Mijin Marigayiya Page 8 Hausa Novel
Kafin su Isa gida sai da ya siyo magungunan, suna dawowa ya mikawa Baba Habi magungunan yayi mata bayani. Ya shiga dakini inda Khadeeja take kwance ya tsaya a kanta yace ‘Ki daure Habi ta hada miki abinci ki ci ki Sha magani, shine zaki ji dadin jikinki. Kin ga wadannan magungunan ita Ma’u idan tana sha ko laulayin kirki bata yi, haka take ci gaba da harkokinta har ta haihu.’’Yanzu zan fito ai.’Yayi mata sallama ya tafi office.Indomie din dai Baba Habi ta dafa mata sannan ta shiga dakin ta taso ta, ta Sha maganin ta dan ci abinci sannan ta koma ta sake kwanciya. Kafin Habi ta dauko yara daga makaranta ta dan ji kwari, zuwa dare rashin kwarin jikin ya ragu don da kanta ta lallaba tayi musu tuwo miyar kuka. ……… Kwana biyu laulayin ya yiwa Khadeeja sauki don tana dagewa tana shirya yara makaranta kuma tana shiga kitchen tayi abinci da taimakon Baba Habi. Ranar laraba suna zaune a parlor da magriba ita da yara da Abbansu; tana zaune a tsakiyarsu tana yi musu homework yayinda shi kuma Abbansu yake zaune a kan kujera yana ta faman danna waya yana kuma kallon labarai a BBC. Baba Habi ta fito daga dakin yara da sallama, bayan Khadeeja ta amsa sallamarta ta tsuguna daga gefe ta dubi Khadeeja tace ‘Uwar dakina ina so zuwa gida gobe, naji ance za a kulle garin. Zan je na dubo yarana idan na kwana daya sai na dawo kafin a rufe garin.’Abbansu ya dago kansa daga kallon wayar yace ‘Baba ai da kin bari muga abinda hali zai yi tunda kin ga itama Khadeejan bata da lafiya.’Ta juya Kai ‘To ai Yallabai kafin a kulle garin, na baro yara gara naje na dubo tunda ana maganar idan an rufe garin za ayi watanni kafin a bude.’ Kafin yayi magana Khadeeja ta dubeshi tace ‘Ka bari take ai na dan ji sauki, gara taje ta dawo kafin a rufe garin ga azumi ma yana tahowa.’’Hakane.’ Ya amsa ya cigaba da abinda yake yi.Gari yana wayewa bayan ya dawo daga kai yara makaranta ya bawa Baba Habi kudin mota Khadeeja kuma ta hada mata abinda zata bata ta kama hanya a kan jibi zata dawo.A ranar da daddare aka sanar da total lockdown a Nigeria, an Hana duk wata zirga zirga sai dai kowa ya zauna a gida.Da farko Khadeeja tayi tunanin idan ta sami ciki Mustapha zai yi doki kuma ya bata kulawa ta musamman kamar ko wacce amarya, sai dai ga mamakinta hakan baya samuwa. Wani lokacin ma sai ta ga kamar bai san ma tana da ciki ba ko kuma ba da son ransa ta sami cikin ba; halin ko in kula din da yake nuna mata yayi yawa.Tunda aka saka lockdown sai ya zamana kullum suna gida ita da shi da yara, ta so sosai taje gida ta wuni kafin a kulle garin amma bata sami dama ba. Duk da haka kullum sai sun yi waya da Mommy da Yaya Mama; don tun satin da za a fara lockdown su Nabila suka zo mata wuni da suka je gida suka gayawa Mommy ciki ne da ita. Don haka kullum da safe sai ta kirawota ta duba ta.……….Hayaniyar da su Afaf suke yi a gidan ba kadan bace don haka idan gari ya waye ko gyangyadi bata samu tayi; ko ta fara baccin ma haka za ayi wata hayaniyar a tasheta.Bata gane yanayin da jikinta yake ciki, ita dai kawai ta san tana shan wahala. Kullum jikinta babu kwari gashi bata son cin abinci, gashi kullum cikin jin bacci take. Ga hidimar yara, wadda duk ranar da ta nuna ba zata iya ba haka Mustapha zai yi ta kunci yana kin kulata. Haka take dagewa tayi duk wani abu da ya kamata.——-Kullum wuni suke kallon TV saboda ana samun wuta sosai, idan dare yayi kuma Abbansu ya tada inji su cigaba da kallo. Ita dai bata isa ta canza channel ba don da ta canza za a fara kuka wanda bata son ji sanna kuma a take ubansu zai fito yayi magana.Ta gaji da zaman haka barkatai don haka ta daure take saka yaran a gaba suyi karatun kur’ani.Da safe a jagwale take tashi don haka ta san ba zata iya da safe ba. Amma kullum bayan sallar azahar idan sun ci abincin rana sai ta kashe TV din kowa ya dauki kur’ani ta biya masa. Nasreen ce kawai bata son zama don haka sai Khadeeja ta kyaleta saboda a halin yanzu na zata iya ba. Amma har Shukra ake biyawa karatun.Duk wani motsinsu idonsa a kai, da zarar ya ji wata hayaniya ko ya ji su shiru zai leko ya duba. Kullum yana kwance yana faman latsa waya.Yau ma haka suka tashi tun asuba suke ta guje-guje, TV kuma dama tana kunne don da zarar wani ya kasheta za a yi korafi.Shinkafa da wake ta dafa da manja da yaji; bayan sun gama cin abinci kowa yayi Sallah ta saka su a gaba kowa da kur’aninsa. Sai da suka yi tilawa sannan ta karawa kowa aya biyar amma banda Nasreen.Ba zata iya surutu ba saboda yanayin jikinta da kuma yanda yawu yake yawan taruwa a bakinta, sannan kuma idan ta daga murya tana mata fada Abbansu baya so. Don haka sai ta kyaleta, suna zaune gaba dayansu sun kewaye Khadeeja suna karatu, harda Shukra; amma Nasreen tana zaune a kan kujera ta zuba kayan wasa a gaba tana yiwa ‘yar tsanarta kitso.Shiru yaji sai muryoyinsu kadan-kadan suna karatu don haka ya taso ya fito parlor din.Ya kare musu kallo sannan ya sami waje ya kwanta a kan 3-seater. Ya dubi Khadijan yace ‘Ita Nasreen ba a biya mata karatun?’’Tace sai ta gama yiwa ‘yar tsanarta kitso.’ ta bashi amsa ba tare da ta dubeshi ba.Nasreen tace ‘Na ma iya karatun Abba, kitson nan nake so na gama tukunna.’Yayi dariya ya cigaba da danna wayarsa.Bayan sun gama karatun ta koma daki ta kwanta su kuma suka cigaba da kallonsu na TV.………A kwance take a gefen gadon da alawar tomtom a bakinta saboda yawu, ya zauna a kan kujera. Ta juyo ta kalleshi ta koma ta cigaba da kwanciyarta don bata son magana. Jimawa kadan ya kirawo sunanta, ta amsa sannan ta juyo.Ya kalleta yace ‘Wai me yasa bakwa karatun ne da Nasreen?’Tace ‘Bata so ne, ni kuma ba dadi nake ji ba shi yasa ba zan iya surutu da ita ba kawai na kyale ta.’‘Ya kamata idan ma wani abu kika saka a ranki game da Nasreen ki cire, duk abinda zaki yiwa yaran nan kiyi musu gaba daya kuma kiyi musu adalci. Ina kula komai zakiyi sai ki kyale Nasreen, idan banda haka ya za ayi ace Shukra ma da bata shiga islamiyya ba kina biya mata karatun amma ita Nasreen kin yi banza da ita.’Tunda ya fara zancen ta mike ta zauna akan gadon tana kallonsa, maganganun da take so ta fada masa suna da yawa sai dai tana bude bakinta yawu ya cika bakin. Ta taune ‘yar guntuwar tomtom din ta hadiye da kyar, ta tabe baki ta kawar da kai kawai tace ‘Kayi hakuri za a gyara.’’Ya kamata dai ki dinga yi musu adalci don dukansu ‘yayana ne.’ ya fada.Ta zame ta kwanta zuciyarta har turiri take saboda takaici; shi yake hanata takurawa Nasreen, shi yake nuna baya son a dinga yi musu fada amma kuma yanzu yana mata maganar ba a karatu da ita. To ya zata yi da ita? Ita adalci ne wannan yake mata da zai ce ta dinga yiwa ‘yayansa adalci? Ta share kwallar da ta gangaro a idonta tayi kwafa.Jimawa kadan ya tashi ya fice daga dakin.………
