Hausa novels

Asanadin Makwabtaka Book 2 Page 28 Complete Novel

*ASM Bk2028*

 

_Destiny may be delayed but cannot be changed…._

 

 

*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*

 

 

 

 

 

………Bin Khalid da ido Mahaifiyar shi tay har ya fuce fuskarta d’auke da d’an murmushi a ranta take ayyana in ba don yarjejeniyar dake tsakanin shi da Mahaifin shi ba tasan ba yadda za’ai ya yarda da wannan Auren had’in saidae ta wani 6angaren taji dad’in hakan don rashin Auren nashi na damun su tana fatan kuma ya zama silar canzawar shi. Bayan Fatuu ta gama breakfast d’in gyara d’akin ta fara yi yadikko na ta bari tace zatayi, sosae ta gyara su Mino duk sun tafi Makaranta tun kafin ta farka da sun nuna basu zuwa yadikko ta ce in dae don Adda d’in tasu ne ta zo kenan Saboda a garin zata zauna a cikin gidan Gonar Chairman shi kan shi yana zuwa Hutu da iyalan shi wani lokacin amman Khalid d’in ya fi su zama a gidan, bayan sallar Azahar Fatuu tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atampa da sukai mata cif a jiki dama duk haka kayanta suke sai yan k’alilan d’in dogayen riguna, ganin ta shirya yasa Yadikko matsa mata kan ta daure taje ta gaishe da su Ard’o da Yaya ba don ta so ba ta yafa mayafi mahad’in kayan ta tafi, a nutse take tafiya ta shiga shashen Yaya lokacin da ta shiga ba kowa a filin wurin sai su K’anwar Altine dake wanke wanke a gefe, kallonsu kawae tay ta wuce kaman daga sama taji sun sa Dariya k’anwar Altine tace ma d’ayar mai suna zakiyya “Yar uwata ki bar wani yanga da ji da kai wai ke zaki auri mai kud’i duk fa munsan kalan mijin da zaki Aura” Fatuu na jin hakan ta dakata don sai taji tana son jin wani irin miji ne zata auran dama kuma da biyu suke Maganar shiyasa ma suke yi da hausa,

 

Zakiyyar tace “Bai kamata fa in rink’a yanga ba kuka yakamata in yi zan auri mashayi wanda har giya yake sha ya shigo gari yana niyyar taka mutane da Mota” sosae k’anwar Altine ke dariya kafin tace “dama iya hakan ya tsaya ai da sauki kin manta da d’ayan aika aikar da kowa yasan yana yi….” Da sauri zakiyya tasa hannu ta rufe mata baki tana fad’in kada aji mutuwar sarki a bakin su, wata irin mutuwar tsaye Fatuu tay mi take ji haka game da wanda zata aura, Mashayi kuma! Kuma miye d’ayan abunda yake aikatawar, a hankali ta juya ta kallesu sai tik’ar dariya suke suna kashe wa, wani irin nauyi k’afafunta sukae mata taji tamkar bata iya taka su ga jikinta tamkar ana zare mata laka take ji da k’yar ta daure taci gaba da tafiya, lokacin da ta je kopar d’akin Yaya ji tay kaman ta koma kawae ganin takalma tasan ba ita kadai bace da wasu mutanen kuma a halin da take ciki tsoron k’ara jin wani abun da zai iya tarwatsa mata zuciya take sanin sun iya ya6a bak’ar Magana, shahada kawai tay ta cire takalmanta ta shiga da yar sallama duk mutanen cikin d’akin suka d’ago suna kallonta hakan yasa ta sadda kanta duk suna zaune a k’asa su hud’u sai Yaya d’in na zaune a bakin k’aramin gadon k’arfe idon ta akan Fatuu har ta k’arasa gefenta ta tsaya, d’aya daga cikin Matan ta mik’e tana fad’in bari ta bata abun zama tasan yan birni basu zama a k’asa, darduma ta shimfid’a mata Fatun ta hau ta zauna tay shiru kaman bazata ce komae ba can ta d’aga ido a hankali ta gaishe da Yayar dake ta faman bin ta da ido, d’an ta6e baki tay tace “Amarya Sai yanzu aka ga damar zuwa gaishe dani kenan” shiru bata ce mata komae ba innar su Altine tay yar dariya tace “Yaya kin san Amaryar ta Manyan Mutane ce” d’an guntun murmushi yayar tay tace “haka fa ai na manta mune ma Yakamata muje mu mik’a gaisuwa, an zo lafiya Amarsu?” K’asa k’asa tace lafiya lou, innar su Altine tace “to muma bari mu mik’a gaisuwa ga Amaryar manya, ina wuni Amarya an zo lafiya?” Kafin Fatuu ta bata amsa wata tace “aikuwa saidae mu d’in mu gaishe da itan tunda Yaya ma da k’yar ta samu gaisuwar ballantane mu” ita dae Fatuu shiru tay masu can Yaya tace “sai kuka ji abun arzik’i kwatsam abun farinciki, ai dashi Baffan naki har zai maki bakin ciki Allah ya baki miji d’an Arziki muka dage kai da fata tunda da Arziki a garin wasu ai gara a naku a gidan ku ma, ko ba haka ba?” Banza Fatun tay mata ita dama tasan duk zugar Su ce tasa Ard’o ya tursasa ma Baffanta kan Maganar, tsam ta mik’e tace masu sai anjima Yayan na ba ta bari tasha ruwa ko don kar su je gidanta suma ta basu, bata tanka ta ba ta yi wucewarta tana jiyo yadda su innarsu Altine ke dariya suna fad’in ai kuwa dole a basu ruwa harda Naman kaji ma su da sukae ruwa sukae tsaki za’a auri mai Arziki, bayan fitar ta wata mai suna Hasiya ta kya6e baki tace “Sai wani d’aure fuska take don a ga bata so” a harzuk’e Yaya tace “aikuwa ko mutuwa zata yi sai an yi auren nan badae ita ga mara d’a’a ba bata ganin kowa da gashi an d’aure mata wutsiya ta raina kowa dama nace sai nayi maganin ta ai shiyasa Ard’o na yin Maganar Auren ta da d’an gidan chairman d’in na nace sai abun ya yuwu, inda lafiya lafiya ai wllh cikin yaran ku zan sa wata ta Aure shi a k’yaleta to amman gwara ita ta aure shin yadda zata kwashi kashin ta a hannu waye bai san rashin Mutuncin d’an gidan Chairman ba Mutumin dake taka kowa yadda ya ga dama kinga daidai da ita kenan sai taje tayi mashi rashin kunyar da ta saba ma Mutane” kyalkyacewa da dariya innar su Altine tay tace “ya kuwa sassa6a mata kaman ni wllh, wannan wa zai so yaron shi ya aure shi banda shaye shaye ga lalata yaran Mutane yanzu ji bi yarinyar nan Danejo yadda ya d’irka mata ciki hankalin shi kwance k’arshe kuma ya zubar mata tak’amar shi likita ne” Hasiya ta amshe “yo ai ba itace farko ba mata kala kala yake kawo wa a gidan Gonar nan aka ce harda arna” haka suka cigaba da tattauna mugun nufin su kan Auren Fatuu. Har wani duhu duhu take gani ta nufi sashen su lokacin da ta shiga falon su Mino ne zaune suna cin Abinci hakan yasa ta wuce cikin uwar d’aki ba tare data tanka ma kowa ba, Mino na kiranta ko jin ta bata yi ba, tana shiga ta haye saman gado can k’arshe tayi rubda ciki tana numfashi da k’arfi da karfi tana zare ido waye wanda za’a aura mata? Da gaske mai shaye shaye ne? Ita da a rayuwarta ta tsani mashayin mutum shine yanzu zai zama mijinta, shin miye d’ayar aika aikar da taji su zakiyya sun fad’a? Tana haka Mino ta shigo ta zauna a bakin gado tana kallon Fatuu ganin tak’i ce mata komae yasa a sanyaye tace “Adda Fatuu” shiru bata amsa mata ba bata kuma kalleta ba Mino ta sake cewa “Adda Fatuu miya faru kin yi shiru?” Sai lokacin ta kai idonta kanta amman still ta kasa tanka mata ganin hakan yasa ta mik’e ta fita bada jimawa ba sai gata sun dawo tare da Yadikko, a bakin gadon ta zauna ta kai hannu ta ta6a jikin Fatun da harshen fulatanci ta shiga tambayarta lafiya Mike damunta can ta yunk’ura ta tashi zaune idonta akan yadikko cikin karyayyar Murya tace “Don Allah waye za’a Aura man??” Da mamaki yadikkon tace “dama Baffan ki bai fad’i maki wanda zaki Auran ba?” da sauri tace “Ya fad’i man d’an Chairman ne amman ina son ki fad’a man wane irin Mutum ne?” Dam k’irjin yadikko ya buga ta hau had’iye miyau ganin ta kafe ta da ido alamar jiran amsa take yasa tace “Mutum ne kamar kowa kuma likita ne….” Katse ta Fatuu tay “ba wannan nike son sani ba wane irin hali gare shi?” Shiru yadikkon tay tana kallon Fatun ganin haka yasa tasa mata kuka ta kama hannuwanta tana fad’in “ki fad’a man yadikko don Allah da gaske Mashayi ne?” Zaro ido tay cikin rawar murya tace waye ya fad’a mata hakan nan take ta kwashe firan da ta ji su zakiyya nayi ta fad’a mata, shiru bakin yadikko ya mutu don bata san mi zata ce mata ba Fatun ta hau rok’onta kan ta fad’a mata, juyawa yadikko tay tace ma Mino da ke yin hawaye ta fita ta ce to, bayan ta fita yadikko ta juya kan Fatuu ta kama hannuwanta tace “haka ake cewa amman ni ban san ko gaske bane tunda ban ta6a gani da ido na ba na dae san shi tunda yana yawan zama nan gidan Gonar bayan ya gamo karatun likitancin da yayi a K’asar waje…” Tun kan ta rufe baki Fatuu ta tari numfashin ta “to bayan shi naji sun ce akwae wani abun da yake aikatawa miye?” Wani abu Yadikko ta had’iya a ranta take raya taya zata ce mata yana neman Mata ko shaye shayen ta san da gaske yana yi don kada ta tada mata hankali ne yasa ta nuna mata bata san ko gaske bane, ganin tayi shiru yasa Fatuu d’an girgiza hannunta tace “Yadikko ta don Allah kar ki 6oye man ki fad’a man” sauke ajiyar zuciya tay cikin rawar murya tace “k…kin gane w..wai ana zargin yana neman Mata ne a gidan gonar da yake zama…..” Zaro ido Fatuu tay a kidi’me tace “Neman Mata kuma kenan Mazinaci za’a Aura man!!” ganin yadda ta rud’e yasa da sauri yadikkon tace “a’a fa kawae ana zargi ne wai ana ganin shi da mata amman kuma ai zai iya yuwuwa Abokan aikin sa ne tunda ba wanda ya ta6a shiga ya kama su suna aikata ba daidai ba kinsan irin Wannan baka saurin gasgata wa” girgiza kai Fatuu ta shiga yi cikin kuka take fad’in “ai yadikko in dae aka cika Maganar abu to tabbas akwae alamar gaskiya, mi zai sa ya rink’a zuwa da mata gidan gona in Abokan aikin nashi ne suyi aikin acan wurin aikin su mana, ni dae na bani na lalace k’arshe na ya zo za’a lalata man rayuwa taya zan yi rayuwar Aure da Mashayi kuma Mai neman mata, Ya akai Baffana ya amince a jefa man rayuwa cikin had’ari yadikko ya akai kuka amince bacin kun san halin shi haka yake so kuke ya lalata man rayuwa ne??” Itama Yadikkon kukan ta sa tana fad’in “a’a Fatuu kar ki ce haka Don Allah kin fi kowa sanin yadda muke son ki muka damu da rayuwar ki hakan ne ma yasa lokacin da Ard’o ya sanar da zancen Auren naki Baffan ki ya shiga mawuyacin hali har yay sanadin kwanciyar shi ciwo duk Saboda jin Mutumin da za’a aura maki k’arshe dae har zuwa yay wurin Chairman ya rok’e shi kan a hak’ura da had’a ku Aure koda ya tambaye shi dalili bai 6oye mashi komae ba game da halin yaron nashi da ake fad’a kuma ya nuna mashi ke karatun likita kike son yi anan ya nuna mashi ya kwantar da hankalin shi in dae wannan ne damuwar shi to saida ya tabbatar da d’an nashi ya shiryu ya daina komae sannan kuma har yarjejeniya sukae kan ko bayan auren ya kama shi yana aikata wani abu ba daidai ba sai ya sa6a mashi don dama a bisa sharad’i ya nema masa auren kuma ya tabbatar ma Baffan ki cewa da kunyi auren zaki cigaba da karatun ki don ya fahimci kina da kokari sosae tun lokacin da ya fara ganin ki tun sannan yaji kin burgeshi har yayi sha’awar D’an nashi ya aure ki, wannan ne dalilin da ya sa har Baffan ki ya gamsu sanin chairman d’in Mutumin Arzik’i ne ba zai ta6a had’a aurenku don son zuciya ba” shanye kukan Fatuu tay sai taji hankalin ta ya d’an kwanta ganin haka yasa Yadikko cigaba da lallashin ta tana k’ara kwantar mata da hankali had’i da nuna mata wani abun da biyu suka fad’a dama don su tada mata hankali su k’untata mata, ganin ta d’an samu natsuwa yasa ta d’agota ta tambayeta taje ta gaida Ard’o ta girgiza mata kai alamar a’a ta ce to ta daure taje in Baffanta ya dawo yaji bata je ba bazai ji dad’i ba a sanyaye tace to ta sauka daga saman gadon ta fita idon yadikko akan ta cike da tausayi take kallonta tana d’an girgiza kai. Koda taje iske shi tay da Mutane hakan yasa ba yabo ba fallasa ta gaishe su ta juyo ta dawo ta koma kan gado tay lamo. Sai bayan Magrib Baffanta ya shigo d’akin lokacin duk sun gama salla suka gaishe shi da fara’a ya amsa kafin ya zauna a nan yake sanar da yadikko game da zuwan wanda Fatun zata Aura gobe in Allah ya kaimu da yamma ta amsa da to ya nuna mata k’atuwar ledan da ya shigo da ita yace ga cefane nan sannan a yanka kaza ayi amfani da ita wurin shirya mashi Abinci ta amsa da to Fatuu dae tay tsit kanta a k’asa don wani irin bugu kirjinta ke mata jin wanda aka ce zai zo d’in, ganin yanayin ta yasa Baffan tambayar ta lafiya ta d’ago da d’an murmushi tace mashi lafiya lau daga baya ya fita, da daddare bayan ta kwanta duk kewar gwaggo ta dame ta don har yanzu basu yi waya ba can ta d’auki wayarta ta kirata tana jin ta fara ringing ta tashi zaune har kiran ya kusa katsewa bata yi picking ba har Fatun ta fidda ran zata d’auka sai gashi gab da zai tsinke ta d’aga tay yar sallama wani kalan lumshe ido Fatuu tay da d’an murmushi ta gaidata gwaggon ta amsa mata suka d’an yi shiru can gwaggon tace “anje lafiya, koda yake mun yi Magana da Kamalu yace kun isa lafiya” Fatun ta amsa mata da lafiya lau daga haka tace mata ta kwanta sai da safe bata jira cewarta ba tay cutting kiran, cire wayar tay daga kunnanta ta bita da ido kawae.

 

Washe gari tun bayan da ta gama gyara d’akunan da suka gama karin kumallo wanda bata wani ci sosai ba ta yi wanka tasa doguwar riga ta haye gado, tana kwancen yadikko ta shigo ta zauna gefen gadon da d’an murmushi tayi mata sannu a hankali Fatuu ta amsa mata da yauwa yadikkon tace “Dama shawara nazo tambaya ku yan birni kun fi mu sanin kalolin Abinci masu dad’i wanne kike ganin ya kamata ay ma bak’on naki” shiru Fatuu ta d’an yi sai kuma cikin sanyin murya tace “Yadikko kema ai kin san Abincin masu dad’i ko” yar dariya tay tace “to ai duk na manta zuwa yanzu kuma ai nasan akwae wasu iri iri da ni ban sani ba” kaman bazata ce komae ba ganin yadikkon na kallonta yasa tace “ba naji Baffa yace a yanka kaza ba kawae ayi mashi pepper chicken ba sai anyi wahalar yi mashi wani Abinci na daban ba” shiru yadikkon ta d’an yi alamar tunanin sai kuma tace “amman kina ganin shi kawae ya isa, kamar da Abincin zai fi nike gani” d’an ta6e baki Fatuu tay tace “ai ba lalle fa yaci Abincin ba fa in aka yi wannan d’in sai a had’a mashi da fura sai in ga ya isa” cike da gamsuwa yadikkon tace hakan yayi ta mik’e Fatun ma ta yunk’ura zata tashi tace mata tay kwanciyar ta zasu yi komae dasu Mino daga haka ta fita, komawa tay ta kwanta don duk jikinta a sake yake ga fargaba had’i da zullumi da suka mata yawa, Bayan sallar Azahar Baffan ya dawo ya kawo Drinks masu sanyi yace ma yadikko tasa wanda za’a bashi cikin cooler sauran sai su sha tayi mashi godiya, koda Fatuu tay salla komawa tay ta kwanta da aka mata Maganar Abinci cewa tayi ba yanzu ba saida Yadikko ta matsa mata sannan ta d’an tsakura kad’an, ganin har k’arfe ukku tana kwance yasa Yadikko ta shiga tayi mata Magana kan ta tashi ta shirya kar yazo kuma bata kimtsa ba, zuru Fatuu tay mata har saida ta k’ara mamaita abunda tace Matan sannan tace ba sai ta shirya ba ai tayi wanka d’azun,

 

“To ki tashi ki canza kaya ko” tsuke fuska tay idanunta har sun kawo ruwa ganin haka yasa yadikkon fara rarrashin ta ta shiga nuna mata in tayi shigar kirki hakan zai sa ya mutunta ta amman in taje mashi a yamutse zai iya raina ta, da k’yar ta tashi don ta shiryan, wanka tayo lokacin an fara kiran la’asar hakan yasa ta d’auro Alwala saida tay salla sannan ta fara kokarin shiryawa tama rasa wane kaya zata saka can dae ta fiddo wata straight gown ta Maroon lace da touch d’in golden ta saka ta sa yan kunnan zinarin ta da yan hannu tana cikin shiryawa ta jiyo Muryar Kamalu a Parlor yana fad’in “Yadikko ga bak’on nan ya iso” ta amsa mashi da to ta mik’e tana tambayar yana ina ne yace mata yana a Fadar Ard’o, shigowa tay cikin uwar d’akan ta iske Fatuu zaune a gefen gado ta rafka tagumi itama ta zauna gefenta ta dafa Shoulder d’inta tace “bak’on naki ya iso Fatuu” kallonta tay ta fara d’an ta6e baki alamar zata fara kuka yadikko ta girgiza mata kai tace “Don Allah Fatuu ki yi hakuri ki fawwala ma Allah komae, shi mai ji ne kuma mai gani yafi kowa sanin halin da kike ciki don haka ki dogara da shi na tabbatar zai baki mafita ya za6a maki abunda yafi Alkhairi gare ki” d’aga mata kai tay ta kama hannunta ta mik’ar da ita, gaban mirror ta kai ta tasa ta ta shafa powder har jan baki tace ta shafa amman ta k’i tasa lip glow kawae yadikkon ta gyara mata d’aurin kallabin ta ya zauna sosae gashin ta dama ta lankwasa shi ya fito yay tum a baya, golden brown gyale mahad’in kayan ta yafa haka takalma ma sosae tay kyau duk da ba wani make up tay ba, tun da ta fito ta nufi hanyar soron k’irjinta ke bugu tamkar ana mata luguden ta6are hakanan take jin tsananin fargaban zuwan ganin abun take kaman almara ba gaske ba wai wurin wanda zata Aura nan da sati biyu zata je, da yar sallama ta shiga lokacin da ta k’arasa ko cire takalman k’afafunta bata yi ba tun a bakin kopar kamshin turaren da ya baza a jikinshi ya d’aki hancinta, a d’arare ta idasa shiga idonta a kan shi yana zaune akan kujerar da Ard’o ke zama ya sadda kanshi yana latsa wayarshi yana sanye da shadda brown wanda ta hau da fatar jikin shi sosae anyi mashi irin fav d’inkin Haisam wato senator style saidae basu amshe shi kaman yadda suke amsar jikin Haisam ba don yanayin halittar jikin ba d’aya ba, bai sa hula ba hakan ya bayyanar da sumar shi dake a lallank’washe hannunshi sanye da brown wrist watch, ba laifi shigan tay kyau kana ganin shi kaga wayayyan d’an boko, tsaye tayi daga d’an can nesa bayan ta shigo tana kallon shi tana haka su Mino suka shigo da kayan Abinci suka nufi gaban shi suka aje had’i da gaishe dashi kaman bazai amsa ba sai kuma yace “lafiya” ba tare da ya d’ago ba balle su samu Arzik’in kallo suka juya suka fita, sun d’auki lokaci a haka sai da ya mula ya sha iska sannan slowly ya d’ago ya sauke mayatattun idanunshi tamkar na mai jin bacci akan Fatuu dake tsaye a gaban shi, kallo suka bi juna da shi tun bayan da ya d’ago Fatuu ke mashi kallon sani hakanan taji kaman ta ta6a ganin shi to amman a ina? Shine abun da take son ta gano, wani irin jarababben kallo yake bin ta dashi from head to toe tsam ya mik’e walking slowly toward her, a gabanta ya tsaya har saida Fatun tay stepping back Saboda yadda ya k’ure mata, a hankali ta kai idanunta kan fuskar shi lokaci guda k’irjinta yay wani irin bugu tuna inda ta ta6a sanin shi d’an buda ido tay sai kuma da sauri ta sadda kan ta kasa,

 

“Why am I having d feeling dat I know u somewhere??” taji husky voice d’in shi ta fad’a wato shima ashe yaji ya santa wani wurin, K’in d’agowa tay gaban ta naci gaba da fad’uwa wani irin mugun tashi hankalinta yay ganin shi matsayin Mutumin da zata aura, “Hey!” taji ya fad’a da d’an d’aga Murya a hankali ta d’ago duk ta kame kanta sai zare ido take ya k’ara kankance idon shi yana kallon ta da alama so yake ya tuna inda ya santa can bayan d’an lokaci kawae sai gani tay yay wani kalan murmushin mamaki ya d’an kya6e baki kafin ya furta “Wonders Shall Never End, so u’r My Wife to be!!!” bin shi da ido kawae take sai faman sakin Shu’umin Murmushi yake………

.

Asanadin Makwabtaka Book 2 Complete Novel Txt

Back to top button