamaki ma ya ban har saida na kira uwar tata nai mata korafin baza’a sanar mutum zai zo ba a shirya masa take ce man wai ita ta hana a sanar mana tana so ne ta bamu mamaki nace aikau ta bamu mamakin gashi tazo ma tak’i cin Abinci wai sai kazo zaka bata a baki nace ai sai taita jiranka tunda ita ba ranar da zata girma da hakan” shidae Murmushi kawae yake can ya mik’e ya d’agata ganin zasu nufi Dining area yasa tace mashi “but Babe u need to take bath ka dawo daga wani wuri nasan ka gaji” girgiza mata kai yay suna nufar dining table d’in yaja kujera ya zaunar da ita yace “eat first” yaja kujeran gabanta shima ya zauna k’in ci tayi wai sai dae ya bata a baki tayi missing hakan dole a bakin ya rink’a bata cike da kulawa, bata wani ci mai yawa ba tace ta koshi yace bai yarda ba tace ai ta d’an ci agidansu khairat tunda acan suka fara sauka sannan ya kyaleta, k’ara kama hannun juna sukai suka nufi cikin Falon zasu fita yace ma Hajiya zaije yay wanka tace to,ganin zasu fita tare tace ma Fanan bazata jirashi ya dawo ba ta mak’e mata kafad’a wai zata je ta za6ar mashi kaya ne, d’an ta6e baki Hajiyar tay tace adawo lafiya.
Jama’a ina Fatuu???
Tunda ta kwanta bata mik’e ba sai faman sak’e sak’e take aranta ga wata irin fargaba data mamayeta ,fitowa gwaggo tay daga dakinta idanunta suka sauka kan takalman Fatuu dake ajiye a bakin kopa da mamaki aranta tace wannan ai takalman da Fatuu ta fita dasu ne ta dawo ne, nufar d’akin tayi tana kwala mata kira tana jin muryar gwaggon ta rufe fuskarta da gyalenta dake yashe gefe yabar saman kanta, d’aga labulan tayi ta hangota a kwance har lokacin da mamaki akan fuskarta ta kira sunanta amman bata amsa ba har saida ta k’ara kiranta sannan ta amsa tace “yaushe kuka dawo ne?” daga yadda take tace “yanzu ba dad’ewa Kawu shi6ado na gaidaki sun bada sak’on dawon Fura da Nono ma akawo maki yana Mota” da kyar take Maganar hakan yasa gwaggon cewa “To lafiya kika wani dukunkune saman gado?” shiru ta d’anyi tana tunanin abunda zata ce mata can tace “banjin dad’i ne kaman zazza6i zai kamani nike ji shiyasa ma dana shigo ban maki Magana ba” shiru gwaggon tayi tana k’are mata kallo kafin tace “ina shi yayan naki yake?”
“Muna dawowa yaga sun yi bak’i ya tsaya wurinsu shine ni kuma na shigo” jinjina kai tayi tace “halan kinyi wasa da ruwa ne ko, nasan halinki sarai baki ganin ruwa ki k’yale” sai lokacin ta cire gyalen fuskarta ta bayyana ta kalli gwaggon tace “a’a wllh ai Ya Handsome bazai barni ba kawae dai banjin dadin jikinne”
“To Allah ya sawake ki tashi kici Abinci sai kisha Magani” tace “na k’oshi da Abincin bari dae insha maganin kaina ciwo yake man sosae” tana gama Maganar ta saukko daga gadon da k’yar ta tunkari kopa gwaggo ta saki labulan ta koma d’akinta ta d’aukko mata Maganin ta fito ta bata, ganin yamma tayi sosae yasa tace ta shiga Falo ta zauna Magriba ta kusa ba’ason kwanciya a irin wannan lokacin in tayi Salla sai ta kwanta tace mata to.
Some Of Related Hausa Novels
Be With Us
-
- Follow our Facebook Page : Ai Hausa Novels
- Follow our Twitter Page : @ Ai Hausa Novels
- Follow our Youtube Channel: Ai Hausa Novels
Download A Sanadin Makwantaka Book 2
Proceed with your download by clicking the below button👇👇
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.