Haihuwa Da Hanji Page 41 Hausa Novel
“Sannunku”Ta faɗa tana ɗauke kanta daga cikin idanun mommyn da ta kusa daskarewa a wurin a zaune. Bata ƙara firgita ba sai da taji matar uncle sanusi na cewa “Sannu Afeefah, jigilar nan ba zai haifar miki da ciwon jiki ba? Kece nan ke ce chan ya kamata kina hutawa fa”Matar uncle Mansur tace “Gaskiya kam ya kamata ki dinga ji da mijinki kawai su jannah duk ba ga mu nan ba, shima ba don baudadden halinshi ba ai da duk sai mu kula da ku don kema na tabbatar raunin tafiyar Mammi na nan ɗanye a zuciyarki.”Murmushi ta ɗan saki tana zama za tayi magana Sameera ta miƙe tsaye don tun dazu duk su huɗun kaman an kafa su ne idanunsu ƙurrr a kanta.Nuna ta take hannunta na rawa “Afee…fah?””Ita ce ko Ya Sameera? Ita ce ba gizo na gani jiya ba ashe!”Samha tayi saurin faɗa kaman jira take wani ya fara magana cikinsu.Mommy ta kasa ma magana tsabar yadda taji da ganin Afeefar ƙare mata kallo take yadda ta wani sauya tayi mugun kyau ko atamphar jikinta ka gani ka san bata cikin wahala sai hawaye suka fara zuba mata ta tuna ranar auren Saleem inda take ce mishi a lokacin Afeefah na chan tana raba wa maza kanta tana samun na cin abinci idan zai mantata gyara ya mantata.”Kun santa ne?”Mama tayi tambayar da mamakin irin shock da ta gani a tare da su ga mommy ta fashe da kuka.Jannah ce da daman ta kasa sakewa dasu saboda har lokacin bakinsu take gani akan abinda suka yi wa Afeefah tace”Sun santa Mama, mommy kin ga ta sauya ko? Kun ga yadda Allah ke ikonshi ko? Ku kun ƙi ta mu mun so ta mun karɓeta hannu bibbiyu, kun muzguna mata hakan bai hana ta muku taimako mafi girma ba a rayuwarku… Ita ce ta taimaka da ayoyi da ruwan tofi ba ji ba gani har saida ta tabbatar asirin da aka yiwa Ya Saleem ya karye, gata nan yanzu haka ana dawowa makaranta exams na karshe zasu rubuta tana kan karatu. Nasara mafi girma da daraja shine tayi aure ta auri namijin nunawa sa’a wanda ko cikin maza sai an tara dubu a samu tamkarsa ɗaya. Afeefar da kuka sani ce dai ita ce matar Ya Rayyan ta sunna a yanzu haka”Afeefah ta mayar da kanta ƙasa hawaye na taruwa a idanunta sam bata san sun zo gangarta ba sai jin mommy tayi ta riƙe hannunta tana sake ƙara fashewa da kuka mai tsuma rai, Abeeha ma bata yi shiru ba ta kara da labarin irin yadda ta taimakesu akan Saleem.”Don Allah ki yafe mana Afeefah, haƙiƙa ba mu da bakin neman yafiyarki saboda mun aikata miki ba daidai ba, mun kasa duba kasantuwarki mace mun kasa yarda cewa Allah ke komai a sadda ya so na bi dare na raba ki da Saleem karfi da yafi na aura mishi wacce nake ganin ta fi cancanta ashe ban sani ba ƙabari na haƙa mana… Haƙiƙa na so na ganki ba tare da aure ba nayi adu’ar Allah ya bayyana mini ke ko ta wani hali in nemi yafiyarki in kuma gyara kuskurena ashe ke kam Allah ya dubeki ya Musanya miki da alkhairinki… Don Allah ki yafe mana ki yafe mana Afeefah!”Sossai duk suke kuka suna neman yafiyarta sai ta nemi rudewa Dukda tayi mamaki amma ta sani duniya aka ce makaranta. “Mommy ku daina neman yafiyata wlh tun kafin na bar gidan duk na yafe muku Yaya Saleem ya wuce yadda kuke zato a wuri na. Ban riƙe ku a zuciyata ba ku daina wannan kukan don Allah”.Samha ta fi kowa bata haƙuri sai Mommy, duk ta nuna ita komai ya wuce a wurinta suka koma gefe suna ta kallonta ko motsi tayi burgesu take, basu taɓa sanin haka take ba sai a yanzu yinin da suka yi a ranar suka kara sanin wacece ita kunyar duniya duk ya rufesu na tunanin duk irin wulakancin da suka yi mata, lallai da gaske ne da aka ce mai haƙuri shi yake dafa dutse har ma ya sha romonta.Mommy ta tabbatar Saleem bai san da wannan labarin ba, gab za su tafi ta kira shi a waya akan ya zo ciki duk jama’ar sun watse a babban parlorn sai Afeefah dake zaune tana duba abu a waya mommyn ta fito daga ɗaki ganinta yasa tace “Yauwa ashe kina nan dama ke zan je dubawa kitchen. Yanzu Saleem zai shigo ku gaisa…”Gabanta ne ya faɗi rabon da su hadu kusan watanni bakwai zuwa takwas kenan, ya rabu da ita cikin kuna da zafin zuciya tare da hawaye a yanzu zai haɗu da ita matsayin matar aure, matar ma ta abokinshi me zata ce mishi? Ta san akwai laifin mahaifiyarshi a rabuwarsu amma ta san dole zai ji zafin samun wannan labari, anya ma zai yi farin ciki da ganinta? Bata gama tunanin ba ta ji sallamarshi gabanta ya sake faɗuwa ta miƙe tsaye sai suka haɗa idanu a lokacin da take amsawa da iyaka lips ɗinta.”A…Afeefah? Ke..ke ce nake gani? Afeefah ba gizo idanuna suke min ba kece tsaye a gabana?Ta yaya kika zo gidan nan? Ina kika shiga Afeefah? Ina kika shiga…?”A ruɗe yake maganan idanunshi na cika da kwallah kaman yadda nata ya cika fal da hawayen ganinshi.”Ya Saleem…!”Ta faɗa a sanyaye sai ta kama hawaye. Sake matsowa yayi kaman zai taɓa ta tayi saurin matsawa baya sossai tana girgiza mishi kai.”Ka gafarceni Ya Saleem yanzu da baya ba ɗaya bane…””Afeefah na san akan mahaifiyata ne wlh yanzu duk sun yi nadamar abin da suka aikata miki, na tabbatar za kuma su nemi yafiyarki don Kullum adu’arsu shine mu ganki mu nemi yafiyarki…ko babu komai a yanzu za mu cika burinmu za mu cika alkawarinmu na mallakar juna…”Daidai lokacin Rayyan ya sanyo kai parlorn he just stood there fuskarshi kadaran-hadaran yana kallonsu.Hawaye take yi sossai “Lokaci ya riga ya ƙure ya Saleem, kayi hakuri Allah bai nufa na zama rabonka ba. Ni din yanzu matar aure ce.”Jikinshi yayi wani irin sanyi wani tashin hankali da damuwa na lallaɓo wa ya rufe shi murya na shaking yake furta “A..a..aure Afeefah? Aure kika yi? Da waye? Me..me yasa?”Idanunta ne suka shiga cikin na Rayyan da sauri ta kawar heartbreat ɗinta na kara gudu ganin kallon da yake mata.”Ka sa a ranka ƙaddara ce ta zo haka, amma ni matar aure ce don Allah ka ajiye zancen alaƙar da ta riga ta wuce Ya Saleem”Daga haka tayi saurin wucewa sashensu ta barshi kanshi a matukar kulle, idan bai ce ya matuƙar kaɗuwa da wannan zance ba yayi ƙarya zuciyarshi raɗaɗi ya shiga mishi, saboda rauninshi tuni hawaye suka shiga zubo mishi haƙiƙa ya so Afeefah kaman ranshi har gobe yana ƙaunarta amma gashi ƙaddarar su ya zaɓar musu rabuwa aure tayi a sadda yana chan ya rasa hankalinshi, me yasa bata yi haƙuri ba? Meyasa bata jira ba? Me yasa yayi jinkiri? Tun da ya dawo hayyacinshi a neman ta yake ko Allah zai sa ya ganta ashe ita kam tana chan tare da mijinta tana rayuwa mai kyau don ko skin ɗinta ya bayyana hakan.Mommy ce ta fito ganin yanayin da yake ciki ta kalli Rayyan dake tsaye har lokacin a bakin kofa hannunshi harde a kirjinshi wanda da alama Saleem ɗin bai kula da wanzuwar shi ba tayi saurin kama Saleem ɗin ta zaunar taje ta kawo mishi ruwa bai karɓa ba sai ma maganganu da ya fara “Mommy ta ya kika ga Afeefah? Me ya kawo ta gidan nan? Mommy wai da gaske Afeefah aure tayi? Aure tayi? A yanzu haka Afeefah ta haramta mini?”Mommy ta kalli Rayyan ta mayar da idanunta kan Saleem.”Saleem Afeefah ta yi aure laifina ne duka, laifina ne ta subuce maka ka yafemin ciwon da nake sakawa zuciyarka ka ɗauki dangana da haƙuri. A gidan nan muka samu Afeefah tana kuma auren abokinka ne Rayyan…”Da ƙarfin gaske ya miƙe har yana Buge ruwan hannunta ya faɗi ƙasa “Rayyan?? Mommy all this while Rayyan na tare da Afeefah? Har ma ya aureta? Rayyan dai Rayyan Moh’d Khamis??”Gabaɗaya wani duhu ne ya taso ya rufe mishi gani tsabar wani irin bacin rai da ya zo mishi juyawa yayi zai fita yaje ya samu Rayyan ɗin sai suka haɗa idanu nan ya nufe shi ya tsaya a gabanshi.”Rayyan da gaske Afeefah ka aura?”Shi karan kanshi ya san yayi mugun ƙoƙari a sadda ya buɗi baki ya furta “Saleem Afeefah matata ce idan har ka san darajar aure da kuma martabarsa za ka kiyaye irin kalmanka a kan matata… Ƙaddara ta riga ta raba ku ta bani ita a lokacin da ban yi zato ko tsammani ba don haka don’t Look at me with those eyes dake nuna kaman I betrayed you or something like that, you should questioned yourself nd your family not me…”Yana kai nan ya wuce don har ga Allah bai san dalilin da yasa yake ji kaman zai kama da wuta ba, mommy ya kalla har kaman zai wuce ya tsayar da idanunshi kanta ba zai iya yi mata magana kai tsaye ba ba kuma don komai ba sai don uwa ce ya juyo ya kalli Saleem dake kallonshi rai a tsananin ɓace yace in a respectful manner.”Rasuwa aka yi mana ko ba rasuwa ba muna da darajar da ba za’a tako har nan a ci mana mutunci ba Saleem, idan ba zaka taya mu baƙin ciki da jajen rasa wani sashe na bangonmu ba za ka iya zama da kai da familyn ka a gida. Mun gode”Daga haka ya nufi sashensu ya bar su nan tsaye calmly kaman ranshi ba suya yake ba.Wani irin duka Saleem ya kaiwa bangon wurin yana yin baya tare da zuba yatsun shi cikin gashin kanshi kaman zai fashe haka yake ji, su Samha ne duk suka fito a tare da Abeeha jin salatin mommy.Ganin yanayin da suke ciki suka shiga tambayar me ya faru? Menene?Mommy tana zubar da hawaye tace “Na sake wani kuskuren, da na san hakan zai kasance Saleem da ban nemi ku gaisa da Afeefah ba! Na zaci zaka yi farin cikin ganinta idan ka ji kuma tana da aure zaka taya ta murna da Adu’a ka karɓi kaddara amma me kayin nan? Abokinka ne fa Rayyan abokin da ya zama ɗan uwa ya kuma tsaya mana duka a sadda muke neman tagayyara. Rasuwa fa mahaifiyarshi tayi ko lafiya bai samu ba me kake yin nan?””Rayyan ya ci amanata mommy, ashe ya san inda Afeefah take ya zaɓi ya ɓoye min? Ashe aurenta yake shirin yi ko da na matsa ya nemo min ita a sadda ba ni da daman hakan saboda kalamanki ya san inda take ya dinga zurma ni akan ya neme ta ya rasa? Meyasa tun farko bai ce min sonta yake in sakawa zuciyata hakan ba? Idan ba da wata manufa yayi hakan ba Meyasa ina zuwa gidan nan bai taɓa nuna min tana nan ko ya bari na ganta ba?”Abeeha da ranta yayi mugun ɓaci tace “Ya Saleem baka kyauta ba sam…! Ban zaci ko Ya Rayyan amanarka ya ci zaka iya aikata hakan kuma ka jefe shi da irin kalaman nan ba. kar hankalinka ya gushe mana… Toh wallahi Yaya Rayyan ya auri Afeefah ne bisa umurnin Mammi, ya karɓi auren cike da tunanin mai zaka ɗauki hakan a duk sadda ka dawo hayyacinka… Idan ma ya faɗa maka a lokacin kake nemanta cewa coincidently sun haɗu a sadda ta taimaki Mammi Mammi ma ta taimaka mata ta kawo ta gidan nan me zaka yi? Kar ka manta a sannan Allah ya isan mahaifiyarka ke kanka muddin ka mata magana? Idan da yana da mugun nufi kanka da ba zai ba da gudummawar dinga kawo ka gidan nan kana ci da sha daga ayoyin Allah ba har ka dawo cikin hayyacinka…idan da yana da wata manufa ta daban da ba zai bari ku kasance tare da ita a zaman makonkin nan ba don kaima ka san zai iya kaita ko ma inane… Wallahi ko ni bayan labarin da Afeefah ta bamu na ji har abada ban bata goyon bayan aurenka ba, Mammi ta zaɓa mata miji kuma ta karɓa hannu bibbiyu kuma take ibadar aure… Ko da Yaya Rayyan baya sonta a baya bai kyamaceta ba Dukda ya san labarinta kaman yadda kaima baka kyamaceta ba bambancin kawai mu da mahsifiyarmu muna sonta kuma muna so rayuwarta ta inganta ashe idan baka godewa Ya Rayyan ba ba zaka ga baƙin shi ba. Ka je kayi nazarin kalamaina kan ka sake yanke kowani irin hukunci ne”Tana kai nan ta juya ta koma ciki cike da jin haushinsu dukkansu, tunanin ta ya tsaya akan ya Rayyan da banzar zuciyarshi Allah ya sa kar ya sauke akan Afeefar.Tana zaune bakin gado ta toshe bakinta da gyalen ta tana kuka kawai taji an turo kofan an shigo, da sauri ta ɗaga idanunta dake zub da hawaye sai suka shige cikin nashi da ya jirkice, wani irin kallo ya mata da ya sa tayi saurin mayar da idanunta ƙasa tana Miƙewa tsaye.”Kin raina ni ko? Ni za ki wulaƙanta??”A hankali yayi maganan. Sai ta ɗago tana cewa “Kayi haƙuri ban san zai shigo ba, ban san mahaifiyarshi ta kira shi ba da na nemi izini…””Shuttt up!! Just shut up Afeefahh”Ya daka mata tsawa har saida ta tsorata tayi baya baya zata faɗi ta dafe jikin gado kirjinta na sama da ƙasa. Yau ne karo na farko da taji sunanta a bakinshi Dukda kaɗuwar da tayi hakan bai hana sunan sake amsa kuwwa cikin kunnuwanta ba da muryarshi.Shiru yayi yana sauke numfashi idanunshi a tsaye a kanta ya ce a zafafe “Ko babyn roba na aura, ko ‘yar tsana ce ta amsa sunan matar Rayyan Moh’d Khamis wallahi billahi na fi ƙarfin ta wulaƙanta min aure… A gabana kike cewa aurena dake ƙaddara ce??””Ka yi ha..kuri ba haka…”Juyawa kawai yayi ya fice yana buga kofar da karfin gaske sai da ta sake razana.”Na shiga uku!”Ta ambata tana zama bakin gadon.


