Zamantakewar Aure

Abubuwa 6 wanda idan namiji na yiwa mace za ta samu kwanciyar hankali

Maza gareku, yi kokarin yiwa mace wadannan abubuwan zai saka ta farin ciki

Wannan darasin na yau don maza da ke son su ga mata suna cikin farin ciki ne amma basu san hanyoyin da za su bi don saka mace cikin kwanciyar hankali da jindadi ba. Maza da yawa na tunanin saka mace farin ciki yana da wuya, amma kuma ba haka bane babu wani wuya yin hakan. Hakan yasa na kawo muku abubuwan da Idan Kuna yiwa mata za su kasance a cikin farin ciki.

Karanta>>> Dalilan Dake Sawa Nonuwa Suke Zama Kanana

Abubuwa 6 wanda idan namiji na yiwa mace za ta samu kwanciyar hankali 

Ga jerin abubuwan da idan maza na yin su za su saka mata cikin farin ciki da kwanciyar hankali

1. Ka Taimaka Mata Yin Wasu Ayyukan Ta; Taimakawa mace yin ayyukan gida na sa taji dadi misali shara da goge gida da gyara gado da tsaftace gidan gabaki daya. Koda bata bukaci ka yi hakan ba yi kokarin yin hakan zai sa ta ji kana tausaya mata yin ayyukan gida, hakan zai sa ta yi farin ciki.

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

2. Ka Siyo Abin Dadi Lokacin Da Za Ka Dawo Gida; Idan Kana da lokaci da kudi ka tsaya a wani wajen ka siyo mata dan abinda za ka shigo mata dashi gida da zai birgeta. Komai kankantar wannan abin zai saka ta ji dadi sosai.

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

3. Yi Kokarin Sakata Farin Ciki; Yi kokarin lokacin da kuke kwanciyar aure ka tabbatar ka fara gamsar da ita kafin ka biya bukatar ka. Yi kokarin yin bincike don gano abubuwan da ake yiwa mace dake sa taji dadi, yin hakan zai sa ta kasance cikin farin ciki da annashuwa.

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

4. Ka Zama Mai Kulawa Da Tallafa Ma Ta; Wasu matan suna rashin Sa’a samun maza marasa kulawa dasu, mata na son samun mazan dake damuwa da kulawa dasu da magance musu damuwar su. Mata na son kulawa da nuna musu kauna.

Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah

5. Kulawa Da Bukatun Ta; Da yawa daga cikin maza basa biyawa mata bukatunsu, misali bayar da kudin kashewa, siya ma ta kayan kwalliya, sutura na gida da na fita unguwa. Ka yi kokarin baiwa matarka kudi ko ba masu yawa ba hakan zai sa ta ji farin ciki sosai.

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

Yi kokarin yin wadannan abubuwan don ganin ka saka matarka farin ciki, ana samun farin ciki a rayuwar aure idan ya kasance kowa na sauke hakkin dake kansa tsakanin ma’aurata. Da fatan maza za ku yi kokarin tabbatar da farin ciki ga matanku.

Ku Karanta Amfanin Hulba Guda 21 Ga Lafiyar Dan-adam Musamman Yan Mata Da Matan Aure.

Back to top button