Halysaah Page 65 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 65…Ajay ya ajiye wayar hannunsa bayan ya ga abinda google ya bayyana masa a matsayin ribbon, kamar zai sake kiran Jay kawai ya fasa ya ja tsaki ya jingina da gadonsa kalmomin Jay na ci gaba da yi masa yawo a kai, sai kuma ya kalli kofar dakinsa don har sannan Khaleesat bata dena knocking continuously ba, kamar bazai tashi ba sai kuma ya tashi daga karshe ya nufi kofar, bude kofar yayi fuska daure yana kallonta without saying anything, ta ɗan koma baya taki barin su hada ido a hankali tana wasa da fingers dinta tace “Don Allah dama gida nake son ka kai ni pls….” Ya dakatar da ita yace “Sai na kai ki? Baki san hanyar gidan ba, ko ni na kawo ki?” Ta daga kai ta kallesa ta ma rasa abinda zata ce, ya wani murtuke fuska yace “Ni ba Jay bane da kike ma iskanci iri iri kina controlling din sa” Juyawa tayi a hankali ta bar bakin kofar yayi banging kofarsa ya kulle, ya koma ya dau wayarsa har yayi dialing number Jay sai kuma ya katse kiran ya ja tsaki, Khaleesat na komawa dakin da take ta dau handbag dinta da wayarta sannan ta fita daga dakin, tana tafiya a hankali ta sauka downstairs ta nufi kofar fita daga babban parlon sai taga kofar a kulle, duk kokarin da tayi na ganin ta bude kofar ta kasa budewa gashi bata ga makulli a jiki ba, ta fi minti biyu tsaye bakin kofar tana jin tana flow a hankali, ta juya ta kalli hanyar sama, komawa tayi tana tafiya kamar bata so ta nufi bangarensa, jingina tayi da bango kamar bazata kwankwasa kofar ba sai kuma dai tayi knocking din kamar tana tausayin kofar, Ajay da har ya kashe wutan dakinsa ya kalli kofar babu ko kiftawa, sai kuma ya gyara kwanciyarsa bai motsa daga inda yake kwance ba, Khaleesat ta fi minti biyar bakin kofar bata kuma fasa knocking din da take ba, cire Duvet din jikinsa yayi ya jefar gefe sannan ya sauka daga kan gadon fuska daure ya nufi kofar ya bude yana kallonta at the same time cutting her a serious warning yace “Ki ka sake knocking din min kofa zan maki walakanci wallahi, why are you such a nuisance? Pls get out before i loose my temper” Khaleesat dake kallonsa ta wani hade rai tace “To ta window kake son in fita daga gidan bayan kofar parlon a kulle yake??” Yace “Ki bi ta roof ma ba window ba” Yana fadin haka zai kulle kofarsa tayi saurin shiga cikin dakin kamar zata fashe da kuka ta nufi tsakar dakin ta tsaya tace “Kasan dalilina na cewa zan tafi gida ne? Kawai kayi ta ma mutum masifa baza ka tsaya kayi considering dinsa ba ka basa listening ears, kawai haka nan zan taso cikin daren nan in ce zan tafi gida? Ni ban ce sai kai ka kaini ba ka zo kawai ka bude min kofa inyi tafiyata….” Magana take amma gaba daya hankalin Ajay na kan dakinsa da ta shiga kai tsaye, he look shock irin he didn’t see that coming, he ignored her ailment that he understood immediately, ya ɗan yi calming din kansa yana kallonta yace “Saboda kin ga ranan ya shigo dake nayi persuading kaina ban yi reacting ba sai kika yi zaton public room ne wannan? An gaya maki ko shi Jay din yana shigar min daki anyhow? Baki da hankali ne or are you out of ur mind? Come and get out before u push me to the wall, kuma kar ki kuskura ki taka min carpet dina da wannan kafafuwan naki, wannan filthy dakin da kika shiga kika kwanta duk ƙura da datti common sense dinki bai gaya maki ki share dakin ki goge ba sannan kiyi changing bedsheet, sannan zaki shigo min daƙi ki kakkabe min duƙ kuran da kika kwasa a jikinki ki cuceni, plss come and get out before i loose my temper….” A fusace ya kare maganar yana kara bude mata kofa da kyau ta yanda zata zo ta fita, Khaleesat ta wani taɓe baki tace “To ai sai kaje ka bude min kofar parlor” Tsawa yayi mata yace “Baza ki fice min daga daki ba?” Ta fashe da kuka ta nufi kofar tace “To kasan me yasa zan je gida ne, ko ba saboda urgent issue bane” Yace “Ke kika san urgent issue din, get out of my room” Ganin he is damn serious don gaba daya mood dinsa ya canza tun da ta shiga dakin yasa ta fita daga dakin tana kallonsa tace “Don Allah ka bude min kofar parlon before it’s too late” Banging kofar dakinsa yayi ya kulle, Khaleesat ta dinga kallon kofar, after a minute sai gashi ya fito, ya saka takalmin da yake yawo da shi a gidan, ta bi sa da kallo sai kuma ta bi bayansa tana hararansa, downstairs ya sauka ya tafi ya bude mata kofar parlon, tana tafiya a hankali ta karasa bakin kofar sannan ta fita tana kallonsa, kulle kofar parlon yayi, Khaleesat taji wani sanyi don iya Hijab ne jikinta babu rigar sanyi, walking slowly ta fita daga compound din gidan gaba daya wani mugun sanyi ke shigarta, sai yanxu ta kara tabbatar da Ajay mugu ne kuma ba shi da conscience, ta ciro wayarta taga ko zata iya order din ride, tana ta tsaye a Neighborhood din bayan ta duba ride din, after almost 5 minutes taga hasken fitilar mota daga compound din gidan, dauke kai tayi har ya fito da motar, taga yayi parking inda take tsaye, ta wani kallesa, fuska daure yace “Do not waste my time Malama” Ta wani tura baki ta bude front seat, sai dai kuma tsoro take kar ta zauna ta ɓata masa motar ta shiga uku, haka dai ta shiga sai bata sake jikinta gaba daya a zaune ba, tana shiga ya ja motarsa, har suka isa apartment dinta bai ce mata komai ba, bayan yayi parking murya can ciki tace “Nagode” Daga haka ta sauka daga motar ba tare da ta kallesa ba ta nufi kofar apartment dinta ta bude da makulli ta shiga ciki, bata kulle kofar ba ta tsaya jikin window ta ɗan bude labule kadan tana lekawa taga ko ya tafi, haska inda ta zauna taga yana yi da wayarsa, ta zaro ido ta juyo hijab dinta da sauri sai taga bata yi stain ba, ta sake kallonsa taga ya gama haske haskensa ya kashe fitilar wayan, ta ma san kilan ya gane me yasa tace zata dawo gida, turo baki tayi saboda kunyan da taji, tana ta tsaye jikin window har bayan minti biyar bata ga yayi Reverse ba, ita kuma so take taga tafiyarsa sannan ta kulle kofarta da makulli don saboda zuwan da yayi daxu ya bar mata kofa a bude Aymaan ya fado mata gida kamar barawo, bude motar taga yayi after almost 10 mins ya fito, sai da taga ya nufo kofar apartment din sannan ta ruga sama da sauri ta shige dakinta… Ko da Khaleesat ta shiga bandaki taga hatta kayan jikinta ma bai yi stain ba, pad din da ta siyo tun daga Nigeria ta dauka a cikin akwatinta, bayan ta gama gyara jikinta ta fito ta canza kaya sannan ta saka rigar sanyinta ta kwanta, wajen karfe dayan dare Khaleesat ta farka daga baccin da ya dauketa a firgice duk da bata dade tana baccin ba ta mike zaune zuciyarta na bugawa, mafarki tayi wai Aymaan ya zo yana ta bubbuga mata kofa, dama kuma har tayi bacci hankalinta na kan kofar parlor ko ya tafi ya kulle mata kofar ko a bude ya bar mata oho, a hankali ta sauka daga kan gadon ta bude dakinta ta fita corridor tana leka downstairs, kwance ta gansa kan kujera idonsa a lumshe ya maida wutan parlon zuwa dim light, a hankali ta sauka downstairs din yanda bazata yi making sound ba, after some seconds ta koma sama ta dauko masa duvet, tana dawowa parlon ya bude ido, ta koma baya tana kame kame tace “Duvet ne, naga akwai sanyi sosai yau….” Ya nuna kansa yace “I should use ur duvet? Me? Ke da kika iya shiga daki duk ƙura da datti comfortably ki kwanta shi ne zaki kawo min duvet din ki i should use saboda nayi hauka, ai duk macen da zata iya zama comfortably cikin daki me datti da ƙura without cleaning it, kuma ta dinga yawo a gida babu takalmi a kafarta to babu kalan kazantar da bazata aikata ba, shi yasa taku ta zo daya da Jay, bird of the same feathers, ba gwara in kwanta sanyi ya kasheni ba da inyi amfani da abinda ya fito daga dakin ki, kujeran nan ma don sabbin furnitures ne yasa na kwanta” Khaleesat ta wani kallesa, sai kuma ta juya ta koma sama da duvet din, kuma sabo ne ko amfani da shi bata taɓa ba a ledansa ma ta ciro yanxu, can kasan ranta ta dinga ce ma kanta Allah ya kara mata, tsaki ta ja bayan ta shiga daki ta kulle kofarta da makulli tayi kwanciyarta. Washegari wajen karfe bakwai Khaleesat ta fito daga dakinta, bata gansa a parlon ba, hakan yasa ta sauka downstairs ta tafi kofar ta murda taji a kulle, ta leka garage taga babu motarsa, tabe baki tayi ta wuce kitchen don dama da yunwa ta kwana, sai wajen karfe goma ta gama duk abinda take ta bar gidan zuwa school, har suka gama lectures bata sake fuska ba ranan, tun Safiyyah na jan ta da magana har ta gaji ta kyaleta, bayan sun fito department Safiyyah na kallonta tace “Is there any problem Khaleesat? Naga gaba daya yau mood dinki babu kyau” A takaice Khaleesat tace “Nothing” Safiyyah tace “Ke dai ki gaya min gaskiya, kila ma haushina kike ji ban sani ba ma” Sai a sannan Khaleesat ta kalleta tace “Saboda me bazan ji haushin ki ba Sophie? Kawai kin ja ɗan iska mara kamun kai ya shigo rayuwata ina zaman zamana, you caused me all this wallahi” Safiyyah tayi shiru, sai kuma a hankali tace “Wai Aymaan? Wallahi ban san ɗan iska bane Khaleesat, kin ji na rantse, na zata yana da kamun kai ne yanda nake ganinsa sumi sumi a department” Khaleesat tace “To jiya wajen karfe shidda na yamma sai gashi a apartment dina unfortunately na bar kofa a bude kawai ya fado min cikin parlor kansa tsaye” Bude baki Safiyyah tayi tana kallon Khaleesat ko kiftawa babu with shock, a hankali tace “Apartment din ki kuma Khaleesat? Na shiga uku, sai aka yi yaya?” Khaleesat taki bata amsa don takaici, Safiyyah ta hade rai tace “To kuwa sai nayi masa hauka, uwarsa yaje nema maki a gida ko an gaya masa kowa shege ne kamar sa?” Kallonsa kawai Khaleesat take daga nesa har ya nufo inda suke zaune, Safiyyah kuwa ko lura da shi bata yi ba rai bace take cewa “To ke baki kira masa Cops ba? don Allah ki gaya min sai aka yi yaya da yaje apartment din naki? Yau ga mahaukaci kai” Juyawa Safiyyah tayi ganin shadow din mutum a gabansu, yana kallon Khaleesat da kyau yace “Kara ta kika kai gun wancen garan don ya min me? Me kike tunanin zai iya min? Muscles dinsa na banza har ni zai nemi ya daka? Who did he think he is? Me yake takama da shi? Sarautar tasu da bata taka kara ta karya ba ko me? Sannan naga kamar yana mance a America mu ke not Nigeria, ni zai nuna ma dabanci bai san course dinsa nayi a Nigeria ba?” Safiyyah ta mike tace “Look Aymaan, ita fa Khaleesat ba irin wa ennan shegun matan da kake tunani bane gaskiya, ka bar ganinta sakaka a Amurka, yarinya ce ita me mutunci da ta san ciwon kanta, kuma harkar duniya bata gabanta wallahi, wannan get together din ma ni na ja ta don dole taje ba wai ra’ayinta bane shi yasa throughout ta kebe gefe daya a wurin u saw that too, shi kuma wanda kake kira da gara fiance dinta ne, ba wai shisshigi yake yi ba, sannan sarautarsu kuwa ta taka kara ta karya don gidansu a nan Amurka ma ba ko wani shege bane a Nigeria ke iya mallakan irin wannan babban gidan a wata kasar, kai kuma naga hayan apartment kake a Amurkan, Sannan iyayen Khaleesat basu fara turata wata kasa karatu ba sai da suka tabbatar da mijinta a hannu, kuma shi ma a kasar yake, ka ga ai baza kace masa gara ba” Aymaan na mata wani kallo yace “Ke ki iya bakin ki kar ki ja ma kanki matsala a rayuwarki, Fiance din banza, a ina Fiance ya zama miji? ranan daurin aure ma an fasa balle common Engagement, shi da Engagement din yake takama dama?” Safiyyah tayi wani shewa tana rike kugu tace “Na ga kamar ba zaman lafiya kake so ba Malam, to wallahi idan baka fita harkar kawata ba a kasar nan a gaban idon ka zan kira maka 911 in lafta maka sharrin da babu me fitar da kai sai Allah, kamar yanda ka fada nan ba Nigeria bane tuni za ayi mana maganinka wallahi, kuma Unguwan da take tsaf za a bincika surveillance camera a ga sanda ka shiga apartment dinta ta yanda za a tabbatar ba sharri aka maka ba…” Aymaan ya gyara tsayuwa yana kallonta da kyau yace “Really?? dama ke mahaukaciya ce ban sani ba?” Safiyyah tace “Dawanau ce ni karewa, wallahi idan baka yi hankali da mu ba a kasar nan zaka ga jahilci tsantsa, ai ni da nake ganin ka sumi sumi a makaranta ban san gogaggen dan iska bane kai sae yanxu, to banda ɗan iska waye zai fada apartment din mutum kamar gidan ubansa? Ashe dama ciwon ƙwaƙwalwa gare ka ake yada jita jitar ciwon zuciya gare ka?” Har ya daga hannu zai wanka mata mari sai kuma ya rike fist dinsa ya cije hakora yana kallonta yana huci, Safiyyah tayi wani dariya tace “No slap me, try it plss, mare ni mana…. wallahi rabon ayi deporting dinka back to Nigeria a cikin jirgin ruwa ne ke tunzura ka, try slapping me ka ga ikon Allah” Yace “Daga ke har kawar taki zan yi maganin ku wallahi….” Daga haka ya juya kamar zai tashi sama ya bar wajen, Safiyyah tace “Ni wallahi da aka ce min babanka Deputy ne sai da kunya ya kamani ranan na rufe fuska, na zata ɗan vice president ne kai irin wannan jijji da kan da kake ashe common Deputy ne ma da ba a san da ku ba a Nigeria, kuma in ka fasa maganinmu baka cika namiji ba wallahi, dama ana ganinka an ga kwararren ɗan shaye shaye ɗan codeine, ban san wani tsautsayin yasa har mu ke gaisawa da kai ba banda nima dai gantalalliya ce bani da kamun kai”*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*_Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albishir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da kayan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you that duk wani product dinmu is tested and trusted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via 0902 469 2720_
